Wata rana wani Bawan
Allah da yake gina gidansa, ya gayyaceni akan na raka shi gewayar ganin gidan
da yake ginawa. Haka kuwa aka yi, domin mun je a wani irin lumshi da kowa zai
so ya danyi tattaki a cikinsa, ba jimawa muka zo unguwar da gidan yake, kasancewar
wajen sabon wajene dukkan gidajan da suke kan layin sabbin gidaje ne da ake
ginawa, wannan ta sanya muka tarar da tsibi tsibin yashi da duwatsu da kan-kura akan layin, dole ta
sanya muka ajjiye mota daga nesa muka taka sayyadarmu domin karasawa gidan.
Isarmu kofar gidan ke da wuya na kalli gidan nayiwa
maigidan murna kasancewar gidan ya kasaita bayan kasancewarsa katafare harda
masallaci a jikin gidan da ake ginawa tare. Mai gida ya shige cikin gidansa kai
tsaye domin yaga yadda ake gini, Ni kuma na nufi dan-karamin masallacin da ke
jikin gidan wanda ake ginawa, shiga cikin masallaci na hangi wani abu da na
kasa gasgata ganina da yake daga nesa na hango.
Ina shiga cikin harabar masallacin ta kofar kudu
kawai sai naga wani baho madaidaici dauke da wasu kananan kwalaben ruwa da wasu
jike-jike a ciki. Abinda ya fara zuwa Raina shine wannan irin kayan masu tallan
maganin gargajiya ne da suke shigowa cikin birni daga Panshekara, tsammanina ko
na tsintuwa ne, ban damu ba na daga kaina sama daga bakin kofa ina kallon gini,
can sai naji sukur-sukur alamar ana motsi, duk da haka ban kawo wani abu mara
kyau na faruwa ba, kawai sai na shiga domin ganin meye yake motsi, cikin mamaki
na hangi bayan mutum a inda Liman yake tsayawa, na kalli mutumin da alama yana
yin wani abu cikin gaggawa, na kara matsawa sosai, sai na hangi wani mutum mai
matsakaitan shekaru yana sauri yana daura tazaugen wandonsa kansa babu hula, da
alamar a rikice yake, bayansa kuma wata yarinya na hanga tana kokarin gyara
kayan jikinta.
Na tsaya ina mamakin abinda idona ya gani, yarinyar
nan ta tashi cikin hanzari ta dauki wannan baho ta kinkima tayi waje. Banyi
magana ba, wannan mutumin kuwa ya zube a gabana yana rokona dan Allah malam ka
rufa min asiri kada ka gayawa Alhaji ka ganni! Nikam Ina tsaye na kasa magana.
Mutumin nan da yaga ban kulashi ba, ya leka waje bai hangi kowaba, har ya fita
sai ya dawo ya dauki hularsa, kafin ya dauki hular tuni ni kuma na fice daga
cikin masallacin.
Na shiga cikin gidan ina mai mamakin abinda na
gani, Mutumin nan hankalinsa ya tashi sosai, domin yana yimun wani irin kallo
na intausaya masa. Haka dai har muka gama ganin ginin nan bashi da kuzari, yana
tsoron kada na fadi abun da na gani. Hakika abinda na gani ya tunasar da ni
abubuwa da yawa da na sha-ji ana fade cewa ana yin Lalata da yara 'yan talle a
cikin kangwaye. Lallai acikin masu yin sana'ar gini akwai mutanan kirki kuma
akwai na banza kamar yadda kowanne fannin rayuwa ake samu. Allah ya shirya ya
karemu da mugun-ji da mugun-gani.
to Allah Ya kare mu daga sharrin kawunanmu da na shaydan.
ReplyDeleteHakika ya kamata duk masu kangwaye suyi kokarin ginesu don wallahi marasa gaskiya sunyi yawa, kusan ko ina akwaisu. Saboda haka, abin da baka zataba sai kaga ya faru.