HUKUNCIN KISAN DA AKA YANKE A JIHAR EDO
HANNUNKA MAI SANDA GA MANJO HAMZA AL-MUSTAPHA
A lokacin da za’a kashe Uwargidan Marigayi MKO Abiola,
marigayiya Kudirat Abiola wasu abubuwa sun faru a daidai wannan lokacin da suke
nuna alamaun cewar tsaro ya sukurkuce a daidai wannan yankin, a kuma wannan
lokacin. Babu jimawa da yin wasu fashe fashe da salwantar rayuka aka kashe Alhaja
Kudirat Abiola Allah ya jikanta. Haka abin yake lokacin da za’a kashe marigayi
Shiekh Jafar Mahmoud Adam, sai da wasu al’amura suka faru da ke nunawa al’umma
cewar akwai alamun cewa tsaro ya dan samu tangarda a yankin dorayi zuwa
fanshekara da kewa, domin sai da aka samu rahoton cewa anyi fashi a caji ofis
na Panshekara kuma an kwashi makamai an gudu, babu jimawa da aikata wannan
fashin aka yiwa Shiekh Jafar Adam kisan gilla a wannan yanki. Allah shine
masani!
A makon da ya gabata, gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole ya
sanya hannu akan dokar zartar da hukuncin kisa akan wasu mutane da kotu ta
yanke musu hukuncin kisa a jiharsa. Kafin zartar da wannan hukunci, tuni aka
jiyo shugaban kasa Goodluck Jonathan yana karfafawa gwamnoni guiwa akan cewa
duk mutumin da aka yankewa hukuncin kisa su gaggauta sanya hannu domin zartar
masa da hukuncin kamar yadda doka ta tanada. Sakamakon da ya biyo baya ya
bayyana cewar an aiwatar da wannan hukuncin kisa akan wadannan mutane da kotu
ta yankewa hukunci, wala’allah bias umarnin Shugaban kasa Adams Oshiomhole ya
sanya hannu. Wallahu A’alam!
Shakka babu wannan hukunci, hannunka mai sanda ne ga tsohon
dogarin shugaban kasa Gen Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha cewar, za’a aiwatar
da irin wannan hukunci akansa, matukar bai samu nasara ba a daukaka karar da
yayi akan hukuncin kisan da wata kotu ta yanke masa a jihar Legas, ko da kuwan
anje kotun Allah ya isa. Kamar yadda muka sani ne, cewar wata kotu ta yankewa
Manjo Mustapha hukuncin kisa ta hanyar rataya a jihar Legas bisa zarginsa da
ake yi wajen shirya da kisan da aka yiwa Marigayiya Kudirat Abiola. Allah shine
masanin hakikanin wadan da suka kashe Kudirat.
Amma dai kisan Kudirat Abiola ba shine zai sanya a kashe Hamza
Al-Mustapha ba ko da kuwa an tattabatar da cewar da umarninsa aka yi kisan.
Sanin kowa ne, kamar kuma yadda shi kansa Manjo Mustpha ya bayyana, yasan
sirrinin kasarnan ciki da waje, kuma yana da masaniyar irin yadda tsaffi da
sabbin shugabannin Najeriya suka aiwatar da wasu al’amura na rashin gaskiya. Wadannan
mutane da suka san da cewar Mustapha yana da masaniyarsu a hannunsa, dole zasu
yi dukkan maiyuwuwa wajen ganin baifita raye ba, domin kuwa bazasu kai labari ba.
Kasancewar Manjo Mustapha
ya kwashe tsawon lokaci a daure wannan ta sanya ya samu tausayawar al’ummar
Najeriya da dama a ciki da wajen Najeriya, wannan kuma wata manuniya ce da take
nuna cewar dukkan ranar da Allah madaukakin sarki ya kaddari Manjo Mustapha da
fitowa to hakika zai samu farin jini mai yawan gaske a idan talakawa wanda
hakan kan iya zama silar shigarsa siyasa har ya kai ga tsayawa takarar Shugaban
kasa, abinda ba zai yiwa Mafiyoyin kasarnan dadi ba.
Wadannan mutane da suke da wannan danyan kashi a gidinsu,
shakka babu suna yin wannan lissafin, sannan kuma suna tunanin makomarsu. Dan
haka kullum suke kwana suke tashi da batun Mustapha. Wannan ta sanya, Sai kaji
an dauko shari’ar kamar da gaske za’a yita, sai kuma kaji ta lafa can sai bayan
wani lokaci a kuma daukota a sake dogon turanci sannan a kara tafiya dogon
hutu. Hakika tsare Mustapha tsawan wadannan shekaru babban zalunci ne da aka yi
masa. Dan a kasarnan babu wata Shari’ah da ta taba daukar lokaci irin wannan.
Domin kuwa ita kanta matar da ake zargin su Hamza Al-Mustapha da shirya kisan
ta, ba wata muhimmiyar mace bace a tarihin siyasar Najeriya, babu wani mukami
da ta rike wanda zai sanya a kalleta a matsayin wata mashahuriya, wancan
laifukan da gungun mafiyoyin kasarnan suka aikata kuma suke da labarin Mustapha
yana da masinyar inda aka je aka dawo, ya sanya aka yi amfani da shari’ar dan
dauke hankulan mutane. Ai a Najeriya an kashe Su Tafawa Balewa da Sardauna da
Murtala wadan da muhimman muatne ne wanda tarihin Najeriya ba zai taba cika ba
sai an lissafo su, amma ba’a dauki wani mataki irin wannan da aka dauka akan
kisan Kudirat Abiola ba, na shari’ah, ko kuwa wannan yana nuna mana cewar
Kudirat Abiola ta fi su Sardauna da Tafawa Balewa da Murtala muhimmanci a
Najeriya ne?
Al-Mustapha idan har anyi masa Shari’ah ta Gaskiya kuma an
same shi da laifi aka yanke masa hukuncin kisa babu wanda zai ce ba’a kyauta
ba. Amma shakka babu anzalunce shi a bisa tsawon lokacin da ya kwashe ba’a yi
masa hukunci ba. Lokaci ne kadai zai bayyana mana gaskiyar yadda lamura suke.
Allah ya raba nagari da mugu ya raba yari da barawo.
Yasir Ramadan Gwale
No comments:
Post a Comment