TITANIC
. . . bayan da jirgi ya nutse gabaki daya a
cikin ruwa, nan mutane suka shiga neman tsira, wasu na ta kokarin samun wani dan
tudu da zasu dafa dan tsreatar da rayuwarsu. Duk da wannanhali na kidimewa da
tashin hankali da mutane suke ciki JACK yana tare da ROSE, a lokacin dajirgi
yake nutsewa, igiyar ruwa ta ja Jack ya yi kasa Rose tana saman ruwa tana
lalubansa, can sai ga shi ya dago,
yaga wani yana kokarin dannata domin ya
dago sama, nan-fa Jack ya kai masa naushi inda ya tunkude shi. Daman ita Rose
tana sanye da rigar kariya wadda bazata nutse ba, sai Jack yayi fundun-fundun
ya kamo wani allon jirgi inda ya janyoshi kusa da Rose domin su samu su makale
akansa, amma ina wannan allon jirgi bazai iya daukarsu. Dole Jack ya hakura
yabar Rose ta hau kan wannan allon jirgi, cikin matsanancin sanyi ga duhu ga
kuma talatainin dare. Da Jack da Rose gabaki daya sun galabaita! Jack yana
makale a gefen inda Rose ta sanya kanta shi kuma ya dafe wajen yana gaya mata
cikin murya mai kama da rada, cewa ki rike alkawarin soyayyarmu. Bayan
matsanancin sanyi ya bugi Jack ya saki wannan allo da yake makale da shi, ai
kuwa sakin sa keda wuya sai ya lume, a wannan lokacin Rose bata san inda kanta
yake ba! Jack dai ya tafi har Abada domin ya nutse can kasa kuma yayi
galabaitar da bazai iya fundun-fundun ba, cikin wata murya mai ban-tausayi Rose
ta kira sunan Jack taji shiru, daga nan sai hawaye ya fara zubu mata. Can tana
kwance kan wannan allon jirgi sai ga masu bayar da agajin gaggawa suna bincike
ko da akwai sauran wani mai rai suna haskawa da cocila amma duk wanda suka taba
sai su ga ya mutu, daya daga cikinsu yace "can any body hear me" a wannan
lokacin Rose ta bude Idonta, sai taga alamun sun juya zasu koma, cikin
dasashshiyar Murya ta ringa cewa "come back" ko kadan basu jita ba.
Nanfa Rose taga cewa lallai komawa zasu yi, kawai sai ta duba gefenta sai taga
gawar wani mutum rataye da wusur a wuyansa, nan tayi lunkaya ta kai zuwa
gareshi, inda ta dauki wannan wusur ta busa, masu bayar da agaji suka fahimci
lallai akwai sauran me RAI nan da nan suka dawo cikin hanzari suke kawo mata
dauki. . .!
*Shin ya zaka iya kwatanta jarumatar JACK kasancewar ya yarda ya rasa rayuwarsa domin ROSE ta rayuwa duk kuwa da cewa a wannan lokaci budurwarsa ce ba matarsa ba, kuma iyayanta basa kaunarsa.
*Shin ya zaka iya kwatanta jarumatar JACK kasancewar ya yarda ya rasa rayuwarsa domin ROSE ta rayuwa duk kuwa da cewa a wannan lokaci budurwarsa ce ba matarsa ba, kuma iyayanta basa kaunarsa.
No comments:
Post a Comment