ME KA SANI DAN-GANE DA HALITTAR
RAKUMI
Rakumi daya ne daga
cikin dabbobin ni’ima guda huda da ALLAH ya yi yiwa musulmi nuni izuwa garesu
domin yin lallai ko hadaya. Rakumi wata dabbace da ALLAH ya halitta ba domin
kawai a yanka a ci ba, rakumi kan yiwa mutane hidima da dawainiya, ALLAH ya
halicci mafiya yawan rakuma a yanki mai cike da sahara, yanki mai zafin rana.
Yankin gabas ta tsakiya kusan nanne madinar Rakuma domin ALLAH ya halicci
miliyoyin rakuma a wannan yanki haka kuma yankin Arewa wacin Afurka nanma akwai
rakuma masu yawan gaske, kasar Somaliya kusan ita ce kasar da tafi kowace kasa
yawan rakuma a yankin da ake kira kahon Afurka. Haka kuma, akwai wasu miliyoyin
rakuman a yankin Asiya mai nisa wato kasashen Azarbaijan da Tajikistan da
Turkuminstan da Uzbakistan da Kyrgistan suma suna da tarin rakuma masu yawan
gaske, daga nan kuma sai Arewaci da kudancin Amerika wanda rakumansu kalilan ne
sosai.
Rakuman da suke a yankin
Sahara sun sha bamban da rakuman da suke a yankin Asiya mai nisa musamman a
wadancan kasashen da muka lissafa. Rakumansu ba kamar sauran rakuma bane na
gabas ta tsakiya ko Arewacin Afurka, rakuma a yankin suna da yalwar gashi mai
yawa kasancewar yanki ne da suke da yanayi na dusar kankara mai yawan gaske,
dan haka mafiya yawan dabbobinsu suna da gashi mai yawa a jikinsu, haka suma
rakumansu suke. Amma bayananmu zasu fi karkata ne zuwa ga rakuman da suke rayuwa
cikin sahara.
Rakumi yana iya yin gudu
na tafiyar kilomita 65 a cikin awa guda ba tare da ya gajiya ba. ALLAH mai
girma da daukaka ya sanyawa rakumi juriya wajen tafiya, domin a mafi yawancin
lokuta sai dai mai jan rakumi ya gaji ya huta amma ba dai rakumin ya gaji ba.
Haka kuma, duk da irin wannan juriya ta rakumi sai ya dauki lokaci bai sha-ruwa
ba, domin rakumi yakan iya kai watanni uku ba tare da ya sha ruwa ba,
kasancewar ALLAH ya halitta masa wani tanki a cikinsa wanda yake adana ruwa.
Rakumi yakan sha ruwa lita 200 kimamin galan 53 a cikin mintuna uku, rakumi na
iya shan ruwan da ya kai lita 600 a lokaci guda.
ALLAH subhanahuwata ala
ya halicci wasu dabbobi da hikimomi da baiwa mai yawan gaske, kamar yadda ya
halicci kare zai iya sansano wani abu da aka boye ko gano inda aka boye shi,
haka shima rakumi, idan yana bukatar ruwa yana iya sansano inda ruwa yake daga
kimanin nisan mita 200, kamar yadda Shamuwa kan sansano zuwan damina, a wasu
garuruwan da dama alamun zuwan ruwan sama ko damina shine ganin Shamuwa tana ya
yawo domin tana jiyo alamar zuwan ruwa. ALLAH buwayi gagara misali.
Duk acikin dabbobin da
ALLAH ya halatta cin su Rakumi ne dabbar da yafi kowacce kawaici da kunya da
kuma sanin ya kamata. Rakumi yana da ladabi ainun domin yana bin duk umarnin da
aka bashi baya kaucewa, kamar yadda duk inda aka aiki jaki zaije ya dawo ba
tare da ya tsaya ba, haka shima rakumi yake, sannan yana daga cikin hikimar da
ALLAH ya yiwa rakumi baya mantuwa ko da kuwa shekaru nawa zai dauka, rakumi
baya manta uwarsa ko ubansa, sannan baya manta ‘yan uwansa ko abokansa, wannan
ta sanya ko barbara zaiyi baya yi tare da ‘yan uwansa da suka fito ciki daya,
sabanin sauran dabbobi irinsu akuya da rago. Haka kuma, kamar yadda sauran
dabbobi irinsu mage suke da sabo da masu su haka shima rakumi yake da sabo da
mai, domin sau da yawa rakumi yana yin kewar rabuwa da uban gidansa.
Rakumi kusan a cikin
dabbobin da aka halattamana cin-su dan layya ko hadaya yafi kowacce dabba
daukan tsawon shekaru a raye, domin rakumi yakan rayu tsawon shekaru daga 40
har zuwa 60. Sannan kuma, rakumi duk da irin jarumtakarsa ALLAH ya sanya kunama
tana cin galaba akansa, domin duk cikin halittun ALLAH babu abinda rakumi yake
jin tsoron gamuwa da shi kamar kunama, kasancewar kafarsa tana da taushi sosai
kamar ta dan-Adam, wannan ta sanya rakumi yana iya hango kunama daga waje mai
nisa, kuma muddin ya hangota to ba zai bi wannan hanyar ba.
Kamar yadda muka bayyana
cewa Rakumi yana da hakuri sosai, sannan kuma yana da fada sosai idan aka shiga
gomarsa. Kusan duk cikin dabbobin da makiyaya suke kiwo rakumi ne kada ba’a
dukansa, domin na farko shi yasan ya kamata gwargwadon irin tarbiyyar da mai
shi ya bashi, rakumi yana jin magana kamar mutum kuma yana bin dukkan umarnin
da aka bashi, dan haka mai kiwon rakuma zai iya yin gaba ya bar rakumansa ya yi
musu umarnin su sameshi a waje kaza kuma so sameshi. Rakumi duk mutumin da ya
cuceshi sai ya rama komai tsawon lokaci, kuma rakumi yasan Yaro misali idan
Yaro ya tsokaneshi baya damuwa kuma baya masa komai.
A dukkan dabbobin da
ALLAH ya halitta Rakumi ne kadai dabbar da babu wani abu a jikinsa da bashi da
amfani. Bayaga yanka shi da ake a ci nama, ana amfanuwa da nononsa da fitsarinsa da
kashinsa, wannan ya sa rakumi ya yi zarra a cikin dabbobi domin shi fitsarinsa
ba najasa bane kuma ba haram bane. Haka kuma, ALLAH ya yi ishara dangane da yin
tsinkaye dangane da rayuwar rakumi a cikin al-qur’ani mai tsarki a sura 88 aya
ta 17.
Haka kuma, wasu masana
sun tabbatar da cewa Rakumi ya taba rayuwa a wannan duniyar a shekaru sama da
miliyan hamsin da suka gabata! Tsarki ya tabbata ga ALLAH da ya halicci rakumi,
masanan sunce rakuman da suka rayuwa a wancan lokacin girmansu bai wuce na
Akuya ba, sannan sun rayuwa a can a wani yankin kudancin Dakota a kasar Amerika
kenan.
Yasir Ramadan
Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
No comments:
Post a Comment