Shugaba Goodluck Jonathan shine shugaban Najeriya na goma sha biyar (15) idan muka dauki lissafi daga Firaminista Sa Abubakar Tafawa Balewa da kuma shugaba Namandi Azzukuye. Shakka babu a tarihin Najeriya nan gaba ba zai taba cika ba, idan ba'a yi maganar shugaba na goma sha biyar ba wato Goodluck Ebele Azikewe Jonathan, za'a tuna da shugaban kasane ba dan yayi abin kirki ba, sai dan a lokacin sa ne Najeriya ta samu kanta a cikin wani mawuyacin halin da bata taba samun kanta a ciki ba tundaga shekarar 1914 har kawo wannan lokaci.
A lokacin Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne cin-hanci da rashawa ya kai magaryar tukewa, ta yadda babu wani mutum daga cikin gwamnatinsa da za'a zazzage ba'a sameshi da kashi a gindinsa ba. A lokacin shugaba Goodluck Jonathan aka taba samun manyan jami'an gwamnati da muguwar sata da ta shallake hankali da tunanin dukkan wani mai tunani, cin hanci bai tsaya iyakar jami'an gwamanti ba kadai, kusan yayiwa shugaban mugun daurin da bazai taba iya kwancewa ba.
Shugaban kasa Goodluck Jonathan yaki bayyana abinda ya mallaka a zamanin mulkinsa kamar yadda magabacinsa Malam Umaru Musa 'YarAdua (Allah ya jikansa) yayi, domin kuwa rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban a kwance yake akan dukiyar haram faca faca. Haka kuma ana yiwa manyan na hannun damansa zargin cin-hanci mai karfin gaske wanda ya hada da mutum mafi kusanci da shi a majalisar zartarwa wato ministar albarkatun manfetur madam Dazani Alasan Maduwake da kuma hamshakan mutane irinsu fitaccan dan kasuwannan wanda cin hanci ya dabaibaye wato cif Femi Otedila.
Haka kuma shugaban ya kanainaye kansa da miyagun barayi azzalumai irinsu wani tsohon najadu da ake kira cif Tony Anenih wanda ya taba riki mukamin shugaban kwamitin amitattun PDP kuma tsohon ministan ayyuka na gwamnatin tarayya a zamanin Obasanjo, a lokacin da mista Anineh yake rike da mukamin minista ne ya shaidawa maname labarai a ranar 6 ga watan disambar 1999 cewar babu wata kasa da zata cigaba ba tare da kyawawan hanyoyi na gwamnatin tarayya ba, dan haka ya fitar da kwangilar gyara da garambawul na manyan titunan gwamntin tarayya inda aka fitar da zunzurutun kudi Naira Biliyan 200 daga 1999 zuwa 2002, daga bisani aka nemi kudin ko sama ko kasa, kuma babu aikin titunan, wanda mujallar Tell Magazine ta 20 ga watan disambar 1999 ta tallata aikin kwangilar. Haka kuma, a ranar 25 da Oktobar 2002 sai da shugaban kasa na wannan lokacin Olushegun Obasanjo ya shaidawa manema Labarai cewar hankalinsa ya tashi matuka da irin yadda ya samu labarin halin da titunan gwamnatin tarayya suke ciki, amma abin mamakin shine ba'a nemi Mista Anenih yayi bayanin yadda aka yi da kudin aikin titunan ba. Irin wadannan muggan barayi su Tony Anenih sune wadan da Shugaban kasa yake ganin sunfi kowa tsarki wajen iya shirya sata da damfara da sunan aikin gwamnati, inda yanzu haka aka sake bashi wani muhimmin mukami na shugaban hukumar Nigerian Port Authority.
Har ila yau 'yan Najeriya zasu jima basu manta da shugaban kasa Goodluck ba kasancewar a lokacinsa ne mutane irinsu Henry Okah sukayi ikirarin dasawa da kuma tayar da Bom a lokacin bikin samun 'yancin kai, kuma suka aiwatar da wannan nufi nasu, amma saboda tsabar rashin ta ido shugaban ya fito kafafan watsa labarai yana cewa wannan hari ba su Henry Okah bane suka kaishi.
Idan muka kalli yankin kudu maso yamma da kuryar kudancin kasararnan zamu ga cewar satar mutane tare da yin garkuwa da su ta zama abun yayi, ta yadda masu wannan sana'a suke cigaba da cin karansu babu babbaka, abinda ya kai har mahaifiyar Ministar gamayyar tattalin arziki Ungozi Okwanji Iwela aka sace kuma aka nemi kudin fansa kamar yadda al'adar satar take. Haka kuma, masu fasa bututu da satar gurbataccan manfetur sun cigaba da cin kasuwarsu ta wannan aika aika, har sai da ta kai wani kwamiti da shugaban kasar ya kafa karkashin Jagorancin Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewar raba dai-dai ake yi tsakanin Najeriya da barayin danyan manfetur. Sannan saboda shugaban kasa ya kara gwangwaje wadannan barayi 'yan ta'adda yace shi da kansa ya nadasu masu gadin wadannan bututun mai sannan ya sanya musu wani katafarn albashi na Dalar Amurka Miliyan 350 a kowacce shekara, lallai za'a jima ana tunawa da shugaba Goodluck ta wannan janibi.
A yankin tsakiyar Najeriya kuwa anyi ta samun rikicin addini da na kabilanci babu kakkautawa a zamanin shugaba Goodluck Jonatahn a jihar Filato da kuma rikicin manoma da makiyaya a jihar Nassarawa da Bunuwai. Sannan kuma anyiwa wasu musulmi korar kare a karamar hukumar Mokwa dake jihar Neja ko wadanda aka fi sani da 'yan Darul Islam, wanda dukkan bayanai da bincike suka tabbatar da mutanan wannan gari basa wata barazana ga tsaro ko zaman lafiya.
Mutanan Arewa gaba daya kuwa zasu jima suna tunawa da shugaba Goodluck Jonathan, saboda ansamu asarar rayukan da ba'a taba samu ba a wannan yanki karkashin wannan shugaba. Haka kuma jihar Borno ta zama wata karamar Bagadaza a Najeriya musamman lokacin wannan shugaban, domin ankashe muhimman mutane da suka hada da Madu Fannami Gubio wani dan takarar gwamna a jihar ta Borno da kuma Manjo Mamman Shuwa wanda saboda sake da rashin tsaro wasu 'yan ta'adda suka haura gidansa suka kashe shi kuma suka gudu.
A kano kuwa kanawa zasu jima suna tuna ranar 20 ga watan Janairun shekarar da ta gabata domin a wannan lokacin aka samu abinda ba'a taba mafarkin samu ba na tashin bamabamai babu kakkautawa a ciki da wajen birnin kano, wanda rahotanni mabanbanta suka nuna cewa ansamu tashin bamabamai sama da guda sittin (60) a wannan rana, da asarar rayukan mutane sama da 250 duk a wannan rana.
Idan muka leka jihar Kaduna kuwa al'ummar Musulmi da suke a kudancin Kaduna zasu jima basu manta da watan Afrilun 2011 ba, domin ankashe mutane bila adadun sakamakon rikicin bayan zabe, da kisan kan-mai uwa da wabi. Haka kuma, jihohi irinsu Adamawa da Gwambe da Bauchi da Kogi da Taraba suma bazasu manta da shugaba Goodluck Jonathan ba domin kuwa a karan farko a lokacinsa wadannan al'ummomi suka san karar tashin bamabamai. Sannan kuma a lokacin wannan shugaba ne 'yan Najeriya suke karyawa duk safiya da kalmomi irisu GARKUWA DA MUTANE, BOKO HARAM, CIN-HANCI DA RASHAWA, 'YAN TA'ADDAN NEJA DALTA da sauransu.
Shakka babu idan za'a yi bayanin abubuwan takaici da Allawadai da Alla-tsine da suka faru a Najeriya a zamanin shugaba Goodluck Jonathan za'a jima ana zayyanosu. Daga karshe muna rokon ALLAH da sunansa kyawawa kuma tsarkaka, Ya ALLAH kada ka sake Jarrabarmu da Mutum irin wannan shugaban na yanzu Goodluck Jonathan, Ya ALLAH ka jarrabemu da shugaban da zaiji-kanmu ya tausaya mana.
No comments:
Post a Comment