HARIN BOM DIN DA AKA KAIWA 'YAN SHIAH MASU TATTAKI
Da yawan mutane wanda suke cewa su ba Shiah bane, kuma su ba Wahabiya ko 'yan Izala bane, suka cika facebook da surutu wai an kaiwa 'Yan Shiah hari, amma 'yan Izala sunyi shiru sun ki Jajantawa. Abin ya bani mamaki kwarai, idan banda san Jan magana ina ruwanka, da zaka sa dole sai wani yayi magana akan abinda bai shafe shi ba? Hakkin Gwamnati ne kula tare da tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar da ta ke shugabanta, da ya kamata masu wancan zargi su fara yiwa Gwamnati magana akan me yasa bata jajanta musu ba a matsayin su na 'yan Najeriya da alhakin su yake kanta.
Ai sanin kowa ne, kuma a bayyane yake a cikin Karantarwa Malaman Sunnah anyi dukkan dangi Allah wadai da tashin hankali da kisan al'ummar da basu san hawa ba basu san sauka ba, wannan ce ta sanya sam baya daga cikin manufofin Ahlussunnah fita zanga zanga domin baiwa rayuwa kariya. Malamanmu sun cika duniya da karatuttuka da bayanai da Jan hankali akan masu kisan kai babu ji babu gani, kowane malamin Sunnah indai yana da'awa sai ka ji ya fadakar akan illa da nauyin hukuncin kisan al'ummar da ba su da laifi ba.
Amma sabida abin san Jan magana, sai wani dan taratsi, ya zakalkale wai shi 'activist' ko 'liberal' yana fadin har yanzu banji 'yan Sunnah sun Jajantawa 'yan Shiah ba. Kuma fa karya yake, sau nawa Malaman Sunnah suke zuwa asibiti domin Jajantawa wanda harin Bom ya shafa dan kawai nuna tausayawa da jin kai, amma ba hakkin su bane sai sunyi hakan, wasu lokutan ma har tallafi suke bayar wa. Kuma akan wannan hari Shugaban Majalisar malamai na kungiyar Izala ta kasa Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ya fitar da sanarwar ja je ga wanda abin ya shafa, ya nuna musu jin k'ai irin na DanAdamtaka, amma duk wannan bai wadatar ba. Haka kuma, ni tunda nake ban taba ji ko ganin inda El Zakzaky ya Jajantawa al'ummar da harin Bom ya shafa ba, balle kuma duba su, sai akan TATTAKIN da ko a shi'ah ma baida Asali, wai akansa ne mutane ke da bakin magana.
Kuma idan akwai wanda za a zarga a wannan lamari bai wuce Zakzaky ba, domin duk sanda zasu yi taro sai yace za a kawo musu hari, amma duk da haka ya kafe ya kirawo mutane su fito, ai da yana da tausayi da jin k'ai, idan ya samu rahotannin da yace yana samu na kai musu hari, da kamata yayi ya dinga tausayawa mata da yara, a dinga dauke musu zuwa a duk lokacin da yake jin za a iya kai musu farmaki, amma a haka sabida zalinci zai kirasu, mata da d'anyan goyo wasu da katon ciki, ga yara kanana suna ja a hannu, amma haka zai tilasta musu fitowa. Tsakanin mu da shi waye mugu mara tausayi?
A baya har aka biyo Malaminmu Dr. Ahmad Gumi aka sa masa Bom Allah ya tsare shi, amma bamu 'yan Shiah ko Zakzaky dayansu ya jajanta masa ba, haka aka je har masallacin 'yan taya a Jos wajen karatun Malam Sani Yahaya Jingir aka jefa masa Bom, tare da bude wuta akan bayin Allah dake halarce a wajen karatun, bamu ji Zakzaky ko wani dan Shiah ya jajanta masa ba, sannan kuma ka zarge mu wai dan me bamu jajanta musu ba? Me kake so kace? Idan kace Ahlussunnah ne suke yi, sai muce ka dai fake ne kana so ka soki Musulunci ne, saboda su masu yin wancan d'anyan aikin, Domin kuwa Ayoyi da hadisai suke jawowa suce su ne dalilinsu akan ta'addancin da suke wa al'umma, kenan kana son ka soki ayoyi da Hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam cewa su ne suke kunshe da waccan mugunyar koyarwar?
Haka kuma, wani abu da zai sake barrantar da Ahlussunnah daga Tafarkin 'yan ta'adda, shi ne babu wani cikinsu da ke cikin Iftila'i da yake kiran YA MUHAMMAD SAW a matsayin maceci a cikin irin wancan hali, sai dai kaji suna kiran YA HUSSEIN suna neman cetonsa. Dan haka, ko dan gaba, ba alhakin mu ba ne Jajantawa duk wanda harin Bom ya shafa? Wannan hakkin hukumomi ne, su ya kamata ka fara yiwa zargi ba wanda kake gaba da su ko kinsu ba. Baya daga cikin manufofin Ahlussunnah zubar da jini, ko waye yayi haka, ba koyarwar Sunnah bace, kuma ya sabawa Karantarwa sunnah ko da ya jingina kansa da Sunnah. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya.
Yasir Ramadan Gwale
30-11-2015
Wannan gaskiya ne, Duk wani basalafe ko ma a wacce kungiya yake ko ba shi da kungiya ba maso tashin hankali bane.
ReplyDeleteTo wai ko cewa muku kayi (dukkan Ahlussunnah ) ba abinda ya yi manager zafi da dukkan bala'in da zai samu Shi'a munyi laifi ne?