Thursday, December 6, 2012

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN


BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN



Ya maigirma shugaban kasa ina fatan wannan wasika tawa zata sameka cikin Aminci, Ina kuma fatan zaka samu zarafin karanta wannan wasika tawa. A matsayina na dan Najeriya na halaliya  ina ganin ina da hakkin yin kira a gareka dan gane da wani mataki mai cike da hadari da gwamnatinka ta dauka. Ko shakka babu wannan mataki bai kamaci wannan gwamnati taka ba, domin lamarine da ba zai haifarwa da kasar nan da mai ido ba. Ina mai cike da masaniyar cewa kana da mashawarta wadanda aikinsu ne su baka shawara kafin daukan dukkan wani mataki ko yanke dukkan wani hukunci, domin a matsayinka na shugaban kasa dole ka ringa tuntubar mashawartanka domin samun shawara ta gari kafin zartar da dukkan irin wani hukunci. Haka kuma, ina mai cike da masaniyar cewa mafiya yawan masu baka shawara ba al'ummar kasarnan ce a gabansu ba, illa kawai suna baka shawarane bisa san ransu da san zuciyarsu, sama da doraka akan turba sahihiya wadda zata yi maka jagorar samun nasara.

Ya maigirma shugaban kasa, bayan wannan abin Ashsha da ya faru na kai harin bom a coci dake cikin barikin sojoji a Jaji, shugaban hafsan sojojin Najeriya Adimiral Ola Saad Ibrahim ya bayar da umarnin sauke wasu manyan sojoji daga mukamansu a barikin soji dake jaji. Wadannan mutane sune Air Vice Marshal Abdullahi Kure da Manjo Janaral Muhammad D Isa. A matsayinka na shugaban kwamandan rundunar askarawan sojojin Najeriya, nayi Imani babu yadda za'a dauki irin wannan mataki mai matukar hadari ba tare da kana da masaniya akai ba, na tabbatar baza'a kasa tuntubar mashawarta ba kafin daukar wannan mataki mai cike da hadari, ko dai an baka wannan shawarar da gayya ne koma meye, lallai wannan wani muhimmin batu ne da ya kamata shugaban kasa ya yi masa karatun ta nutsu. Amma dai abu mafi muhimmanci shine yadda korar wadannan mutane zai iya haifar da gagarumar baraka a wannan kasa, wanda zan zayyano su kamar haka:

Abu na farko, wadannan manyan sojoji an sauke su ne daga mukamansu ba tare da wata kwakwkwarar hujja ko wani dalili gamsashshe ba. Yana da kyau ace anyi taka tsan-tsan sosai wajen daukar irin wannan mataki, domin sanin kowa ne Najeriya kasace da take a cikin wani irin wadi da ya yi kama da na tsaka mai wuya, sannan kuma Addini da kabila suna taka muhimmiyar rawa a dukkan wasu bangarori dangane da yadda ake tafiyar da wannan kasa. Ko wanne irin yanayi ko hali ake ciki alhakin shugaba ne ya tabbatar da hadin kan wannan kasa tare da kaucewa dukkan wani abu da zai iya kawo zaman doya da manja ko yamusta kasar.

Abu na biyu, dukkan wadannan manyan sojoji da aka cire daga kan mukamansu gaba dayansu Musulumi ne, sannan aka yi gaggawar maye gurbinsu da Kiristoci. A bisa tsarin aiki ana iya canzawa mutum wajen aiki ne a duk lokacin da bukatar haka ta taso, kuma a matsayinka na shugaban kasa kuma shugaban rundunar tsaro ta Najeriya lallai akwai bukatar yin la'akari da halin da kasarnan take ciki na sukurkucewar al'amuran tsaro kafin daukar wannan mataki. Domin har yanzu bamu gama farfadowa daga mawuyacin halin da muka shiga ba tun bayan rikicin da ya biyo bayan sakamakon zaben 2011 da ya gabata. Lallai shugaban kasa ya kamata ya yi aiki da lura musamman wajen sauya Musulmi da wanda ba musulmi ba, musamman waje irin wannan mai cike da kalubale, domin daukar irin wannan mataki abu ne da zai iya tayar da kura da yamusta hazo.

Abu na uku, maye gurbin wadannan manyan sojoji musulmi da kiristoci a cikin irin wannan mawuyacin lokaci da muke ciki na gaba kura baya sayaki, kamar yadda muka karanta a shafukan jaridu cewa yanzu maganar da ake yi Barikin sojoji dake jaji ta dawo karkashin kulawar kiristoci tun bayan sauke Air Marshal Abdullahi Kure da Manjo Janar Muhammad D Isa, ina son shugaban kasa ya kwan da sanin cewar tabbas wannan wani mataki ya dauka na wargatsa kasarnan domin shugabanni na addini da shugabanni na al'umma bazasu zura ido suna kallon irin wannan abun yana faruwa ba, kuma za'a ringa kallon wannan a matsayin wani mataki na kakkabe hannun duk wasu musulmi daga Manyan ayyuka musamman irin wannan mai matukar muhimmanci a wannan lokaci da muke ciki.

Ya maigirma shugaban kasa, Babban dalilin rubuta maka wannan wasika, da kuma buga maka wadannan misalai da na kawo shine, domin na ja hankalinka akan wata guguwa da ka iya kunno kai a tsakanin rundunonin sojin kasarnan, musamman tsakanin Musulmi da Kirista. Tabbas sojojin Najeriya suna cikin wani hali da muke fatan samun tabbataccen hadinkai a tsakanin rundunonin sojin dake wannan kasa. Domin a baya lokacin da kasarnan ta samu kanta a cikin wani mawuyacin hali, wadannan sojoji sune suka sadaukar da rayuwarsu wajen tabbatar da dorewar wannan kasar, sun taka muhimmiyar rawa a yakin basasar kasarnan wajen maido da ita kasa daya al'umma daya. Sojojinmu ba wai kawai kokarinsu iya Najeriya ya tsaya ba, sun taimaka gaya wajen dawo da doka da oda a kasashe makwabta da dama, misali, kasar kwango a shekarar 1950, da kuma kasar Saliyo da Laberiya a shekarar 1990, haka kuma yanzu haka sojojinmu suna aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Darfur. Amma abin da yafi kowanne muhimmanci wanda sojoji suka yi shine kauda kansu daga al'amuran siyasa da sukayi tun bayan da mulki ya komo hannu farar hula a shekarar 1999, shakka babu wannan shine lokaci mai tsawo a tarihin kasarnan wanda aka samu dogon lokaci ana mulkin siyasa ba tare da samun wani tsaiko daga soja ba. Haka kuma, duk da halin rashin tabbas da aka shiga a kasarnan lokacin rashin lafiya marigayi shugaban kasa Malam Mumaru Musa 'YarAdua soja sun kauda kai daga shiga al'amuran siyasa, inda suka yi zamansu a cikin barukokinsu, wannan ce ta baka damar zama mukaddashin shugaban kasa a wancan lokaci, har kuma daga baya ka zama shugaban kasa mai cikakken iko lokacin da mutuwa ta yiwa marigayi YarAdua yankan hanzari. A wancan lokaci duka sojojin kasarnan Musulmi da Kirista sun yi aike tare wajen ganin lamura basu lalace ba, kuma an samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu. Tabbas shugaban kasa zai iya daukar wani muhimmin darasi dangane da wannan abin da ya faru.

Daga karshe, Ya maigirma shugaban kasa, ina mai baka shawara ka guji dukkan wani abu da zai iya yamusta kasarnan musamman ta fuskar soji, domin sakamakon abinda zai biyu baya ba zai zama mai kyau ga al'ummar kasarnan ba. Kuma ina fatan shugaban kasa zai yi duba na tsanaki dangane da abinda ya faru a kasarnan tundaga shekarun 1960 har zuwa shekarun 1970 sannan ya duba irin darauusan da suke cikin wannan zamani da kuma kallon irin yadda al'amura zasu wakana nan gaba. Ina kuma fatan shugaban kasa ya tattauna sosai da magabatansa domin samun sahihan bayanai dangane da harkar soji a Najeriya.

Allah ya taimaki Tarayyar Najeriya.

Wannan wasika na samota ne daga wajen Dr Muhammad Jameel Yusha'u, wadda ya rubuta da turanci domin amfanin wadan da basu samu zarafin karanta ta turancin ba.

Yasir 
Ramadan Gwale.
yasirraramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com/

No comments:

Post a Comment