RADDI AKAN FATAWAR MALAM AMINU GAMAWA KAN ZABEN MACE
Addinin Musulunci shi ne addini a wajen Allah, duk wani addinin da ba shi ba b'ata ne kuma tab'ewa ce. Babu wani abu da Musulunci ya bari bai yi bayani ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam kafin yabar duniya yayi bayanin komai da ya shafi al'amarin Musulmi, musamman Al'amari na shugabanci da Amanw da adalci da zamantakewa da kasuwancin da sauransu. Haka zalika Manzon Allah ya fada cewar "Halal a bayyane take haka ma Haram a bayyane take", Allahumma sai dai abinda Shari'ah tayi shiru akansa kuma malamai sukai sabani akai. Amma duk lokacin da sabani mai girma ya bayyana game da hukuncin wani lamari, abinda Musulunci yayi umurni da shi shine a koma ga Alqur’ani da Hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa sallam don samun mafita.
Jiya naga wata sabuwar fatawa da Malam Aminu Gamawa ya fitar, inda ya bayyana cewar "Munafuki shi ne wanda ya taya Matar Taraba murna ta samu zabe, sannan idan mace ta tsaya zabe a jihar sa ba zai zab'eta ba" Haka Aminu Gamawa ya bada wannan fatawa mai cike da hatsari, domin fatawa ce da kai tsaye ta ke kunshe da kafirta musulmi. A hakikanin gaskiya wannan ba karamin kuskure bane sauyawa abu fassara domin ta dace da son ran mutum akan abinda yake son ya zargi wasu. Haka kuma, irin wannan fatawa ta 'yan boko, tana daga cikin manya manyan sabubban da suke haifar da fikrar khawarijanci, domin tana kara k'aimi ga masu wuce gona da iri a addini, su samu abin fakewa da cewa 'yan boko suna 'bata addini da fikrar yahudawa ko yammacin duniya.
Kai bama batun Musulunci ba, hatta a Demokaradiyya Aminu Gamawa ya tafka babban kuskure, wanda girmansa ya kai ayi Allah wadai ga duk wanda ya furta wannan magana. Domin a tsari na Demokaradiyya, dama ce da aka baiwa duk wanda ya isa jefa kuri'a, ya zab'i wanda yaga dama ko kuma yafi gamsuwa da manufofinsa domin ya Shugaban ce shi ko ya wakilci shi. Ta ina mutum zai zama Munafuki a Demokaradiyyance idan yace shi ba zai zabi mace ba? Shin akwai wata ayar doka a kundin Demokaradiyya da ta ce duk wanda Ya'ki zab'en mace ya zama Munafuki, kamar yadda Aminu Gamawa ya kawo? Bana zaton ko shi kansa Malam Gamawa zai iya kare kansa da hujja me karfi akan wannan ikirari da yayi na cewa wanda duk Ya'ki zab'ar mace a matsayin Gwamna a jihar sa ya zama Munafuki?
Haka kuma, kalmar MUNAFUKI hukunci/kalma ce da Musulunci yayi bayanin ta filla-filla. Baya ga Ayoyi masu tarin yawa da suka yi bayani akan ta, akwai sanannen Hadisi sukutum da gudu, wanda ga duk wanda ya halarci makarantar Islamiyya ya san shi, wanda nayi Imani a matsayin Aminu Gamawa na tsohon Dalibin Sheikh Ibrahim Gomari ya san wannan hadisi? Shin ya akai Aminu Gamawa ya sauyawa wannan hadisi fassara ko ma'ana kawai dan ta dace da abinda yake son yin suka akai? Ta yaya akan Demokaradiyya zaka kifa Musulmi har abada a cikin wutar Jahannama can kasan ta? Idan Malam Aminu Gamawa ya gafala ne to lallai ya sani, abinda kalamin sa ke nufi kenan fa da fassarar da ya kawo kan zaben matar Taraba: wanda Yaki zaben Mace Gwamna a jihar sa ya zama Munafuki kai tsaye ba tare da wani kwane kwane ba, wannan shine zahirin abinda maganar ke nufi.
Lallai ina amfani da wannan damar, in jawo hankalin Malam Aminu Gamawa da ya janye wannan magana tasa, kuma ya nemi gafarar Allah akan abinda ya aikata na kuskure, Allah mai afuwa ne yana son Afuwa, amma cigaba da tafiya ko kafewa kan wannan magana/mahangar kuskure ne babba, ba a Musulunci ba kadai, hatta a ita kanta Demokaradiyya din da Malam Aminu Gamawa yayi wannan magana akanta. Domin duk mai zab'e yana da ikon zab'ar abinda yaga dama a Demokaradiyyance bai aikata wani laifi ba, tunda doka ce ta bashi dama. Ya Allah ka nesanta mu daga sharrin kawukanmu, ka yafe mana kurakuranmu wad'anda mukai muna sane da wad'an da mukai bisa ganganci.
Yasir Ramadan Gwale
08-11-2015
No comments:
Post a Comment