SAKON TAYA MURNA GA MAI DARAJA SARDAUNA KANO
Ina amfani da wannan dama, a wannan rana, a madadin Ni Yasir Ramadan Gwale da mai daki da dangi baki daya, wajen taya Jagoranmu Mai Daraja Sardaunan Kano Malam (Dr.) Malam Ibrahim Shekarau bisa wannan ni'ima da Allah yayi masa, na cika Shekaru 60 cikin koshin lafiya.
Ba shakka, duk wanda rayuwarsa ta tsawaita zai ga al'amura masu yawa, mabambanta. Da yawa an haifesu kuma sun rayuwa, amma mutuwa ta yanke musu hanzari basu iya kaiwa ko cika shekaru 60 a duniya ba, wasu kuma na nan cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai. Muna yiwa Allah Subhanahu Wata'ala godiya da ya baiwa ubanmu kuma Jagoranmu Malam Ibrahim Shekarau aron lokaci har ya riski wannan muhimmin taqi a rayuwarsa.
Mai Daraja Sardauna Kano, Allah ya bashi dama wajen hidimtawa al'umma a cikin wadannan shekaru, wanda kuma har yanzu akan wannan bigire yake na yin hidima ga wannan al'umma tamu. Allah ya yi masa jagora, ya sanya masa alheri a Shekarunsa da zasu zo nan gaba. Kurakuransa na baya Allah ya yafe masa, muma ya yafe mana namu baki daya.
Yasir Ramadan Gwale
05-10-2015

No comments:
Post a Comment