Monday, July 8, 2013

SHUGABA GOODLUCK JONATHAN: SHAIDANIN AFURKA


SHUGABA GOODLUCK JONATHAN: SHAIDANIN AFURKA

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan kusan idan kace duk Afurka babu wani shugaba d’an kama-karya irinsa baka yi kuskure ba. Hakika Goodluck Jonathan cikakken dan kama-karya ne, maci amana, mayaudari, mugu, mara kishin kasarsa da al’ummarsa, mutumin da ya yiwa kansa dabaibayi da cin hanci da rashawa wanda ya wuce kima. Shugaban da a tarihin Afurka ba’a taba samun wata gwamnati da aka sameta da matsanancin cin hanci da rashawa ba kamar tasa, ta kowanne fanni shugaban ya yiwa kansa daurin gwamai da cin-hanci ga lalata da almubazzaranci da dukiyar ‘yan Najeriya, baya ga halin nuna ko inkula da yake yiwa wasu al’ummomi musamman na Arewa, mutanan da suke daukar kaso mafi girma na al’ummar Najeriya.

Shakka babu, shugaba Jonathan bai cancanci shugabancin wannan kasar ba. Domin babu yadda shugaban da ya san meye shugabanci zai bar al’ummarsa cikin irin mugun halin da wannan shugaban ya sanya al’ummar Najeriya musamman na Arewa a ciki, ta ko ina rikici ya dabai baye yankin Arewa, kama daga rikici tsakanin Manoma da makiyaya, da rikicin kablanci da na addini, da harin sari-ka-noke da ake kashe mutanan da basu san hawa ba basu san sauka ba, da kuma uwa uba al’amarin Boko Haram da ya kusan durkusar da yankin Arewa baki daya. Matsalolin tsaro sun addabi kowa, gwamnatin tarayya wadda shugaban kasa yake zamewa shugaban rundunar dukkan masu d’amara, bata yin wani abu da ya nuna da gaske ana son kawo karshen wannan al’amari na tashe tashen hankula.

Abin da za kkara tabbatar maka da hakan kuwa shine, duk da dumbin jami’an tsaron da aka jibge a jihohin da al’amarin yayi kamarai amma basu iya murkushe hare-haren sari ka noke akan talakawa ba, har sai da yanzu babu kunya wai talakawa da basu da wani horo da yashafi harkar tsaro sune suke farautar masu laifi. Abin da ya faru na baya-bayannan a jhar Yobe na kashe dalibai ya isa misalin da zai nuna cewa wannan shugaban ya gaza matukar gazawa wajen tsare amanar ‘yan Najerya da take kansa. A yanzu a fadin Nahiyar Afurka wanne shugaba ne ake kashe al’ummarsa babu kakkautawa amma babu wani mataki da yake dauka na kawo karshen hakan cikin gaggawa irin Jonathan? Amma muna sane da irin siyasar da Shuagabn yake son yi mana, ta hanyar dawo da zaman lafiya kafin zaben 2015.

Shugaba Jonathan yayi kama da takwaransa na Kamaru Poul Biya wajen muzgunawa al’ummar Musulmi. Eh! Shakka babu haka ne, domin kuwa Jonathan yana nuna wariya da bangaranci babu ko kunya a cikin al’amuran tafiyar da gwamnatinsa, kamar yadda Shugaba Biya na kamaru ya nuna musulmin kasarsa da yatsa; tun lokacin da muka fahimci cewa shugaba Jonthan bashi da gaskiya, kuma mugun mayaudari ne shine lokacin da aka kai harin Bom a dandalin Eagle Sqaure a bikin samun ‘yancin kai na shekarar 2010, inda kungiyar MEND ta yankin da shugaban kasar ya fito ta dauki alhakin kai harin amma shugaban babu kunya babu tsoron Allah ya fito yana karesu cewa ba su bane. Kafin daga bisani yayi baki biyu akan lamarin.

Kamar yadda muka samu labari cewar Musulmi a kasar Kamaru ba suda wani katabus a harkar tafiyar da gwamnati, alamu suna kara bayyana mana cewar wannan shugaban shima yabi sahun makwabcinsa Biya wajen aiwatar da irin wannan mugun nufi! Haka shima, tsohon shugaban kasar Ethiopia Melez Zenawi da ya mutu, ya muzgunawa Musulmin kasarsa duk da cewa sune kashi 40 na ‘yan kasar amma aka hana musu wani katabus a gwamnatance, aka ki basu dukkan wata dama da ta kamace su, karshe dai yanzu Zenawi yana can yana ganin abin da ya shuka, idan khairi ne, yana gani idan sharri ne, yana gani, amma dai mun san cewa makomarsa ta munana ainun!

Haka kuma, idan ka dauki nadin mukaman da wannan shugaban yake zaka san cewa yana bn sahun Biya da Zenawi ne, kusan dukan mukamansa da mataimaka na musamman da ministoci da jakadun kasashen waje duk ankwashe kafafun Musulmi a Najerya. Idan muka dauki batun Jakadun Najeriya a kasashen waje idan Banda Dalhatu Sarki Tafida da aka kai kasar Burtaniya (wanda shima mun san bisa yarjejeniya aka yishi) babu wasu Musulmi da aka tura manyan kasashen duniya, daga wadanda aka tura kasashen Arewacin Afurka da ake yaki sai wadan da aka tura yankin gabas ta tsakiya, sai kuma kuma wadan da aka tura matalautan kasashen yankin Afurka da nahiyar Asiya. Amma lokaci ya yi kusa da zamu yanke hanzarin wannan shugaban Insha Allah, ya shirya ko bai shirya ba.

Yasir Ramadan Gwale
08-07-2013

No comments:

Post a Comment