RANAR ASHURA: A Galibin kasashen larabawa da gabashin Afurka, watan Zul-Hajj ya kare a 29 ne da ya gabata, inda a lissafi yau Juma'a ta zama 10 ga sabon watan Muharram Hijira 1437 (Ashura). Yayin da a Najeriya watan Zul-Hajj ya cika kwana 30 dan haka yau Juma'a ta zama 9 ga watan Muharram (Tasu'ah). Malamai da dama sun sha yi mana bayani akan ranar Ashura da falalar azumtarta a addinin Musulunci, a gefe guda kuma, Malamai kan fadakar akan wata gagarumar Bid'ah wanda b'ata ne mabayyani da 'yan Shiah suke yi kuma suke jingina shi ga Musulunci. Dan haka, kamar yadda malamai suka sha fadakar da mu kusan duk Shekara a irin wannan lokaci, duk abinda 'yan Shiah suke yi bata ne kuma kafurci ne, ba Musulunci bane, ba kuma koyarwar addinin Mu lunch bane. Waki'ar da ta faru ga Jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam Alhussain Ibn Aliyu Bin Abi-Talib, Malamai sunyi bayani da dama akai, wannan kokarin jingina kansu da Hussain Ibn Ali Allah ya kara yarda da su shi da mahaifinsa, karya Shiah suke ba suda Alaka da su ko ta kusa ko ta nesa, hasalima su Shiah suka kashe jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Ya Allah ka bamu cikakken Ladan wannan ibada. Ya Allah al'ummar Musulmi na fama da wani mugun ciwo na Shiah Allah ka darkakesu ka wargazasu, Allah ka dammarasu ka hana musu yaduwa, Allah ka kare al'ummar Musulmi daga wannan masifar ta Shiah. Allah ka amshi wannan Ibada da muka yi domin neman yardarka.
Yasir Ramadan Gwale
23-10-2015
No comments:
Post a Comment