DOMIN MAGANCE MATSALOLIN TSARO GWAMNONIN AREWA SU YI KOYI DA JIHAR GOMBE
Jihar Gombe na daga cikin jihohin da suka sha fama da matsalolin tsaro,
kama daga na tashin bama ba ai musamman a tashoshi mota da kasuwanni da
kuma hare hare kuna bakin wake. Gwamnatin Gombe karkashin jagorancin
Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, ta yi himmatu wajen ganin ta shawo kan
tare da kawo karshen matsalolin tsaro a jihar. Bayan tattaunawa da kuma
yin Nazari mai zurfi na bin hanyoyin da za a shawo kan matsalolin tsaron
a jihar. Gwamnatin ta yi wani tsari na dauko hanyar mutanan da ake kira
Civilian JTF da suke Maiduguri domin taimaka musu a sha'anin tsaro.
A dan haka ne Gwamnatin Gombe, tayi musu tsari
na kula da walwalarsu da basu alawus mai kauri domin wannan aiki.
Gwamnatin ta zabe mutane masu Amana, da fatan ganin zaman lafiya ya
dawwama a Najeriya ta zuba su a cikin gari a matsayin masu talla ko masu
goge takalma, amma suna lura da motsin kowa dan haka da zarar sunga
mutumin Borno ko wani Kanuri da suke da shakka akansa zasu cunawa
Jami'an tsaro, haka kuma, suna nan a unguwannin da yawa suna yawo a
matsayin masu talla. Da farko Gwamnati ta so ta basu motoci da babura,
suka shaida mata aikin nasu baya bukatar wannan.
A ranar farko da
wadannan mutane suka fara aiki a Gombe, sai da suka gano gidaje kusan
biyar a cikin garin Gombe da ake kera Bom, kuma sun kama Bamabaman da
aka kera sama da guda dari, bayan an cafke mutanan da suke wannan
danyan aiki. Wannan tasa, Gwamnati tayi Nazarin irin hadarin aikin, kuma
gashi ba ma'aikata bane na din-din-din da suke da fansho da garatuti,
dan haka ne, Gwamna yayi umarnin baiwa wadannan CJTF alawus na Naira
dubu goma a kowacce rana, dan haka Gwamna yace duk sati za'a dinga
biyansu wannan alawus.
Cikin taimakon Allah, tunda Gwamnatin
Gombe tayi wannan tsari har yau Bom bai kuma tashi a Gombe ba. Ba shakka
wani tsari abin yabawa ne, duk da cewa rayuwa da mutuwa duk a hannun
Allah suke, amma yana daga cikin wajibin hukumomi tsare jini da dukiyar
al'umma. Kuma wannan tsari yana da kyau sauran Gwamnatocin Arewa su
kwaikwaya, domin tsare rayuka da dukiyar al'umma. Girma da daraja ta Ran
dan Adam tafi dukkan abinda za a baiwa mutanan a matsayin alawus. Dan
haka, nake kara jinjinawa Gwamnatin Gombe karkashin Gwamna Dankwambo
akan wannan hobbasa da tayi domin kula da tsaron rayukan al'umma. Anan
nake kira da Babbar murya ga sauran Gwamnatocin jihohin Arewa musamman
wadan da suke fama da wannan matsala ta tsaro da su yi koyi da gwamnatin
jihar Gombe.
Domin ko da Gwamnatin tarayya tayi nasarar
fatattakarsu daga dajin Sambisa, to wannan ba shi ne yake nuna kawo
karshen 'yan ta'adda masu tayar da Bamabamai ba, tilas ayyukan tsaro
karkashin jihohi ya cigaba domin amintar da al'umma a gidajensu da
masallatai da guraren kasuwancinsu. Haka nan sauran Jami'an tsaro masu
kaki, tilas a kula da walwalarsu da basu hakkokinsu akan kari domin
samun karsashi da kuzarin yin aiki dan kula da ayyukansu na wajibi da
kuma basu kwarin guiwa ta hanyar ziyarar su da karfafa musu guiwa. Allah
ya tabbatar mana da zaman lafiya mai dorewa a jihohinmu da kasarmu baki
daya.
Yasir Ramadan Gwale
28-11-2015
28-11-2015
No comments:
Post a Comment