Wednesday, February 26, 2014

Uganda Ta Aikata Laifi, Amma Faransa Bata Yi Laifi Ba


UGANDA TA AIKATA LAIFI AMMAFARANSA BATAI LAIFIN KOMAI BA

Kasashen Turai da Amerika suna ta yin Tir da kasar Uganda, bayan da shugaban kasar Yuweri Musaveni ya sanya hannu akan dokar da ta haramta aikata Luwadi da Madigo a kasar, suna ta barazanar yanke dukkan irin taimakon da suke baiwa kasar a saboda wannan doka. A cewarta Uwargida Cathrine Ashton Sakatariyar Harkokin wajen Tarayyar Turai, take hakkin Bil-Adama ne haramta aikata Luwadi da aka yi a Uganda, a fadarta, tauyewa mutane hakki ne, yin irin wannan dokar a irin wannan lokaci, matukar mutane sun zabi kasancewa 'yan Luwadi. 

Haka aka ruwaito Shugaban Amerika Obama yana sukar Shugaba Musaveni da kakkausar Murya akan sanyawa wannan doka hannu da ya yi. Sun ce bai kamata a hana mutane zabin abin da suka yi aniyar yi ba.

Amma kuma, a kasar Faransa, gwamnatin kasar a baya ta ce ta Haramta Sanya Niqabi da hijabi a bainar jama'a. Duk kuwa da cewar Musulmi sunyi Imani da yin Lullubin da zai suturce jiki, kamar yadda Allah ya Umarci Manzon Allah SAW yayi kira ga matan Muminai da su suturce jikinsu. Amma babu daya da yace anci zarafin Musulmi da sanya wannan doka. Suna ta kururuwa da baiwa 'Yan Adam 'yancinsu na yin duk abinda suka ga dama.

Amma duk 'yancin da suke kira, shi ne na aikata Alfasha, da 'yancin namiji ya koma mace, da 'yancin Dan Adam ya koma Dabba, Da makamantansu.

26-02-2014

Shin Wa Ye Zai Yiwa Shugaban Kasa Wa'azi?


SHIN WA YE ZAI YIWA SHUGABAN KASA WA'AZI?

Na tambayi kaina, cewa, anya kuwa an taba yiwa Shugaban kasa Wa'azi, ya ji zancen Allah? Lallai Annabi Ibrahim Alaihis-Salam da kansa ya je ya yiwa Nimrud (Lamarudu) Wa'azi ya gaya masa zancen Ubangiji; Annabi Musa Alaihis-Salam ya yiwa Fir'auna Wa'azi ya gaya masa sakon Allah; Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da kansa ya dinga bin Mushrikai yana yi musu wa'azi yana gaya musu sakon Ubangiji, da dama suka ji zancen Allah kuma suka yi Imani; Shekhu Usmanu Bin Fodiyo ya dinga bin fadar Sarakunan Arewa yana yi musu wa'azi yana gaya musu sakon Ubangiji, Allah kuma ya sanya da dama suka karbi wannan kira da Shehu Umsanu ya yi musu, suka yi Imani da Allah da ManzonSa SAW, shi ya sa har duniya ta tashi ba za'a daina ambaton Shehu Usmanu ba a kasarnan.

Lokacin da naga sanarwa cewar, Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan ne babban bako a wajen Wa'azin Izala da za'a yi a Legas, na ji dadi kwarai, domin nasan za'a gayawa Shugaban kasa Sakon Ubangiji, kuma za'a karanta masa Al-Qur'ani ya saurara. Amma daga baya Murna ta ta koma ciki, kasancewar Shugaban bai samu halartar Wa'azin ba, saboda wasu Uzurori da aka ce sun hana shi zuwa. Ina kuma fatan nan gaba Kungiyar Izala zasu sake gayyatar Shugaban Kasa wajen Wa'azi su gaya masa sakon Ubangiji. Na taba jin cewar Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya taba zuwa Gidan Gwamnatin Kaduna da kansa ya yiwa tsohon Gwamna Patrick Yakowa wa'azi ya karanta masa Al-Qur'ani ya saurara, ya isar masa da sakon Ubangiji, ance Yakowa yaji dadin wa'azin yayi godiya ga Sheikh Gumi, domin yace shi ne karon farko da aka taba zuwa aka yi masa wa'azi, aka karanta masa Al-Qur'ani, duk da cewa Allah bai nufi Yakowa da yin Imani da Allah da Manzon Allah ba.

Lallai, muna bukatar a samu wasu malamai masu tsoron Allah, su je har fadar Shugaban kasa su yi masa wa'azi su gaya masa sakon Ubangiji su karanta masa Al-Qur'ani, su gaya masa Allah mai Rahama ne da Jinkai ga Talikai, kuma Mai tsananin Azaba ne ga wadan da suka kangare suka ki yin Imani alhali sakonSa ya je garesu. Lallai, muna fatan samun irin wadannan Malamai, kamar yadda na taba jin cewa Sheikh Muhammad Ibn Uthman ya taba zuwa har Gidan Gwamnati a Umuahia ya yiwa tsohon Gwmnan Jihar Orji Orzu Kalu Wa'azi ya gaya masa sakon Allah, kuma Gwamnan shima ya yi Murna da jin dadin wa'azin, wannan ce ma ta sanya ya zo har Kano lokacin wata karamar Sallah aka yi Bikin Sallah tare da shi har ya halarci Kallon hawan Daba, muna fatan Allah ya buda Kirjinsa ya karbi sakon Ubangiji.

Yana da kyau Malamai su dinga zuwa wajen Masu Mulki suna yi musu wa'azi suna gaya musu sakon Ubangiji, kamar yadda Annabawan Allah suka yi. Turawa suka dinga ratsa Teku suna keta Dazuka suna yawon yada Addinin Kiristanci, Shin irin wadan can Turawan sun fimu son Shiga Al-Jannah ne? Lallai mu ne a Hakku da shiga Al-Jannah ba su ba, munyi Imani da cewar duk wanda ya yi Imani da Allah da Manzon Allah SAW kuma ya mutu akan haka, zai samu rahamar Allah. Ya ALLLAH ka shiryi Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ka sanya haske na Imani a zuciyarsa. Allah ka sa ya fahimci irin hakkin da yake kansa na kare rayukan al'ummar Najeriya. Allah ka shirya Shugabanninmu Gaba daya, ka azurtamu da Shugabanni na gari Adalai.

YASIR RAMADAN GWALE 
26-02-2014

Tuesday, February 25, 2014

Yobe


YOBE: Labarin da muka samu a yau, na cewa, an kuma zuwa makarantar kwanan dalibai 'yan sakandare a jihar Yobe an kashe su, abin ya matukar tayar mana da hankali. Har yanzu babu wani rahoton bincike da muka ji ko muka gani akan kisan da aka yi a Oktoban bara na dalibai sama da 50 da aka kashe a garin Mamudo a yoben, sai kuma ga wannan a sakandaren Gwamnatin Tarayya. Ba shakka Tura ta kai bango, angama kuremu, ba zai yuwu kullum ana yin haka ba, abin yana tafiya babu wani daukar mataki daga jiha ko tarayya al'amura suna wuce babu wani mataki na zahiri da ake dauka dan kawo karshen wadannan hare-hare na babu gaira babu dalili ba, muna murna da farin ciki zaman lafiya ya dawo a Yobe ashe da sauran rina a kaba.

Wane irin hali, iyaye zasu shiga a kawo musu labarin cewar wasu 'yan Bindiga sun je cikin dare sun kashe musu yara, an yiwa wasu yankan rago wasu an kona su da ransu! Subhanallah, Ina wadan da alhakinsu ne kula da wannan amanar ta yaran? Ina Hukuma? Lallai wannan al'amari ya kamata indai da gaske yinsa ake yi ya zo karshe. Kuma wajibin hukumomi ne su biya diyyar rayukan da aka rasa wannan Negligence ne na hukuma.

Shugabanni suji tsoron Allah, kullum rayuka na salwanta babu wani mataki da ake bi na bin kadu, jinin al'umma ya zama ba shi da wata kima, wallahi Allah ba zai kyale wannan al'amari ba. Dole a dauki mataki na karshe dan sanya aminci da nutsuwa a zukatan al'ummar da ake shugabanta.

Su kuma, masu aikata wannan ta'addanci, su sani Allah da gaske akwai shi, batun cewa yana nan yana jiran kowa a madakata, gaskiya ne ba tatsuniya bace. Babu wani mahaluki da zai yi saura a duniya face mai riska ta riskeshi, ya yarda ko bai yarda ba, ya shirya ko bai shirya ba. Kowa kuma zaiga sakamakon abinda ya aikata. Wanda ya aikata alkhairi zaiga alheri, wanda ya yi sharri ya kashe mutane ya mayar da yara marayu, ya raba mata da mazajensu ya raba tsakanin dangi, wallahi Azabar Allah na nan na jiransu.

Lokacin da Sahabbai suka shiga cikin tsanani sun tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa YAUSHE NE NASARAR ALLAH ZATA ZO? Manzon Allah ya kwantar musu da hankali cewa Nasara na nan gaba garesu. Lallai mu sani nasarar Allah a kusa take, Allah da muke kira yana jinmu dan ba kurma bane ba makaho bane, yana ji yana ganin abinda ake yi mana. Ya Allah bamu yanke tsammani daga gareka ba, Ya Allah ka Amintar da mu a gariruwanmu, Allah ka jikan wadannan Dalibai ka yafe musu. Wadan da suka aikata musu wannan ta'addanci Allah ka dandana musu azaba sama da wadda suka yi idan sun kasance kangararru ba masu shiryuwa ba.

25-02-2014

Monday, February 24, 2014

Borno


BORNO: Jaridar SundayTrust ta ruwaito wani tsegumi da ta samu daga fadar Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan cewa ana shirin sauya Gwamna Kashim Shettima da Gwamnan soja nan gaba a mako mai kamawa. Sannan kuma a BBC yau naji sun ce ankai wani sabon hari a garin Izge a jiya Asabar bayan marece an kone garin kurmus. Shin anya kai wannan harin baya karfafa Labarin da ST suka yi? Allahumma Asleh A'immatana Wa'ulata Umurina. Allah ka amsa rokonmu ba dan halinmu ba. Allah ka amintar damu. Allah ka kawo mana karshen al'amarinnan.

Yasir Ramadan Gwale
24-02-2014

Iran


IRAN: Lallai akwai sharri mai yawan gaske, wajen daukan yaranmu a kaisu Iran domin yin karatu, wallahi mun gwammace a kaisu ko wacce kasa daga cikin kasashen Turai akan su je Iran. Lallai iyayan yara su sani babu wani alheri da yake tattare da zuwa Iran karatu ga Dan Musulmi. Iyaye zasu kasance abin tambaya ranar gobe kiyama akan abinda aka basu kiwo ('ya 'ysansu), Wajibinmu ne mu tsaya kai da fata wajen ganin ba'a canza yaranmu Aqeedah ta Musulunci zuwa wani abu daban ba. Shi'anci ba Musulunci bane.

Sunday, February 23, 2014

Godiya Ta Musamman Ga Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso

GODIYA TA MUSAMMAN GA GWAMNAN KANO RABIU MUSA KWANKWASO

Dole a wannan gabar, mu yabawa Mai Girma Gwamnan Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso a bisa nuna mana cewar shi shugaba ne mai sauraron koke-kokenmu, munyi korafi dangane da wata kutunguila da manakisa da aka shirya mana, aka rufe kura da fatar akuya da sunan taimaka mana. Ba shakka, mun yabawa Gwamnan akan yadda ya nuna mana shi mai sauraran al'umma ne, irin haka muke fatan Shugabanni su kasance masu bibiyar ra'ayoyin al'umma.

Tun bayan da aka ce Jakadan Iran a Najeriya ya kaiwa Gwamna ziyara a masaukinsa dake Habuja, ya yi tayin baiwa Yaran Kano tallafin yin karatu a kasar 'Yan SHIAH ta Iran masu bautar son zuciya, masu zagin Sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam da Iyalansa da kafirta Musulmi, muka kasa samun nutsuwa akan wannan makircin da aka so yi mana.

Alhamdulillah, munyi korafi, mun nuna rashin amincewarmu ga wannan shiri na daukar yaranmu don a kaisu Iran karatu, mun bi dukkan hanyoyin da suka halatta a garemu wajen jan hankalin Mai Girma Gwamna wajen nuna masa irin mummunan hadarin da yake tattare da wannan yunkuri na daukar mana yara a kaisu su koyo Zagin Manyan bayin Allah da Iyalan Gidan Manzo da sunan karatu.

Mai Girma Gwamna yaji kukanmu, ya kuma gamsu da irin hadari da mummunar aniyar da aka kudunduno ake son shiryawa al'ummar Kano. Muna nuna farincikinmu da karyewar wannan mummunar manufa ta Farisawa masu bautar son zuciya. Babu shakka, wannan wani al'amari ne mai girma da zamu yiwa Allah SWT godiya a kai. Tare da rokonsa ya karemu, ya kare jiharmu daga dukkan wani makirci da makida irin ta 'Yan SHIAH masu shigo da muggan makamai suna jibgewa a unguwar Bompai dan sanya tsoro da firgici da halaka dubban al'ummar Kano babu gaira babu dalili.

Muna rokon Allah da sunayansa tsakaka madaukaka, Ya Allah ya karemu daga dukkan masu shirya mana sharri, ka mayar da sharrinsu a garesu, Ya Allah ka shiryar da shugabanninmu shiriya ta gaskiya, ka basu ikon fahimtar gaskiya tare da karbarta da kuma aiki da ita. Allah ya sakawa Gwamna da alheri. Allah ya taimaki Jihar Kano.

YASIR RAMADAN GWALE
23-02-2014

Saturday, February 22, 2014

Abishir Dan Gane Da Ramadan

ABISHIR DANGANE DA RAMADAN!
 
Kamar yadda yake a cikin al'adarmu, kusan duk lokacin da aka tashi Dauka ko Ajiye Azumin watan Ramadan sai an samu mushkila a tsakanin al'ummarmu, amma sauran watanni sai kaji duk matsalolin babu su, wannan matsala tana faruwa ne sakamakon rashin kula da kamawa da faduwar watannin Musulunci gaba daya. To Alhamdulillah, wannan matsalar na gab da zuwa karshe In Sha Allah. Idan kana son samun bayanin nawa ga watan Musulunci, kuma saura kwana nawa Ramadan ya kama kai tsaye ka shiga http://www.countdowntoramadan.com/ dan ganewa idonka. Wannan Shafin an gina shi ne akan lissafin ganin wata na zahiri ba kirgen kalanda ba. Dan haka a duk lokacin da ka bukaci ganin Kwanakin Ramadan saura kwana nawa su kama, kawai ka shiga shafin dan samun bayani. A cikin shafin zaka iya bamu ra'ayinka a rubuce.

YASIR RAMADAN GWALE
22-02-2014

Thursday, February 20, 2014

Sanusi Lamido Sanusi: Abinda Ka Shuka Shi Zaka Girba!

SANUSI LAMIDO SANUSI: ABINDA KA SHUKA SHI ZAKA GIRBA!

Kamar yadda Malam Sanusi Lamido Sanusi ya fada, wannan dakatarwa da aka yi masa bata zo masa da wani mamaki ba ko bazata. Haka kuma, da daman 'yan Najeriya wannan dakatarwa bata zo mana da mamaki ba, domin kamar yadda Malam SLS ya fada, duk wanda ya yi irin abinda ya yi, to, ba shakka, sai wani abu ya biyo bayan haka. Kamar yadda gidan talabijin na Aljazeera ya fada cewa, Malam Sanusi ya yi bankadar abin kunya mai muni a cikin wannan gwamnati ta Shugaban kasa Goodluck Jonathan. Wanda a bayyane take cewa hankalin Gwamnati bai kwanta ba tunda Malam SLS ya kwarmata badakar bacewar Dala Biliyan 20.

Ko shakka babu, muna alfahari da aikin da Malam Sanusi ya yi a Babban Bankin kasa, ya shuka alhairai masu yawa, kuma zai girbi alheri a nan gaba In Sha Allah. Ya tsaftace tare da inganta harkar Banki a Najeriya, ya sanya nutsuwa a zukatan masu ajiya a cikin bankuna. Abu mafi muhimmanci da ba zamu manta da shi ba, shi ne yadda ya tsaya kai da fata wajen samar mana da Banki Musulunci wanda baya ta'amuli da Riba, wannan kadai ya isa ya sanya mu cira masa tuta.

Muna masa fatan alheri a rayuwarsa, Allah ya musanya masa da aiki na gari wanda zai hidimtawa al'ummar Najeriya. 

YASIR RAMADAN GWALE 
20-02-2014

Abinci



ABINCI: Ko tantama babu, cewar ABINCI jigo ne a zamantakewar Aure da Iyali, ABINCI yana sanya farinciki a zukatan iyalai matuka gaya, sannan rashinsa yana sanya bakin ciki da damuwa. Alkhairan da suke tattare da Aninci suna da tarin yawa wanda kowa zai iya yin bayaninsu, misali da abinci ne gabbai ke bubbuga gangar jiki kan wanzu darajarta kan karu, abinci kan sanya Nishadi da walwal. Haka kuma, sharrin da yake tattare da rashin abinci yana da tarin yawa, misali rashinsa kansanya yunwa da da kanjamewa da cituttuka, kai rashin abinci kan sanya wasu zautuwa.

Yanzu ya zaka iya kwatantan farincikin da yake zuciyar wannan yaron? Me ya sanya shi wannan farinciki mabayyani? Amsar ita ce ABINCI. Amma sai dai Kash! Abinci fa yana wahalar da mu kwarai da gaske, duk fadi tashinmu bai wuce na ABINCI ba, kowa ka gani a ko ina yake babu abinda yake sai neman ABINCI. Ba shakka ABINCI damuwarmu ne sosai.

Lallai yana da kyau mu sani cewar, duk ABINCIN da zamu ci a cikinmu dan jin dadi ko dan Larurar yunwa, to kodai ya zama alheri ne garemu dan ya tsurar da tsokokin jikinmu idan ya kasance Halal ne a garemu. Idan kuwa ya kasance ABINCIN da muka ci Haram ne to babu shakka mun ciwowa kanmu Nadama da tashin hankali.

Lallai wajibinmu ne, mu sanya farin ciki a cikin zukatan Iyalanmu da 'yan uwanmu ta hanayar ciyar da su Halal. Ya Allah ka ciyar da Mu Halal ka shayar da Mu Halal.

20-02-2014

Wednesday, February 19, 2014

Idan An Doki Jaki, A Doki Mangala


IDAN AN DOKI JAKI, A DOKI MANGALA

Idan mun doki Jaki mu bugi Mangala. Mukan zargi Shugabannin Arewa sau da dama akan halin da muke ciki, amma, mu kan kyale Shugabanni wadan da muka zaba da hannunmu wajen tafiyar da al'amuranmu da jagorantarmu. Muna yawan kalubalantar Shugabannin da su ne suka nada kansu ba mu ne muka zabe su ba. Duk wanda ya sha inuwar gemu ai bai kai ya makogaro ba, Shugabannin da muka zaba kuma suke karbar Dirkeken Albashi da sunan Shugabanninmu su ne a hakku da zamu tuhuma akan dukkan wasu al'amura da suke same mu.

Muna da Gwamnonin da muka zaba, muna da 'yan Majalisar dattijai da na wakilai wadannan duk mun zabesu da kuri'unmu, kuma ana biyansu albashi mai tsoka akan zaben da muka yi musu. Lallai su ya kamata mu mayar da karfin tuhumarmu akansu, ba wai wadan da su Ikirari kawai suke cewa su ne shugabannin Arewa ba, wadan da ba suda Dansanda ko Soja ba suda Babban Bankin Kasa ba su da ikon yin abinda suka ga dama.

Lallai muna cikin wani hali, da yakamata mu turke Shugabanninmu wadan da muka zaba, akan su yi mana bayanin meya sa muke cikin halin da muke ciki, amma suka kasa daukan matakin kawo karshen al'amuran da suke faruwa na sukurkucewar tsaro da salwantar rayuka babu gaira babu dalili.

Maganar da Gwamnan Borno Kashim Shettima ya yi cewa idan akwai kayan aiki a wajen jami'an tsaro, za'a fatattaki masu tayar da Hankalin nan a cikin kwana 30! Wannan babbar magana ce, amma har yanzu mun tsuke tunaninmu cewar CAN ce ke mana wannan aikin, mun zuba ido muna jiran Kaddarar Ubangiji. Dole mu farka mu san abinda muke yi, mu kuma san su waye ya kamata mu kalubalanta dangane da halin da muke ciki.

Yasir Ramadan Gwale 
19-02-2014

Monday, February 17, 2014

RE: Boko Haram


RE: BOKO HARAM: Matsalar Boko Haram, matsala ce mai sarkakiya. Da Farko sam ni ban gamsu da matakan da gwamnatoci ke dauka ba na dakile 'yan kungiyar a Jihohin Arewa ba. Domin yau Dan Talaka nawa zai iya shiga Jami'a har ya Kammalata? Dan Talaka nawa zai iya samun aikin Gwamnati ko na Kamfani koma ya iya samun Jari domin ya dogara da kansa? Idan na ga gwamnatoci sun horar da matasa, nakan yi dariya, domin mutumin da baida cikakken ilimi da gogewa da sanin yadda duniya ke sauya launi koda yaushe to yana da wahala ko an ba shi jari da horo ya kulla wani abin kirki. 

Wannan yasa a daidai wurin da aka kammala horon, anan wadanda aka horas din ke sayar da kayayyakin aikin da aka ba su, su sai kwayoyi masu sanya maye. Idan mutum ya shiga Arewa maso Gabas, Yankin da ya fi kowane yanki ci baya a Najeriya zai sha mamaki. Babu wata tsiya da gwamnonin ke yiwa Talakawa a yankin sai karya da yaudara. Sai ko hotunansu da gumakansu da suka cika manyan biranen jihohi, da tallace tallace a gidajen Talabijin da Rediyo na ayyukan boge da suka aiwatar, ayyukan da na ha'inci ne da aringizo.

Yau takai 'yan Boko Haram za su shiga Makarantu su harbe Dalibai, su kwashi 'yan mata 'ya' yan musulmi su tafi da su cikin kungurmin dajin Sambisa su dirka masu cikin shege sannan su ce addini suke karewa. Shi ko Dan Arewa, ya takaita tunaninsa cewa Goodluck Jonathan ne ke ba da ummarnin hakan dan biyan bukatarsa. Mutane sun gaza gane cewa, Gwamnatin Tarayya bata isa ta shirya wani makirci mai girma irin wannan ba, domin a sama Musulmi nada wakilci, wanda da wahala a shirya makirci mai girma da zai ci gaba da tasiri kamar abin da ke faruwa ba. To amma zan iya yarda da cewa, wata kila a cikin Jami'an tsaro akwai baragurbi, kamar yadda a cikin gwamnatin ba za a rasa masu assasa wannan ta'asar ba.

Bishir Dauda Katsina 

Kamar yadda Bishir ya fada, al'amarin Boko Haram akwai sarkakiya sosai a cikinsa. Zance na gaskiya kowa yasan abin da yake faruwa yafi karfin Boko Haram. Amma su sunce su ne, kuma hukuma ma tace su ne, kuma mu idan muka ce ba su bane babu wasu Dalilai masu karfi da zamu iya cewa ba su din bane, amma a zahiri mun san cewar wannan al'amarin yafi karfin mutanan da aka ce Almajirai ne suna kyamar karatun Boko amma suke sunkurun da aka kasa gane ko kama su. Kamar harin 10 Oktoba 2010 ne da aka kai Eagle Square a Abuja, MEND sunce su ne, amma shugaban kasa ya ce ba su bane, wanda ba shi da wani dalili da zai iya cewa ba su din bane tunda sunyi Ikirari da kansu tun ma kafin faruwar abin.

17-02-2014

Boko Haram

BOKO HARAM: Da farko, ina farawa da Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Labaran da muke ji na irin abin tashin hankalin da yake faruwa a kasar Ifriqiyyal-Wusd'a ko Afurka Ta Tsakiya, kusan shi ne babban abin da yake tayar mana da hankali, irin yadda muke ji, muke ganin irin halin da Musulmi suka shiga a hannun kiristocin kasar, inda ake kashe babba da yaro mace da namiji aci namansu danye, bayan an kone gidajensu, tare da wawashe kayansu a kan idanun mutanan da ake ce musu jami'an tsaron kiyaye zaman lafiya, ba tare da sun daga ko kara ba! Ni dai har ga Allah ban san laifin me wadannan Musulmi suka yi a wannan kasar ba, da ake yi musu irin wannan ta'addanci duniya tana kallo babu wanda ya hana. 

Wannan al'amari kusan shi ya ke tayarwa da duk wani mai Imani hankali a ko ina yake. Ba shakka, wadan da ake kashewa tare da azabtar da su ake sace kayansu, Ubangijinsu yana nan gaba garesu, kuma duk rokon da suka yi da wanda aka yi musu, yaji, watakila yana son daukaka darajarsu ne a ranar gobe kiyama ne shi ya sanya mutuwarsu ta wannan hanyar. Allah shi ne masanin gaibu!

Tare da wancan bakin labarin da yake faruwa a Afurka Ta Tsakaiya muke kwana muke tashi, ashe bamu sani ba, ga wata Afurka ta tsakiya a kusa da mu. Kamar yadda 'yan Anti-Balaka ke kashe Musulmi son ransu a Afurka Ta Tsakiya, muma nan ga wasu 'yan ta'adda miyagu Azzalumai  da ake kira Boko Haram suna kashe mutane babu ji babu gani. Hakika, alkaluman da na gani na adadin mutanan da wadannan Azzalaumai suka kashe a Fabrairun nan, abin ya munana, ya kazanta, yakai duk inda ya kai abin tayar da hankali ne. Wannan duk yana zuwa ne bayan irin daruruwan mutanan da aka dinga kashewa a baya a  Ben-Sheikh da sauran yankunan kan iyakar Borno da Yobe da kuma daidaiku da ake kashewa nan da can.

Wadannan azzaluman mutanan, masu jin kishirwar jinin Musulmi 'yan ina da kisa su aka ce wai a kwanakin baya ana tattauna yadda za'a yi musu ahuwa, kuma a basu makudan kudade su tafi abinsu, sun kashe banza. Su kuma wadan da aka kashe sai dai idan an hadu a Lahira su nemi hakkin jininsu da aka zubar ba dan sun cancanci hakan ba, zasu nemi kadin abinsu kamar yadda Allah ya fada a cikin Alqur'ani.

Lallai lokaci yayi, kuma dukkan wata tura ta riga ta gama kaiwa bango, dangane da wannan tashin hankali. Amfanin shugabanci shi ne hidmtawa al'umma da kare musu rayukansu da dukiyoyinsu da mutuncinsu da hankulansu, kamar yadda Larabawa suke cewa "Sayyidul Qaumu Hadumuhum" Idan duk za'a dinga yi mana irin wannan aikin ta'addanci, shugabannin da muka aminta su ne ke da hakkin jagorantarmu suna ji suna kallo ana karar da adadinmu ina amfaninsu yake a garemu? Wace irin rana zasu yi mana alhali muna raye? Ko sai bayan mun mutu baga daya? Ya zama tilas hukumomi su farauto wadannan miyagun mutane duk inda suke a kamosu a hukuntasu gwargwadon abinda suka aikata.

Wannan al'amarin kullum kara daure mana kai yake yi, ace har yanzu an gaza gano maboyar wadannan mutane, an gaza sanin su waye, kuma makamansu sun ki karewa. Shin aljanu ne ko Mala'uku Subhanallah! Wannan magana ce da zamu dawo daga rakiyarta, a yi mana bayanin gaskiya dangane da wannan lamari, shin su waye ke aikata wannan kisan rashin Imani da rashin tausayi? Na yi imani cewar a cikin Musulunci  babu inda aka yi umarni da kisan rashin Imani na mutanan da basu jiba basu gani ba. Duk wani wanda yake wannan ta'addancin da tunanin samun rahama ba shakka yana kara tonawa kansa wawakeken ramin azabar Allah ne.

Da can muna jin wannan al'amarin yana faruwa ne tsakanin su wadannan miyagun 'yan Ta'adda da jami'an tsaro masu damara. Amma yanzu kwata-kwata lamarin ya sauya daga yadda muka sanshi, an koma kashe talakawa har cikin gidajensu da kame matayensu! Wal'iyadhubillah.

Shakka babu, Allah da muke kira a kullum ya yi mana maganin wannan al'amari ba kurma bane, yana ji, yana gani, kuma wadan da ake kashewa bayinsa ne. Mu Musulmi munyi Imani Azabar Allah gaskiya ce, Allah bai yi wata halitta da zata iya jure tsananin azabarsa ba, babu kuma wanda ya taba kubucewa mutuwa Fir'auna ya mutu, Sharon ya mutu da sauran dukkan wadan da suka yi duk abinda suka yi na rashin mutunci da ta'addanci sun mutu kuma zasu riski Alkawarin Allah gaskiya ne, sunyi Imani ko basu yi ba.

Muna kara jan hankalin hukumominu akan lallai su sani wajibinsu ne kare mana rayukanmu da dukiyoyinmu, wallahi dole su zama ababen tuhuma a ranar gobe kiyama akan duk wanda ya rasa ransa ba tare da hakki ba. Za su yi nadama a lokacin da ba zata amfanesu ba. Dole ne a tashi haikan dan kawo aminci a dukkan garuruwan wannan kasar, babu wani dalili da zai sanya ace wani bangare na kasarnan yana zaune lafiya, amma wani yana cikin masifa da tashin hankali amma an kasa yin maganin abin.

Ya 'yan uwa, wata mashahuriyar kissa da muka sani ta wani Dattijo matafiyi, gajiyayye, mayunwaci, mabukaci a cikin halin tafiya, yana tsananin neman taimakon Ubangijinsa daga dukkan dangin abin bukata, ya daga hannu yana cewa Ya-Rab! Ya-Rab! Ya-Rab, amma ya kasance Abincisa Haram ne, abin shansa Haram ne, Tufafinsa Haram ne . . . Yana daga cikin Sharuddan amsa ko wacce irin addu'ah, sai idan ya kasance wanda yake rokon Ubangiji maji rokon bayinsa, ya tsarkake kansa daga cin Haram, da Shan Haram, da Tufafin Haram! Ya yan uwa masu girma, lallai ya zama wajibi a garemu mu tsarkake kawukanmu daga Haram, mu kuma tambayi kawukanmu Anya kuwa bama cin Haram? Kar mu wayi gari mun tsinci kanmu a cikin hali na gaba kura baya siyaki, mun samu kanmu a irin halin kissar wancan dattijo, muna tsananin bukatar agajin Ubangijinmu, amma mun cika cikkunanmu da haram, mun tufatar da kawukanmu da Haram, mun sha mun shayar da haram! Allah ya karemu.

Ya Allah mun tuba ka yafe mana, Ya Allah kajikan yara da mata da tsofaffi; Ya Allah ka kawo mana dauki ta inda bamu zata ba, Ya Allah ka bamu aminci a garuruwanmu. Allah ka kawo mana karshen wannan masifa da bala'i da 'yan uwanmu suke ciki a Borno da Yobe da Afurka ta Tsakiya da Suriya da Iraki da Palastine dukkan inda Musulmi suke. Ya Allah ka shiryi shugabanninmu.

YASIR RAMADAN GWALE 
17-02-2014

Sunday, February 16, 2014

Abdul-Aziz Umar Fadar Bege

FADAR BEGE: Lokacin da naga jama'a na ta yin rubutu akan wannan bawan Allah da ya rasu, na yi ta karanta irin abinda aka dinga rubutawa akansa. Na kuma karanta irin baitocin wakarsa da su Yakubu Musa suka dinga sakawa. Na samu kalubale da yawa akan wannan mutumin, domin da dama sun aiko min da sako wai Yasir me yasa kowa yana yin rubutun fadin albarkacin bakinsa tare da yiwa Fadar Bege addu'ah amma kai baka yi ba, irin wannan sakon na same shi da yawa, wasu ma har akan Timeline dina suka dinga rubutawa, amma bana yin martani ga duk wanda ya turomin, illa nakan garzaya turakarsa dan fahimtar ko waye shi.

Wani abu da ya bani mamaki shi ne, yadda Abubakar Attahiru ya yi rubutu yake tambayar waye Fadar Bege dan shi bai sanshi ba, kuma bai taba jin wakarsa ba. Naga yadda mutane suka dinga karyata shi, wasu ma har da zagi wai kawai dan bai taba jin wakarsa ba. Nima irin ta Attahiru din, Ban san wannan bawan Allah ba, ban kuma taba jin wakarsa ba, sai da naga ana maganar rasuwarsa. Kuma dan mutane basu sanshi ko taba jin wakarsa ba, ai wannan ba shi ne zai rage darajarsa ba.

A kwanakin baya kuma naga ana ta yada wani zance a nan Facebook cewa WAI Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya gamu da gamonsa saboda ya yi wata magana akan Fadar Bege, aka yi ta yada karairayi akansa, har naji Shekhin Malamin da bakinsa ya sanya lada akan duk wanda ya fada masa inda ya yi maganar da aka ce yayi akan Fadar Bege. Ban sani ba ko an kawo masa kasset din da ya nema.

Abin da na ke so na kai gareshi shi ne, shin wa ye wannan Fadar Bage da har ake cewa wani Malami ya gamu da gamonsa saboda WAI ya zage shi. Shin ya matsayinsa yake idan aka kwatanta shi da Sayyadina Abubakar da Umar da Usman da Matan Manzon Allah iyayan Muminai da 'Yan Shi'ah suka cika duniya da zaginsu? Fadar Bege dai tasa ta kare, kuma nasan dai ba Dan Shi'ah bane, dan haka ina yi masa addu'ar Allah ya jikansa ya gafarta masa ya yafe masa kurakuransa. Muma Allah ya jikanmu ya kyauta karshenmu.

Yasir Ramadan Gwale
16-02-2014

Friday, February 14, 2014

Me Kae Yi A Afurka Ta Tsakiya Idan Ba ta'addanci Ba!


ME AKE YI A AFURKA TA TSAKIYA IDAN BA TA'ADDANCI BA!

Hakika irin abin da na gani ana nunawa na ta'addanci ban taba ganin irinsa ba a kasar Afurka ta tsakiya. A lokacin da na kalli wani Bidiyo na wani da ake kira MAD DOG yana cin naman mutum hankalina ya yi matukar tashi, abinda nake ji ana cewa wasu na cin naman mutum; sai gashi na gani. Abin ya bani tsoro sosai, babu shakka irin abinda ke faruwa a kasar ya zarce dukkan nau'in ta'addanci. Abin kuma yana faruwa akan idanun jami'an tsaron da aka jijjibge a kasar dan kawo zaman lafiya. Saboda kawai Musulmi ne ake kashewa, ana wawashe gidajensu, ana kone gidjensu tare da rugurguza masallatansu.

Abin mamaki lokacin da Kungiyar Saleka mai rinjayen Musulmi take fatattakar shugaba Bozizi mafi yawancin 'yan kasar sunyi murna da farinciki, duk kuwa da sanin cewar galibin 'yan kungiyar Musulmi ne. Bayan darewarsa shugabancin riko Michal Djotodia, su, 'yan kasar wai ba su dauka Musulmi bane, ana ganin yaje Masallacin juma'a shi kenan hankalin jama'a ya tashi, sai kuma 'yan Anti-balaka dake da makamai suka farwa Musulmi; sai tashin hankali; sai kashe-kashe; sai kone-kone da sace-sace.

A kasar Tchadi kasashen yankin suka tursasawa Shugaba Djotodia sauka daga shugabancin da samun zaman lafiya, da yake shima ba mai son tashin hankali bane ya bi ra'ayin 'yan kasar ya sauka, dan samar da zaman lafiya. 

Faransa ta bayar da soji 1600 tarayyar Afurka ta bada soji 4000 tarayyar Turai tayi alkawarin soji 1000 amma duk suna gani 'yan Jarida suna yada irin yadda ake kashe Musulmi sai dai kawai surutun da su Ban-ki Moon suke yi. Ina Amerika ko duriyarta baka ji tunda ta yi alkawarin taimakawa da kudi. 

Amma a Kwango da Sudan ta Kudu saboda kiristoci ke kashe junansu nan da nan ana lura da abinda ke zuwa yana komowa. Ana ta kokarin yadda za'a sasanta. Babu shakka Allah shi ne gatan Musulmi a duk inda suke, duk wasu masu ihu da ikirarin 'yancin dan adam makaryata ne, tunda gashi nan ba wai danne hakkin Musulmi aka yi ba, namansu danye ake ci duniya tana gani. Amma Allah baya gyangyadi bare bacci, daman kuma ya fada a cikin Sura ta 29 aya ta 2 cewa tsammaninku dan kunyi imani ba zamu jarrabeku ba! Hakika an jarrabi Musulmin Afurka ta tsakiya. Muna rokon Allah ya kai musu mafita da Dauki ta inda basu zata ba.

YASIR RAMADAN GWALE 
14-02-2014

Thursday, February 13, 2014

GENERAL MURTALA MOHAMMED: Najeriya Ta Yi rashin Shugaba


GENERAL MURTALA MUHAMMAD: NAJERIYA TA YI RASHIN SHUGABA

Yau Laraba 13 ga watan fabrairu, tayi dai dai da ranar da marigayi General Murtala Ramat Muhammad ya cika shekaru 38 da rasuwa, kwatankwacin Shekarunsa na rayuwar duniya, Ya rayuwa a duniya Shekaru 38, yanzu ya shafe tsawon wadannan shekaru kwance a Kabarinsa, a irin wannan ranace akayiwa wannan dan tahaliki kisan gilla, awani yunkuri na juyin mulki wanda baici nasaraba. Da ace Gen. Murtala yana raye har wannan shekarar, da ya cika shekaru 76 a wannan duniyar, an haifeshi a shekarar 1938 a tsakiyar birnin kano, Gen. Murtala ya rasu yana matashi domin bai cika shekaru 40 a duniya ba, an kasheshi a lokacin da yake da shekaru 38 da haihuwa, ya rasu yana begen ganin wannan kasar ta sami ingataccen shugabanci, da cigaba mai dorewa, sai dai har yanzu wannan buri da ya rayu kuma ya rasu tare da shi bai cika ba.

Zaiyi kyau a ce gwamnati ta sauya darussan Social Studies domin karantar da yara manyan gobe irin gudunmawa da nagartar mutane irinsu Gen. Murtala Muhammad. Hakika gwarzo ne abin koyi da tarihin kasarnan bazai cika ba idan babu tarihin irin gudunmawar da ya baiwa cigaba da wanzuwar wannan kasa da kuma wannan nahiya tamu ta Afrika, abin kaico, shi ne yara da dama kawai suna ganin hotonsa ne ajikin takardar kudi ta Naira 20 ba tare da sun san hakikanin waye shi ba. Ka kamanta dukkan wani shugaba mai kishin al’umma da son cigabansu da kaunar kasarsa da irin so da kaunar da wannan dan tahaliki ya nunawa wannan kasa, shin ko Asibitin Murtala dake birnin kano da filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas da titunan Murtala Muhammad dake galibin jihohin kasarnan sun isa su biya abinda wannan bawan Allah ya yi wa kasarnan a kwanaki 199?

Gen. Murtala kusan ya shafe kwanaki 199 a kan kujerar shugabancin kasar nan a matsayin Head of state, ya hau mulki daga 29 ga watan yuli 1975, zuwa 13 ga watan fabrairun 1976. Murtala shi ne mutum na biyar a jerin shugabannin kasar nan goma sha biyar, a iya tsawon kwanakin da ya shafe yana shugabanci bai kama ko kadangare ya daureba da sunan tuhumarsa da cin amanar kasa, kusan tarihi ya nuna cewa shi ne shugaban da bai taba daure kowaba a mulkin wannan kasar, haka kuma shi ne mutumin da ya fara assasa cewa mulki zai koma hannun farar hula, wanda mataimakinsa da ya dora daga inda ya tsaya Gen. Olushegun Obasanjo ya cika wannan alkawari a shekarar 1977, inda Shehu Aliyu Usman Shagari ya zama zababben shugaban kasa, haka kuma, shi ne ya kirkiro jihohi da dama da kuma inganta al’amarin kananan hukumomi, haka nan kuma shi ne mutumin da ya kafa harsashin maida cibiyar mulki daga Legas zuwa tsakiyar Najeriya inda ake kira Abuja, yanzu mutumin da ya yi wadan nan muhimman ayyukan ya dace tarihi ya mance da shi? Ko shakka babu amsar zata zama a’a, don haka ya zama dole gwamnati ta yi wani tsari domin koyar da yara halayyar mutanan kirki irinsa.

Ance kusan shi ne mutumin da ya fara daidaitawa ma’aikatan gwamnati sahu musamman ta wajen zuwa aiki akan lokaci da hukunta dukkan wanda ya karya doka. A wani littafi da fitaccen marubucin nan Mista Chinua Achebe ya rubuta mai suna The Trouble with Nigeria, ya yi bayanin kwanakin Murtala na farko-farko a mulkin wannan kasa, yace ko wane ma’aikaci na dari-dari da aikinsa da kuma tsoron karya doka musamman a birnin Legas inda nanne fadar gwamnati a wancan lokaci ta ke. Yace sau da yawa Gen. Murtala ya kanyi bazata ya fito kan titi da safe ya tsallaka ba tare da danja ta bashi hannun ba domin ganin matakin da ‘yan sanda zasu dauka, ance wata rana ya tuka mota danja ta tsaidashi amma ya wuce abinsa, da yalo fifa ya kamashi yace sai sunje caji ofis, ya nemi ya bashi dan na goro amma dansandan nan yace atafau, domin laifine akama ka kuma ka bada kudi domin fansa, suna zuwa ofishin ‘yan sanda kawai sai ya ware nadin da ke fuskarsa nan da nan DPO ya gane shugaban kasa ne inda ta ke ya sara masa, yalo fifa kuma yace kafa me naci ban baki ba domin yana tunanin ya gamu da gamonsa. Haka dai Achabe ya cigaba da bayyana Gen. Murtala wajen nuna kwazonsa da jajircewarsa, akan wannan kasa.

Gen. Murtala wadan da suka sanshi, sunce mutumne mai kwarjini da babu alamun wasa a tattare da shi, ance da zarar ya kalleka da ido idan baka da gaskiya sai kaga mutum ya hau tsuma yana kyarma, haka kuma Murtala mutumne da yake son yin abu da gaggawa ba tare da bata lokaci ko jin kiri ba, don haka ne akoda yaushe yake yawan maimaita kalmar "DA GAGGAWA" , Allahu akbar irin mutanan da Arewa ta fitar a wancan loakcin kenan, Bahaushe mutumin kano a birnin ikko ikon Allah. Ance lokacin da yake Head of state gidansa da yake aciki a lokacin da yake rike da mukamin Director of army signal corps kafin zamansa shugaba bai fita daga ciki ba domin haka kullum yake fita daga shi sai direba zuwa Dodan Barrack a Legas, shi mutumne da bai cika son wasa ba, don haka ko jerin gwanon motoci baya yi, haka kuma, baya kunna jiniya a lokacin da yake fita ko dawowa, shi kadai, daga shi sai direbansa suke zuwa kano tun daga Legas a motarsa ba ta gwamnati ba, tafiyar sama da kilomita dubu 1000.

Wani marubuci, Aliyu Ammani ya bayyana Murtala a zaman wani gwarzo a lokacinsa wanda aiki kawai ya sanya a gaba, mutum mai saukin kai kuma maras girman kai. Yace wani tsohon Lauya kuma tsohon malamin jama’ar Legas mai suna Dr. Obarogie Ohanbamu ya rubuta a Mujallarsa mai suna African Spark cewa Gen. Murtala ya azurta kansa kafin ya zama shugaban kasa da mallakar dimbin dukiya da gidaje, amma duk da haka Gen. Murtala baiyi amfani da ikon da yake da shi ba wajen ci masa mutunci ko sanyawa a kameshi tare da gana masa gwale-gwale kamar yadda aka san sojoji da yi a Najeriya, kawai sai ya kai shi kara zuwa Igbosere magistrate Court a Legas domin ayi musa shari’a da mutumin da ya bata masa suna a cikin jarida, ance kotu ta zauna ta saurari wannan kara, kuma ta dage zaman zuwa 17 ga watan maris 1976, Allah mai yadda yaso Gen. Murtala bai riski wannan lokacin ba Allah ya cika masa ajalinsa, sai dai a wata hira da abokin Gen. Murtala na kusa ya yi da jaridar The Punch ta ranar 4 ga watan mayu 1982, marigayi Cif MKO Abiola ya ce Gen. Murtala ya rasu ya bar Naira bakwai da kwabo ashirn da biyu(N7.22) a cikin asusunsa na ajiya, tabdi jan! kaji fa shugaban kasa kenan! Allahu Akbar! Haka kuma ya bar duniya bashida gida ko katuwar gona ko gandun daji da gandun dabbobi.

Ammani, ya cigaba da cewa a ranar 11 ga watan Janairun 1976, Gen. Murtala ya kada hantar kasashen yamma da wata kasida da ya gabatar a taron kasashen Afrika na OAU da akayi a birnin Adis Ababa na kasar Eithiopia akan ‘yancin kasar Angola mai taken Africa has come of age. Gen. Murtala ya yi jawabi kamar haka, ya ce “ ya mai girma shugaba, idan ina tuna irin yadda fararen fata suka bautar tare da nuna wariya ga bakaken fata a kasar Afurka ta kudu, zuciyata tana tafarfasa tana kara bugawa ne, wannan al’amari yana dugunzuma tunani na matuka kamar yadda dukkan wani mai kishi yake jin ciwo idan ya tuna wani abu irin wannan” haka Gen. Murtala ya ci gaba da jawabi yana cewa “ yanzu fa kasar Afurka ta kawo karfi, babu wata kasa da zata cigaba da bamu umarni muna bi, kowacece kuma duk karfinta, dole mu hada karfi da karfe wajen yakar wannan cin-kashi da aikin bauta a cikin 'yanci da akeyi mana domin kwatowa ‘yan uwanmu ‘yanci ko da kuwa hakan zai kai ga salwantar rayuwarmu” Allahu akbar haka ikon Allah yake Gen. Murtala yana wannan jawabi ne a lokacin da tuni Allah ya rubuta cewa kwanaki 34 ne kacal suka rage masa a duniya, haka dai ya cigaba da jawabi mai cike da armashi da kwarin guiwa da nuna rashin tsoro ko gazawa.

Haka Gen. Murtala yake da karfin hali da rashin nuna tsoro ga kuma kwarjini. Kamar yadda marigayi Sunday Awoniyi yace shi mutumne da ko da yake a makaranta a Barewa College Zariya baya fada da sa’anninsa sau da dama zaka samu yana fada da na gaba da shi akan anzalinci na kasa. Kamar yadda masana sukayi bayani ana son shugaba jarumi mai kwarjini maras tsoro da kuma karfin hali, hakika Gen. Murtala ya cika dukkan wadannan abubuwa da suka sanya zai iya zama kowane irin shugaba.

Haka dai mutanan kirki suke cigaba da gushewa a wannan rayuwa, a dai-dai lokacin da ake bukatar juriyarsu da jajircewarsu. Hakika Najeriya ta yi rashin gwarzo abin koyi, daya tamkar da dubu, muna addu’ar Allah ya jikan Gen. Murtala ya kai rahama kabarinsa ya sanya mutuwa ta zamo hutu a gareshi, Ya Allah ka arzurta wannan al’umma da mutane masu karfin hali da kwazo irin nasa koma wadan da suka fishi. Allah ya jikan General Murtala Ramat Muhammad . . . Yallabai kamar yadda ka nuna kishi da kauna garemu da kuma kasarmu muma muna yimaka addu’ar fatan alheri, duk da nasan bakajina a halin yanzu, amma inada yakinin insha Allah addu’ata zata riskeka. Allah ya hadamu a darussalam da alheri. Bahaushe yana cewa kada Allah ya kawo ranar yabo! Amma nikam ina fatar Allah ya cigaba da nunamin ranar da zan yabi mutanan kwarai irinka. 

Yasir Ramadan Gwale 
13-02-2014

Wednesday, February 12, 2014

Wani Shaidanin Malami A Najeriya



WANI SHAIDANIN MALAMI A NAJERIYA

A Lokacin da Quraishawa suka fito domin Yakar Manzon Allah SAW da Sahabbansa Allah ya yarda da su, a yakin Badar, duk da Sahabban basu da yawa, basu da Makamai, basu Kware a wajen Yaki, amma saida Shaidan yayiwa Mushrukai ta ke yace dasu:

"لاغالب لكم اليوم من الناس واني جار لكم".

"YAU FA BABU WANDA ZAIYI RINJAYE AKANKU,TABBAS KUMA NI INA TARE DAKU".

Amma bayan Shaidan yaga Malaiku suna sauka daga sama da Makamansu, suna kawowa Mumunai da Manzon Allah SAW taimako, sai ya zura a guje, kuma ya kara cewa dasu: "اني برىء منكم اني ارى مالا ترون اني اخاف الله،والله شديد العقاب".

"LALLAI KAM NI BANA TARE DAKU, DON NI INA GANIN ABINDA BAKWA GANI, NI KAM INA JIN TSORON ALLAH, DON ALLAH MAI TSANANIN UQUBA NE".

Hakika Malaman tafsiri sunce Shaidan yazowa Quraishawa ne a cikin Siffar Mutane, ya yi musharaka da su a cikin Shawarwari da kuma farkon Yakin. In Mutane suka lura duk sanda shaidan zaiyi abu tare da Mutane, to cikin Surar shaidan din yake zuwan musu, domin a Lokacin yafi Sharri da kuma tunzurasu. A yanzu ma muna tare da Shaidan a matsayinsa na Mutum, kuma yana nufin ya zuga Mumunai ya hadasu FADA ko kuma yaga suna Kashe Junansu ko ana Kashe su.

Kowa yasan Ahlussunnah wajen bin koyarwar Manzon Allah SAW a lokacin da wata fitina ko Balai ya taso musu, basa daukar doka a hannuwansu, basa afkawa wani domin zargi ko kuma zato. Wannan yana kara sanyawa Jama'a suna kara Fahimtar Sunnah da kuma mabiyanta, da aikinsu a sarari da fili; ba boye boye.

Lokacinda aka Kashe Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah, duk duniya an dauka Mumunai zasu fito da rikici da kuma kone kone da sallawantar da dukiyar Jama'a da kisan wadan da basu san hawa ba basu san hausa ba, sai gashi ko ja'ba babu wanda ya Kashe, balle kuma Dan Adam, tunda ba a san Makasan ba. Yanzu ma an Kashe sheikh Auwal Adam Albani Zaria Rahimahullah ,shima ana zaton za ayi tunzuri a kara kashe Jama'a a zaria, amma dai wannan dai koyarwar ta Manzon Allah SAW bata sanya Jama'a sun dauki doka a hannunsu ba.

Kwatsan aka Kawo Sojoji cikin Zaria don kawai suna zaton Mumunai zasuyi Rikici, shima basu sami sa'ar yin hakan ba. Ganin haka ne ya sanya wani Shaidani cikin bakar Alkhabba da rawani, Makaryaci kuma Matsoraci ya fito har yana tutiyar wai Salafawa sun san wanda ya kashe Albani, tsoro ne kawai suke ji suka ki fadan makasan. Burin wannan Sahi dani, shi ne, Mutane su tunzura su fito rikici karnukan Gwamnati su kara hallakasu, sai kuma ya fake da cewa wai shi yasan ko suwaye, kuma zasu fito su fadesu.

1-Abin Tambaya ta yaya ya san haka din?

2-Ko don haka mukaga duk sanda Za'a kama Makamai an shigo dasu Najeriya sai aga 'Yan Shi'a ne, kuma ba ayi musu Komai ba?

3-Yana so yace dama yasan za'ayi Kisan kawai fadane yaki yi, ko kuma sai bayan Kisan aka sanar dashi ko su waye suka yi?

4-Su waye Jami'an Tsaron farin Kayan da suke bashi labari kamar yadda yake cewa???

5-Hakika a fili yake a SOKOTO munga 'Yan Shi'a sunyi kisan kai, kuma Hukumomin Nigeria sun fito dasu wai da tutiyar rashin cikakkiyar shaida (Beyond Reasonable Doubt), amma kuma har yanzu Jama'a basu manta da wannan ba. Dan haka, Ahir Hukumomi suka maida wasu Mutane 'Yan Mowa, wasu kuma 'Yan Bora, domin Hukomomi su bada Tsaro ga wasu, da kuma suka ga abin ya bada Mamaki,s ai kuma suka fito suna neman Wawantar da Mutane. Idonmu a bude yake,muna Karatu ko da wasali ko ba wasali, don haka muna fadake muna ankare muna kuma fadakarwa.

Hattara muke so Hukuma da Sauran Jama'a suyi akan wannan rikici da Wannan Shaidanin Malamin yake Kokarin kawowa a Kasar nan. Allah yasa masu hakkin daukar mataki sun ji,kuma suna gani.

Yasir Ramadan Gwale
12-02-2014

Tuesday, February 11, 2014

Matsalar Shi'ah Ta Su Wa Ye?


MATSALAR SHI'AH TA SU WAYE?

Kusan da dama daga cikin mutane ba su fahimci meye gaskiyar al'amari game da Shi'ah ba. Wa su da dama suna kallon mun cika matsawa da muke yawan magana akan 'Yan Shi'ah, kuma sau da dama, sukan kalli cewar Matsalar Shi'ah ta 'Yan Ahlussunnah ce su ya su! Da daman mutane wadan da basu san komai game da Shi'ah ba haka suke kallo, a saboda haka ne, suke ganin matsantawa ne, zafin Addini ne ya sanya muka cika yin magana akan Shi'anci, dan haka, duk wani Malami ko mai isar da sako da yin Da'awa da zai yi magana akan Shi'ah sai a dinga yi masa kallon ya cika zafin kishi addini, sau da yawa sukan kafa hujja cewa, ai 'yan Shi'ah Musulmi ne, dan haka abar kowa ya yi abinda yaga dama ko ya fahimta a matsayin addini. Masu irin wannan fahimtar a cikinmu suna da yawa, sai dai sau da yawa nakan yi musu Uzurin rashin sanin meye Shi'anci yake dauke da shi.

Matsalar 'Yan Shi'ah ba ta 'yan Salafiyyah/Wahabiyawa/Izala da duk sunan da aka kiramu ba ce, Al'amarin Shi'ah  batu ne da ya shafi Musulunci gaba daya. Domin dukkan Musulmi na hakika sunyi Imani da cewar garin Makkah nan ne ALKIBLAR Musulmin Duniya gaba daya, kuma Makkah nan ne, inda duk Musulmin Duniya suke haduwa dan yin daya daga cikin Ibadu mafi girma a cikin rukunan Musulunci, wanda a bayyane take cewar a tsarin Shi'ah  babu wani abu da ya yi kama da cewa Makkah ko Ka'abah ita ce alkiblarsu, suna ganin Karbala, nan ne birnin mafi tsarki duk duniya, kuma nan ya kamata Musulmi su maida hankali don ya zama Alkibla. Wannan bayyanannen al'amari ne, domin duk wanda ya ji abinda Shugaban Iraki Nuri Maliki ya fadi a yayin bukukuwan Arba'in da Ashura zai gasgata hakan, ko da bai bibiyi ainihin meye Shi'anci ba. Wannan fa, da kansu suke fada, cewa biranen KARBALA da NAJAF sune birane mafiya tsarki duk duniya, suna ganin MAKKAH da MADINA birane ne da suke dauke da Najasa da datti. Wal'iydhu Billah!

Dukkan Musulmi na hakika da ya Yarda da manzancin Annabi Muhammada Sallalahu Alaihi Wasallam, ya sabawa 'Yan Shiah, ya san karya ce kafirci ne, ba Musulunci bane. Irin wadan nan da suke jingina kansu cewa Musulunci suke yi, su ne wasu ke kiran wai an cika matsanta musu. Bayan a bayyane take cewar mutane ne masu dauke da datti da mugunyar Aqidah da ta ke gurbata addinin Musulunci.

Baya ga wannan, ga aibata da zagin Sahabban Manzon Allah SAW wadan da su ne mafiya daraja a cikin al'ummar Manzon Allah bayansa, suna kafitasu da jifansu da munanan kalmomi, ga zagin Matan Manzon Allah SAW iyayan Muminai. Duk wanda ya tashi a cikin Shiah to akan haka aka tarbiyyantar da shi. 

Dan haka kullum Shi'ah ba su da wani aiki sai rabewa jikin Musulmi domin gurbata musu tunani da sahihiyar Aqidah ta Musulunci. Tayaya zamu bari a dauki yaranmu a kaisu Iran domin yin karatu ko wane iri ne? Wasu na kafa hujja da cewar, mutanan da suka tafi ENGLAND da AMERIKA da FARANSA da CANADA da sauran kasashe shin su me ya sa ba'a ce zasu juye zuwa Kiristanci ba, wanda duk wanda ya yi wannan magana, yana da rarraunan tunani game da sanin meye Shi'ah, ai sauyawa Mutum Aqidah abu ne mai sauki ainun akan sauyawa Mutum addini. A iyakar sanina babu wani mutum da ya je Iran Karatu face sai da ya juye zuwa Shi'anci.

Dan haka, dole muyi Allah wadai da duk wani yunkuri na daukar yaranmu dan kaisu Iran neman karatu ko wanne iri ne, komai tsananin bukatarmu gareshi.

Yasir Ramadan Gwale 
11-02-2014

Sunday, February 9, 2014

RE: Ko Shugaban Kasa Bai Isa Ya Gina Coci A Jami'ar Bayero Ba - Galadiman Kano


RE: KO SHUGABAN KASA BAI ISA YA GINA COCI A JAMI'AR BAYERO BA- Galadiman Kano

Jiya na tuntubi makusantan Masarautar Kano dan tabbatar da gaskiyar wannan labari, kuma Alhamdulillah, an tabbatar da cewa wannan al'amari na shari'ar da kungiyar CAN ta kai karar fadar Ma Martaba Sarki akan rushe ginin cocin da aka fara a cikin jami'ar Bayero gaskiya ne, sai dai a yadda aka bada labarin akwai karin gishiri akansa.

Abu na farko dai Mai Girma Galadiman Kano Alh. Tijjani Hashim ya kai ziyarar gani da ido a wajen da ake gina wannan coci a cikin BUK, amma bayan barinsa wajen babu jimawa wasu suka sauke ginin Cocin amma ba Galadima ne ya basu umarnin yin hakan ba. Daga baya labari ya je wajen Galadima cewar ya sanya an rushe ginin cocin, Mai Girma Galadima ya fusata yace, yaga uban da zai gina cocin a BUK ko za'a gina sau goma sai ya sa an rushe sau goma tunda abin rashin kunya ne. Ya kuma kalubalanci duk wanda yake shakka akan haka, ya kuma ce a fara baiwa Musulmi damar gina Masallaci a jami'ar Fatakwal da Nsukka da sauran jami'o'in kudu kafin su bayar da dama a Kano.

Dan gane da batun Shari'ar kuma, kotu ta zauna har karo biyu ba tare da bayyana wakilan Mai Martaba Sarki ba, kamar yadda su CAN suke karar Mai Martaba Sarki akan Zargin Masarauta ta sanya a rusa ginin cocin, inda suke ganin taya za'a ce ana karar wasu amma sunki bayyana a gaban kotu kuma sun ki turo wakilansu. Wanda tun farko da aka nemi mai Martaba Sarki akan ya bayar da Iznin gina cocin, ya shaida musu cewar ba shi da hurumin a cikin jami'ar Bayero da ya shafi wannan aiki.

Sannan kuma, batun cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya ya wakilci Sarki a kotu nan ma ba gaskiya bane, hasalima shi Dr. Anyim su ne suke daurewa CAN gindin samar da cocin. Haka kuma, batun cewar dukkan alkalan kotun da Babbar Mai Shari'ah ta kasa Maryam Aloma Mukhtar su gurfana a gaban Mai Martaba Sarki, wannan ma akwai zukale, fadar Mai Martaba Sarki ta bukaci ganin Justice Maryam Aloma Mukhtar zuwa fada a matsayinta na 'yar Kano. Tun cikin Shari'ah ita Kotu ta bukaci a warware wannan al'amari a wajen Kotu.

Yasir Ramadan Gwale
09-02-2014

Ko Shugaban Kasa Bai Isa Ya Gina Coci A Jami'ar Bayero Ba- Galadiman Kano



KO SHUGABAN KASA BAI ISA YA GINA COCI A JAMI'AR BAYERO BA- Galadiman Kano

Zaman babbar kotun Shariah (Federal High Court) dake babban birnin tarayya Abuja, akan karar da kungiyar Kiristoci ta kasa CAN ta kai Masarautar Kano saboda Mai-martaba Sarkin kano Alh Dr Ado Bayero yasa an rushe wata coci da ake ginawa a cikin tsohuwar Jami'ar Bayero kano (BUK). A zaman koton da akayi a ranar litinin din da ta gabata, kotu ta nemi Mataimakin Shugaban Jami'ar Bayero Prof Rasheed, da wakilin kungiyar kiristoci ta kasa, da kuma Mai Martaba Sarkin kano da su bayyana a gabanta, a zaman kotun, anga prof Rasheed da mataimakin shugaban CAN sun mike tare da lauyoyinsu amma ba a ga Mai Martaba Sarki ba.

Daga nan sai jagoran alkalan kotum Justice Alakola Nweri yace dayake muna da sauran mintuna 10 kafin fara Shari'ar zamu jira zuwan Mai Martaba Sarkin kafin wadannan mintoci. Daga nan sai Justice ya dubi prof Rasheed yace a baya Kotu ta baku umarnin Gina coci a jami'ar ko kunbi umarnin kotu? Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa munbi umarnin kotu, dan sai da ginin Cocin ya kai linta sannan Mai Martaba Sarkin Kano ya bamu umarnin tsayar da aikin, daga baya kuma sai ga Mai Girma Galadiman Kano Alh Tijjani Hashim ya jagoranci Rushe ginin gaba daya. Justice yace, kuna nufin kenan kunyi watsi da umarnin kotu kunbi na sarki? Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa saboda Sarki Ubanmu ne kuma shi ne Sarki mai daraja ta daya a kasar nan bayan sarkin Musulmi saboda haka, bazamu iya kin yi masa biyayya ba.

Daga nan sai Justice ya ya Umarci Farfesa Rasheed da ya zauna. Justice ya ce da wakilin CAN kaji abinda ya fada kana da abin cewa? Sai yace Eh, wakilin CAN yace gaskiya ne hukumar Makarantar Jami'ar Bayero ta fara gina Cocin aka Hanasu saboda haka muke rokon wannan kotu da ta hukunta Sarkin Kano bisa shiga hurumin da ba nasa ba. Daga nan shima akace ya zauna. sannan kotu ta nemi Sarkin daya bayyana a gabanta, ana haka sai ga Sakataren Gwamnatin Tarayya Dr Anyim Payios Anyim ya bayyana a gaban kotun, anga alkalan kotun sun mike tsaye domin girmamawa ga Dr Anyim, daga nan Dr. Anyim yace ya mai shari'ah ni ne wakilin Mai martaba Sarkin kano Alh. Dr. Ado Bayero, ya umarceni dana wakilceshi a wannan koto domin amsa kira.

Justice yace, kana nufin kana tsaye anan a matsayin Maimartaba Sarki kenan? Dr. Anyim yace kwarai kuwa, kuma duk abinda zan fada ba ni na fada ba His Royal Highness ne ya fada. Justice yace, muna jinka, Dr. Anyim yace, sarki yace na sanar da wannan Kotu shiya sa a rushe Cocin, badan komai ba sai dan basa bukatar ganin cocin a Jami'ar, Sannan yace na gayawa wannan kotu mai daraja cewar, idan za'a gina Coci sau 10 a Jami'ar to kuwa zai sa a rusheta sau 10! Sannan Galadiman kano Alh Tijjani Hasheem yace na gayawa wannan Kotu ko Shugaban kasa Goodluck Jonathan bai isa ya gina Coci ba a harabar Jami'ar Bayero ba tare da yardar Mai Martaba Sarki ba, Dr Anyim ya cigaba da cewa, wannan shi ne sakon da Mai martaba sarkin kano da Mai Girma Galadiman Kano suka turo ni domin na sanarwa da wannan kotu na gode.

Daga nan, anga alkalan kotun suna tattaunawa a tsakaninsu, kafin daga bisani akaga Babbansu ya daga waya yana magana, daga nan sai Alkalin yace to duk munji baya nan ku, dan haka, wannan kotu tana kira ga Shugaban kasa daya duba wannan Lamari idan yaga da yiwuwar gina Cocin to ya bada umarnin ginin, idan kuma yaga ba sai an gina ba to shikenan. Daga karshe kotu ta Sallami wannan Kara kuma tana yiwa Mai Martaba Sarkin Kano fatan alkhairi da fatan Allah ya kara masa lfy da adalci. Wannan shi ne hakikanin abinda ya gudana a wannan Shari'ah da akai.

Sai dai bayan gama wannan Shari'ah, Mai Girma Galadiman Kano, ya bayar da sanarwar cewa Babbar Mai Shari'ah ta kasa Justice Maryam Aloma Mukhtar da Alkalan kotun da suka jagoranci Shar'ar da su gurfana a fadar mai martaba Sarkin Kano, Alh. Dr. Ado Bayero LLD JP.

ME YE GASKIYAR WANNAN LABARIN DA NA GANI A WALL DIN Abba Muhammad Lawan?

Sunday, February 2, 2014

Sheikh Auwal Adam Albani Zaria: Kullu Man Alaiha Faan!

SHEIKH AUWAL ADAM ALBANI: KULLU MAN ALAIHA FAAN

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Daga gareshi muke, kuma gareshi zamu koma Subhanahu Wata'ala. 'Dazu da safenna dan uwa Malam Aminu Sani Musa ya kirani a waya yake yi min ta'aziya. Yasir ya hakuri? Ya tambayeni, hakika gaba na ya fadi, duk da na amsa masa da godiya tare da jiran bayanin dalilin ta'aziyar. Ya sanar da ni cewar wasu 'yan binduga 'yan ta'adda miyagu azzalumai fajirai fasikai zindikai tambadaddu sun kashe Malaminmu Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria! Hakika na ji kaduwa ainun da wannan bakin labari. Na yi masa addu'ar fatan samun rahama a wajen ubangiji.

Babu shakka, Sheikh Adam Albani ya rasu a tafarkin da muke fatan Allah ya dauki rayuwarmu akai. Wannan tafarki da muke kai, hakika an kashe Annabawa da Siddikai da salihan bayi, ba dan sun aikata wani laifi ba, sai dan sun bi tafarkin da Manzon Allah ya zo da shi. Wadan da suke yin wannan kisa, dangi da tsatso ne na wadan can miyagu azzalumai na farko da suke kashe mutanan kirki akan hanyar Allah. Wadan da suke yin wannan kisan, su sani cewa, barazanar kisa da tsoratarwa ba zai bata dusashe sautin gaskiya ba, sautin gaskiya sai ya daga yayi sama yana madaukaki, ko da kafurai da munafukai sun ki.

Ya 'yan uwa, yana da kyau mu tuna cewa, An kashe Sayyadina Umar Bin Khattab an kashe Usman Bin Affan an kashe Aliyu Abul Hasnain, an kashe manyan bayin Allah duk akan wannan tafarki. Irin  Wannan kisa da ake yiwa manyan bayin Allah wanda ya gangaro har kan Malamanmu na wannan zamanin, wani alkhairi ne wanda sai zababbu daga cikin bayin Allah suke tafiya ta wannan hanya. Kisan da aka yiwa Malam Adam Albani a daren jiya babu shakka ya tuna mana mutuwar Marigayi Sheikh Jaafar Adam, duk sun rasu akan wannan tafarki. Wadannan masu kisan ba zasu taba dainawa ba, domin mabiyan shaidan ne, dan Manzon Allah yayi ishara da hakan, a karshen zamani fadace-fadace da kisan babu gaira babu dalilai zai yawaita. Amma, su sani da sannu ajali zai riski kowannenmu ko mai daren dadewa, babu ko shakka akan cewa mutuwarmu ita ke yi mana gadin rayukanmu, lokacin da wa'adi ya yi, wayo da dabara ba zasu taba zama abin dogaro ba.

A saboda haka, yana da kyau mu sani, wannan kuma ba zai taba zama dalili na cewar mu zauna kara zube ana yi mana irin wannan kisan gillah ba. Ya zama dole mu tashi mu kawo karshen wannan al'amari, mu ne zamu baiwa Malamanmu kariya da garuruwanmu da dukiyoyinmu tare da taimakon Allah. Lallai ne dukkan hukumomin tsaron da abin ya shafa su tashi haikan wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma, wajibin gwamnati ne ta Tarayya da ta Jiha su kare martaba da jinin al'ummar da suke shugabanta.

Muna tunawa, miyagu Azzalumai cewar, tunda Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam ya bar duniya, babu wani mahaluki da zai yi saura a raye. Kowacce rai sai ta dandani zafin mutuwa kamar yadda Sheikh Albani tuni ya dandana nasa, babu wanda zai rage face mai riska ta riske shi. Manyan 'yan Ta'adda na da can da na wannan zamanin sun dandana zafin mutuwa kuma suna ganin sakamakon abinda suka aikata. Ina suke da dama da suka kashe mutanan da basu san hawa ba basu san sauka ba? A ranar Badar da aka kashe Manyan kafurai sai da Manzon Allah SAW ya tsaya a bakin rijiyar da aka zuba gawarwakin Mushrikai ya tambayesu Ya Utbah Ibn Rabi'ah! Ya Shaiba Ibn Rabi'ah shin kun sami alkawarin Allah gaskiya ne! Haka nan suma wadan da suka biyo tafarkinsu zasu samu alkawarin Allah gaskiya ne.

Ina mai amfani da wannan dama wajen taya 'yan uwana dubban jama'a dake ciki da wajen Najeriya ta'aziya da Alhinin wannan gagarumin rashi da mukai, wanda irinsa ne karo na biyu da ya faru garemu ta irin wannan hanya a wannan lokacin. Allah ya jikan Sheikh Adam Albani Zariya da Iyalinsa da Dansa, Allah ka karbesu a matsayin Shahidai, Allah ka daukaka darajarsu. Allah ka jikan Musulmi da duk inda suke. Babu shakka duk inda aka samu babban rashi irin na Malamai dole zukata su kadu hankula su dugunzuma idanu su raurawa, amma mu tuna idan akwai wani rashi da zai dugunzumar da mu shin akwai rashin da ya kai na Manzon Allah SAW? Ya Allah ka kashemu akan wannan tafarki.

Yasir Ramadan Gwale 
02-02-2014