SANUSI LAMIDO SANUSI: BAZAN
DAINA MAGANA BA
Gwmanan Babban Bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi ya
mayar da martani a jiya dan gane da masu sukarsa akan kalaman da ya yi a makon
da ya gabata. A makon da ya gabata dai an ruwaito Sanusi Lamido yana cewa kusan
kashi 70 na dukiyar kasar nan gwamnati take kashewa kanta, yayin da ake kashewa
al’ummar kasa kashi 30 kacal, ya ce tattalin arziki zai bunkasa ne idan aka
zabtare kashi 50 na masu karbar dirka dirkan albashi.
Tun bayan da Sanusi ya yi wadancan kamalamai ne ake ta mayar
masa da martani kama daga ‘yan majalisar tarayya da kungiyoyin kwadago da
sauran al’umma. Inda suke ta kira ga gwamnati akan lallai ta sallame shi daga
Babban banki.
Amma sanusi da ya yi jawabi a wajen taron National Econmic
Summit ya mayar da martani akan masu sukar kalamansa. Ya ce shi kam ba zai taba
daina magana ba, dole ne na cigaba da yin fashin baki akan tattalin arziki inji
shi. Zan ta yin fashin baki akan sha’anin tattalin arziki har sai naga al’amura
sun daidaita. Kuma Ina son jama’a su fahimta daman ni aikina ba yana nufin
kullum na saka jama’a cikin farinciki bane. Duk mai bukatar farin ciki da
annashuwa ta ya tafi wajen iyalisan su kashe dare. Dan haka jama’a su sani
aikina shine na gano yadda tattalin arzikin kasarmu zai samu bunkasa. Ai daga
lokacin da muka daina magana saboda tsoron kada a kalubalance mu, to daga
wannan lokacin tattalin arzikinmu zai shiga cikin halin ha’ula’i.
Sanusi Lamido ya zargi kundin tsarin mulkin Najeriya da cewa ya
sanya al’umma cikin mawuyacin hali ta hanyar sahalewa da masu rike da mukaman
siyasa masu yawan gaske, wadan da suke karbar dirka dirkan albashi da alawus ba
tare da sunyi wani aiki na ku zo mu gani ba. Dan haka wadannan wasu matsaloli
ne da dole mu kalubalance su, kuma mu samo hanya sahihiya da za’a fita daga
cikin al-mubazzaranci da dukiyar kasa. Yana da kyau mu fahimta gwamnati ba wai
kawai tana biyan ma’aikata albashi bane. Muna da kananan hukumomi 774 kowacce
daga cikinsu tana da shugaba da mataimaki da akalla kansiloli 10, shin nawa
kake jin yake tafiya wajen hidimta musu?
Bari mu buga misali da jihar kano, idan ka dauki tsohuwar jihar
kano, yanzu ta zama Kano da Jigawa. Lokacin da tana a matsayin jiha daya tana
da gwamna daya da mataimaki da kwamishinoni akalla ka ce goma, amma yanzu fa?
Waccan jihar guda daya ta zama biyu, dan haka kana da gwaman biyu mataimakin
gwamna biyu, idan da kwamishinoni 10 ne yanzu sun zama kusan 40 da ‘yan
majalisu sama da 80, masu bada shawara da mataimaka na musamman kuwa ALLAH ne
kadai ya san yawan wasu. Nawa kuke zaton
ana kashewa wajen yiwa wadannan mutane hidima? Maganar ba wai ta kungiyar
kwadago ko majalisa bace, muna maganar ‘yan Najeriya ne kusan miliyan 167. Dan
haka wannan kundin tsarin mulki da muke amfani da shi, kwata kwata baida wata
ma’ana, ga al’ummar kasa.
Kundn tsarin mulki yayi tanadin cewa dole ne kowace jiha a fadin
tarayyar Najeriya ta samu minista guda daya wanda zai wakilce ta. Bari na
tambayi masu ilimi, shin meye alakar minista da jiharsa? Wannan yana nuna kenan
idan kana da jihohi 50 dole ka samu ministoci 50, haka kuma, idan kana da
jihohi 100 dole ka samu ministoci 100 ko shakka babu wannan dirkaniyace a cikin
kundin tsarin mulki. Me ya sa mu kadaine muke da irin wannan a duk fadin
Nahiyar Afurka?
Malam Sanusi Lamido ya kara da cewa hakkin gwamnati ne ta kula
da dukkan bukatun al’ummarta. Yanzu idan har za’a ce gwamnati na kashe kashi 70
na kudin kasa wajen yiwa kanta da ma’aikatanta hidima, sannan ta kashe kashi 30
kacal domin al’ummar kasa, shin korar Sanusi daga aiki zai zama masalaha kenan?
Yanzu ‘yan majalisa suna gyaran kundin tsarin mulki, bamu da bukatar ‘yan
majalisa 500 domin su yi doka. Ya kara da cewa wata babbar matsala da Najeriya
take fuskanta bayan cin-hanci ita ce rashin mutane na gari a matsayin
shugabanni. Ba'a yin k’mai bisa doka, am maida komai ya zama kabilanci da
bangaranci, ga mutane da suka cancanci a basu wasu muhimman ayyuka da zasu
hidmtawa al’umma amma sai a kauce musu saboda bambancin kabila.
Kuma ina kalubalantar ku kanku ‘yan Najeriya mai makon jama’a su
mayar da hankali wajen tattauna muhimman al’amura da suka shafi cigaban wannan
kasa sai suka bige da tattauna wace irin mota wane yake shiga? Ina wane yake
zuwa? Me ya sa bazamu maida hankali wajen tambayar kanmu shin titi mai tsawon
kilomita nawa aka gina mana a yankunanmu ba? Me ya sa bazamu maida hankali
wajen tattaunawa akan me ya sa haryanzu wutar lantarki bata samu ba? Shin yara
nawa ne suka samu nasarar cin darasin Turanci da Lissafi a makarantun
sakandare! Lallai muna da babban kalubale kuma muna da babbar matsala agabanmu.
No comments:
Post a Comment