Monday, December 31, 2012

ME YAKE FARUWA A KANGWAYE NE?


Wata rana wani Bawan Allah da yake gina gidansa, ya gayyaceni akan na raka shi gewayar ganin gidan da yake ginawa. Haka kuwa aka yi, domin mun je a wani irin lumshi da kowa zai so ya danyi tattaki a cikinsa, ba jimawa muka zo unguwar da gidan yake, kasancewar wajen sabon wajene dukkan gidajan da suke kan layin sabbin gidaje ne da ake ginawa, wannan ta sanya muka tarar da tsibi tsibin yashi da duwatsu da kan-kura akan layin, dole ta sanya muka ajjiye mota daga nesa muka taka sayyadarmu domin karasawa gidan. 

Isarmu kofar gidan ke da wuya na kalli gidan nayiwa maigidan murna kasancewar gidan ya kasaita bayan kasancewarsa katafare harda masallaci a jikin gidan da ake ginawa tare. Mai gida ya shige cikin gidansa kai tsaye domin yaga yadda ake gini, Ni kuma na nufi dan-karamin masallacin da ke jikin gidan wanda ake ginawa, shiga cikin masallaci na hangi wani abu da na kasa gasgata ganina da yake daga nesa na hango.

Ina shiga cikin harabar masallacin ta kofar kudu kawai sai naga wani baho madaidaici dauke da wasu kananan kwalaben ruwa da wasu jike-jike a ciki. Abinda ya fara zuwa Raina shine wannan irin kayan masu tallan maganin gargajiya ne da suke shigowa cikin birni daga Panshekara, tsammanina ko na tsintuwa ne, ban damu ba na daga kaina sama daga bakin kofa ina kallon gini, can sai naji sukur-sukur alamar ana motsi, duk da haka ban kawo wani abu mara kyau na faruwa ba, kawai sai na shiga domin ganin meye yake motsi, cikin mamaki na hangi bayan mutum a inda Liman yake tsayawa, na kalli mutumin da alama yana yin wani abu cikin gaggawa, na kara matsawa sosai, sai na hangi wani mutum mai matsakaitan shekaru yana sauri yana daura tazaugen wandonsa kansa babu hula, da alamar a rikice yake, bayansa kuma wata yarinya na hanga tana kokarin gyara kayan jikinta.

Na tsaya ina mamakin abinda idona ya gani, yarinyar nan ta tashi cikin hanzari ta dauki wannan baho ta kinkima tayi waje. Banyi magana ba, wannan mutumin kuwa ya zube a gabana yana rokona dan Allah malam ka rufa min asiri kada ka gayawa Alhaji ka ganni! Nikam Ina tsaye na kasa magana. Mutumin nan da yaga ban kulashi ba, ya leka waje bai hangi kowaba, har ya fita sai ya dawo ya dauki hularsa, kafin ya dauki hular tuni ni kuma na fice daga cikin masallacin.

Na shiga cikin gidan ina mai mamakin abinda na gani, Mutumin nan hankalinsa ya tashi sosai, domin yana yimun wani irin kallo na intausaya masa. Haka dai har muka gama ganin ginin nan bashi da kuzari, yana tsoron kada na fadi abun da na gani. Hakika abinda na gani ya tunasar da ni abubuwa da yawa da na sha-ji ana fade cewa ana yin Lalata da yara 'yan talle a cikin kangwaye. Lallai acikin masu yin sana'ar gini akwai mutanan kirki kuma akwai na banza kamar yadda kowanne fannin rayuwa ake samu. Allah ya shirya ya karemu da mugun-ji da mugun-gani. 

Sunday, December 23, 2012

ZA A JIMA ANA TUNAWA DA SHUGABA GOODLUCK JONATHAN A NAJERIYA


Shugaba Goodluck Jonathan shine shugaban Najeriya na goma sha biyar (15) idan muka dauki lissafi daga Firaminista Sa Abubakar Tafawa Balewa da kuma shugaba Namandi Azzukuye. Shakka babu a tarihin Najeriya nan gaba ba zai taba cika ba, idan ba'a yi maganar shugaba na goma sha biyar ba wato Goodluck Ebele Azikewe Jonathan, za'a tuna da shugaban kasane ba dan yayi abin kirki ba, sai dan a lokacin sa ne Najeriya ta samu kanta a cikin wani mawuyacin halin da bata taba samun kanta a ciki ba tundaga shekarar 1914 har kawo wannan lokaci.

A lokacin Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne cin-hanci da rashawa ya kai magaryar tukewa, ta yadda babu wani mutum daga cikin gwamnatinsa da za'a zazzage ba'a sameshi da kashi a gindinsa ba. A lokacin shugaba Goodluck Jonathan aka taba samun manyan jami'an gwamnati da muguwar sata da ta shallake hankali da tunanin dukkan wani mai tunani, cin hanci bai tsaya iyakar jami'an gwamanti ba kadai, kusan yayiwa shugaban mugun daurin da bazai taba iya kwancewa ba. 

Shugaban kasa Goodluck Jonathan yaki bayyana abinda ya mallaka a zamanin mulkinsa kamar yadda magabacinsa Malam Umaru Musa 'YarAdua (Allah ya jikansa) yayi, domin kuwa rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban a kwance yake akan dukiyar haram faca faca. Haka kuma ana yiwa manyan na hannun damansa zargin cin-hanci mai karfin gaske wanda ya hada da mutum mafi kusanci da shi a majalisar zartarwa wato ministar albarkatun manfetur madam Dazani Alasan Maduwake da kuma hamshakan mutane irinsu fitaccan dan kasuwannan wanda cin hanci ya dabaibaye wato cif Femi Otedila.

Haka kuma shugaban ya kanainaye kansa da miyagun barayi azzalumai irinsu wani tsohon najadu da ake kira cif Tony Anenih wanda ya taba riki mukamin shugaban kwamitin amitattun PDP kuma tsohon ministan ayyuka na gwamnatin tarayya a zamanin Obasanjo, a lokacin da mista Anineh yake rike da mukamin minista ne ya shaidawa maname labarai a ranar 6 ga watan disambar 1999 cewar babu wata kasa da zata cigaba ba tare da kyawawan hanyoyi na gwamnatin tarayya ba, dan haka ya fitar da kwangilar gyara da garambawul na manyan titunan gwamntin tarayya inda aka fitar da zunzurutun kudi Naira Biliyan 200 daga 1999 zuwa 2002, daga bisani aka nemi kudin ko sama ko kasa, kuma babu aikin titunan, wanda mujallar Tell Magazine ta 20 ga watan disambar 1999 ta tallata aikin kwangilar. Haka kuma, a ranar 25 da Oktobar 2002 sai da shugaban kasa na wannan lokacin Olushegun Obasanjo ya shaidawa manema Labarai cewar hankalinsa ya tashi matuka da irin yadda ya samu labarin halin da titunan gwamnatin tarayya suke ciki, amma abin mamakin shine ba'a nemi Mista Anenih yayi bayanin yadda aka yi da kudin aikin titunan ba. Irin wadannan muggan barayi su Tony Anenih sune wadan da Shugaban kasa yake ganin sunfi kowa tsarki wajen iya shirya sata da damfara da sunan aikin gwamnati, inda yanzu haka aka sake bashi wani muhimmin mukami na shugaban hukumar Nigerian Port Authority.

Har ila yau 'yan Najeriya zasu jima basu manta da shugaban kasa Goodluck ba kasancewar a lokacinsa ne mutane irinsu Henry Okah sukayi ikirarin dasawa da kuma tayar da Bom a lokacin bikin samun 'yancin kai, kuma suka aiwatar da wannan nufi nasu, amma saboda tsabar rashin ta ido shugaban ya fito kafafan watsa labarai yana cewa wannan hari ba su Henry Okah bane suka kaishi.

Idan muka kalli yankin kudu maso yamma da kuryar kudancin kasararnan zamu ga cewar satar mutane tare da yin garkuwa da su ta zama abun yayi, ta yadda masu wannan sana'a suke cigaba da cin karansu babu babbaka, abinda ya kai har mahaifiyar Ministar gamayyar tattalin arziki Ungozi Okwanji Iwela aka sace kuma aka nemi kudin fansa kamar yadda al'adar satar take. Haka kuma, masu fasa bututu da satar gurbataccan manfetur sun cigaba da cin kasuwarsu ta wannan aika aika, har sai da ta kai wani kwamiti da shugaban kasar ya kafa karkashin Jagorancin Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewar raba dai-dai ake yi tsakanin Najeriya da barayin danyan manfetur. Sannan saboda shugaban kasa ya kara gwangwaje wadannan barayi 'yan ta'adda yace shi da kansa ya nadasu masu gadin wadannan bututun mai sannan ya sanya musu wani katafarn albashi na Dalar Amurka Miliyan 350 a kowacce shekara, lallai za'a jima ana tunawa da shugaba Goodluck ta wannan janibi.

A yankin tsakiyar Najeriya kuwa anyi ta samun rikicin addini da na kabilanci babu kakkautawa a zamanin shugaba Goodluck Jonatahn a jihar Filato da kuma rikicin manoma da makiyaya a jihar Nassarawa da Bunuwai. Sannan kuma anyiwa wasu musulmi korar kare a karamar hukumar Mokwa dake jihar Neja ko wadanda aka fi sani da 'yan Darul Islam, wanda dukkan bayanai da bincike suka tabbatar da mutanan wannan gari basa wata barazana ga tsaro ko zaman lafiya.

Mutanan Arewa gaba daya kuwa zasu jima suna tunawa da shugaba Goodluck Jonathan, saboda ansamu asarar rayukan da ba'a taba samu ba a wannan yanki karkashin wannan shugaba. Haka kuma jihar Borno ta zama wata karamar Bagadaza a Najeriya musamman lokacin wannan shugaban, domin ankashe muhimman mutane da suka hada da Madu Fannami Gubio wani dan takarar gwamna a jihar ta Borno da kuma Manjo Mamman Shuwa wanda saboda sake da rashin tsaro wasu 'yan ta'adda suka haura gidansa suka kashe shi kuma suka gudu.

A kano kuwa kanawa zasu jima suna tuna ranar 20 ga watan Janairun shekarar da ta gabata domin a wannan lokacin aka samu abinda ba'a taba mafarkin samu ba na tashin bamabamai babu kakkautawa a ciki da wajen birnin kano, wanda rahotanni mabanbanta suka nuna cewa ansamu tashin bamabamai sama da guda sittin (60) a wannan rana, da asarar rayukan mutane sama da 250 duk a wannan rana.

Idan muka leka jihar Kaduna kuwa al'ummar Musulmi da suke a kudancin Kaduna zasu jima basu manta da watan Afrilun 2011 ba, domin ankashe mutane bila adadun sakamakon rikicin bayan zabe, da kisan kan-mai uwa da wabi. Haka kuma, jihohi irinsu Adamawa da Gwambe da Bauchi da Kogi da Taraba suma bazasu manta da shugaba Goodluck Jonathan ba domin kuwa a karan farko a lokacinsa wadannan al'ummomi suka san karar tashin bamabamai. Sannan kuma a lokacin wannan shugaba ne 'yan Najeriya suke karyawa duk safiya da kalmomi irisu GARKUWA DA MUTANE, BOKO HARAM, CIN-HANCI DA RASHAWA, 'YAN TA'ADDAN NEJA DALTA da sauransu. 

Shakka babu idan za'a yi bayanin abubuwan takaici da Allawadai da Alla-tsine da suka faru a Najeriya a zamanin shugaba Goodluck Jonathan za'a jima ana zayyanosu. Daga karshe muna rokon ALLAH da sunansa kyawawa kuma tsarkaka, Ya ALLAH kada ka sake Jarrabarmu da Mutum irin wannan shugaban na yanzu Goodluck Jonathan, Ya ALLAH ka jarrabemu da shugaban da zaiji-kanmu ya tausaya mana.
 

Friday, December 21, 2012

JOHN DANFULANI FUTSARARRAN KIRISTA


JOHN DANFULANI FUTSARARRAN KIRISTA
Yau kusan na wayi gari da samun bakaken maganganu da zagi daga John Danfulani a cikin Inbox dina, amma da yake ba tsoronka nake jiba, munyi karo da kai, duk da cewa ni ban iya zagi ba kuma addinina bai koyar da ni hakan ba. Haka kuma, duk a post dinka na yau da zagi da cin mutunci da kayi mana wannan abin dariya ya bamu, domin ko kadan bai yi mana ciwo ba. Bari na gaya maka abinda baka sani ba, Kafurai na gaske ba 'yan tasha 'yan gareji ba irinka, Manya su ABU-JAHAL babu irin maganganun da basu yi ga addinin Musulunci ba. Sai da Abu-Jahal ya fadi magana marar dadi ga fiyayyan halitta ALLAH da kansa ya saukar da sura ta 112 acikin Al-Qur'ani domin rarrashi ga Fiyayyan halitta, dan haka:

Ina son Mista John Danfulani ka sani duk abinda zaka kiramu sai dai ka kiramu, Yakowa dai ya riga ya mutu har abada kuma ba zai dawo ba. Mu Musulmi ba Jahilai bane muna rayuwa bisa koyarwar addininmu ne, ka sani mu ba wai murna muke da Mutuwar Yakowa bane, ba kuma muna fadar haka bane domin ku yarda damu, kunyi kadan domin mu fadi abu dan mu burgeku (kadangaru ma irinku Aljifan baya). Babban bakin cikinku shine Malam Ramalan Yero ya zama gwamnan Kaduna abinda ko kadan bai yi muku dadi ba, ko ka kiramu 'ya 'yan almajirai koma duk sunan da zaku kiramu da shi, muna tabbatar maka mu ba jemagu bane. 

Muna da Addini da sana'a da kuma al'adunmu kyawawa da suka dace da addini, sannan kuma muna da harshenmu abin alfaharinmu. Turawan mulki basu ci nasarar wanke mana kwakwalwa ba da sauyawa mana tunanin mu dauki sunayansu da addininsu da dabi'unsu. Yanzu bai isheku abin kunya ba, a ce kai kana takamar Kiristanci amma ko kadan 'yan kudu da kuke danganta kanku da su suna kallonku kirsitocin karya(Suna nesanta kansu da ku, amma kuna nanike musu), sannan mu kuma anan muna kallonku Jemagu.

Wallahi ka sani mu ba matsorata bane, kuma ba jahilai bane irinku da muka kasa fahimtar rayuwa. Ashirye muke ga dukkan wani dan iskan mara kunya irinka, ina tabbatar maka kuma dan shege ka fasa . . . Dan bantan Uba.

Wednesday, December 19, 2012

AL-BISHIR GA JOHN DANFULANI


AL-BISHIR GA JOHN DANFULANI
Ina yiwa John Danfulani albishir da cewa Alhaji Malam Mukhtar Ramalan Yero shine sabon gwamnan jihar Kaduna. Ina kuma sanar da Mista Danfulani cewar a cikin Littafin ALLAH mai tsarki (Al-Qur'ani) ALLAH ta'ala ya gaya mana a cikin sura ta 2, aya ta 26 cewa Mulki nasa ne, yana bayar da shi ga wanda ya so, a lokacin da ya so. ALLAH shine mamallakin Komai kamar yadda ya baiwa Yakowa mulkin Jihar Kaduna a lokacin da babu wanda ya zata Haka ya baiwa Ramalan Yero a yanzu.

Manyan Arna kafurai na gaskiya ba 'yan gareji ba irinsu Utba Ibnu Rabi'a babu irin maganganu na batanci da basu yi ba akan Musulunci da Musulmi, amma yau ina suke? Bayan da aka kashe su Sai da manzon ALLAH ya je kan gawarsu, yana yi musu magana "Shin kun gasgata al'qawarin ALLAH ko kuwa" a dai-dai lokacin da suka kasance masu nadama. Har sai da Umar Bin Khattab ya ce da Manzo Ya Rasulillah yaya kake magana da mutanan da suka mutu, Manzon ALLAH Salallahu Alaihi Wasallam ya shaida masa ko kai baka fisu jin abinda nake fada ba.

Dan haka Mista Danfulani ku sani me aukuwa ce ta auku akan Yakowa kuma ta katse masa hanzari kamar yadda komai tsahon Lokaci sai ta auku akanmu gaba daya. Yanzu kuma mun kara fahimtar mugun Nufinku akanmu, ko ku zargi Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sombo ko Kada ku zargeshi babu wani abu da zai faru face mukddari ne daga ALLAH Ubangijin Halittu, Tsarki ya tabbata a gareshi, Subhanahu Wata'ala.

Tuesday, December 18, 2012

TITANI


TITANIC
. . . bayan da jirgi ya nutse gabaki daya a cikin ruwa, nan mutane suka shiga neman tsira, wasu na ta kokarin samun wani dan tudu da zasu dafa dan tsreatar da rayuwarsu. Duk da wannanhali na kidimewa da tashin hankali da mutane suke ciki JACK yana tare da ROSE, a lokacin dajirgi yake nutsewa, igiyar ruwa ta ja Jack ya yi kasa Rose tana saman ruwa tana lalubansa, can sai ga shi ya dago, 

yaga wani yana kokarin dannata domin ya dago sama, nan-fa Jack ya kai masa naushi inda ya tunkude shi. Daman ita Rose tana sanye da rigar kariya wadda bazata nutse ba, sai Jack yayi fundun-fundun ya kamo wani allon jirgi inda ya janyoshi kusa da Rose domin su samu su makale akansa, amma ina wannan allon jirgi bazai iya daukarsu. Dole Jack ya hakura yabar Rose ta hau kan wannan allon jirgi, cikin matsanancin sanyi ga duhu ga kuma talatainin dare. Da Jack da Rose gabaki daya sun galabaita! Jack yana makale a gefen inda Rose ta sanya kanta shi kuma ya dafe wajen yana gaya mata cikin murya mai kama da rada, cewa ki rike alkawarin soyayyarmu. Bayan matsanancin sanyi ya bugi Jack ya saki wannan allo da yake makale da shi, ai kuwa sakin sa keda wuya sai ya lume, a wannan lokacin Rose bata san inda kanta yake ba! Jack dai ya tafi har Abada domin ya nutse can kasa kuma yayi galabaitar da bazai iya fundun-fundun ba, cikin wata murya mai ban-tausayi Rose ta kira sunan Jack taji shiru, daga nan sai hawaye ya fara zubu mata. Can tana kwance kan wannan allon jirgi sai ga masu bayar da agajin gaggawa suna bincike ko da akwai sauran wani mai rai suna haskawa da cocila amma duk wanda suka taba sai su ga ya mutu, daya daga cikinsu yace "can any body hear me" a wannan lokacin Rose ta bude Idonta, sai taga alamun sun juya zasu koma, cikin dasashshiyar Murya ta ringa cewa "come back" ko kadan basu jita ba. Nanfa Rose taga cewa lallai komawa zasu yi, kawai sai ta duba gefenta sai taga gawar wani mutum rataye da wusur a wuyansa, nan tayi lunkaya ta kai zuwa gareshi, inda ta dauki wannan wusur ta busa, masu bayar da agaji suka fahimci lallai akwai sauran me RAI nan da nan suka dawo cikin hanzari suke kawo mata dauki. . .!

*Shin ya zaka iya kwatanta jarumatar JACK kasancewar ya yarda ya rasa rayuwarsa domin ROSE ta rayuwa duk kuwa da cewa a wannan lokaci budurwarsa ce ba matarsa ba, kuma iyayanta basa kaunarsa.

Monday, December 17, 2012

GWAMNA GEBRIEL SUSWAM MUGUN KIRISTA



GWAMNA GEBRIEL SUSWAM MUGUN KIRISTA
Gwamna jihar Bunuwai Gabriel Torwua Suswam, ya fada a cikin wata majami'a NKST Church, kuma jaridar Blueprint Newspaper suka buga wannan magana tasa inda yake cewa "Mu hudu ne kadai Kiristoci da aka zaba a matsayin gwamnoni a duk fadin Arewa " Me kake zaton wannan magana take nufi? Arewa Mu Musulmi muke da kaso akalla 75, sannan idan ka dauke jihar Bunuwai da shi Suswam yake Gwamna, sai Jihar Filato nan ne kadai Jihohin da suke da kiristoci da yawa, amma Filtoma muna da yakinin 50-50 muke tsakaninmu da su. Ko kuwa Suswam yana Nufin a samar da Kirista ya zama Gwamna a Jigawa ko Zamfara ne? Wannan ko shakka babu magana ce da bai kamata ta fito daga bakinsa ba a matsayinsa na shugaba.

Sannan ya kara da cewar,"Mutuwar Yakowa a cikin wannan hadarin jirgi ta sanya al'ummar kiristoci cikin wani mawuyacin hali" Shin me Suswam yake nufi akan wannan magana tasa? Shin Ya manta cewa Yakowa Gwamnan Kaduna ne ba Gwamnan Kirista ba? Ko kuwa yana son ya nunawa duniya cewa kulle-kulle aka yiwa Yakowa? Allah mai hikima, Yakowa ya mutu a cikin 'yan uwansa, ba a yankin Arewa ba! na tabbata yau da ace a daya daga cikin Jihohin Arewa wannan jirgi ya rikito da Yakowa sai kaji ana ihu ancika jaridu da hayaniya cewa Musulmi ko kuma a ce Boko Haram ne suka harbo jirginsa, da yake su din makirai ne, suyi amfani da wasu baragurbi suyi Ikirarin cewar dukan jirgin akayi. Amma Allah sai ya sanya abin bai faru a Arewa ba. Alhamdulillah! Da a Arewa ne da bamu san me zai faru ba ya zuwa yanzu.

Gwamna Suswam ya kara da cewa "idan kuma aka lura da mutuwar Gwamna Patrick Yakowa da kuma mawuyacin halinda Gwamna Suntai yake ciki mun zama saura mu biyu kacal kenan" ko kuwa ya manta da cewa Mu mutanan Arewa an kashe mana Sardauna, an kashe tafawa Balewa, an kashe Murtala, an kashe Abacha sannan kuma da Abinda ya faru da 'YarAdua! Shin kana zaton yau wadannan mutane da Kirstoci ne Musulmi suka kashe su Kasar nan zata cigaba da amsa sunan da take amsawa yanzu? Ai da tuni ko dai an fatattaki wasunmu sun koma Nijar ko kuma anyi uwar watsi. Amma da yake mu ba masu son fitina bane lafiyalau kake ji. sannan ya kara da cewa "Rahotannin da nake ta samu na tsaro suna tabbatar min da cewa ni dinnan 'yan Boko Haram zasu kawo mun hari a koda yaushe, a kowanne wuri, a kowanne irin yanayi." "Don haka ina cikin tsananin bukatar addua." Me kaka ke zaton wannan gabar maganar take Nufi? Shin tunda muke mun taba jin Gwamna Suswam a sahun Mutanan da Boko Haram sukewa barazana? Bama kare Boko Hara a cikin dukkan abubuwan da suke aikatawa, domin muna zarginsu duk kullin su Suswam ne da iyayan gidansa. Wannan ko shakka babu Gwamna Suswam ya fada ne domin ya janyo hankalin Kiristoci, dan su kara tsananta kiyayyarsu ga Musulmin Arewa.

Shakka babu Su Suswam sunci nasarar jingina Boko Haram da Musulmi, wanda dukkan mutanan da ake kamawa da daddasa bama-bamai galibinsu kiristoci ne, idan banda Kabiru Sokoto babu wani Musulmi da aka kama da wani laifin kai hari a coci. ko Ali Konduga da aka kama ai babu wani rahoto da ya nuna da hannunsa akan kai hari a coci.Lokaci da zo da wasu zasu kwashi kayansu a hannu insha ALLAH.

SUWAYE SUKE KOKARIN RURA WUTAR RIKICI A AREWA?


SUWAYE SUKE KOKARIN RURA WUTAR RIKICI A AREWA?

Tun bayan da gwamnan Taraba Danbaba Danfulani Suntai yayi hadarin jirgi ya haukace, hankalin shugabannin CAN ya tashi ganin cewar babu makawa sai Taraba ta kubuce musu wanda kuma har Abada bazata dawo ba.

Sannan da abunda ya faru na mutuwar Gwamna Kaduna Patrick Ibrahim Yakowa kusan wannan shine abinda yafi tayar musu da hankali da rikitamusu lissaf
i, domin wata babbar dama ta kubuce musu.

Kwatsam sai gashi mun wayi gari Gwamnan Benuwai da kansa ba aikeba yana maganganu da zasu haifar da rashin zaman lafiya a kasarnan. Wannan ko shakka babu yana kara bayyana irin mugun nufin shugabannin CAN akan Musulmin Arewacin Najeriya.

Tun suna turo kana nan mutane suna maganganu na tashin hankali har aka fara jin limamancoci da kansu suna wa'azin Takalar fada. Har ta kai yanzu shugabanni da kansu zasu fito suna maganar irin wadda Susuwam yayi wannan ko shakka babu yana kara bayyana cewa lallai suna da mugun kulli a tare dasu.

Alhali mun san Tunda muke a Arewa kullum kiristoci ne suke takalar musulmi da tashin hankali. Rikicin addini na farko wanda Rabaran Abubakar Bako ya yi wani wa'azin takalar musulmi a 1989 inda ya yi maganganun batanci ga fiyayyan halitta, wata dalibar Jami'a ta nuna damuwa, wannan ta sanya aka samu rikici a Kafanchan aka kashe Musulmi da dama.

Sannan bamau manta da lokacin da shugabannin kiristoci suka yi kokarin takalar Musulmi 1991, na kokarin kawo wani Pasto dan kasar Jamus Rein Hart Bonkey ya yi wa’azi a Kano. Inda aka ce zai zo ya tayar da guragu kuma ya bude idanun makafi, wannan ya tayar da kura sosai.

Haka kuma, a cikin shekarar ta 1991, a Tafawa Balewa, Sayawa kiristoci suka yi wa hakimin Lere, Malam Abubakar Bawa kisan gilla; duk da kasancewrsa tsohon da ya haura shekaru 80. Kotu ta samu jagoran wannan ta’asa; Mr. Kyauta (wanda ake wa lakabin Kyankyaso), da laifi ta daure shi. Wanda wannan shine rikici na farko da ya hana Tafawa Balewa zaman lafiya har yau dinnan Rahoton Babalakin ya tabbatar da Hannun shugabannin kirista dumu-dumu wajen shirya kai hari wa Musulmi a wannan gari.

Sannan bamu manta da Katafawan da suka ka kai mummunan hari a kan Musulmi cikin watannin Fabrairu da Yulin 1992; suka kashe daruruwan Musulmi, suka kone gidajensu da dukiyoyinsu. Wanda kotun Kotun Karibi Whyte kirista ta samu Lekwot Zamani da hannu dumu-dumu wajen shirya kai wadannan hare-hare kuma ta yanke masa hukuncin kisa saboda rashin Adalci shugaban kasa na wannan Lokacin IBB yace ya yafe masa wannan mummunar aika-aikar da yayi.

Tun wancan Lokaci har yanzu Kiristoci suna ta kai munanan hare-hare babu kakkautawa a Shandam da Yelwa da Barikin Ladi da Bukur da Jos ta Arewa tun daga 2004 har kawo yanzu ALLAH ne kadai yasan adadin Musulmin da suka rasa rayukansu a Jos har kawo yau dinnan ana ci gaba da kashe Musulmi.

Babu wani rahoton bincike da aka taba kafawa a kasar wanda aka samu hannun Musulmi dumu-dumu da hannu wajen wani tashin hankali. Amma saboda tsabar rainin hankali da Rainin wayo kadangaru irinsu Gwamnan Benuwai Gabriel Torwua Suswam zasu fito suna irin wadannan maganganu na rashin hankali da rashin sanin Inda aka dosa.

Sunday, December 16, 2012

GWAMNA RAMALAN YERO KADA KA BUTULCEWA UBANGIJI


GWAMNA RAMALAN YERO KADA KA BUTULCEWA UBANGIJI

Jiya yuwar haka, baka taba zaton zaka zama gwamna a yau dinna ba, amma ALLAH shine me yadda ya so, yanzu gashi ka zama gwamna. Kafin haka, Rahotanni suna nuna cewa ana ta kokarin tsigeka kafin wannan lokaci, koma dai wanne irin dalili aka bayar dan yin haka, abu mafi ban mamaki shine Yau gashi ka zama gwamna mai cikakken iko. Dan haka kirana a gareka, kada ka yiwa ni'imar ALLAH dubale kamar yadda sauran shugabanni suke yi ta hanyar ganin wayonsu da dabarunsu na iya basu, ko kuma bin ayarin shaidan wajen samu mulki ta kowacce hanya. Ka sani babu ko daya daga cikinsu da ya baka! Mulki na ALLAH ne kuma shine ya baka shi a dai-dai wannan marra, ka sani wani baya iya baiwa wani mulki.

Dan haka kirana a gareka shine kaji tsoron ALLAH wajen tsare gaskiya da amana da yin adalci tsakanin al'ummar da kake shugabanta a jihar kaduna. Shakka babu kazo a cikin wani lokaci mai cike da kalubale, a wannan mawuyacin
 lokaci babu abinda ya kamace ka illa tsayar da adalci tsakanin dukkan bangarorin Musulmi da Kirista na jihar kaduna.

Ka tsaya tsayin daka wajen tabbatar da Adalci tsakanin al'ummarka, duk kuwa irin kalubalen da zaka gamu da shi wajen yin wannan aiki. Shakka babu wasu zasu kalubalanceka ta karkashin kasa wasu kuma zasu yi hakanne ba tare da jin kunyarka ko tsoronka ba. Idan ka kuskura kabi irin waccan hanya ta gurbatattun mutane tabbas zaka kasance mai nadama matuka da gaske, bayan ka butulcewa ni'imar da ALLAH yayi maka.

Lallai kofarka ta kasance a bude ga kowa da kowa wajen sauraran koke-koken jama'a da korafe-korafen su, ciki kuwa harda wannan kafa ta sadarwa ta yanar gizo wajen jin ra'ayoyin jama'a. Sannan kuma ka baiwa mutane damar mika korafinsu gareka kai tsaye ba tare da wani shamaki ba. Ka yi kokari matuka wajen kaucewa duk wani abu da zai sa ka iya aikata rashin gaskiya ko rashin adalci a tsakanin al'ummarka. Kada ka bari a rabaka da masu fada maka gaskiya, kada ka duba masu fada maka gaskiya ka kalli abin da suke fada, duk wani abu da zai sa ka samu nasara wajen tafiyar da gaskiya da Adalci ka karbeshi ko da kuwa daga hannun wa yake. ALLAH ya yi maka Jagoranci.

BAN-KWANA DA MALAM IBRAHIM YAKOWA


BAN-KWANA DA MALAM IBRAHIM YAKOWA

Masu magana suka ce idan an bugi jaki a bugi taiki! Idan zamu fadi magana ta gaskiya akan tsohon gwamnan Kaduna Marigayi Malam Patrick Ibrahim Yakowa lallai mutum ne da ya siffantu da wasu kyawawan dabi'u da wasu halaye na gari. Yakowa tun bayan hawansa gwamnan Kaduna shi da kansa yasan yana da babban kalubale akansa domin ya zama gwamna a jihar da galibin al'umm arta suke da rinjayen Musulmi, dan haka yasan wannan gagarumin kalubale ne akansa.

Yakowa ya yi kokarin gyara siyasarsa da kuma dangantakarsa ko alakarsa da Musulmi. Amma kuma ya tsinci kan-sa a wata tsaka mai wuya, domin ya zama gaba kura baya sayaki. Abu na farko yana kokarin ganin ya samu goyon bayan musulmi masu rinjaye kasancewar jihar kaduna tayi kaurin suna wajen rashin zaman lafiya musamman tsakanin Kiristoci da Musulmi. Da farko Yakowa yayi ta kokarin mika hannunsa ga musulmi domin su yarda da shi a matsayin sabon jagoran jihar, kasancewar irin yanayin da ya kawo shi gwamnan musamman a matsayinsa na sabon zababben gwamna zaiyi wahala a yarda da shi kai tsaye ko lokaci guda.

Sannan kuma ta bangaren 'yan uwansa tsirarun kiristoci da suke ganin nasu ya samu, sai suke masa wani irin kallo na Inuwar giginya. Kalubalen da yakowa ya samu a karon farko shine su tsirarun kiristoci suna masa kallon daman can a cikin Musulmi ya taso tun rayuwarsa, kuma sune abokan mu'amalarsa, dan haka sai ya samu kansa a wani irin yanayi ta yadda 'yan uwansa kiristoci suna masa kallon yana neman juya musu baya a matsayin nasu, sannan kuma musulmi na dari-dari da shi. Amma duk wannan yayi ne domin gyara siyasarsa.

Yakowa yayi kokarin ganin yayi mulki ba tare da nuna wani bambanci na zahiri ba tsakanin Musulmi da Kirista. Kuma kamar yadda aka bayyana shi dan kishin kasa ne da kishin Arewa wannan yabo kam shakka babu anyi masa, kuma biri yayi kama da mutum. Haka Kuma, a yadda yake gudanar da gwamnati hakika yana taka tsantsan wajen ganin bai bata zamansa ko alakarsa da Musulmi ba. Kamar yadda rahotanni suka nuna a aikin hajjin da yagabata Yakowa yayi rawar ganin wajen ganin gwamnatin Kaduna ta taimakawa Alhazan Jihar Kaduna. Hakika idan zamu kalli wadannan halaye dama wasu zamu ga cewa yayi kokari.

Haka kuma wasu suna ganinsa a matsayin macijin sari ka-noke ta yadda yake ta kokarin daddasa 'yan uwansa a manya manyan mukaman gwamnati domin basu dama. Wannan kuma a siyasance a Najeriyyance haka kowanne gwamna yake yi wajen ganin mutunan da zai nada ya nada na-gindinsa ko da kuwa basu cancantaba.

Sai dai a tsarin addinin Musulunci duk wani mutum da ya mutu baiyi Imani da ALLAH da manzonsa ba, haramun ne a roka masa gafara a wajen ALLAH duk kuwa irin alkhairin da ya shuka. Hakika dukkan wani yabo ko suka da za'a yiwa Yakowa a yanzu babu ko daya da zai amfaneshi, dan munyi Imani duk mutumin da ya mutu ba akan hanyar ALLAH ba shakka babu makoma ta munana a gareshi. Anan sai dai mue ALLAH ya tabbatar masa da makomarsa. Haka kuma, Musulmi basa yin murna da wani mutum ya mutu, ko mutum yayi murna ko kada yayi wanda ya mutu ya riga ya mutu. Sannan kuma kowannemu jiran lokaci yake, kamar yadda ALLAH yayi alkawari kowacce Rai sai ta dan-dana dacin mutuwa. ALLAH ya jikan Musulmi.

Ta bangaren Sabon gwamna Malam Ramadan Yero, muna yi masa addu'ah ta fatan alheri ALLAH yayi masa jagoranci ALLAH ya bashi ikon sauke nauyin da yake akansa. Muna kuma yi masa addu'ah ALLAH ya sa ya kasance abin misali wajen yin adalci tsakanin Musulmi da Kirsita a Jihar kaduna. ALLAH ya taimakeshi.

Yasir Ramadan Gwale

Saturday, December 15, 2012

UMAR LAWAN MUHD: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook (2)


UMAR LAWAN MUHD: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook (2)
Da sunan ALLAH mai gamammiyar Rahama, mai gamamman jin kai, tsiranSa da AmincinSa su kara tabbata ga baban fatima Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam. Ina shaidawa babu abin bauta bisa gaskiya da cancanta sai ALLAH kuma shi ya aiko mana Manzon ALLAH da sakon musulunci.

Kamar yadda ya gabata a fitowa ta farko, na zabi Malam AbdulQadir Muhammad Bello ya zama gwarzo na daya, kuma wannan munasaba ta kama na zaben gwarzo na biyu. Alhamdulillahi na sake lalubawa da kuma yin nazari akan wannan bawan ALLAH Umar Lawan Muhd. Hakika shima kamar Malam AbdulQadir yana kokari babu dare babu rana wajen ganin ya shiryar da mutane suwa ga hanayar ALLAH karkashin koyarwar Salafussaleh.

Hakika duk mai bibiyar sakonnin da suke fitowa daga turakar wannan bawan ALLAH a shafinsa na facebook zai gasgata ni. Yana da himma da kwazo ainun wajen ganin ya isar da sakon ALLAH zuwa ga ‘yan uwa. Ina bibiyar kusan dukkan sakonnin da wannan bawan ALLAH yake fitarwa ta shafinsa. Na bibiyeshi a lokacin da yake kawo tarihin sahabbai khulafa’urra Shidun da sauran Asharatul Mubashshirina Bil jannah, ya yi kokari matuka gaya wajen bayyanawa mutane irin darajar wadannan bayin ALLAH abokan Manzon ALLAH Salallahu Alaihi Wasallam. Bai gajiya ba wajen wannan muhimmiyar karantarwa wadda muke matukar kishirwarta a wannan lokaci, hakika muna bukatar mutane hazikai kuma jajirtattu irinsu wajen kokarin shiryar da mutane zuwa ga hanyar ALLAH ta wannan shafin.

Haka nan, kaima Malam Umar Lawan Muhd, Ina mai yi maka addu’ah ta fatan alheri tare da tawassuli da sunayan ALLAH tsarkaka madaukaka, ALLAH ya sanyawa rayuwarka Albarka, ya kareka daga da-nasani da kuma kasawa. ALLAH ya yi maka jagora a dukkan lamuranka, Ya sadaka da alkhairan duniya da lahira, ALLAH ya ya daukaka darajarka. ALLAH ya amfanar da al’ummar musulmi da rayuwarka.

Ya ALLAH wannan bawa naka Umar Lawan Muhd ka yafa masa kurakuransu wadan da ya sani da wadan da bai sani ba. Ya ALLAH kasa muyi tarayyah da shi acikin Al-jannarka. ALLAH ka karfafeshi ka kara masa juriya da kwarin guiwa, Ya ALLAH kar ka baiwa Shaidan dama akansa.

Daga karshe ina mai kira ga Gwarzona Malam Umar Lawan Muhd da ya zage dantse ya kara kokari akan kokarin da yake da shi, haka kuma Ina mai yiwa kaina da kai da sauran ‘yan uwa Nasiha da muji tsoron ALLAH acikin dukkan lamuranmu, kuma mu dogara ga ALLAH a cikin dukkan lamuranmu, Lallai ALLAH mai rahama ne mai jinkai, kuma maji rokon bayinSa ne Subhanahu Wata’ala. ALLAH ya hada fuskokinmu a Al-Jannah baki daya.

Yasir Ramadan Gwale

Friday, December 14, 2012

ABDULQADIR MUHAMMAD BELLO: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook


ABDULQADIR MUHAMMAD BELLO: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook
Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga ALLAH madaukakin sarki, ubangijin talikai, wanda ya dauki wannan al’umma ya fifita ta akan sauran al’ummatai, ya sanya ta jagora ga sauran mutane don ta shiryar da su ga hanyar cin nasara a rayuwarsu ta duniya da lahira. Tsira da aminciSa su tabbata ga fiyayyen Manzanni, cikamakin Annabawa, wanda ALLAH ya fifita shi ya ba shi littafi mafi cika da kamala wanda ya ke shafe-zane ne ga sauran littatafai, Annabi Muhammadu da Alayansa da Sahabbansa dakuma wadan da sukabi tafarkinsu har ya zuwa ranar sakamko. Dukkan wanda ALLAH ya shiryar shi ne cikakken shiryayye, haka kuma duk wanda ALLAH ya batar babu mai iya shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai ALLAH kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonSa ne.

Hakika nayi nazari sosai kafin zabar wannan gwarzo nawa. Malam AbdulQadir Muhammad Bello matashi ne mai hazaka da juriya kuma jajiratacce. Hakika ina bibiyar dukkan wani rubutu da wannan bawan ALLAH yake yi da kuma wanda yake sharing dare da rana a shafin facebook, na yaba da kwazonsa da juriyarsa wajen kokarin shiryar da mutane ya zuwa ga hanyar ALLAH mikakkiya, bai taba gajiyawa ba wajen sadar da mutane da abubuwan da zasu taimakawa rayuwarsu ta duniya da lahira.

Wannan bawan ALLAH yana kokari matuka da gaske wajen yin da’awa ta gaskiya, tare da kira zuwa ga kadaita ALLAH da bauta akan tafarkin Sunnah da kuma fahimtar magabata na kwarai. Wallahi a wannan zamani Da’awar Sunnah tana bukatar mutane irinsu Malam AbdulQadir, domin samun mutum mai juriya da jajircewa abu ne mai matukar amfani musamman akan hanyar ALLAH.

Malam AbdulQadir ina bibiyar dukkan wasu sakonninka ko da kuwa baka ga comment dina ba. Hakika muna yiwa ALLAH godiya akan wannan baiwa da ya yi mana ta samun matasa jajirtattu masu hazaka irinka. ALLAH ya kara maka san alkhairi da yada shi ga sauran jama’a.

Ina mai yi maka addu’ah tare da tawassuli da sunayan ALLAH tsarkaka madaukaka, ALLAH ya sanyawa rayuwarka Albarka, ya kareka daga dukkan abubuwan ki da kuma kasawa. ALLAH ya yi maka jagora a dukkan lamuranka, Ya sadaka da alkhairan duniya da lahira, ALLAH ya ya daukaka darajarka. ALLAH ya amfanar da al’ummar musulmi da rayuwarka.

Ya ALLAH wannan bawa naka AbdulQadir Muhammad Bello ka yafa masa kurakuransu wadan da ya sani da wadan da bai sani ba. Ya ALLAH kasa muyi tarayyah da shi acikin Al-jannarka. ALLAH ka karfafaeshi ka kara masa juriya da kwarin guiwa, Ya ALLAH kar ka baiwa Shaidan dama akansa.

Daga karshe ina mai kira ga Gwarzona Malam AbdulQadir Muhammad Bello da ya zage dantse ya kara kokari akan kokarin da yake da shi, haka kuma Ina mai yiwa kaina da kai da sauran ‘yan uwa da muji tsoron ALLAH acikin dukkan lamuranmu, kuma mu dogara ga ALLAH a cikin dukkan lamuranmu Lallai ALLAH mai rahama ne mai jinkai, kuma maji rokon bayinSa ne Subhanahu Wata’ala.

Yasir Ramadan Gwale

Wednesday, December 12, 2012

ZOGALE SAMARIN DANGA


ZOGALE SAMARIN DANGA
Ada can akan yiwa zogale kirari da “zogale samarin danga” saboda itacansa bashi da wata wuyar samu a garuruwan Arewa. Zogale yakan fito ne birjik galibi lokacin da ruwan sama ya zuba wato lokacin damina. ‘yan uwanmu na karkara sukan yi kariyar gidajensu da itacansa, su ringa gyara katangar zana da shi inda a mafiya yawancin lokuta ake yin dirka da shi, domin rike dangar kara ko zana da akayi, amma cikin ikon ALLAH da albarkar kasa da muke da ita, ruwan sama na dukansa sai kaga ya yi tsiro kuma bishiya ta tashi a jikin dangar kara, sai aka wayi gari kusan galibin gidaje sai ka samu zogale ne ya kewayesu, wannan ta sanya ake masa kirari da zogale samarin danga. Saboda shi zai fara yi maka maraba idan ka shigo gida. Wannan ta sanya har manoma suke amfani da shi wajen sanya alama ta iyakar gona, saboda bashi da wuyar tashi.

Bayan haka, bincike a baya bayannan yana kara fitowa dangane da irin muhimmanci da ganyan zogale yake da shi. Masana a wannan zamanin suna ta kara fadada bincike dan gano irin muhimmanci da kuma irin sinadaran da zogale yake da su dan taimakawa rayuwar dan adam. A halinyanzu dai masana sun tabbatar da cewar babu wani ganye da yakai zogale amfani ga rayuwar mutane a wannan zamanin, domin yana dauke da sinadarar masu bayar da garkuwa ga lafiya, da kuma kawar da ciwace-ciwace. Kamar cowon suga, damuwa da sauran cututtuka da dama.

Mu kam a kasar Hausa munyi dace, domin tun tale-tale mun taso mun tarar da iyayanmu da kakanninmu suna dafa zogale inda ake yin kwadansa domin aci dan marmari. Wasu kuma suna yin miya da shi, kusan mu haka muke amfani da zogale tun zamani na dauri. Sai yanzu da ilimi da bincike na masana yake ta gano irin alfanun da zogale yake da shi. Domin ba wai ganyansa da muke ci ba, saiwarsa da itacensa da kwayoyinsa duk abubuwa ne masu matukar amfani da kara lafiya. Ana yin shayinsa a sha ko a tafasa shi a sha, yana maganin ciwuka irinsu shawara basur da sauransu.

Masana sun gano cewa Zogale yana dauke da sinadarin Betamin A wanda ake samu a jikin karas har sau 10, sannan yana dauke da kashi 17 na sinadarin da ake samu a jikin madara, sannan kuma yana dauke da kashi 5 na sinadarin betamin C wanda ake samu a jikin lemon zaki da dangoginsa da kuma kashi 15 na sinadarin da ake samu a jikin ayaba, dukkan wadancan sinadarai zogale ya hadasu shi kadai.

Saboda irin yadda bincike ya tabbatar da sahihancin magungunan da zogale yake yi ya sa kasashen Thailand da Malaysiya da Meziko da Kambodiya da Indonisiya da Afurka ta kudu da sauran kasashe da dama suka maida hankali sosai wajen nomansa da sarrafashi domin amfanin jama’a. Lallai muma bai kamata a barmu a baya ba, lallai mu tuntubi masana domin sanin irin alfanun da zogale yake da shi domin cin moriyarsu.
Yasir Ramadan Gwale

Thursday, December 6, 2012

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN


BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN



Ya maigirma shugaban kasa ina fatan wannan wasika tawa zata sameka cikin Aminci, Ina kuma fatan zaka samu zarafin karanta wannan wasika tawa. A matsayina na dan Najeriya na halaliya  ina ganin ina da hakkin yin kira a gareka dan gane da wani mataki mai cike da hadari da gwamnatinka ta dauka. Ko shakka babu wannan mataki bai kamaci wannan gwamnati taka ba, domin lamarine da ba zai haifarwa da kasar nan da mai ido ba. Ina mai cike da masaniyar cewa kana da mashawarta wadanda aikinsu ne su baka shawara kafin daukan dukkan wani mataki ko yanke dukkan wani hukunci, domin a matsayinka na shugaban kasa dole ka ringa tuntubar mashawartanka domin samun shawara ta gari kafin zartar da dukkan irin wani hukunci. Haka kuma, ina mai cike da masaniyar cewa mafiya yawan masu baka shawara ba al'ummar kasarnan ce a gabansu ba, illa kawai suna baka shawarane bisa san ransu da san zuciyarsu, sama da doraka akan turba sahihiya wadda zata yi maka jagorar samun nasara.

Ya maigirma shugaban kasa, bayan wannan abin Ashsha da ya faru na kai harin bom a coci dake cikin barikin sojoji a Jaji, shugaban hafsan sojojin Najeriya Adimiral Ola Saad Ibrahim ya bayar da umarnin sauke wasu manyan sojoji daga mukamansu a barikin soji dake jaji. Wadannan mutane sune Air Vice Marshal Abdullahi Kure da Manjo Janaral Muhammad D Isa. A matsayinka na shugaban kwamandan rundunar askarawan sojojin Najeriya, nayi Imani babu yadda za'a dauki irin wannan mataki mai matukar hadari ba tare da kana da masaniya akai ba, na tabbatar baza'a kasa tuntubar mashawarta ba kafin daukar wannan mataki mai cike da hadari, ko dai an baka wannan shawarar da gayya ne koma meye, lallai wannan wani muhimmin batu ne da ya kamata shugaban kasa ya yi masa karatun ta nutsu. Amma dai abu mafi muhimmanci shine yadda korar wadannan mutane zai iya haifar da gagarumar baraka a wannan kasa, wanda zan zayyano su kamar haka:

Abu na farko, wadannan manyan sojoji an sauke su ne daga mukamansu ba tare da wata kwakwkwarar hujja ko wani dalili gamsashshe ba. Yana da kyau ace anyi taka tsan-tsan sosai wajen daukar irin wannan mataki, domin sanin kowa ne Najeriya kasace da take a cikin wani irin wadi da ya yi kama da na tsaka mai wuya, sannan kuma Addini da kabila suna taka muhimmiyar rawa a dukkan wasu bangarori dangane da yadda ake tafiyar da wannan kasa. Ko wanne irin yanayi ko hali ake ciki alhakin shugaba ne ya tabbatar da hadin kan wannan kasa tare da kaucewa dukkan wani abu da zai iya kawo zaman doya da manja ko yamusta kasar.

Abu na biyu, dukkan wadannan manyan sojoji da aka cire daga kan mukamansu gaba dayansu Musulumi ne, sannan aka yi gaggawar maye gurbinsu da Kiristoci. A bisa tsarin aiki ana iya canzawa mutum wajen aiki ne a duk lokacin da bukatar haka ta taso, kuma a matsayinka na shugaban kasa kuma shugaban rundunar tsaro ta Najeriya lallai akwai bukatar yin la'akari da halin da kasarnan take ciki na sukurkucewar al'amuran tsaro kafin daukar wannan mataki. Domin har yanzu bamu gama farfadowa daga mawuyacin halin da muka shiga ba tun bayan rikicin da ya biyo bayan sakamakon zaben 2011 da ya gabata. Lallai shugaban kasa ya kamata ya yi aiki da lura musamman wajen sauya Musulmi da wanda ba musulmi ba, musamman waje irin wannan mai cike da kalubale, domin daukar irin wannan mataki abu ne da zai iya tayar da kura da yamusta hazo.

Abu na uku, maye gurbin wadannan manyan sojoji musulmi da kiristoci a cikin irin wannan mawuyacin lokaci da muke ciki na gaba kura baya sayaki, kamar yadda muka karanta a shafukan jaridu cewa yanzu maganar da ake yi Barikin sojoji dake jaji ta dawo karkashin kulawar kiristoci tun bayan sauke Air Marshal Abdullahi Kure da Manjo Janar Muhammad D Isa, ina son shugaban kasa ya kwan da sanin cewar tabbas wannan wani mataki ya dauka na wargatsa kasarnan domin shugabanni na addini da shugabanni na al'umma bazasu zura ido suna kallon irin wannan abun yana faruwa ba, kuma za'a ringa kallon wannan a matsayin wani mataki na kakkabe hannun duk wasu musulmi daga Manyan ayyuka musamman irin wannan mai matukar muhimmanci a wannan lokaci da muke ciki.

Ya maigirma shugaban kasa, Babban dalilin rubuta maka wannan wasika, da kuma buga maka wadannan misalai da na kawo shine, domin na ja hankalinka akan wata guguwa da ka iya kunno kai a tsakanin rundunonin sojin kasarnan, musamman tsakanin Musulmi da Kirista. Tabbas sojojin Najeriya suna cikin wani hali da muke fatan samun tabbataccen hadinkai a tsakanin rundunonin sojin dake wannan kasa. Domin a baya lokacin da kasarnan ta samu kanta a cikin wani mawuyacin hali, wadannan sojoji sune suka sadaukar da rayuwarsu wajen tabbatar da dorewar wannan kasar, sun taka muhimmiyar rawa a yakin basasar kasarnan wajen maido da ita kasa daya al'umma daya. Sojojinmu ba wai kawai kokarinsu iya Najeriya ya tsaya ba, sun taimaka gaya wajen dawo da doka da oda a kasashe makwabta da dama, misali, kasar kwango a shekarar 1950, da kuma kasar Saliyo da Laberiya a shekarar 1990, haka kuma yanzu haka sojojinmu suna aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Darfur. Amma abin da yafi kowanne muhimmanci wanda sojoji suka yi shine kauda kansu daga al'amuran siyasa da sukayi tun bayan da mulki ya komo hannu farar hula a shekarar 1999, shakka babu wannan shine lokaci mai tsawo a tarihin kasarnan wanda aka samu dogon lokaci ana mulkin siyasa ba tare da samun wani tsaiko daga soja ba. Haka kuma, duk da halin rashin tabbas da aka shiga a kasarnan lokacin rashin lafiya marigayi shugaban kasa Malam Mumaru Musa 'YarAdua soja sun kauda kai daga shiga al'amuran siyasa, inda suka yi zamansu a cikin barukokinsu, wannan ce ta baka damar zama mukaddashin shugaban kasa a wancan lokaci, har kuma daga baya ka zama shugaban kasa mai cikakken iko lokacin da mutuwa ta yiwa marigayi YarAdua yankan hanzari. A wancan lokaci duka sojojin kasarnan Musulmi da Kirista sun yi aike tare wajen ganin lamura basu lalace ba, kuma an samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu. Tabbas shugaban kasa zai iya daukar wani muhimmin darasi dangane da wannan abin da ya faru.

Daga karshe, Ya maigirma shugaban kasa, ina mai baka shawara ka guji dukkan wani abu da zai iya yamusta kasarnan musamman ta fuskar soji, domin sakamakon abinda zai biyu baya ba zai zama mai kyau ga al'ummar kasarnan ba. Kuma ina fatan shugaban kasa zai yi duba na tsanaki dangane da abinda ya faru a kasarnan tundaga shekarun 1960 har zuwa shekarun 1970 sannan ya duba irin darauusan da suke cikin wannan zamani da kuma kallon irin yadda al'amura zasu wakana nan gaba. Ina kuma fatan shugaban kasa ya tattauna sosai da magabatansa domin samun sahihan bayanai dangane da harkar soji a Najeriya.

Allah ya taimaki Tarayyar Najeriya.

Wannan wasika na samota ne daga wajen Dr Muhammad Jameel Yusha'u, wadda ya rubuta da turanci domin amfanin wadan da basu samu zarafin karanta ta turancin ba.

Yasir 
Ramadan Gwale.
yasirraramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com/

SANUSI LAMIDO SANUSI: BAZAN DAINA MAGANA BA


SANUSI LAMIDO SANUSI: BAZAN DAINA MAGANA BA

Gwmanan Babban Bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi ya mayar da martani a jiya dan gane da masu sukarsa akan kalaman da ya yi a makon da ya gabata. A makon da ya gabata dai an ruwaito Sanusi Lamido yana cewa kusan kashi 70 na dukiyar kasar nan gwamnati take kashewa kanta, yayin da ake kashewa al’ummar kasa kashi 30 kacal, ya ce tattalin arziki zai bunkasa ne idan aka zabtare kashi 50 na masu karbar dirka dirkan albashi.
Tun bayan da Sanusi ya yi wadancan kamalamai ne ake ta mayar masa da martani kama daga ‘yan majalisar tarayya da kungiyoyin kwadago da sauran al’umma. Inda suke ta kira ga gwamnati akan lallai ta sallame shi daga Babban banki.

Amma sanusi da ya yi jawabi a wajen taron National Econmic Summit ya mayar da martani akan masu sukar kalamansa. Ya ce shi kam ba zai taba daina magana ba, dole ne na cigaba da yin fashin baki akan tattalin arziki inji shi. Zan ta yin fashin baki akan sha’anin tattalin arziki har sai naga al’amura sun daidaita. Kuma Ina son jama’a su fahimta daman ni aikina ba yana nufin kullum na saka jama’a cikin farinciki bane. Duk mai bukatar farin ciki da annashuwa ta ya tafi wajen iyalisan su kashe dare. Dan haka jama’a su sani aikina shine na gano yadda tattalin arzikin kasarmu zai samu bunkasa. Ai daga lokacin da muka daina magana saboda tsoron kada a kalubalance mu, to daga wannan lokacin tattalin arzikinmu zai shiga cikin halin ha’ula’i.

Sanusi Lamido ya zargi kundin tsarin mulkin Najeriya da cewa ya sanya al’umma cikin mawuyacin hali ta hanyar sahalewa da masu rike da mukaman siyasa masu yawan gaske, wadan da suke karbar dirka dirkan albashi da alawus ba tare da sunyi wani aiki na ku zo mu gani ba. Dan haka wadannan wasu matsaloli ne da dole mu kalubalance su, kuma mu samo hanya sahihiya da za’a fita daga cikin al-mubazzaranci da dukiyar kasa. Yana da kyau mu fahimta gwamnati ba wai kawai tana biyan ma’aikata albashi bane. Muna da kananan hukumomi 774 kowacce daga cikinsu tana da shugaba da mataimaki da akalla kansiloli 10, shin nawa kake jin yake tafiya wajen hidimta musu?

Bari mu buga misali da jihar kano, idan ka dauki tsohuwar jihar kano, yanzu ta zama Kano da Jigawa. Lokacin da tana a matsayin jiha daya tana da gwamna daya da mataimaki da kwamishinoni akalla ka ce goma, amma yanzu fa? Waccan jihar guda daya ta zama biyu, dan haka kana da gwaman biyu mataimakin gwamna biyu, idan da kwamishinoni 10 ne yanzu sun zama kusan 40 da ‘yan majalisu sama da 80, masu bada shawara da mataimaka na musamman kuwa ALLAH ne kadai ya san yawan wasu.  Nawa kuke zaton ana kashewa wajen yiwa wadannan mutane hidima? Maganar ba wai ta kungiyar kwadago ko majalisa bace, muna maganar ‘yan Najeriya ne kusan miliyan 167. Dan haka wannan kundin tsarin mulki da muke amfani da shi, kwata kwata baida wata ma’ana, ga al’ummar kasa.

Kundn tsarin mulki yayi tanadin cewa dole ne kowace jiha a fadin tarayyar Najeriya ta samu minista guda daya wanda zai wakilce ta. Bari na tambayi masu ilimi, shin meye alakar minista da jiharsa? Wannan yana nuna kenan idan kana da jihohi 50 dole ka samu ministoci 50, haka kuma, idan kana da jihohi 100 dole ka samu ministoci 100 ko shakka babu wannan dirkaniyace a cikin kundin tsarin mulki. Me ya sa mu kadaine muke da irin wannan a duk fadin Nahiyar Afurka?

Malam Sanusi Lamido ya kara da cewa hakkin gwamnati ne ta kula da dukkan bukatun al’ummarta. Yanzu idan har za’a ce gwamnati na kashe kashi 70 na kudin kasa wajen yiwa kanta da ma’aikatanta hidima, sannan ta kashe kashi 30 kacal domin al’ummar kasa, shin korar Sanusi daga aiki zai zama masalaha kenan? Yanzu ‘yan majalisa suna gyaran kundin tsarin mulki, bamu da bukatar ‘yan majalisa 500 domin su yi doka. Ya kara da cewa wata babbar matsala da Najeriya take fuskanta bayan cin-hanci ita ce rashin mutane na gari a matsayin shugabanni. Ba'a yin k’mai bisa doka, am maida komai ya zama kabilanci da bangaranci, ga mutane da suka cancanci a basu wasu muhimman ayyuka da zasu hidmtawa al’umma amma sai a kauce musu saboda bambancin kabila.

Kuma ina kalubalantar ku kanku ‘yan Najeriya mai makon jama’a su mayar da hankali wajen tattauna muhimman al’amura da suka shafi cigaban wannan kasa sai suka bige da tattauna wace irin mota wane yake shiga? Ina wane yake zuwa? Me ya sa bazamu maida hankali wajen tambayar kanmu shin titi mai tsawon kilomita nawa aka gina mana a yankunanmu ba? Me ya sa bazamu maida hankali wajen tattaunawa akan me ya sa haryanzu wutar lantarki bata samu ba? Shin yara nawa ne suka samu nasarar cin darasin Turanci da Lissafi a makarantun sakandare! Lallai muna da babban kalubale kuma muna da babbar matsala agabanmu.

Wednesday, December 5, 2012

RISALA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNA: Engr (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso FNSE


RISALA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNA: Engr (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso FNSE

Bayan Sallama irin ta addinin musulunci, Assalamu Alaikum, Ya maigirma Gwamna, ina son nayi amfani da wannan damar wajen yabawa tare da jinjina a gareka bisa namijin kokari da gwamantinka ta yi wajen samarwa da yankinmu na Arewa maso yamma jami’a wadda aka radawa sunan yankin, hakika wannan wani babban ci-gaba ne kuma abin a yaba, mun gode maigirma gwman, haka kuma, sauran kwalejojin da aka kirkiro ko ake kan kirkirowa wannanma wani babban al’amari ne kuma abin a yaba, sannan uwa uba, ga dimbin al’ummar kano da aka dauka aka kaisu kasashen da dama domin karo ilimi wannan ma wani muhimmin ci-gabane ya maigirma gwamna muna yabawa tare da fatan alheri. Sannan kuma, dole mu gode tare da yabawa musamman yadda gwamnati ke ci-gaba da kawata cikin birnin kano, da kunna fitulu a manyan tituna, da tsabtace gari, duk wannan abun a gode ne kuma abin a yaba.
Ya maigirma gwamna, Ina mai amfani da wannan damar wajen yin fatan alheri a gareka da kuma gwamnatinka. Hakika Ya maigirma Gwamna wannan wani muhimmin al’amari ne akanka a matsayinka na shugabanmu kuma jagoran jihar kano, ina fatan ALLAH ya sa ka gama da wannan shugabanci lafiya. Ya maigirma gwamna na kira wannan sako nawa zuwa gareka da sunan RISALA wanda asali kalmar larabci ce, wadda take nufin SAKO, ina fata sakona ya isa zuwa gareka cikin aminci.

Ya maigirma gwamna a ranar 21 ga watan Nuwamban da ya gabata, a shafinka na facebook ka saki wani sako kamar haka “Mu duk wata sarauta ta gado muna yinta, amma sarauta ta kale ba ruwanmu da ita, mu duk wani nadi da baka gajeshi ba sunansa TUKUNKUNJI” wannan shine sakon da ya fito daga shafinka a wannan rana, inda kuma ya ja hankalin mutane da yawa. Ya maigirma gwamna, kai shugabane kuma jagora ne na duk al’ummar Jihar kano walau ‘ya ‘yanta ne ko baki, duk mutumin da yake kano karkashin ikonka yake. Ya maigirma Gwamna, hakika wannan magana da ta fito ta shafinka magana ce ta kananan mutane bayan kuma mun san kai ba karamin mutum bane.

Ya maigirma gwamna, duk wani mutumin kano na haliliya yana girmama masarautar kano. Duk wata sarauta da mai martaba sarki ya bayar ga kowa ye, muna kyautata zaton cewa mai martaba sarki ba zai baiwa mutumin banza sarauta ba, haka kuma, duk wata sarauta da wani ke da ita a jihar kano indai masarauta ce ta bashi muna kallon masarauta ne ba shi mai rike da sarautar ba. Ya maigirma gwamna akwai al’amura da yawa a gabanka wadanda ya kamata su dauke maka hankali sama da kankananan maganganu irin wadannan. Ya maigirma Gwamna, dukkan gwamnonin Najeriya 36 kai yayane a garesu domin lokacin da ka zama gwamnan farar hula a zangonka na farko, wasu daga cikinsu ko ritaya daga aikin gwamnati basu yi ba, abin da muke fata, Ya maigirma gwaman, shine ka zame musu alkibla kuma jagora, kamar yadda Jihar kano ta yiwa sauran jihohi zarra a fadin tarayyar Najeriya, haka muke fatan ka yi zarra a tsakanin takwarorinka gwamnaoni.

Ya maigirma gwamna, duk wani mutumin kano burinsa jihar kano ta ci gaba ko da kuwa waye yake rike da akalar gwamnati a jihar kano. Col. Dominc Oneye ba Bahaushe bane karewa ba ma Musulmi bane amma ya bautawa jihar kano da al’ummar jihar kano, haka muke fatan duk wani mutum da zai hidimtawa jihar kano ko waye kuma ko daga ina yake matukar zai kiyaye da yanayinmu da addininmu, Ya maigirma gwamna, hakika muna kyautata maka zaton cewa kai me kishin jihar kano ne da kuma son ci-gabanta da al’ummarta, kuma Alhamdulillah babu abinda zamu ce sai ala-san-barka.

Ya maigirma gwamna, a kwanakin baya kayi wata muhimmiyar magana wadda ta tayar da kura musamman a majalisarku ta gwamnonin Najeriya, wannan magana ta rabon arzikin kasa, da kuma batun man da ake hakowa a cikin teku da kuma man da ake hakowa a tsandauri (off-shore On-shore Dichotomy), Ya maigirma gwamna lallai wannan magana da ka kawo kuma da yawa daga cikin gwamnoni ka motsasu dangane da wannan batu, irinsu muke fatan ji daga bakinka a koda yaushe, domin kare martabar yankin Arewa da al’ummar Hausawa, amma Ya maigirma gwamna, yawan maida martani ga Babban abokinka kuma Amininka tsohon gwamna Malam Dr. Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, wannan ba girmanka bane Ya maigirma gwamna. Malam Shekarau ya yi gwamna a Kano kuma ya bautawa jihar kano tsahon wa’adinsa, fatanmu shine ku kasance abokai kuma aminan juna kasancewar kun hidimtawa al’ummar jihar kano.

Ya maigirma gwamna, a har kullum a rayuwa bama fatan a ce jiya tafi yau, domin wannan shine ma’auni da yake nuna rashin ci-gaba, kullum fatanmu a ce Yau tafi Jiya. Batun da ake ta yawan yi na cewa gwamnatin da ta gabace ka ta Aminika, kayi aikin da bata yi ba a cikin shekaru takwas, wallahi kullum fatanmu shine na-gaba ya fi na baya, idan har kullum zamu ringa cewa na baya yafi na gaba lallai babu ci-gaba, dan haka fatanmu shine gwamnatinka ta yi sama da abinda gwamnatin baya bata yi ba, kamar yadda muke fatan duk gwamnan da zai biyo bayanka ya yi sama da abinda ka yi, wannan shine zai daukaka martaba da kimar jihar kano.
Ya maigirma gwamna, babbar matsalar da take damun al’ummar jihar kano bata wuce matsalar tsaro da zaman zullumi da jama’a suke ciki ba. Ya maigimra gwamna lallai kamar yadda kake da labari kuma ka sani al’umma suna cikin hali na rashin kwanciyar hankali da zaman zullumi wanda yau Takai mutum hatta a cikin gidansa ba shi da kwanciyar hankali kasancewar yana tsoron ko za’a iya jefo masa wani abu da zai halaka shi nan take, Ya maigirma Gwamna nemo hanyar da za’a magance wadannan matsaloli sune abinda suka kamata su daukewa gwamnatinka hankali, ba maganganu irin na hamayya ba, hakika kamar yadda muka sani kuna yin kokari akan haka, fatanmu kuma shine ku kara kokari akan kokarin da kuka yi a baya.

Ya maigirma gwamna, Lallai babban abinda mu al’ummar jihar kano muka dogara da shi shine kasuwanci (saye da sayarwa) lallai makiya da mahassada suna ta yin aiki babu dare babu rana wajen kassara kasuwancinmu, domin yanzu duk kasuwanninmu sun rage lokacin tashi, kasancewar mafiya yawansu matasa ne, masu amfani da kananan ababen hawa, ga kuma dokokin da aka sanya saboda su, lallai ya maigirma gwamna a duba wannan lamari da halin da al’umma suke ciki, domin wani ya fito kasuwa ana kiran sallar la’asar kuma za’a fara tunanin tashi daga kasuwa wanda ko shakka babu wannan gurgunata kasuwanci ne ainun.

Daga karshe, Ya maigirma gwamna ina fatan alheri a gareka da gwamnatinka. Ina kuma yi maka addu’ah ta musamman tare da tawassuli da sunayan ALLAH tsarkaka madaukaka ALLAH ya sahale maka gamawa lafiya da mulkinka, ALLAH ya yi maka jagora a dukkan lamuran rayuwaka, sannan ina fata Ya maigirma gwamna yawan kalamai na hamayya da suke fitowa daga bakinka zasu samu raguwa, duk da cewa ba laifi bane idankayi hakan a siyasance, amma muna ganin girmanka da kimarka ya wuce a ji wasu kalaman daga bakinka. Ya maigirma gwamna ina mai yi muku fatan alheri da fatan gamawa da duniya lafiya kai da Babban abokinka kuma Amininka Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano. ALLAH ya taimaki Jihar Kano ya bamu lafiya da zama lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com