GWAMNONI NA WADAKA DA KUDIN AL'UMMA SUNA KIRAN BA KUDI
Abin mamaki ne Gwamnonin Nigeria da suke wadaka su ci su sha a kudin Al'umma, wai ba zasu iya biyan mafi karantar Albashi ba. A cikinsu fa babu wani Gwamna da ya rage irin wadakar da yake da dukiyar al'umma, kowa wane Gwamna idan kaga yadda yake dibar 'yan rakiya a yawace yawacensa bai rage ba, ga shatar jirgi da suke dauka ba kan gado, tafiya Kano zuwa Abuja Gwamna zai dau shatar jirgi ya kwashi mutane cikin dukiyar al'umma. Ko a satin da ya gabata Gwamnatin Kano Shatar Jirgi sukai aka kwashi mutane zuwa Adamawa daurin auren wani Kwamashina cikin dukiyar al'umma.
Ga wani yawon karya da Gwamnonin suke fita kasashen waje wai kiran masu zuba jari jihohinsu, cikinsu kuwa har da Gwamnan Yobe wai yaje Japan da China yana kiran 'yan Kasuwa su zo Yobe su zuba jari, shin wannan ba wauta bace da barna da dukiyar al'umma, ko tsammanin Gwamna su 'yan kasuwar basu san me ke faruwa a Yobe ba? Shugaban Gwamnonin Najeriya Abdulaziz Yari kullum a tafiye yake yana yawace yawace a jirgin shata, Yaki zama ya yiwa al'ummar sa aiki. Tun daga hawansu mulki babu wani Gwamna da bai je kasar waje ba da sunan ziyarar Bogi wai ta Kiran masu zuba jari?
Gwamnan Bauchi har wata ziyarar bige yaje Jamhuriyar Czech wai kiran yan Kasuwa, shin 'yan Kasuwa nawa ne suka zo Bauchi daga Czech? Haka nan fa, Gwamnan Katsina da yake ta korafin ba a yiwa Jihar komai ba, ya kwashi kudi zai gina Hotel a inda baida amfani, shin wannan Hotel din ita ce Bukatar talakawa a Katsina? Ya kamata Gwamna ya sani yanzu lokacin aiki ne domin amfanin al'umma ba amfanin wasu tsirarun ba.
Gwamnan Kaduna da ya kaddamar da wasu dankara dankaran motocin haya a Kaduna wannan ba barna ce da kudin al'umma ba? Shin wannan motocin al'umma suka fi bukata? Kaduna din da suka ce tayi shekaru 16 babu tituna masu kyau a cikin gari, kuma shi ne za a kawo tsala tsala motocin da aka saya da kudin al'umma dan kawai su lalace a cikin shekara guda? Wadannan Gwamnonin ba su da tausayi idan har suka tabbatar da wannan batu na kin biyan mafi karancin Albashi, a lokacin da rayuwa take kara tsada.
Farashin komai ya daga, kud'in buhun shinkafa ya haura dubu goma, kayan masarufi duk sunyi tsada, mai yayi karanci kuma yayi tsada, rayuwa ta tsananta ga al'umma, basa neman mafita dan ce to al'umma daga halin kangi da mawuyacin hali sai wadakarsu suke yi? Bama yi musu Hassada su ci kaji su hau zunduma zunduma motoci daga cikin dukiyar al'umma, amma ya dace suji tsoron Allah su tausayawa al'umma, ana rayuwa hannu baka hannu kwarya, komai ya tsananta ga al'umma, ace dan Albashin da bai taka kara ya karya ba, ace wai ba zasu iya biya ba. Haba Nigeria har tayi tsiyacewar haka dan Allah. Da ace ana yin Mid-term election a Nigeria da Gwamnonin sun sha mamaki.
Ya kamata kowanne Gwamna ya dakatar da duk wasu yawace yawace da suke a Abuja na ba gaira babu dalili suna kwana a Hotel da katuwar tawaga su tsaya su duba abinda ya dace da zai kawowa jihohinsu cigaba da zai amfani rayuwar al'umma da suka fito suka zabe su, haka nan tafiye tafiyen da suke zuwa kasashen waje na rashin lissafi dole su dakatar, a tsara gudanar da rayuwar al'umma cikin ingataccen yanayi da kwanciyar hankali da karuwar arziki. Allah ka fid da mu daga wannan mawuyacin hali.
Yasir Ramadan Gwale
20-11-2015

No comments:
Post a Comment