ZUWA GA GWAMNAN KANO ENGR RABIU MUSA KWANKWASO
Bayan haka, ya mai girma Gwamna, Ina son yim amfani da wannan dama domin nayi kira tare da roko ga wannan gwamnati taka, akan a taimaka a sassauta dokar hana goyo a babur. Ya mai girma gwamna hakika muna da masaniyar cewa wannan doka ta hana goyo akan babur an dauke ta ne da kyakykyawar niyya, da kuma buri tare da fatan samun ingataccen tsaro a Jiharmu mai Albarka. Ya maigirma gwamna, muna masu roko akan a sassauta wannan doka akan kananan yara da kuma mata.
Da yawan Iyaye musamman masu amfani da babura suna shan bakar wahala, musamman wajen jigilar 'ya 'yansu zuwa makaranta. Mafiya yawancin masu amfani da babura daga cikin magidanta sukan so su kai yaransu makaranta akan babur dinsu cikin sauki, amma a sanadin wannan doka ta sanya dole mutane sai dai su dauki hayar babur din Adaidai Ta Sahu wajen kai yaransu makaranta. Hakika, da yawan magidanta Aljihunsu yayi kuka ainun wajen biyan kudin Adaidaita Sahu, wanda inda an sassauta musu daukar yara, wata kila su yi amfani da wannan rarar kudin wajen sayawa yaransu litattafi da takalman makaranta.
Haka kuma, wasu magidanta sukan buraci daukar Iyalansu dan kaisu Asibiti ko wata gajeriyar unguwa a bayan baburansu. Hakika da yawansu, suma sun shiga cikin mawuyacin hali a sanadiyar rashin daukar iyalansu a bisa baburansu. Allah ya taimaki mai girma Gwamna, muna rokon Alfarma, kamar yadda mun san kai me kishin Kano ne da kanawa, hakika tarihinka ya nuna kana tausayin yara kanana da kuma mata da dattawa. Ya maigirma Gwamna, a taimaka a sassauta wannan doka akan Yara kanana da mata a cikin kwaryar birnin Kano.
Ya maigirma Gwamna, muna san da cewa a himmace kake wajen ganin ka hidimtawa al'ummar jihar kano ta kowane fanni iyakar iyawarka. Dan haka wannan ma wani aiki ne da daman can naka ne, na tausayawa al'umma musamman mata da yara kanana. Haka kuma, muna sane da yadda gwamnatinka ta himmatu wajen taimakawa mata da kananan sana'o'i da jari wajen ganin sun taimakawa yaransu. Wannan kam babu abinda zamu ce sai muyi maka fatan Alheri. Allah ya taimakeka.
Sannan kuma, Ina kira tare da Roko ga Gwamnatin Kano da masu hannu da shuni akan su kara himma wajen samar da karin ababen sufuri na zamani, wajen saukakawa al'umma wahalar zurga zurga, musamman irin manyan motocin nan na safa-safa masu Iya kwandeshan cikin rahusa. Wanda muna sane cewa Gwamnati tana kokari akan hakan, muna rokon a kara kokari.
Daga karshe, Ya maigirma Gwamna, Ina rokon Gwamnatinka ta duba yuwuwar sassauta wannan doka akan yara kana da kuma mata. Haka kuma, mun gamsu da dukkan matakan da gwamnati take dauka wajen ganin an samu ingantaccen tsaro a ciki da wajen jihar Kaqno. Allah ya kara tabbatar mana da dawwamammen zaman lafiya a jihar kano da Najeriya baki daya.
Allah ya taimaki jihar kano, Allah ya taimaki Najeriya.
Yasir Ramadan Gwale
05-06-2013
No comments:
Post a Comment