MUTUWA DAYA CE IDAN AN TAFI BABU DAWOWA
Sau da yawa wasu mutane kan rud'a kansu, ta hanyar gaggawar bayar da labarin da hankali ba zai kama ba. Ga duk mutumin da yake da lafiyayyane hankali, ai ba yadda za a tabbatar da mutum ya mutu, sannan wani Wustaz yace wai zai masa addu'ah ya tashi, kuma wasu su yarda, har ana gaggawar yadawa cewar wane bai mutu ba. Hankali ba zai kama wannan ba, banga dalilin da mutane zasu dinga gaggawar yada irin wannan magana da ba gaskiya ba. Da ana Mutuwa a dawo ko a yiwa Gawa addu'ah ta tashi, da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam har yanzu yana raye. Wanda duk ya mutu kwanan sa ya kare, kuma ya tafi kenan.
Audu dai ya mutu, kuma an binne shi. Ya rage namu, shi kam zai riski abinda ya aikata, muna masa fatan Allah ya yafe masa. Dan haka koda yaushe mutuwa take zama wa'azi ga wanda yake raye, a talaka da mai mulki duk mutuwarsu wa'azi ce, domin tabbaci ne, kowa zai riski lokacinsa, ya sani ko bai sani ba. Mai hankali shi ne yake daukar izna, duk lokacin da yaji anyi mutuwa, dan ya kara jin tsoron Allah ta hanyar kiyaye dokokinsa, da neman Rahama da GafararSa Subhanahu Wata'ala. Allah ka jikan mamatanmu, Allah ka kyauta karshen, ka yafe mana kurakuranmu da laifukanmu.
Yasir Ramadan Gwale
23-11-2015
No comments:
Post a Comment