RISALA ZUWA GA MAI GIRMA
GWAMNA: Engr (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso FNSE
Bayan Sallama irin ta addinin musulunci, Assalamu Alaikum, Ya
maigirma Gwamna, ina son nayi amfani da wannan damar wajen yabawa tare da
jinjina a gareka bisa namijin kokari da gwamantinka ta yi wajen samarwa da
yankinmu na Arewa maso yamma jami’a wadda aka radawa sunan yankin, hakika
wannan wani babban ci-gaba ne kuma abin a yaba, mun gode maigirma gwman, haka
kuma, sauran kwalejojin da aka kirkiro ko ake kan kirkirowa wannanma wani
babban al’amari ne kuma abin a yaba, sannan uwa uba, ga dimbin al’ummar kano da
aka dauka aka kaisu kasashen da dama domin karo ilimi wannan ma wani muhimmin
ci-gabane ya maigirma gwamna muna yabawa tare da fatan alheri. Sannan kuma, dole
mu gode tare da yabawa musamman yadda gwamnati ke ci-gaba da kawata cikin
birnin kano, da kunna fitulu a manyan tituna, da tsabtace gari, duk wannan abun
a gode ne kuma abin a yaba.
Ya maigirma gwamna, Ina mai amfani da wannan damar wajen yin
fatan alheri a gareka da kuma gwamnatinka. Hakika Ya maigirma Gwamna wannan
wani muhimmin al’amari ne akanka a matsayinka na shugabanmu kuma jagoran jihar
kano, ina fatan ALLAH ya sa ka gama da wannan shugabanci lafiya. Ya maigirma
gwamna na kira wannan sako nawa zuwa gareka da sunan RISALA wanda asali kalmar
larabci ce, wadda take nufin SAKO, ina fata sakona ya isa zuwa gareka cikin
aminci.
Ya maigirma gwamna a ranar 21 ga watan Nuwamban da ya gabata, a
shafinka na facebook ka saki wani sako kamar haka “Mu duk wata sarauta ta gado
muna yinta, amma sarauta ta kale ba ruwanmu da ita, mu duk wani nadi da baka
gajeshi ba sunansa TUKUNKUNJI” wannan shine sakon da ya fito daga shafinka a
wannan rana, inda kuma ya ja hankalin mutane da yawa. Ya maigirma gwamna, kai
shugabane kuma jagora ne na duk al’ummar Jihar kano walau ‘ya ‘yanta ne ko baki,
duk mutumin da yake kano karkashin ikonka yake. Ya maigirma Gwamna, hakika
wannan magana da ta fito ta shafinka magana ce ta kananan mutane bayan kuma mun
san kai ba karamin mutum bane.
Ya maigirma gwamna, duk wani mutumin kano na haliliya yana
girmama masarautar kano. Duk wata sarauta da mai martaba sarki ya bayar ga kowa
ye, muna kyautata zaton cewa mai martaba sarki ba zai baiwa mutumin banza
sarauta ba, haka kuma, duk wata sarauta da wani ke da ita a jihar kano indai
masarauta ce ta bashi muna kallon masarauta ne ba shi mai rike da sarautar ba.
Ya maigirma gwamna akwai al’amura da yawa a gabanka wadanda ya kamata su dauke
maka hankali sama da kankananan maganganu irin wadannan. Ya maigirma Gwamna,
dukkan gwamnonin Najeriya 36 kai yayane a garesu domin lokacin da ka zama
gwamnan farar hula a zangonka na farko, wasu daga cikinsu ko ritaya daga aikin
gwamnati basu yi ba, abin da muke fata, Ya maigirma gwaman, shine ka zame musu
alkibla kuma jagora, kamar yadda Jihar kano ta yiwa sauran jihohi zarra a fadin
tarayyar Najeriya, haka muke fatan ka yi zarra a tsakanin takwarorinka
gwamnaoni.
Ya maigirma gwamna, duk wani mutumin kano burinsa jihar kano ta
ci gaba ko da kuwa waye yake rike da akalar gwamnati a jihar kano. Col. Dominc
Oneye ba Bahaushe bane karewa ba ma Musulmi bane amma ya bautawa jihar kano da
al’ummar jihar kano, haka muke fatan duk wani mutum da zai hidimtawa jihar kano
ko waye kuma ko daga ina yake matukar zai kiyaye da yanayinmu da addininmu, Ya maigirma
gwamna, hakika muna kyautata maka zaton cewa kai me kishin jihar kano ne da
kuma son ci-gabanta da al’ummarta, kuma Alhamdulillah babu abinda zamu ce sai
ala-san-barka.
Ya maigirma gwamna, a kwanakin baya kayi wata muhimmiyar magana
wadda ta tayar da kura musamman a majalisarku ta gwamnonin Najeriya, wannan
magana ta rabon arzikin kasa, da kuma batun man da ake hakowa a cikin teku da
kuma man da ake hakowa a tsandauri (off-shore On-shore Dichotomy), Ya maigirma
gwamna lallai wannan magana da ka kawo kuma da yawa daga cikin gwamnoni ka
motsasu dangane da wannan batu, irinsu muke fatan ji daga bakinka a koda
yaushe, domin kare martabar yankin Arewa da al’ummar Hausawa, amma Ya maigirma
gwamna, yawan maida martani ga Babban abokinka kuma Amininka tsohon gwamna
Malam Dr. Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, wannan ba girmanka bane Ya maigirma
gwamna. Malam Shekarau ya yi gwamna a Kano kuma ya bautawa jihar kano tsahon wa’adinsa,
fatanmu shine ku kasance abokai kuma aminan juna kasancewar kun hidimtawa al’ummar
jihar kano.
Ya maigirma gwamna, a har kullum a rayuwa bama fatan a ce jiya
tafi yau, domin wannan shine ma’auni da yake nuna rashin ci-gaba, kullum
fatanmu a ce Yau tafi Jiya. Batun da ake ta yawan yi na cewa gwamnatin da ta
gabace ka ta Aminika, kayi aikin da bata yi ba a cikin shekaru takwas, wallahi
kullum fatanmu shine na-gaba ya fi na baya, idan har kullum zamu ringa cewa na
baya yafi na gaba lallai babu ci-gaba, dan haka fatanmu shine gwamnatinka ta yi
sama da abinda gwamnatin baya bata yi ba, kamar yadda muke fatan duk gwamnan da
zai biyo bayanka ya yi sama da abinda ka yi, wannan shine zai daukaka martaba
da kimar jihar kano.
Ya maigirma gwamna, babbar matsalar da take damun al’ummar jihar
kano bata wuce matsalar tsaro da zaman zullumi da jama’a suke ciki ba. Ya
maigimra gwamna lallai kamar yadda kake da labari kuma ka sani al’umma suna
cikin hali na rashin kwanciyar hankali da zaman zullumi wanda yau Takai mutum
hatta a cikin gidansa ba shi da kwanciyar hankali kasancewar yana tsoron ko za’a
iya jefo masa wani abu da zai halaka shi nan take, Ya maigirma Gwamna nemo
hanyar da za’a magance wadannan matsaloli sune abinda suka kamata su daukewa
gwamnatinka hankali, ba maganganu irin na hamayya ba, hakika kamar yadda muka
sani kuna yin kokari akan haka, fatanmu kuma shine ku kara kokari akan kokarin
da kuka yi a baya.
Ya maigirma gwamna, Lallai babban abinda mu al’ummar jihar kano
muka dogara da shi shine kasuwanci (saye da sayarwa) lallai makiya da mahassada
suna ta yin aiki babu dare babu rana wajen kassara kasuwancinmu, domin yanzu
duk kasuwanninmu sun rage lokacin tashi, kasancewar mafiya yawansu matasa ne,
masu amfani da kananan ababen hawa, ga kuma dokokin da aka sanya saboda su,
lallai ya maigirma gwamna a duba wannan lamari da halin da al’umma suke ciki,
domin wani ya fito kasuwa ana kiran sallar la’asar kuma za’a fara tunanin tashi
daga kasuwa wanda ko shakka babu wannan gurgunata kasuwanci ne ainun.
Daga karshe, Ya maigirma gwamna ina fatan alheri a gareka da
gwamnatinka. Ina kuma yi maka addu’ah ta musamman tare da tawassuli da sunayan
ALLAH tsarkaka madaukaka ALLAH ya sahale maka gamawa lafiya da mulkinka, ALLAH
ya yi maka jagora a dukkan lamuran rayuwaka, sannan ina fata Ya maigirma gwamna
yawan kalamai na hamayya da suke fitowa daga bakinka zasu samu raguwa, duk da
cewa ba laifi bane idankayi hakan a siyasance, amma muna ganin girmanka da
kimarka ya wuce a ji wasu kalaman daga bakinka. Ya maigirma gwamna ina mai yi muku
fatan alheri da fatan gamawa da duniya lafiya kai da Babban abokinka kuma
Amininka Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano. ALLAH ya taimaki Jihar Kano ya
bamu lafiya da zama lafiya.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
No comments:
Post a Comment