SHUGABA UMAR HASAN AHMAD AL-BASHIR: ZAKIN AFURKA [2]
Da farko yana da kyau mu fahimci cewar wannan yanki na Dafur yana da kusanci da kasashen Libiya da Tchadi sama da gwamnatin da take Khartoum, domin daga Khartoum zuwa Darfur akalla kana neman kwana uku idan motarka mai gudun tsiya ce. Haka kuma, yankin Darfur ya samu kansa a tsakiyar kasashen da suke da saukin shigar Makamai, misali kasar Tchadi ta sha fama da hare haren 'yan binduga wanda daga Tcadi sukan kwararo zuwa garuruwan El-Jineyna da El-Zalinje da El-Fashir da ke a yankin Darfur kuma suke da iyaka da Tchadin dan neman mafaka, wannan daga yamma kenan; sannan kuma, saharar dake Arewa maso yammaci da tayi iyaka da Libiya itama wata babbar dama ce ga batagari wajen safarar Makamai cikin sauki zuwa yankin Dafur, da kuma yankin Kudancin Sudan musamman a garuruwan West Bahr El-Ghazal da ya dare a yanzu zuwa sabuwar kasar Sudan ta kudu.
Haka kuma, shi wannan yanki na Dafur zaka iya kwatantashi da cewa kamar wata katafariyar kasa ce a cikin Sudan. Domin yankin Dafur yana da wasu maka-makan jihohi guda biyar, wato akwai jihar Dafur ta Gabas da ta yamma da ta Arewa da ta Kudu da kuma jihar Dafur ta Tsakiya. Mutanan da suke zaune a wannan yankuna kabilun Fur ne da Hausawa da sauran tsirarun kabilun Afurka da suke zaune a yankin ko dai ta sanadiyar hanya da ta kawosu dan zuwa Makkah ko kuma masu tafiya Libya dan isa tsibirin Malta dan zuwa Turai.
Meye musabbabin rikicin yankin Dafur? Kafin mu yi bayanin musabbabin rikicin yankin Dafur yana da kyau mu sani cewar ita kasar Sudan ta sha fama da yakin Basasa daga kabilun Jange da Dunka daga Kudanci da kuma wasu 'yan tawaye daga Yankunan Damazien da Kasala dake yankin Gabshin kasar da kuma yankin Kordofan, an kwashe tsawon shekaru sama da 20 ana gwabzawa tsakanin Gwamnatin tsohon shugaba El-Numeri, wanda a shekarar 1975 yace ya kori duk wasu baki da suke zaune a kasar cikinsu kuwa harda Hausawa 'yan Najeriya masu yawan gaske da suke makale akan yankunan kan iyaka.
Asalin wannan rikici na yankin Dafur ya faro ne sakamakon rashin fahimta da kuma rashin yiwa gwamnati Uzuri watakila harma da gazawar gwamnatin. Domin mutanan wannan yanki sun zargi gwamnatin da ke Khartoum da maida yankin baya ta fuskar abubuwan more rayuwa da harkar Ilimi da Lafiya da sauransu. Wannan shine abinda ya dinga cin mutanan yankin a zuciya inda kasashen Tchadi da Libya suka yi amfani da wannan damar wajen baiwa al'ummar makamai akan su yaki Gwamnatin Khartoum; watakila ka ce Sukansu kasashen Tcadi da Libiya an zuga su akan su shigar da Makamai yanki, daga nan Ghaddafi yayi ta amfani da mutane irinsu Ibrahim Khalil da wani Abdulwahid Muhammad Nour a matsayin 'yan barandansa yana basu kudi da makamai suna kashe al'ummarsu da kansu.
Shakka babu an kafsa yaki a wannan yanki tsakanin Gwamnati da masu dauke da makamai. Ita gwamnatin Khartoum tana zargin kasashen Libya da Tchadi bisa zugar kasashen Turai da Amurka ba da yi mata kutsen kan iyaka da 'yan ta'adda masu dauke da makamai. Kuma wannan yaki zaka iya cewar daman turawa ne na yammacin duniya suka kitsashi, domin abinda zaka fara tambayar kanka shine mutanan da suke ikirarin gwamnati ta waresu ta mayar da su baya ina suke da kudaden mallakar makaman da zasu yaki hukuma? Ghaddafi yayi amfani da karfin tattalin arzikinsa wajen ruruta wannan rikici sannan kasashen turawa sun baiwa mutanan Kudanci wadan da Kiristoci ne makamai akan su samar da kungiyoyin da zasu taya 'yan yankin Dafur yaki da gwamnatin Khartoum, sannan kuma a gefe guda ga kasar Tchadi ita ma na tata hidimar wajen daurewa wannan fada gindi.
A cikin irin wannan yanayi sai gwamnatin Khartoum ta samu kanta a cikin wani irin yanayi na gaba kura baya siyaki. Domin a bangaren Kudu tana fama da Jangunawa da Dunkoki wadan da turawa suke zugawa, sannan a bangaren Gabas akwai su kansu wasu 'yan tawaye a yankunan Damazien da Kasala da Ghadaref da kuma Dalang a yankin Kudancin Kurdofan. Kai tsaye bazaka ce gwamnatin Khartoum bata aikata ba dai-dai ba a yankin Dafur, anyi barna da ta'adi tsakanin bangarorin guda biyu, amma fa gaskiya ba kamar yadda kafafan watsa labarai na turawan yamma suka dinga bayar da rahotannin cewar ankahe sama da mutane 200,000 sannan sama da mutum Miliyan Biyu sun tsere sun bar gidajensu ba, wannan ko kadan ba gaskiya bane. . . . . . . . . Zan cigaba Insha Allah.
Yasir Ramadan Gwale
17-07-2013
No comments:
Post a Comment