SHUGABA UMAR HASAN AHMAD AL-BASHIR: ZAKIN AFURKA [4]
Bayan da gwamnatin Khartoum taci nasarar kawo karshen yakin da aka jima ana gwabzawa da Mutanan kudanci, da kuma wani bangare na mayakan yankin Dafur wadan da suka mika wuya domin samun zaman lafiya. A nan ne masu adawa da shugaba Bashir suka maida hankali wajen taimakon daya bangaren na ‘yan tawayen Dafur day a taurare karkashin jagorancin Ibrahim Khalil, wannan ta baiwa Khalil damar kulla dangantaka mai karfi da Kanal Gaddafi na Libya idan aka dinga shigo masa da makamai da kuma bashi maqudan kudaden gudanarwa, da nufin maida hankali akansa dan sabauta gwamnatin Bashir.
Shi Gaddafi yana fama da wani irin ciwo na san sai ya shugabanci kasashe da dama. A karon farko ya fara neman kafa Katafariyar kasar Larabawa wadda zata game dukkan kasashen Larabawa, kuma sannan shi Gaddafi ya zama shugabansu, wannan kuduri na Gaddafi bai samu shiga kunnan Shugabanni kasashen Larabawa ba musamman hadaddiyar kungiyarsu ta “Arab League” tuni kasashe irinsu Masar wadda itace kasa mafi tasiri ta fuskar Diplomasiyya ta sa kafa ta shure wannan bukata ta Gaddafi duk kuwa da dimbin kudaden da ya dinga zurarawa AlQahira a matsayin tashiyar baki.
Daga baya Gaddafi ya koma neman kafa hadaddiyar Kasar Afurka kwaya daya wadda shine zai zama shugabanta. Wannan ya kara nuna kulafucin Shugaba Gaddafi na san mulkar kasashe da dama bayan kasarsa ta Libya da ta zama Mallakinsa, kasancewar kasashen Afurka mafiya yawancinsu ‘yan Rabbana ka wadata mu ne, Gaddafi yayi amfani da kudi da kuma nuna isa a duk lokacin da aka tashi yin taron kasashen AU, inda shine mutumin da yafi kowanne shugaba zuwa da tawaga mai dauke da mutane masu yawa, sannan duk inda zashi da Motocinsa yake yawo sama da guda Hamsin, haka kuma, idan antashi taro baya daukar ko tsinke ya koma da shi Turabulus. Kasashen Afurka da dama sun masa tustu akan wannan bukata tashi Musamman Shugaban Ethiopia Meliz Zenawi shine ya fito karara ya fara sukar wannan bukata ta Gaddafi kafin daga bisani ya samu goyon bayan kasashe da dama.
A saboda haka ne, Giyar mulkin da take dibar Gaddafi ta gaya masa karya, inda ya dinga amfani da kudi yana daurewa Tawayen da a Karshe shine silar ajalinsa gindi tare da basu makamai da kudade. Babu ko tantama duk inda kaji wasu ‘yan tawaye a Afurka nason kifar da gwamnati ko mayar da wata gwamnati “ungovernable” to kada kaji da wai ko dai wadanda Gaddafi ya daure musu gindi ne ko kuma wasu daga cikin wadan da kasashen Turai suka assasa ne dan amfani da su wajen cigaba da mulkin mallaka ta barauniyar hanya. Gaddafi ya zamewa kasashen Afurka da dama wata irin “zuma” ga zaki kuma ga harbi, dan suna son kudinsa sannan kuma suna tsoron tawayen da zai kai ga subucewar gwamnatocinsu.
A dan haka ne, wuta ta kara ruruwa a yankin Dafur, ana haka sai akaji bullar wasu mutane da suke yakar Bangaren Ibrahim Khalil dan mara baya ga Gwamnatin Khartoum, wadannan mutane su ake kira da sunan JANJAWEED! An zargi gwamnatin Khartoum da cewar itace ta daurewa Janjaweed gindi suke aitaka ta’addanci a yankin Dafur, abinda Gwamnatin Khartoum din ta sha musantawa cewa bata da hannu a cikin al’amarin Janjaweed, Allah Masani! Su wadannan mutane kafofin watsa labarai na kasashen waje suna kiransu da cewa “Larabawan Janjaweed” wanda hakan kai tsaye kamar dangantasu ne da Gwamnatin Khartoum. Amma abin lura anan shine ko shakka babu Turai da Amerika sunyi amfani da wasu kalamai na rashin gaskiya, domin da farko su wadannan Janjaweed din Bakaken Mutane ne kamar yadda Shugaba Bashir yake Bakar fata ko da ka kirashi balarabe, amma saboda cimma manufar muzantawa da nuna cewa akwai wariyar Launin fata a tattare da Gwamnatin Khartoum (wanda kai tsaye bazaka karyata nan take ba) sai ake bayar da rahotannin cewa Larabawan janjaweed suna kashe Bakaken fatar yankin Dafur, a zahiri wannan karya ce, domin su kansu Janjaweed bakaken fata ne, kawai wannan wata shegantaka ce ta kasashen Turai dan cimma boyayyar manufarsu akan gwamnatin Bahsir.
Babu wanda zaice Gwamnatin Khartoum bata aikata laifi a Dafur ba, anyi dukkan abinda akayi marar kyau. Amma dai rahotannin da aka dinga bayarwa na cewa an kashe sama da mutum 200,000 da warwatsa sama da Mutum miliyan biyu wannan katafariyar karya ce da Majalisar dinkin duniya suka shara, domin shi kansa yankin Dafur din mutane nawa yake kunsa na al’ummar Sudan mai mutane Miliyan 40 idan ka hada da mutanan da suka balle suka kafa kasar Sudan ta Kudu.
Duk wannan abinda yake faruwa ana yi ne dan samun hanyar kaiwa zuwa ga shigar da kasashen Turai kasar Sudan, dan yin leken asiri na keke-da-keke, domin tun zamanin Shugaban Amurka Bill-Williams Clinton da suka kaiwa Sudan din hari suke da kulafucin wargaza kasar ta kowanne hali. Kamar yadda muka fada a bayanan da suka gabata da farko anso ayi amfani da mutanan Kudancin Sudan dan wargaza kasar, wanda wannan hakar bata cimma ruwa ba. Kuma hakan ya kai ga kisan Shugaban mutanan kudancin Sudan John Garang, sai kawai a 2005 Majalisar Dinkin duniya ta kafa kwamitin binciken abinda yake faruwa a Dafur da ya kai ga Kafa United Nation Mission in Dafur (UNAMID) . . . . . . . . Zan cigaba insha Allah.
Yasir Ramadan Gwale
20-07-2013
No comments:
Post a Comment