SHIN BUHARI NE KE DA MATSALA
KO MAGOYA BAYANSA?
Lokaci yayi da ya kamata mu san gaskiyar al’amura
dangane da yadde siyasar General Muhammad Buhari take tsakaninsa da mogaya
bayansa. Wannan wani batu ne mai muhimmanci a tunanina, kasancewar Buhari mutum
daya tamkar da dubu a tsakanin dukkan ‘yan siyasar Arewacin Najeriya ko ma
Najeriya gaba daya kwata, wannan ta sanya ya yiwa tsaraiku zarra, a dukkan
harkokin sisaya, haka kuma, Buhari ya zama mutum mafi girman tasirin fada a ji
a harkokin siyasar Arewacin Najeriya a tsakanin ‘yan Arewa.
Tun lokacin da General Buhari ya shiga harkokin
siyasa a kusan gab da zaben 2003, al’amura suke ta wakana dangane da yanayin
siyasarsa. A lokacin da Buhari ya kama harkokin siyasa gadan-gadan ya samu
dumbin masoya talakawa da magoya baya daga cikin manyan ‘yan Siyasa da kuma
tsaffin ma’aikatan gwamnati da tsaffin ‘yan sanda da uwa uba tsaffin sojoji. A
takarar da Buhari ya fito ta farko a 2003 da ake ganin cewa babu makawa shine
ya lashe zaben aka murde, a wannan lokacin shi ne kusan zamanin da za’a
kwatantashi da cewa lokacin da Buhari ya tara
dumbin magoya baya a tattare da shi kafin daga bisani al’amura su sauya.
Kamar yadda muka samu labarin cewar a lokacin da
Buhari ya fito takarar farko akwai tsaffin manyan sojoji da ake kira “former
retired Generals” sama da guda ashirin da biyar (25) wadan da suka rufawa
Buharin baya tare da fatan ganin ya kai ga nasara, banda wadan da ake ganin
manyan ‘yan siyasa ne wadan da sun isa su yi Magana a sauraresu ko dai a
yankunansu ko kuma a cikin jam’iyyar APP da ta rikide zuwa ANPP. Kamar yadda
wadan da suke sukar Buhari suke fada cewar kafin shigarsa harkokin siyasa
jam’iyyar da ya shiga ta APP mai hamaya tana da kusan gwamnonin jihohin Sokoto,
Kebbi, Zamfara, Borno, Yobe, Gombe, Jigawa, Kogi da kuma Kwara; wadannan jihohi
tuni jam’iyyar Adawa ta Buhari ta yi musu kwab daya tun a zaben farko na 1999,
wanda bayan da aka gudanar da zaben 2003 sai lissafin ya sauya. Domin jihar
Kwara da take da mutum mafi girman fada a ji a cikin jam’iyyar APP wato
marigayi Alhaji Olusola Saraki da magoya bayansa suka kauracewa jam’iyyar. APP
ta yi kokari ta sake ciwo jiha mai matukar muhimmanci wato Kano a zaben 2003 da aka ce Buhari bai samu
Nasara ba, a hankali ana tafiya, kida na canzawa rawa ma na canzawa. Inda
Buhari ya yi asarar manyan magoya bayan da aka dinga cewa su tafi Allah ya raka
taki gona daman su ba na gari bane, kamar yadda abin yake Jam’iyyar Burai ta
ciwo Kano kuma
ancinye mata wasu.
Jam’iyyar Buhari ta tafka wawar asarar wasu muhimman
gurare duk kuwa da zargin da wasu suke yi cewar ba da Allah da Annabi aka kayar
da Buhari a wuraren ba, Misali Jihohin Kwara, Kogi, Gombe, Jigawa, Sokoto,
Kebbi duk suka koma kasrkashin Jam’iyyar PDP kafin daga bisani jihar Bauchi ta
fado hannun jam’iyya mai masara ta Baba Buhari a wancan lokacin. Kamar kulab
din wasan kwallaon kafa ne da ya rasa mahara da tsayayyun masu kare gida, dole
idan abokin karawarsa ya iyi taka leda yadda ya kamata yayi ta shansa kwallaye
babu kakkautawa, kusan haka ne abinda ya faru da Buhari inda aka yi ta zurawa
jam’iyyarsa kwallaye duk kuwa da tunanin da ake na cewa yana da zakakuran ‘yan
kwallo da tunda suke wasa a baya ba’a taba cin galaba akansu ba.
Da gumu tayi gumu, tafiya kuma tayi tafiya a
harkokin siyasar General Muhammadu Buhari shi kansa ya sa-kafa ya tsallake ya
bar jam’iyyar tasa ta ANPP inda ya kafa sabuwar jam’iyyar CPC. Kafin fitar
Buhari daga ANPP tuni jam’iyyarsu tayi asarar Jihar Bauchi inda gwamnan jihar
Isa Yuguda ya fice ya koma PDP. Fitar Gen Buhari daga ANPP ya kafa sabuwar
jam’iyyar CPC da yawan masu sharhin siyasa sun ga gajen hakurin Buhari na
rashin hakuri a tafi tare a tsohuwar jam’iyyar tasu da take da dumbin magoya
baya daga cikin manyan ‘yan siyasa.
Kafin kaiwa zuwa ga kafauwar sabuwar jam’iyyar CPC wadda
ta kafu cike da rudani da hayaniya, tuni jiga-jigan mutane wadan da ake musu
kirari da cewa idan ka gansu
tamkar kaga Buhari ne suka raba gari da Buharin. Mutane irinsu Hajiya Najatu
Muhammad, wadda take zaman mace mafi kusanci da Buhari a siyasance ta raba
tafiya da tsohon ubangidanta da mutane irinsu Muhammad Adamu Bello da su Brig.
Gen Magashi a gefe guda kuma tuni aka raba hanya da irinsu Attahiru Dalhatu
Bafarawa inda suka kafa sabuwar jam’iyyarsu mai abarba, wanda shima ya yagi na
yaga daga cikin magoya bayan Buharin.
A jumlace baya ga jihohin da jam’iyyar su Buhari
suka yi asara sun kuma yi asarar manyan mutane wadan da ko dai suka fito karara
suka bayyana basa tare da Buhari ko kuma wadan da suka ja baki suka yi shiru
amma kuma sun janye jikinsu a tare da Gen. Buhari, a har kullum masu hikima na
cewa shi jari a wajen dan siyasa shine jama’a. Buhari ya rasa mutane irinsu
Bukar Abba Ibrahim, Sanata Ali Shareeff, Yariman Bakura, Adamu Aleiru, Ibrahim
Shekarau, Bafarawa, Najatu Muhammad da sauransu masu yawan gaske, watakila wasu
su zargi wadannan mutane da cewar daman sune suka ciwa Buhari dunduniya a
tafiyar ANPP har suka yi masa hayaki,
Allah shine masani.
Bayan da Buhari ya kafa sabuwar jam’iyyar CPC ta
samu farin jini tare da karbuwa a wajen talakawa ainun. Jam’iyyar da kusan zaka
ce tun da aka kafata da sabbin rikice-rikice ta fara wadan da ake ganin irinsu
ne suka sa Buharin ya baro tsohuwar jam’iyyarsa ta ANPP, kafuwar CPC ke da wuya
mutane masu bukatar kashin kansu suka dinga yi mata tururwa suna kunno kai
ciki, da nufin samun albarkacin Buhari dan kaiwa zuwa ga madafun iko a matakai
daban-daban, wanda wannan yana daya daga cikin abubuwa da suka dagwalgwala
tafiyar CPC a kusan galibin jihohin Arewa, misali a Kaduna kowa yasan cewar Hon
Sani Sha’aban shi ne kusan mutum na farko da zaka lissafa a matsayin na hannun
daman Buhari, wanda saboda kaunarsa da Buhari yake sai da Buharin yaki halartar
gangamin kaddamar da dukkan ‘yan takara na CPC a jihar Kaduna amma ya halarci
gangamin kaddamar da takarar Sha’aban, daga bisani tafiya bata yi nisa ba aka
nemi Sha’aban aka sara ya sulale yabar CPC.
Haka kuma, a jihohi irinsu Kano da Katsina da Bauchi
da Taraba da Bauchi aka dinga samun rikicin da ya hanawa jam’iyyar wani katabus
da zai kaita ga iya kaiwa zuwa ga samun Nasara, duk wannan an zargi wasu daga
cikin manyan magoya bayan Buharin da haddasa wannan sabatta-juyatta dan a
gurgunata tafiyar CPC da Buhari a wannan jihohi.
Wani muhimmin batu anan shi ne yadda Buhari ya kasa
gane masoyansa na hakika da kuma makiyansa na zahiri. Eh! Wannan batu gaskiya
ne, domin a jihar Kebbi, Buhari ya dauki al’amuran jam’iyyar CPC sukutum ya
mikawa tsohon Gwamna Adamu Aleiru wanda da dama daga cikin makusantan Buhari
suka ga baikensa, domin ya kasa fahimtar masoya na hakika, daga cikin wadan da
suka ja hankalin Buhari akan kuskuransa na danka ragamar CPC a hannun Adamu
Aleiru har da tsohon dogarinsa tsohon sarkin Gwandu Jakolo, haka aka wayi gari
Aleiru ya kwarewa Buhari baya inda da shi da dantakararsu na gwamna Gari Malam
da sauran magoya bayansu duk suka yiwa PDP kome.
Idan kuma ka dauki jihar Buhari ta Katsina suma haka
al’amura suka dagule aka yi kiki-kaka tsakanin bangaren Lado Danmarke da ake
ganin babu makawa da ya tsaya a tutar jam’iyyar CPC sai ya kai labari, da kuma
tsohon kakakin majalisa Aminu Bello Masari. Itama jihar Kano haka abin yake, inda aka ja tunga
tsakanin bangaren Muhammadu Abacha da kuma na Jafaru Isa wanda ake ganin idon
Buhari akansa yake, da kuma wanda yake ikirarin cewar shine mutumin da aka yiwa
CPC rijista da sunansa, kuma ya bata gidansa a matsayin shalkwatarta wato
Sanata Rufai Hanga. A Bauchi da Taraba ma haka labarin yake inda akayi ta samun
jumurda a tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar ta CPC. Duk wadannan abubuwa da suka
wakana marasa dadi, rana a tsaka Buhari ya janyo tsohon Minister Nasiru Elrufai
a matsayin bakaniken Jam’iyyar CPC, abinda watakila zamu iya tambaya, rikicin
da Buhari duk da kima da tasirinsa ya gagareshi shawo kansa, El-Rufai zai iya?
Idan kuma, muka koma batun cewa Buhari ya kasa
fahimtar magoya bayansa na hakika da makiyansa na zahiri, sai muga cewa rana a
tsaka Buhari ya tsinci wasu mutanen da basu sha wata wahala a tare da shi ba,
ya ture wandan da aka dauki dogon lokaci tare da su, ya janyo wadannan
tsintattun magunan da PDP ce tayi musu dumi suka tsallake ta, misali mutane
irinsu tsohon Minister Nasiru ElRufai da tsohon Kakakin Majalisa Aminu Bello
Masari da tsohon Minister Hassan Lawal, wadannan mutane Buhari ya fifita
bukatunsu sama da na kowa a cikin sabuwar CPC din, a cikin wadannan mutane
wanda zaka ce yana gaba da su a wajen Buhari shine Sule Hamma Yahaya sai kuma
Injiniya Buba Galadima.
Kwatsam kuma a makon da ya gabata sai muka ji cewa
Buba Galadima ya bayyana ficewarsa daga dukkan al’amuran siyasa inda zai koma
gefe ya zama dan kallo. Haka kuma, dukkan wanda ya karanta hirar Buba Galadima
a jaridar Aminiya kuma ya yi masa adalci zaiga cewar batun fifita su Elrufai da
aka tsinta rana a tsaka aka dankwafe su Buban da dasu aka dinga fadin tashin
ganin al’amura sun gudana na daga cikin dalilin barin Buban harkokin siyasa. Na
taba jin Dr.
Aliyu Tilde ya fada cewar idan gaskiya ta shafi Gen. Buhari sai dai mutum ya ja
bakinsa ya tsuke dan gudun bakin jini ko rashin fahimta. Haka ma, a wata wasika
da Alhaji Abdulkarim Daiyabu ya taba aikewa da Gen. Buhari mai suna HATTARA DAI
GEN BUHARI ya ja hankalin Buhari akan yadda ya fifta Sule Hamma Yahaya akan
dukkan wani dan siyasa da yake a tare da shi, Alh. Daiyabu ya gayawa Buhari a
cikin wannan wasika cewar shi Abdulkarim Daiyabu yafi Buhari sanin waye Sule
Hamma, domin yace tare suka yi karatu kuma suka shiga harkokin siyasa tun
jamhuriya ta biyu, inda ya tabbatarwa da Buhari cewar akwai kuskuren sakarwa
Hamma ragama da yayi, domin kuwa ya tunawa Buhari cewar a lokacin da Buhari
yake shugaban kasar soja shi da kansa ya kama Sule Hamma ya daure a saboda
Sulen ya ci amanar kasarnan, wanda yace Sulen na nan da bakin cikin daurin da
Buhari yayi masa, amma duk da haka Buhari ya cigaba da maida Sule Hamma danlele
da baya laifi.
Koma dai me ya faru lallai yana da kyau mu sani cewa
Buhari ba Allan-Musuru bane, mutum ne dan Adam kamar kowa. Dan haka yana da
kyau a tunkareshi gaba da gaba a gaya masa irin abubuwan da suke wakana a kuma
ja hankalinsa, duk da cewar yana da masaniyar kusan dukkan zarge zargen da
akeyiwa na jikinsa akansa, dan yasan mutane na hakika da zai tafi da su a
jikinsa da kuma wadan da za’a yi baya-baya da al’amarinsu. Sau da dama mu
talakawa da muke nuna soyayya ga Buhari galibinmu daga nesa ne, bamu san yadda
al’amura ke gudana ba, ta yadda soyayya ta rufe mana ido muke ganin dukkan wani
wanda zai zargi Buhari to shine bashi da gaskiya! Shakka babu Buhari shine
mutum na farko da aka fi kyautatawa zato sama da dukkan wani mahaluki a
kasarnan, amma wannan ba zai zama madubin da zai nuna cewar komai na Buharin
gaskiya ne dari-bisa-dari ba, dole ne a samu kurakurai masu tarin yawa a
tattare da Buhari. Idan duk muka kalli abubuwan da suka faru wadan da na fada
da wadan da ban fada ba, sai mu tambayi kanmu Shin Buhari Ne Ke Da Mtsala, Ko
Kuwa Magoya Bayansa? Magoya baya anan ina nufin manyan ‘yan siyasar da suke
tare da shi ba talakawa Masoya ba.
Fitar Buba Galadima daga harkokin siyasa ta sanya
dole a sake kallon al’amuran Gen. Muhammadu Buhari da idon basira a kuma gayawa
Buharin inda yake da kurakurai kuma suke da bukatar gyara a gyara, shakka babu,
duk wanda yasan yadda mutane irinsu Buba Galadima suka yi kaurin suna ba dan
komai ba sai akan Buhari, kuma yaji irin wannan korafi na Buban dole yaji
damuwa a ransa, ganin cewar gashi kullum kwanan duniya muna kara tunkarar
shekarar 2015 ne, wadda zabenta zai fi dukkan zabukan da suka gabata a baya
jan-hankali da daukar ido, amma haka da rana tsaka ana samun irin wannan wawar
Baraka, lallai da sake wai ambaiwa mai kaza kai.
Lallai mu sani yakin zaben 2015 yaki ne tsakanin
gungun barayi, da kuma masu kaya a gyefe guda da suke son karbar kayansu ko da
tsiya ko da arziki, haka kuma wannan yaki, bana wasu tsirarun mutane bane, yaki
ne da yake bukatar hadin kan kowa da kowa wajen ganin an fitar da al’ummar
kasarnan daga cikin halin kangin da jam’iyyar PDP a mataki na tarayya ta sanya
al’ummar kasarnan a ciki.
Daga karshe ina kira ga Gen. Muhammadu Buhari da
cewa lallai ne ya fahimci gaskiyar yadda lamura suke, a san abinyi, ba dai-dai
bane ana samun irin wannan zogayewar manyan mutane a tare da tafiyar hamayya
kuma a ja baki a tsuke kowa ya kama gabansa ace masa Allah ya raka taki gona.
Ya kamata Buhari ya sasanta da dukkan wadan da suke ganin anyi musu ba daidai
ba, haka kuma wadan da Buhari yake ganin sunyi masa ba daidai ba, suma dole ya
yafe musu wajen ganin angudu tare kuma an tsira tare.
Mun san da cewar Buhari talakawa ne a gabanka, amma
da dama daga cikin wadan da suke cikin wannan tafiya taka akwai wadan da basu
da wata alaka ko ta kusa ko ta nesa da talakawa illa iyaka bukatun kansu, ko
kuma wani laifi da suke ganin PDP tayi musu, dan haka suka dawo bangaren Adawa
dan su huce haushinsu.
Yasir Ramadan Gwale
28-07-2013
No comments:
Post a Comment