Friday, August 31, 2012

CPC Ba Su Da Kwarin Gwiwar Cin-zaben 2015



CPC Ba Su Da Kwarin Gwiwar Cin-zaben 2015

“Ina fatan duk mutumin da zai yi min martani ya tabbata ya karanta abinda na rubuta har karshe.”

Bisa ga dukkan alamu wannan zaben na 2015 da yake tunkaromu Jam’iyyar Hamayya ta CPC bata shiryawa cin zaben da gaske ba. Don bayanai da rahotanni suna tabbatar da cewar kwarin gwiwar da CPC suke da shi, shi ne idan aka samu hadewa da jam’iyyar ACN, kusan mafiya yawancin ‘yan cpc wannan shi ne tunaninsu cewar idan an hade za’a iya cin zabe. Shakka babu Jam’iyyar ACN jam’iyya ce da ta ke da tsari musamman a inda tayi kakagida wato yankin Kudu maso Yamma ko ka ce yanki Yarabawa, hakika duk wanda ya kalli irin yadda suka mamaye wannan yanki dole ya tabbatar da cewar suna da kyakykyawan shiri, da tsari karkashin Jagorancin Shugabansu Asiwaju Bola Ahmwd Tinubu.

Karkashin Jagorancin shi wannan mutum Tinubu ACN ta karbe ragamar iko daga PDP a jihar Ogun, jihar da ke zaman mahaifa ga tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo. Wanda wannan ba karamin aiki suka yi ba na karbe ragamar ikon wannan jihar daga hannun PDP duk kuwa da cewar Obasanjo shi ne kusan ya yi uwa ya yi makarbiya a PDP amma kuma jiharsa ta gagareshi, Wani abu da zai baka mamaki da shi wannan mutum (Tinubu) wai shin kudi yake rabawa mutanan yamma suke zaban jam’iyyarsa? Ko kuwa tsabar iya zance ne da iya siyasa? hakika wannan tambaya ta jima tana yimin zillo a raina.

Alamu sun tabbatar da cewar ACN ba burinsu su kafa gwamnati a Najeriya ba. Kawai suna bukatar kasancewar yankin yarabawa ya kasance karkashin Jam’iyyar hamayya, domin a yadda suke ganin sun fi kowa wayewa da sanin ilimin boko, kuma zaben da ya gabata na 2011 ya kara nunawa cewa basu da burin kafa gwamnatin tarayya, kuma da wahala su yarda su yi tarayya da sauran ‘yan Najeriya a cikin Jam’iyya daya, tabbas yau ko da a ce ACN zata kafa Gwamnatin tarayya, lashakka yarabawa sai sun balle sun kafa jam’iyyar hamayya ta daban, domin su sumfi gwammacewa su yi ta kasancewa ‘yan Hamayya ko Adawa, kamar yadda Hausawa muke musu kirari da cewa “Yarabawa masu kwalo-kwalo” shakka babu suna da kwalo-kwalo sosai da gaske. Kamar yadda na ce, duk wanda ya kalli zaben da ya gabata, ACN ta fi mayar da hankalinta ne akan yankin Yarabawa ya ci zabe, sabanin sauran jihohin Najeriya wanda suna ganin idan tayi ruwa rijiya idan kuma bata yi ba daman haka ake zato.

Idan muka kalli yadda ACN suka yi ruwa suka yi tsaki akan shari’ar da suka kai ta jihar Osun wanda Rauf Aregbesola yake zame musu dan takara, nu nace akan wannan shari’ah kwarai da gaske har sai da hakarsu ta cimma ruwa, amma kuma idan muka kalli zaben da ya gabata na jihar Benue shedu da bayanai sun tabbatar da cewar ACN ita ce ta samu nasara a wannan jihar, amma uwar jam’iyyar ta kasa basu maida hankali akan shari’ar wannan jihar ba  kamar yadda suka yi a jihar Osun, wannan ya kara tabbatar mana da cewar ba burinsu su mamaye Najeriya ba illa yankinsu kawai.

Idan kuma, muka sake duba Arewa muka kalli Jam’iyyar CPC da Jagoranta Gen. Muhammadu Buhari, zamu ga cewar tabbas babu wani shiri a kasa na kafa gwamnati a 2015, kullum kawai surutai ake yi a kafafen yada labarai, da tunanin waccan hadewa, babu wanda zai yi shakkar cewa CPC bata da dumbin magoya baya a Arewa, tana da su na ban mamaki kuwa, amma zaka iya kiransu da cewar taron tsintsiya ne babu shara, domin mafiya yawan ‘yan Jam’iyyar nema suke jam’iyyar ta taimaka musu, ba wai su su taimakawa jam’iyyar ba. Kusan tun kafuwar CPC ta kafu da rikici da hayaniya, domin da yawan mutane sun shiga Jam’iyyar da tunanin samun makoma, wasu na ihun sai sun zama shugabanni a Jihohi wasu a kananan hukumomi wasu a mazabu, wasu kuma suna son su zama ‘yan takara ko ta halin kaka. Wannan rikicin ya hana CPC katabus a Arewa, kuma idan ba hankali aka yi ba shine zai ci gaba da mamaye Jam’iyyar har zuwa lokacin zabe mai zuwa.

Akwai dubban mutane suna nan sun dana tarko jira suke lokaci ya yi su zo domin su shiga Rigar Buhari ko suma zasu dace da al’farmarsa domin ‘yan Najeriya su sahale musu, kuma kamar yadda ake kyautata zato ga Jagoran Jam’iyyar Gen. Buhari mutumin kirki ne, haka ya kamata mutanan da ke cikin jam’iyyar su kasance, amma kusan akasin haka ya fi faruwa, domin anyi sake da karnuka da kuraye da muzurai da aladu duk sun shiga cikin jam’iyyar sunyi kaka-gida kuma suna ta yi mata kafar ungulu tare da nuna cewar su sun shigo Jam’iyyar ne saboda Buhari, wanda a zahiri halayyar su da dabi’unsu da ayyukansu sun sha bamban da na Gen. Buhari. Saboda irin wannan kwamacala da rikita-rikitar jam’iyyar CPC ta sanya ala dole, jagoran Jam’iyyar Gen. Buhari ya dauki Jam’iyyar dungurungum ya mikata ga tsohon ministan Abuja Mallam Nasiru el-Rufai ya yi mata garambawul, saboda yakini da yake da shi cewar el-Rufai kwararre ne da zai iya saita jam’iyyar ta zauna kan turba.

Mafiya yawan ‘yan Najeriya duk zatonsu shi ne cewar jam’iyyar CPC ta Gen. Buhari ce. Sai gashi mutane irin su Sule Yahaya Hamma da Rufai Hanga suna ikirarin cewar Jam’iyyar tasu ce su suka kafa ta da sunansu su suka samarmata da ofis da sunansu aka kafa wannan jam’iyya, dan haka sai wanda suke so shi zai tsaya takara a cikin jam’iyyar, wannan ya haifar da yin jabun katin shiga jam’iyyar a nan Kano inda na fito, kai rahotanni ma sun nuna cewar har jabun katin tsayawa takara aka yi tun daga matakin unguwanni har zuwa kananan hukumomi zuwa Jiha, wanda wannan batu kusan haka ya faru a jihohin Kano da Bauchi da katsina da Neja kamar yadda muka karanta a Jaridu kuma wannan ne dalilin da ya sanya uwar jam’iyyar dakatar da zaben shugabannin jam’iyyar a wadancan johohi a ranar Asabar 11 ga watan Disambar 2010.

Kamar yadda muka sani tsarin jari hujja shine linzamin siyasar wannan lokacin. Shakka babu, duk harkokin siyasa baza su yiyuba sai da kudi, to yana daga cikin abinda CPC ta rasa shine wadan da zasu taimakawa Jam’iyyar ko da badan Allah bane. Domin dai dole ka bude ofis a kusan galibin mazabu dole a samar da abinda ake fada da yaren siyasa wato kayan aiki, dole ayi abubuwa da dama wadan da suke bukatar kayan aiki, amma manyan masu kayan aiki da suke a cikin jam’iyyar irinsu Sanata Rufai Hanga da Sule Hamma duk sun shagaltu da yiwa juna kafar ungulu da shatile kafafuwan Jam’iyyar matukar ba nasu bane suka sami takara ba, haka kuma jam’iyyar ta yi wawar asarar mutane irinsu Adamu Aleiru da Gari Mallam a jihar kebbi, da Gamaliya dan takararta na Gwamna a Jihar Taraba da sauransu da dama, ita asarar magoyin baya a siyasa ko da babu abinda yake tsinanawa matsala ce, indai har zai fita bainar jama’a ya ce yabar wannan tafiyar.

A nata bangaren ita ma Jam’iyyar PDP a shirye ta ke na kare kambunta na ci-gaba da rike madafun iko. Shakka babu PDP aiki suke yi tukuru domin samun Nasarar jam’iyyar a 2015, dan haka ne ma suke ta kokarin hadiye ‘yan CPC din. A loakcin da CPC suke ta dogon turanci da yawan mitin tsakanin kaduna zuwa Legas shin a hade tsakanin ACN da CPC ko kuwa, su kuma a nasu bangaren PDP suna nan suna raba dare suna mitin akan ya zasu samu nasara a 2015, Bahaushe ya ce shirin zaune yafi na tsaye, tabbas cpc shirin tsaye suke a yayin da PDP suke shirin zune.

Idan muka kalli zaben gwamnonin da akayi a jihohi biyar wato Sokoto da Adamawa da Kogi da Bayelsa da Cross-Rivers, ya nuna cewar PDP sun shirya tsaf domin fuskantar CPC a 2015, domin da zaben sokoto ya zo kusan ‘yan jam’iyyar musamman gwamnonin Arewa tarewa suka yi a sokoton har sai da suka ga Alu ya kai labari duk kuwa da ana kallon kamar yana takun saka tsakaninsa da shugaban kasa a wannan lokacin, kuma wani abu da zai tabbatar da yunkurin PDP na sake kafa gwamnati, kusan idan mun lura ita PDP duk danta sai ya yi mata aiki, ko da kuwa ba’a zaman lumana da shi a jam’iyyar, idan muka kalli zaben Adamawa kowa yasan akwai tsamin dangantaka tsakanin Atiku Abubakar da Murtala Nyako tun kusan zaben fitar da gwanin da aka yi tsakanin Atiku da Jonathan, amma sai da Atiku ya fito ya taya Nyako yakin neman zabe domin samun nasarar Jam’iyyar PDP.

Kamar yadda Sanata Gemade ya fada a karshen wannan makon cewar tattaunawar CPC da ACN zata sake wargajewa ne, wannan magana ce mai yuwuwa. Domin mutumne ya samu fili ya gina gida yana cikin gidansa sai abokinsa ya zo ya ce ya fita daga cikin wannan gidan nasa ya zo su kafa wani sabon gidan mai kayan alatu! Kaga abu ne da kamar wuya, to kusan haka batun CPC yake da ACN, domin ni kam bantaba zaton cewa ACN zasu saki jam’iyyar da suka sha gwagwarmayar rayata a yankin kudu maso yamma ba, rana a tsaka kuma su ce sun barta sun koma CPC wannan kam da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Ko dai shi Buhari ya yarda ya koma ACN dan ya zama dantakararsu na shugaban kasa, ko kuma a dauki dogon lokaci ana ta mitin tsakanin Legas da Abuja da Kaduna har lokaci ya kure daga karshe kuma tattaunawar ta sake karyewa. A sake komawa gidan jiya.

Idan ance za’a hade shin jam’iyya biyu za’a zaba da dantakara guda daya wanda wannan ya ci karo da tsarin hukumar zabe, ko kuwa kamar yadda na fada yarabawa ne zasu bar ACN su koma CPC ko kuwa Gen. Buhari da magoya bayansa ne zasu bar CPC su koma ACN? Lallai amsar wannan tamabayar zata nuna alkiblar inda aka dosa, hakika halin da muke ciki yanzu lokaci yana kara tafiya, kuma yana kara yiwa CPC karanci. Domin dai tsarin hukumar zabe ya ce sai dan takarar ya samu kashi 25 na kuri’ar da aka kada a jihohi 23 sannan ya iya zama shugaban kasa, mu dauki yankin Arewa maso yamma da Arewa maso gabas shakka babu CPC tana da karfi kuma zata samu fiye da wannan kashin da tsarin hukumar zabe ya yi tanadi, mu dauka ma CPC tana da goyon bayan jihohin Arewa 19 wanda ana bukatar sauran jihohi hudu kenan domin samun zabe, wanda kai tsaye wani zai ce dan jihohi hudu ai ba matsala bane, wanda gagarumin aiki ne samun wadan nan kuri’u a jihohi hudu daga kudu, domin kowa yasan cewa mafiya yawancin jihohin kudu dangwale ake yi ba zabe ba. Kuma kar mu manta a Arewa muna da jihar Plateau da Benue wanda ko ana ha-maza ana ha-mata baza su zabi Dan Arewa musulmi ba.

Kuma suma a nasu bangaren masu adawa da CPC zasu yi ta hura mata wutar rikici, su hana jam’iyyar sakat ta yadda zasu sami lagon jam’iyyar a zaben. Tabbas alamu sun nuna cewar wannan shugaban me ci wato Goodluck Jonathan yana son tsayawa wani zaben a 2015, wanda abu ne mai yuwuwa, amma PDP suna da hasashe kuma suna da zurfin tunani, domin idan suka ga cewar GEJ zai kada Jam’iyyar to shakka babu zasu fitar da dan takara daga Arewa wanda zasu marawa baya dan ganin bata bare musu ba, kamar yadda rade-radi yake bayyana cewar ana yunkurin tsayar da gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido da Gwamnan jihar Rivers Rotimi Ameachi, wanda a turance wannan shi ne Plan B na jam’iyyar PDP, domin da su rasa gara su dauko wanda suke ganin zai iya cin zabe ko da kuwa a wajen Jam’iyyar yake.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Mallam Nuhu Ribadu Waliyyi Ne



Mallam  Nuhu Ribadu Waliyyi Ne

Sunan Mallam Nuhu Ribadu ya fara bayyana ne a lokacin da ya jagoranci hukumar yaki da yiwa tattalin arzikinsa zagon kasa da kuma yakar cin-hanci da rashawa a Najeriya, wadda akafi sani da EFCC, hakika ya nuna kwazo sosai lokacin da ya shugabanci wannan hukuma, domin ya kama tare da gurfanar da mutanan da ake ganin baza su iya tabuwa ba a kasarnan, bisa zarginsuko kama su da yin almundahana da dukiyar kasa. Misali bayan da sashi na 308 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa masu rike da mukamin shugaban kasa da mataimakinsa da gwamnoni kariya daga gurfana gaban kowane irin kwamitin bincike ko kotu, wanda wannan sashi ya taimakawa Muggan barayin gwamnoni Jidar dukiyar kasarnan suna kaiwa kasashen Turai da Amerika suna jibgewa, duk da haka Ribadu ya kafa musu tarko, shakka babu wannan ba karamin aiki ya yi ba, ko iya nan ya tsaya, kwalliya ta biya kudin Sabulu.

Bayaga damke tsohon gwamnan jihar Bayelsa DSP Aliemieghsigha, ya kuma kama takwaransa na Jihar Delta Mista Jame Ibori wanda ake ganin babu wanda ya tallafawa takarar marigayi Umaru YarAdua da kudi irinsa, Ribadun karkashin hukumarsa ya zargesu da zambar kudi kusan dubban miliyoyin daloli, rahotanni sun nuwa cewa Mista Ibori ya yi kokarin baiwa Ribadu toshiyar baki ta kusan Dala miliyan goma sha biyar ($15) kimanin Naira Biliyan Uku (N3B) amma Ribadun yaki karba. Sannan kuma ya fallasa irin adadin kudaden da gwamnoni sukayi rubdaciki da su a yayin da suke kan mukamansu, misali inda ya bayyana tsohon gwamnan Jihar Jigawa Ibrahim Saminu Turaki ya yi almundahana da kusan Naira Biliyan 36, da sauran gwamnoni da daman gaske ya yinda wasu kuma suka arce suka bar kasarnan wanda suka hada da tsohon gwamnan Jihar Edo Mista Locky Igbinideon da Adamu Mu’azu na jihar Bauchi da sauransu da dama a wancan lokacin.

Mallam Nuhu Ribadu dai shi ne mutumin da ya sa aka sauyawa Najeriya suna daga ta sahun gaba akan cin-hanci zuwa ta kasas-kasa. Wannan ce ma ta sanya majalisar dinkin duniya ta zabeshi a matsayin wanda zai binkito badakar cin-hanci da rashawa da ta mamaye gwamnatin Afghanistan. Hakika aikin da EFCC ta yi karkashin Jagorancin Ribadu na kokarin tatse mista James Ibori da mayar da abinda ya sata zuwa asusun gwamnati, aiki ne gagarumi kuma irinsa na farko a tarihin Najeriya, amma sai dai wannan yunkuri na Nuhu Ribadu ya gamu da cikas lokacin da Marigayi Umaru Musa ‘YarAdua ya zama shugaban kasa, domin zamansa shugaban kasa ke da wuya aka fara takawa Nuhu Ribadu birki sakamakon taba Ibori da ya yi, wanda a lokacin nan yake da uwa a gindin murhu. Dan shugaban kasa Umaru ‘yarAdua ya sakawa Ibori, ya nemi ya bayarda wadan da yake son a nada mukamai, inda shi James Iborin ya bayar da sunan babban yaronsa Mista Micheal Kaase Aoandoakaa a matsayin wanda za’a nada Babban Antoni Janar kuma Ministan Shari’ah domin ya binne badakar da Ribadu ya bankado ta Ibori, hakan kuwa aka yi Inda Aoandoakaa ya zama ministan Shari’ah kuma ya lalata binciken da Hukumar EFCC ta yi karkashin Ribadu, akan me gidan na Ibori.

Wannan ne dalilin da ya sa Shugaba ‘YarAdua Allah ya jikansa a wancan lokaci da Mista Ibori suka yi ta yiwa Mallam Nuhu Ribadu bita da kulli kawai dan ya ce a dawo da dukiyar da Ibori ya sata, Ribadu dai yaga takansa, domin bayan da aka ce ya koma makaranta kuma aka rage masa mukamin da yake da shi a rundunar ‘yansanda, sannan ma aka ce karatun da ya yi a Kuru dake Jos haramtacce ne, haka dai Mallam Ribadu ya samu ya sulale ya bar kasarnan domin tsira da rayuwarsa daga barazanar su Ibori da ‘YarAdua.

Sai ga shi a ‘yan watannin da suka gabata  Majalisar kasa karkashin jagorancin kwamitin Hon. Farouk Lawal ta gudanar da binciken cin-hanci mafi girma a tarihin kasarnan, inda aka kama manyan mutane da kamfanoni da ci-da gumin talakawa na kusan sama da Naira Tiriliyan daya, hakika ‘yan Najeriya sun yabawa Farouk Lawal bisa yadda ya gudanar da wannan bincike kuma ya kama mutane da yawa da ake ganin bazasu tabu ba. Kwatsam kuma sai gashi daya daga cikin mutanan da aka zarga Mista Femi Otedola yana ikirarin cewar ya baiwa Farouk Lawal din toshiyar baki ta kusan dala dubu dari shida da ashirin ($620) kimanin Naira Miliyan tasa’in da uku (M93), har kuma ya ce yana da faifan bidiyo da yake tabbatar da wannan ikirari nasa. A karshe dai ta bayyana cewar Lawal ya karbi wannan toshiyar baki, inda Jaridun Najeriya suka yi ta ya-madidi da wannan batu.

Idan har za’a ce Farouk Lawal da ya jagoranci wancan binciken cin-hanci mafi girma kuma ya karbi toshiyar baki ta Naira Miliyan 93 kacal ko $620, to Lallai zamu kwatanta Mallam Nuhu Ribadu da cewar waliyyi ne, domin kamar yadda muka fada Ibori ya baiwa Ribadu cin-hancin kimanin Naira Biliyan Uku amma Ribadun yaki karba, inda ya sanar da Babban bankin Najeriya akan wannan batu. Hakika Najeriya tana bukatar mutane irinsu Ribadu wadan da za’a basu irin wadan nan makudan kudi da sunan cin-hanci amma su tsallake.

Sai gashi a kwanakinna kuma wata sabuwa ta bulla, inda Andy Uba, yake ikirarin wadan nan kudi da aka baiwa Ribadu ya ki karba mallakarsa ne. Shi dai Andy Uba wani irin mugun uban gida ne, domin idan zamu iya tunawa shine mutumin da ya hana Jihar Anambara zama Lafiya lokacin tsohon gwamna Ingige. Inda har ya taba sanyawa aka sace gwamnan sukutun saboda yaki yarda da muguwar manufarsa ta raba kason jihar gida biyu a bashi rabi. Koma dai me ye, wannan ya tabbatar da cewar Ribadu bai ci wannan kudi ba, kuma indai Farouk Lawal zai karbi hancin Miliyan 93 kacal to tabbas Ribadu waliyyi ne idan ka kwatanta shi da farouk.

Lallai  Najeriya tana bukatar shugaba wanda zai yaki cin hanci da rashawa da gaske, irinsu Mallam Nuhu Ribadu.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Tuesday, August 28, 2012

Kotu a Zamfara Ta Daure Wani Matashi Shekara Daya Saboda Ya Saci Hular Dan Minista


Kotu a Zamfara Ta Daure Wani Matashi Shekara Daya Saboda Ya Saci Hular Dan Minista

Kotun shari’ar Musulunci da ke kanwuri a gusau ta Jihar Zamfara ta zartarwa da wani matashi mai suna Shehu Jiga wanda aka fi sani da Lalo daurin shekara daya a gidan kaso tare da biyan tara ta Naira 20,000 saboda kama shi da laifin Satar hular dan gidan Minista Safiyanu Bashir Yuguda, ita dai hular an kiyasta kudinta da cewar ya kai kimanin Naira 47,000.

Kamar yadda bayanai suka tabbatar, yana daga cikin al’adar danginsu Lalo sukan kai ziyarar barka da Sallah ga ‘yan uwansu da danginsu ciki kuwa harda karamin Ministan ayyuka Alh. Bashir Yuguda, wanda yake zaune a unguwar GRA da ke cikin birnin Gusau.

Kamar yadda aka shaidawa kotu cewa Lalo sananne ne a danginsu ministan, kuma yana daga cikin wadan da suka kai wannan ziyara ta Barka da Sallah zuwa gidan, sai dai bayan fitarsu ne aka lura da cewar hular Safiyanu wato dan ministan ta yi layar zana inda aka nemeta sama ko kasa. Dan haka ne Iyalan ministan suka yi yunkurin bibiyar wadan da suka kawo ziyara a wannan gida da nufin gano wanda ya dauki wannan hula. Daga baya bayanai suka nuna cewar anga wannan hula a wurin lalo inda ya tabbatar da cewar ya dauki wannan hula, kuma ya sayar da ita akan kudi Naira 15,000.

Da yake gabatar da hukunci mai shari’ah Alhaji Hadi Sani, ya ce bisa la’akari da bayanan da wanda ake zargi ya gabatar dan haka kotu bata da wani hukunci illa ta yanke masa daurin shekara daya a gidan kaso tare da biyan tara ta Naira 20,000.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Monday, August 27, 2012

Wannan Tashin Hankali Ne Kuma Bala’i Ne


Wannan Tashin Hankali Ne Kuma Bala’i Ne

Wani bawan Allah ne, ya kamala karatunsa na jami’a akan abinda ya shafi harhada sinadarai kuma ya yi sa’a ya fita da saka mako mai daraja ta daya. Bayan da ya yi hidimar kasa ya gama, ya mika takardunsa na neman aiki zuwa gurin wani mutum dan siyasa wanda yana ganin zai iya yi masa hanya ya samu aiki a daya daga cikin manyan kamfanonin mai na kasa, aka yi sa’a kuwa wannan dan siyasa ya karbi takardunsa ya gani ya ce masa lallai ka samu sakamako mai kyau, ya ce masa ka zo gobe office din aka sameni.

Bayan da ya koma gida yana mai alla-alla gobe ta yi, da gari ya waye ya kama hanya zuwa ofishin wannan mutum, yana zuwa kuwa ya yi sa’a ya taras da shi, wannan mutum ya dauko irin dan karmin katin nan ya yi rubutu a bayansa, ya dauko ambulan ya saka a ciki, sannan ya sa sitefula ya matse, ya bashi ya ce ka je Abuja ofishin kaza ka nemi wane kaza ka bashi, ni zan masa Magana daga nan.

Bawan Allah ya kama hanya zuwa Abuja, ya yi sa’a daman anbayar da sunansa a wajen masu gadi, nan da nan aka barshi ya isa har zuwa wajen wanda aka tura shi, bayan ya yi jira wannan mutum ya fito ya mika masa wannan ambulan, da ya bude ya gani, ya tashi ya gaida wannan matshi ya yi masa iso cikin ofis, da suka zauna ya karbi takardunsa ya duba ya gani, ya ce lallai ka samu sakamako mai kyau, sannan ya kawo bandir din dari biyu ya bashi ya ce ka koma gida bayan sati daya ka dawo. Bayan sati daya da ya koma Abuja, sai aka yi masa iso ya shiga ofis sai ya tarar da wannan mutum shida wani abokinsa suna hira, sai ya ce wa abokin nasa ai wannan yaron shi ne wanda nake baka labari, ya mike tsaye ya gaida shi. Nanma dai suka bashi bandir na dari biyu suka ce ya koma zuwa wani makon.

Ya dawo gida yana jiran karshen sati ya kama hanyar Abuja, da lokaci ya yi sai ya kama hanya, yana zuwa  ya samu wannan mutum da abokin nan nasa, nanma dai aka ce masa ya jira kwana uku masu zuwa, inda aka bashi masauki, bayan kwana uku yana kwance a masaukinsa sai aka buga masa waya cewa ya zo ofis yanzu, nan da nan ya kama hanya, yana zuwa sai ya tarar da wannan mutumin da abokinsa da ya tarar da su kwana ki, suka mika masa hannu suka gaisa, suke ce masa albishirinsa ya yi murmushi ya ce goro, suka dauko Offer aka bashi ya karanta ya gani sunansa ne, murna da farin ciki basu iya buya daga fuskarsa ba, nan ya yi hamdala yana godiya ga Allah, ashe bai sani ba tashin hankali ne zai biyo bayan wannan albishir.

Abokin mutumin ya ce masa muga Ofar ya karba, ya ce masa ina taya ka murna, ya amsa masa da cewa na gode. Ya ce kaga wannan takarda, ya ce, e, naganta, ya ce to taka ce, kaine zaka yi aiki a nan, amma kuma fa da sharadi LALLAI ne zaka bada kanka, ya ce ban gane ba, suka ce masa zaka maida kanka mace kuma za’a yi tarayya da kai, nan ya ji gumi ya karyo masa hankalinsa ya tashi, ya ji abin kamar a mafarki, suka ce masa kaga Yaro ba wai zabi muke baka ba abun da muka gaya maka Tabbas ne sai anyi tunda yake anbuga takarda da sunanka, amma yanzu abinda muke so da kai ka koma gida zuwa sati mai zuwa ka dawo idan ka yanke hukunci, suka kawo bandir din dari biyar suka bashi.

Nan fa ya kamo hanya zuwa gida hankalinsa a tashe, bayan da ya dawo gida kai tsaye ya wuce wajen wannan dan siyasa da ya tura shi wajensu, ya kwashe labarin duk abinda ya faru ya gaya masa bai boye masa komai ba, da wannan mutum ya bude baki sai ya ce SAU DAYAN KAWAI! Nan hankalinsa ya kuma tashi, ya ce wannan maganar taka tafi tayar min da hankali sama da wadda suka gayamin. Atakai ce dai wannan bawan Allah yana can yana more katafaren Albashinsa da sabon gidan da ya mallaka a babban birnin tarayya! Abin tambaya shi ne shin ya bayar da kansa kamar yadda aka nema ko bai bayar ba . . . . . . . . . Sanin gaibu sai Allah.

Ya ‘yan uwa wannan fa shi ne bala’I ko masifa da take zaune ta ke jiran da yawa daga cikin ‘yan uwanmu musamman masu neman aiki a gwamnatin Tarayya da manyan kamfanoni na gwamnatin tarayya . . .  wannan batu ko shakka babu kada ka ji ko dar haka yake faruwa a kusan Dukkan ma’aikatun da suke da maiko na gwamnatin tarayya wadan da ake kudancewa dare daya. Ya Allah ka kiyayemu ka karemu daga wannan tashin hankali, Allah ka yi mana katangar karfe daga fadawa wannan mummuna lamari, Lallai abin akwai ban tsoro kwarai da gaske Allah ya kiyaye mu ya kiyaye al’ummarmu.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Sunday, August 26, 2012

Yadda za a shawo kan matsalar Boko Haram


Yadda za a shawo kan matsalar Boko Haram

Matsalar Boko Haram, matsala ce da kowa yake jin tsoron yin sharhi akanta. Dalili kuwa shine jama’a na ganin muddin suka yi magana akan abinda ya shafi kugiyar watakila ‘yan Boko Haram din su kai masu hari. Amma kuma a matsayinmu na ‘yan Najeriya dole ne mu yi tsokaci dangane da abubuwan da ke faruwa a kasarmu da nufin neman hanyoyin warware wadannan matsaloli tunda yake al’ummarmu ce take shiga cikin tashin hankali da shiga halin kunci da kaka naka yi da asarar rayuka da dukiyoyi. .

Boko Haram ta somo asali yau kusan shekaru 4 da suka gabata, inda ake daukar jihar Borno da Yobe dake Arewa maso gabashin Nijeriya a matsayin hedikwatar su. Ana ganin aikace-aikacen ‘yan kungiyar da cewa kokari ne na ganin an kaddamar da Shari’ar Musulunci a Nigeria kamar yadda suka ce suna ikirari, amma kuma mun san da cewa babu inda addinin musulunci ya yi umarni da tayar da hankali domin samun biyan bukata. 

Hare-haren da Boko Haram ke kaiwa sun tsananta ne bayan kashe shugabansu 
Mohammed Yusuf da jami’an tsaron Nigeria suka a Yulin 2009. Tun a wancen lokacin ne ‘yan Boko Haram suka sha alwashin daukar fansa tare da yaki da duk wadanda suke ganin makiyin su ne, inda hare harensu suka faro daga Arewa maso gabas.

Yanzu haka dai abu yayi abu, kuma gumu tayi gumu, kowa ya ji a jikinsa, daga bangaren gwamnati da su kansu Boko haram din da kuma Talakawa bayin Allah wadan da basu san hawa ba basu san sauka ba, kuma galibi wadan nan hare hare daga bangaren gwamnati da kuma su ‘yan kungiyar ya fi shafa. Boko Haram na kai hari ta ko ina, duk dai a kokarin cimma manufofinsu. A lokacin da ya kai ziyara Amurka, Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya bayyana cewa yana neman a tattauna da ‘yan Boko Haram din, da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake samu a wasu sassan kasar. Sai dai bayan kalamin na sa, sai aka ambato tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan Nigeria Hafiz Ringim yana yin barazana ga ‘yan Boko Haram yana mai cewa karyar su ta kusan karewa, wanda wannan ya nuna baki biyu na gwamnatin Najeriya, shugaban kasa yana magana daban kuma sipeton ‘yan sanda shima yana magana daban, masu sharhi dai sunce kungiyar ta Boko harm ita ce tayi sanadiyar saukar da Hafiz Ringin daga mukaminsa na sipeton ‘yansand. 

Ana dai bayyana cewa wai wannan furuci ne ya tunzura ‘yan Boko Haram suka kai hari a hedikwatar ‘yan sandan Nigeria dake Abuja. Daga bisani kungiyar ta fitar da sanarwa tana mai daukar alhakin harin bam din da yayi sanadiyyar hasarar rayuwa da dukiya, da ma wasu karin tayar da bama bamai a sassa da dama na Arewacin Najeriya, musamman harin 20 ga watan Janairun wannan shekara da aka kai birnin kano.

To yanzu da aka zo wannan matsaya, ta yaya za’a tunnkari matsalar Boko Haram? Gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai tattauna da ‘yan kungiyar wanda daga bangaren kungiyar suka amince da Dr. Ibrahim datti Ahamed a matsayin mai shiga tsakani, sai dai daga baya tattaunawar ta watse sakamakon kwarmatawa ‘yan jarida tattaunawar da gwamnati ta ringa yi, wannan ya sa Dr. Datti ya janye daga sasantawar, kuma al’amuran kungiyar suka kara tsananta a yankin na Arewa.

Ni dai har yanzu banga wani wanda a yanzu ya lashi takobin cewa yana da wata cikakkiyar masaniya ba. Amma a matsayin mu na masu sharhi kan al’amuran da suka shafi kasar mu wajibi ne mu nemi amsa ga wasu mahimamman tambayoyi. Wadannan kuwa sune kashin bayan kawo al’amarin wannan kungiya, tambayoyin sune:

Menene ya janyo matsalar Boko Haram? Su wanene ‘yan Boko Haram? Ta yaya za’a fara tattaunawa da su domin neman sulhu, tattaunawa dorarriyar ba kamar wadda ta ruguje ba? Yaya shugabannin Nijiriya zasu kasance masu tausayin jama’ar su ta yadda jama’a zasu daina yi musu kallon makiya? Yaya ‘Yan Nigeria suke san makomar kasar a gajeren lokaci da kuma a shekarun gaba ya kasance? Wadanna matakai za’a dauka na zahiri wadan da zasu tabbatar da cewa lallai da gaske ake so ake a kawo karshen wannan al’amari na Boko Haram? Sannan su wa ke da alhakin mutanan da suka rasa rayukansu ta sanadiyar wannan al’amari?

Samun amsar wadan nan tambayoyi zai iya zama digon dambar kawo karshen wannan matsalata Boko Haram. Bayan mun yi wadannan sai mu hada da addu’ar neman Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu Nijeriya maidorewa.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Saturday, August 18, 2012

Harshen Hausa Na Ci-gaba Hausawa Na Ci-baya



 Harshen Hausa Na Ci-gaba Hausawa Na Ci-baya

Hakika a wannan karni na 21 Harshen Hausa ya samu ci-gaba sosai kuma me ma’ana. Tabbas duk wanda ya kalli irin yadda al’amura ke gudana a duniyar Harshen Harshen Hausa dole ya yi murna da cewar wannan Harshe yana kara samu ta gomashi sosai, misali ada can jaridar da take fitowa da Hausa akusan kasarnan ko ma ka ce duniya gabaki daya itace Gaskiya Tafi Kwabo wadda kamfanin buga Jaridu na Arewa ke bugawa na NNN, amma kuma yanzu adadin jaridun da ake bugawa da Harshen Hausa ya karu sosai da gaske, domin yanzu muna da jaridu da suke karade kasarnan baki daya kamar Aminiya da Leadership Hausa da Rariya da suransu, haka kuma ta bangaren mujalluma ansamu ci gaba sosai domin kamar yadda duk me bibiyar lamuran mujallun Hausa ya sani ya san  da cewa Mujallar Fim kusan itace mujalla daya tilo da take fitowa da Harshen Hausa amma yanzu adadi na mujallun Hausa na karuwa cikin sauri.

Hakika wannan yake kara nuna bunkasa da buwayar Harshen Hausa a tsakanin Harsunan Najeriya. Domin ko wane Harshe yana bunkasa ne ta hanyar rubuta shi da kuma karantashi, kuma wani abun farinciki shi ne adadin masu karanta Hausa shi ma yana karuwa cikin sauri, duk wanda ya ke bibiyar inda ake hada-hadar jaridun Hausa zaiga yadda ake wawasonsu, domin irin yadda Harshen Hausa yake da sauki a wajen Bahaushe akwai wadan da sun iya rubutawa tare da karanta Hausa ba tare da sunje wata makaranta sun koya ba, sabanin sauran Harsuna wadda sai mutum ya yi da gaske sanna ya kware wajen rubutu da kuma iya karantawa.

Wani bangare kuma da yake kara nuna bunkasar Harshen Hausa shi ne irin yadda ake samun sabbin kafafen watsa labarai masu watsa shirye-shiryensu da Hausa. Sanin kowa ne cewar kusan sama da shekaru 50 ana watsa shiri da Hausa a gidan radiyoyin kasashen Turai da Amerika kamar BBC HAUSA da DW HAUSA (docabele) da VOA Hausa (Muryar Amerika), amma ya zuwa yanzu adadin gidajen radiyon da suke watsa shirinsu ga duniya da Hausa shi ma ya karu domin yanzu akwai sabbin gidajen Radiyoyi kamar RFI Hausa (faransa) da Radiyo Taiwan da Radiyo Sin da Muryar Afurka na kasar Masar da sauransu. Duk wannan yana kara nuna mana cewa lallai Haurshen Hausa yana samun bunkasa da ci-gaba.

Haka zalika inda Harshen Hausa ya yiwa sauran Harsuna zarra shi ne, bayan karantar Harshen na Hausa kuma ana iya Nazarin Al’adun Hausawa da kuma Adabi (Language, Literature and culture) sabanin sauran Harsuna da dama, misali Harshen Turanci da ba’a iya nazarin al’adun turawa da sauransu, wannan ya tabbatar da cewar Lallai Harshen Hausa yana bunkasa sosai kuma ya tserewa sa’a.

Lallai kamar yadda muka fada cewar Harshen Hausa yana bunkasa, a gefe guda kuma Hausawa na ci-baya! Domin duk wanda ya kalli ko ya nazarci yanayin Hausawa yanzu zai ga cewa suna komawa baya ta fuskar wannan Harshe. Misali wadan da ake kallo sune ‘yan Boko basu Baiwa Harshen Hausa wani muhimmanci ba, hasalima kalilanne daga cikin ‘yan Boko wadan da zaka taras suna karanta rubuce-rubucen Hausa, ko yin rubuce-rubuce da Hausa, wannan ya ke kara maida Hausawa baya domin sun nuna fifiko akan wani Harshe sama da nasu wanda ya dara wanda suke kodawa.

Shakka babu wannan maganar haka ta ke ya dan uwa mai karatu, domin idan ka shiga Jami’o’inmu sai ka tarar cewar kusan daliban Hausa ne kawai ke mu’amala da takardun Hausa, daliban da suke karanta sauran fannonin kimiyya da tattalin arziki da fasaha duka da wahala kaga suna karanta wani abu na Hausa a jami’a sun gwammace su karanta takardun turanci ko da kuwa rabin abinda suka karanta zasu fahimta.

Kuma bayanai suna kara nuna cewar hattana daliban da suke karanta Harshen Hausa a jamio’I su kansu da yawa ba suna karanta Hausar bane domin it ace zabinsu na hakika. Wasu da dama suna karanta Hausa ne domin kodai basu ci kyakykyawan sakamakon jarabawar NECO da WEAC ba da zai iya basu damar karanta wani fannin na daban ko kuma abin nan ne da ake neman takardar shaidar kammala DIGIRI dan kare yawa, cewar nima nayi digiri ba wai dan hakika tun farko sun zabi su karanta Hausa ba domin bunkasar Harshen.

Wani abu da yake kara nuna cewar Hausawa na mayar da kansu baya ta fannin Harshen Hausa shi ne cewar, ko a jami’o’I da kwalejoji zaka samu Malaman Hausa suna yin amfani da Harshen Ingilishi wajen karantar da Hausa, sai kayi mamaki malamin da yake karantar da Hausa yana ta yiwa dalibai turanci, wasu malaman sukanyi haka ne suma domin kare yawa dan kada dalibai su dauki cewar malamin da yake karantar da Hausa bai iya turanci sosai ba, su kuma dan su kare kansu daga wannan kaskanci na dalibai sai kaji malamin Hausa ya zage yana ta turanci da dalibansa a cikin aji ko a wajensa, ko kuma suma Malaman neman burga ce da rashin kishin ainihin Harshen Hausar.

Haka kuma, ga duk mai bibiyar irin muhawarorin da ake tafkawa a shafukan sada zumunta na facebook da Twitter da Googl Plus da sauransu zai ga cewa galibi ‘yan Boko basa karanta Hausa ko yin rubutu da Hausa, mafiya yawan wadan da suke yin rubutu da hausa kodai basu iya turanci ba wannan ta basu damar yin rubutu da Hausa, ko kuma sun iya turanci amma basu kware ba, domin suma su kare yawar kada a yi musu dariya sai suyi rubutunsu cikin Harshen Hausa, ko kuma ka samu wadan da suke rubutu da Hausar irin wadan da suka koyi karatu da rubutu ne a sama.

Wata matsala kuma it ace ta yadda Harshen Hausa yake gurbacewa. Shakka babu Harshen Hausa yana gurbacewa sosai ta yadda zakaji Hausawa suna Magana da Hausa amma kuma a zahirin gaskiya turanci suke yi, domin kalmomin turanci suke fassarawa kai tsaye suke Magana da su, misali Bahaushe zai gaida kai sai ya ce maka ‘ya kake’ kaga a Hausa babu gaisuwa ya kake, kai turanci ne ko wani yaren aka fassara shi kai tsaye, da sauran irin yadda ake yiwa Harshen Hausa dandantsa irin haka.

Dole ne duk mai kishin Harshen Hausa ya ji kwarain gwiwa a duk lokacin da yaga mutane sun dauki wannan Harshe na Hausa da muhimmanci. Akwai mutanen da ko wasika ka rubuta musu da Hausa bazasu karanta ba, kuma Hausawa ne, amma duk irin maganar da ka rubuta mara ma’ana da rashin tsari indai da turanci ne sai kaga ana bata lokaci ana karantawa, Haka suma wadan da suke aiki da kafafen watsa labarai na Hausa da muryoyinsu suka cika gidajen Radiyoyi suma sunfi gwammacewa su yi maka rubutu ko karatu da turanci akan abinda ya shafe su.

Sannan yana daga cikin ci-bayan Hausawa kuma ci-gaban Harshen Hausa shi ne irin yadda ahankali wadan da ba Hausawa ba ke mamaye Radiyon Murayar Amerika. Ga duk wanda yake bibiyar Muryar Amerika yasan da cewar da Sunday Dare ne kadai wanda ba Bahaushe ba yake a wannan gidan radiyo harma ya zama shugaban sashen Hausa na VOA wanda abin kunya ne a ce wanda ba Bahaushe bane yake shugabantar irin wannan gidan radiyo na sashin Hausa, yanzu haka akwai akalla mutum biyu a wannan kafa ta Murayar Amerika wadan da suke karanta labarai da Hausa kuma ba Hausawa bane, ko shakka babu wannan ci-gaba ne ga Harshen Hausa kuma ci-baya ga Hausawa, domin zakaji suna fassara turanci da Hausa gurbatacciya irin yadda suka ga dama, tun Hausawa suna jin banbarakwai har ya zama jikinsu.

Sanin kowa ne, Babban abin da fassara ke bukata shi ne lakanta sosai ta harsunan guda biyu  wanda za ka yi fassara daga gare shi da wanda za ka fassara zuwa gare shi. sannan Yana kuma da kyau ka san wani abu na al’adun wadanda ke magana da wannan harshe, domin wani lokaci sanin ma’anar kalmomin kawai ba zai ba ka cikakkar fahimtar da kake bukata ba don yin fassara. A fassara kuma, ma’ana ce ya kamata a fi baiwa muhimmanci ba kalmomin da aka yi magana da su ba. Misali, Ingilishi da Hausa sun sha bamban da juna. Don haka, ba kome ba ne mutum zai iya fassarawa kai tsaye. Mu dauki bankwanan bature a lokacin tafiya barci, “Good night”; in aka fassara kai tsaye cewa za ka yi, “Dare mai kyau” abin da zai iya sanya Bahaushe yin dariya idan ya ji. Amma in ka fassara da “Sai da safe” ko kuma “Mu kwana lafiya”, to a sannan ne Bahaushe zai fahimce ka. Kuma bature yakan amsa “Good night” ne, ko kuma “Night” kawai, abin da zai kasance shirme a Hausa in ka fassara shi da “Dare” kawai. Shi ma bature zai ji abu banbarakwai idan ka fassara masa “Ina kwana?” kai tsaye.

A ‘yan kwanakin da suka gabata angudanar da gasar OLYMPIC a birnin landan kuma ‘yan najeruya sun shiga wannan gasa. Wani abu da ya bani mamaki shi ne daga cikin wadan da aka dauka domin nishadantar da ‘yan Najeriya da wakokinsu harda wani mai suna EMMANUEL wanda yana daga cikin masu waka da Hausa, anyi hira da shi a filin taba-kidi-taba-karatu na BBC Hausa, kuma ya yi waka da hausa, abin gwanin ban dariya kuma abin haushi domin na farko Hausar yanayinta tsararo wato a gaggatse, amma kuma bunkasa Hausar yake yi. Zaka samu yanzu Bahaushe dan Boko yafi jin kunyar ya yi kuskuren turanci akan ya yi kuskuren hausa, idan mutum ya yi kuskuren turanci aka yi masa gyara sai kaga duk ya damu, amma idan Hausa ce sai kaga ya zama abin raha da dariya.

Kamar yadda sauran Harsuna suke da ka’idar rubuta su haka ita ma Hausa ta ke da irin wadan nan ka’idoji wanda yanzu da yawan Hausawa babu ruwansu da kiyaye wadannan ka’idoji, misali, ka’idojin rubutun Hausa suna taimakawa matuka wajen saukaka karatu, da kuma saukakawa me rubutawa ko kuma me neman kwarewa, dan gane abin da kai kanka kake cewa, da kuma fahimta daga shi wanda kake rubutawa ko kuma karantawa idan misali Radiyo ne. Babbabn abu shi ne sanin yadda ake harhada bakake a tada kalma.

Hakan ya hada da sanin cewa idan ka hade kalmar da ya kamata ka raba za ta bayar da wata ma’ana daban da wadda kake so. Misali, idan ka rubuta “koyaushe” a matsayin kalma guda, ma’anarta na nufin kowane lokaci, amma in ka rubuta “ko yaushe...”, ka soma da yin tambaya ke nan, wanda watakila, ke bukatar kammalawa ko amsawa. Misali, “Ko yaushe Musa zai zo?” kaga wannan tambaya ce, amma Idan aka yi kuskuren rubuta wadda ba ita ba ce, to za a faro karatun ba daidai ba, sai daga baya a gane ashe ba haka ya kamata a dauko karatun ba.

Haka batun dangantaka ko mallaka. Idan ka ce “rigarta” kana nufin wadda ta mallaki rigar kenan, amma idan ka ce “rigar ta...” to mai karatu ko kuma mai sauraronka idan Radiyo ne zai jira ya ji abin da rigar ta yi. Salon karanta su ma daban yake. Da yake ba kowa ne ya san ka’idar rubutun Hausa ba sosai, shi ya sanya rubutun wani da Hausa, wanda aka yi ba kan ka’ida ba, yakan yi ma wani wuyar karantawa.

Lallai ne mu Hausawa mu sani duk wanda ya sha inuwar gemu bai kai ya makogaro ba. Domin duk wani wanda ba Bahaushe ba ya kaiga son ya bunkasa Hausa bai kai Bahaushe ba, domin akwai al’adu wandan da duk yadda mutum ya kai ga nakaltar Harshe ba zai iya saninsu ba idan dai ba harshensa bane, kuma dole Hausawa su nuna martaba da kimar Harshen Hausa wannan shi ne zai jawowa Hausawa martaba da kima a idan duniya. Tabbas karatun turanci abu ne da Duniyar Hausawa ta ke bukatarsa sosai da gaske, amma kuma wannan ba zai zama dalilin da zai zubar da ajin Harshen Hausa ba. Bahaushe yana cewa kowa ya bargida  . . .!
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Bikin Sallah Ba Bikin Nuna Tsiraici Ba Ne!



Bikin Sallah Ba Bikin Nuna Tsiraici Ba Ne!

Haka Allah yake ikonsa komai yayi farko tabbas koshakka babu yana da karshe, haka abin yake ga kowane irin lamari na rayuwa, Bayan kamala azumin watan Ramadan mai dumbin falala da tarin albarka sai kuma ashiga shagulgulan bikin karamar sallah. Hakika lokacin sallah karama lokacine na farin ciki da ciye-ciye da lashe-lashe tare da ziyarar dangi da sada zumunci tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki.

Haka kuma lokacin sallah lokaci ne da ya halatta ashariance asanya sabbin tufafi da fesa turare mai kanshi da sabbin takalma da dukkan wasu al’amura da zasu nuna wal-wala da jin dadi tare da iyalai ammafa bisa koyarwar sharia. Amma abin mamaki wani yanayi da muke ciki yanzu ko kuma zamani na nuna waye da kaiwa matuka wajen nuna burgewa da cigaba. Galibi lokacin bikin sallah samari da ‘yan mata kan fita ko zaga dangi da ziyarar ‘yan uwa ko kuma zuwa gurare na shakatawa da gwangwajewa ko kuma zuwa wajen wasu bukukuwa na gargajiya kamar hawan da masu martaba sarakuna kanyi a fadojinsu koma wani abin da ba wannan ba cikin shiga ta fitina da tashin hankali.

Abin da kamfaru yayin bikin sallah shi ne galibi da yawa yara ko kuma samari da ‘yan mata kan soma lalacewa ne a ranar sallah domin kuwa alokacin bikin sallah ne zaka ga mata da dinkuna na tashin hankali duk wai domin nuna burgewa, abin takaici shi ne iyaye kan sakarwa ‘ya ‘yansu mara alokacin bikin sallah suyi duk abin da suka ga dama babu kwaba, ba tankawa. Galibi abin yafi kazanta acikin birane inda zakaga ana bajekolin futsara da rashin kunya afili, samari anan ina nufin ‘yan mata kan fita cikin ado da kwalliya mai dauke da janhankalin duk wani baligi mai hankali, ta yadda wani lokacin sai ka kasa bambance tsakanin budurwa da matar aure, da yawan ‘yan mata kan fake da zuwa gun samari da sunan karbar goron sallah inda zaka iske budurwa ta je dakin saurayi cikin shiga mai motsa sha’awa wai da sunan taje karbar yawan sallah ne wanda shi kuma idan akayi rashin sa’a mara tsoron Allah ne yafito da kudi ya nuna mata amma ya ja hankalinta sosai kafin ya bata daga nan Allah ya kiyaye kaji labarai marasa dadi.

Da yawa daga cikin ‘yan mata kanyi dafe-dafe ga samarinsu da sunan barka da shan ruwa inda zaka ga dukkansu sunsha ado da kwalliya inda galibi akanyi amfani da wannan lokaci wajen aikata badala, wata budurwar idan tayi maka wata shigar zakaga batada maraba da tsirara kuma ta fita gaban iyayanta duk da sunan murnar sallah, haka kuma abin bai tsaya ga samari ‘yan mata ba harda kana nan yara inda zaka ga an caba musu ado da kayayyaki masu ban sha’awa da kayatarwa wanda anan ma ana samun bata gari masu fakewa da daukar yarinya da sunan zasu bata goron sallah su kaita dakinsu daga karshe kaji labarin aikata badala da ita; lallai Manzon Allah ya yi gaskiya inda ya ce a karshen lokaci mata za su ringa yawo da kaya amma a tsirara suke yace kasiyatun ariyatun .

Kamar yadda nace yara da yawa na fara lalace wane alokutan da ake bukukuwan sallah domin anan ne kanan yara kan koyi zukar taba sigari samari kuma da suke dan busa taba kan cigaba zuwa busa tabar wiwi, ‘yan wiwi da shalisho kuma kan kurba ruwan  kamru uwar laifi, haka kuma a wannan lokacin akan motsa sha’awa tsakani samari da ‘yan mata wai da sunan Happy Sallah, wanda daga nanne yara kan zarce da fitsara da rashin kunya domin kuwa galibi samari da ‘yan mata kowa da dan kudi a kugunsa sukuma mata ga kwadayi da son abin duniya, zaka ga yarinya bata iskanci amma arudeta da cewa yau kawai akarshe kaga shaidan yayi rinjaye yarinya ta bada kanta.

Haka abin yake idan kaje gidajen shakatawa inda zakaga abin ma yafi muni anan gurin domin guri ne inda kowa bashi da mafadi galibi abubuwa marasa dadin ji kan faru a irin wadannan gurare na shakatawa, musamman ma idan akace akwai dan karamin kududdufi da zaka shiga kayi linkaya inda zaka iske karti mata da maza cikin ruwa wai suna wasa ko kuma yana koya mata ruwa Allah ya kiyaye.

Haka kuma lokacine da ake fitowa kallon sarki akan fito cikin ado da kasaita da nuna bajinta da iya kwalliya da yawan iyaye kanbar ‘ya ‘yansu zuwa kallon sarki amma basu san irin illar da hakan kan haifarba domin guri ne da ake cika mata da maza babu wani guri da aka ware na maza daban ko na mata daban a gwamatse ake tsayuwa irin munanan abubuwan da suke faruwa a yayin hawan sallah kunne bazai so jinsu ba.

Anan nake son nayi amfani da wannan dama nayi kira na farko ga samari musamman ‘yan mata da maza da suji tsoran Allah sudaina shiga mai bayyana tsiraici da surar jiki, kusani mutuncinku shi ne ku sanya sutura ta gari wadda zata suturce jiki gaba daya, kuma wallahi kisani ko dan iska burinsa shi ne ya auri tagari ba sai kin nuna albarkar jikin ki zai sa samari su soki ba, duk wani saurayi daya rudeki da cewa shigarki tayi kyau kisani wallahi yaudararki yake yi, Don Allah ayi shiga da ta dace da Addininmu da kuma al’adarmu kisani komabayan tunani ne kiringa kwaikwayon turawa da indiyawa.

Haka kuma ina kira ga tailoli da suji tsoron Allah aduk al’amuransu kuma su sani cewa zasu kasance ababen tuhuma ranar gobe kiyama a wajen Allah, domin  sune suke bada wannan damar ga ‘yan mata ta nuna albarkar jiki, ta hanyar yi musu dinkuna na tashin hankali.

Abu na uku shi ne Iya ye yaka mata su sani ‘ya ‘ya fa amana ne Allah ya baiwa kowane magidanci kuma zai yi masa tambaya akan yadda ya gudanar da harkar iyalansa. lallai ne asanya ido sosai akan yara aga ina suke zuwa kuma wace irin suturace ke jikinsu kuma su wane suke yawo tare dasu idan har sukayi haka wallahi sunyi abin daya dace kuma zasu kubuta har gaban Allah, dafatan za’akiyaye da wdan nan ‘yan shawarwari nawa, kuma Allah yasa ayi bikin sallah lafiya agama lafiya Allah kuma yasa ibadun da mukayi awatan Ramadan karbabbune.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Monday, August 13, 2012

Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #5



Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #5

Bayan sallama irin ta addinin musulunci Assalamu Alaikum Warahmatullah, Ya ‘yan uwa masu girma, ina yi mana barka da sake saduwa a wannan makon, kuma mako na karshe a cikin wannan wata mai albarka na Ramadan, da wannan shafi ya kwashe kusan makwanni yana kawo muku maudu’in da muka ambata a sama, hakika wannan ita ce ranar Litinin ta karshe a wannan wata da muka shafe lokaci muna azumtarsa, muka kara kusanta kanmu zuwa ga mahaliccinmu Subahanahu wata’ala.

Kamar yadda Bahaushe ke cewa komai ya yi farko shakka babu zai yi karshe. Tun kafin zuwan Ramadan da kwanaki koma watanni muke ta addu’a Allah ya nuna mana wannan wata, to dai yau gashi muna cikin kwanakin da muke karkare wannan ibada ta Azumi, mun dauki lokaci muna kauracewa ci-da-sha da jima’i da tundaga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana ba don komai ba sai dan gasgata alkawarin Allah, sai dan gasgata sakon da Allah ya turo ManzonSa Salallahu Alaihi Wasallam da shi, muna kara shaidawa babu abin bauta da gaskiya bisa cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne.

Ya ‘yan uwa masu girma, saninmu ne mun shafe tsawon wadan nan kwanaki muna karatun al-qur’ani da salloli na nafila da na farilla da zikiri da yawan addu’o’i. Ya ‘yan uwa lallai mu sani Ramadan makaranta ce da ba’a kammalata har sai randa wa’adi ya tsaya akanmu, lallai wa’azozi da darusan da muka koya ba wai kawai zasu tsaya a iyakar kwanakin Ramadan bane kawai, a’a zasu dore ne har iyakar karshen Rayuwarmu, mu yawaita karatun al-qur’ani da sallolin nafila da addu’o’i kamar yadda muka yi a Ramadan.

Wasu da yawa sunan nan sunyi ibada karbabbiya, kuma Allah ya yarda da su, ya yi musu rahama daga cikin rahamarSa subanahu wata’ala, saboda sun mika lamuransu ga Allah, sun karanta al-qur’ani sunyi kuka sun zubar da hawaye, sunyi azkar safe da yamma. Muna fatan Allah ya sanya muna daga cikinsu. Wasu kuma suna nan babu abinda suka yi illa wahalar da kansu da kishirwa da yunwa domin da dama wasu Azumin da yake bakinsu bai hana su karya da yaudara da cin-amana da cin mutunci ba da gulma da kinibibi da yaudara da sata da kisan kai da zina da shaye-shaye! kai wasu ma Azumin da suke bai hanasu kallon fina finan batsa da kallon tsiraici ba, muna rokon Allah ya sa bama daga cikin wadan nan mutane. Hakika mun aikata kurakurai da dama acikin wannan wata mai albarka, muna rokon Allah ya yafe mana kurakuran da muka aikata, wadan da muka sani da wadan da bamu sani ba.

A yayin da muke shirin bankwana da wannan wata na Ramadan, muna kara kusantar lokacin Idin karamar sallah ne (Idil Fitr) jama’a da dama hankalinsu yanzu ya karkata zuwa ga hidundumun da suka shafi masalar duniya, wato kayan sallah da kuma irin kayan tande-tande da lashe-lashe da ake ta kokarin tanadi domin bikin sallah tare da iyalai da ‘yan uwa da abokan arziki, lallai ba haramun bane a musulunci muci me kyau mu sha me kyau kuma mu sanya sutura mai kyau.

Ya ‘yan uwa masu girma, kamar yadda mukaji malamai suna fada daga manzon Allah salallahu alaihi wasallam cewar, a wadannan kwanaki goma da suka rage ne ake sa ran dacewa da daren lailatul kadari, wanda Allah ya ce alkhairinsa ya fi na watanni dubu, haka kuma wannan dare ana sa ran dacewa da shi ne a kwanakin da ake kira wuturi, wato 19, 21, 23, 25, 27, 29 lallai yanzu kwanakin da suka rage mana sune 27 da 29 kada mu yi sake da wadan nan kwanaki lallai mu dage da addu’o’i da rokon Allah dukkan bukatnmu na alkhairi.

Daga karshe, ina mai amfani da wannan damar wajen rokon Allah ya yafe mana kurakuran da muka aikata a cikin wannan watan wadan da muka sani da wadan da bamu sani ba, Allah ya sa ibadunmu karbabbu ne, Allah ya sa muna daga cikin wadan da Allah ya yarda da ayyukansu a cikin wannan wata; halin da muke ciki na zullumi da tashin hankali a wannan kasa tamu muna rokon Allah ya yaye mana ya bamu lafiya da zaman lafiya, Ya Allah muna tawassali da wannan ibada da mukayi, muna tawassali da kyawawan sunayanka tsarkaka madaukaka Allah ka dawo mana da zama na aminci acikin garuruwanmu, Allah ka bamu zaman lafiya mai dorewa.

Hakika baza mu manta da ‘yan uwanmu da suke a asibitociba cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai, Ya Allah ka basu lafiya, mu da muke da lafiya Allah ka kara mana lafiya, ‘yan uwanmu Musulmi da suke cikin matsanancin hali a kasar Syria da Burma da Afghanistan da Iraqi da Somalia da duk inda musulmi suke Allah ka amintar da su, Allah ka kaimusu dauki. Allah ya yafewa wadan da suka rigamu gidan gaskiya mu kuma Allah ya kyauta namu karshen.

Har ila yau zanyi amfani da wannan damar domin yin godiya ga hukumar gudanarwa ta wannan gida mai albarka bisa wannan dawainiya da suke na kokarin tunasar da al’ummar kulluma rana, Allah ya saka da alheri, haka kuma ina addu’ar fatan alheri ga abokanan da muke gabatar da shirye-shirye tare da su Allah ya sakawa kowa da alheri. Haka suma zaratanmu kuma sarakan aiki wato Auwal Adamu Tahir Sabon Gida da Aliyu Danlabaran Zaria wallahi babu abinda zamu ce da ku sai godiya da fatan alheri, wannan zumunci da mukayi Allah ya sa ya dore har zuwa ga ‘ya ‘yanmu da jikokinmu, sannan shima madugu uban tafiya yayanmu Mallam Muhammad MK hakika bakinmu ya yi kadan wajen nuna godiyarsa da farincikinsa a gareka, hakika ka cancanci a gaishe ka da dukkan gaisuwa irin ta girmamawa bisa wannan muhimmin aiki, Allah ya saka maka da alheri, ya yawaita mana irinku acikin al’umma, Allah ya sanya albarka a cikin rayuwarka da rayuwar iyalinka da zurriyarka, Allah ya sakawa kowa da alheri.

Wassalamu Alaikum Warahmatullah.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale