Wednesday, June 12, 2013

SABON SALON GWAGWARMAYAR SIYASA: JAWABIN MALAM NUHU RIBADU mni A TARON MAJALISAR WAKILAI TA KUNGIYAR DALIBAN JAMI’AR AHMADU BELLO (ABU) ZARI MAI TAKEN “MATASA: GINSHIKIN KOWACCE AL’UMMA” RANAR ASABAR YUNI 8, 20




SABON SALON GWAGWARMAYAR SIYASA: JAWABIN MALAM NUHU RIBADU mni A TARON MAJALISAR WAKILAI TA KUNGIYAR DALIBAN JAMI’AR AHMADU BELLO (ABU) ZARI MAI TAKEN “MATASA: GINSHIKIN KOWACCE AL’UMMA” RANAR ASABAR YUNI 8, 2013.

A ko da yaushe na ziyarci wannan jami’a da ta bani madubin nazarin rayuwa kuma ta zama tushen ilimi na, na kan ji shauki ya kama ni. Wajibi ne in godewa malamai na saboda wannan horo da suka yi min sannan kuma kalubale ne gare ni in yi amfani da wannan ilimi wurin kyautata makomar al’umma domin amfanin ‘yan baya. Don haka ya zama tilas in ce na gode!

Ina godewa malamaina na fuskar nazari, tarbiya, kai har ma da siyasa da suka nuna min muhimmancin gaskiya da rikon amana da jajircewa wurin bautar al’umma. Ku kuma daliban da kuka ga na cancanci zama abin koyi da har kuka gaiyace ni in yi muku wannann jawabi, ina yi muku gagarumar godiyar da girmanta sai dai a kwatantashi da darajar wannan jami’a ta mu. Mun taru ne a karkashin wannan inuwar a yau saboda wani mutum ya gano muhimmancin assasa wannan cibiya. Jami’ar Ahmadu Bello makarantace mai dimbin tarihin da ke kalubalantarmu mu yi adalici a duk inda muka samu kanmu. Wannan na koya mana cewa a kowanne zamani, wajibi ne wani ya sadaukar da kan sa domin ci gaban na baya. 

Ire-iren kabilu, addininai da yankunan al’ummar da ke jami’ar nan tare da darussa daga rayuwar Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto wanda jami’ar ta ci sunansa na sa mana kishin juna ta yadda mu kan kasance masu juriwa bambanci da fahimtar wadanda muka saba a duk inda muka samu kanmu a aikin al’umma ko kuma namu na kashin kanmu. Hakika kun ci sa’a da ku kasance cikin jerin fitattun ‘yan Najeriya, domin a cikinku ina iya ganin jagororin siyasa na nan gaba, da ‘yan gwagwarmayar neman sauyi, shugabannin masana’antu da kuma manyan ma’aikatan gwamnati – a takaice dai makomar kasar nan na hannunku!

Kamar yadda masana suka ce, komai na sauyawa. Don haka ba ma bukatar wani masanin falsafar siyasa ya gaya mana cewa ana samun sauye-sauye da dama a fagen siyasa. Siyasarmu ce ke baiyana su waye mu, meye mu, da kuma akidunmu. Rudanin da muke ciki yanzu haka a sha’anin siyasarmu shi ne abinda zamu yi nazarinsa a yau- kuma wajibi mu yi nazarin a tare. Samuwar fasahar intanet ta kara motsa siyasar zamani saboda damar da ta baiwa matasa su shiga a dama da su cikin harkokin siyasa da cigaban al’umma. Sai dai kuma matasan na fuskantar mummunan kalubale saboda shugabannin sun mai da siyarmu ta zamo mulkin tsofaffi domin amfanin tsofaffi.
A tsarin da muke kai yau, ba’a baiwa sababbin manufofi da dabaru damar da za su kafu har su bunkasa. Abin takaici a dimokradiyyar da mu ke kai shi ne yadda ake murkushe matasa domin tabbar da zalunci da son ran wadansu mutane. Hakika ya isa zalunci idan wasu tsirarun mutane suka tilasatawa mafi yawan al’umma biyan bukatun kansu. Zalunci ne ke sa a jefa dakarun kawo sauyi cikin masifar rashin aikin yi, talauci, rashin tsaro, rashin ingantaccen ilimi, da kuma uwa uba cin hanci da rashawa. Don haka ba mamaki don matasa sun fidda rai da samun mafita daga shugabanninmu na yanzu. Dama ana gane al’umma ta gari ne ta hanyar damarmakin da take baiwa matasanta.

Sai dai kuma bai kamata matasa su yadda ayi amfani da su wurin raba kan al’ummarmu ba. Tamu ta kare a matsayin kasa guda, da zarar matasa suka yaudaru da sabanin da ke tsakanin ‘yan siyasar da basu da hanyar daukaka sai sun shuka gaba tsakanin ‘yan kasa. Abin na koya a siyasa kawo yanzu ya nuna min cewa tsufa ba shi ne dattaku ba musamman a wannan yanayi na matsananciyar adawar siyasa. Sa’a daya, wannan lokaci ne na intanet; musayar ra’ayi da muhawara ta wannan kafa ya bude kofa ga matasa da ma duk wadanda ake zalunta su yi tasiri a fagen siyasar zamani. Wannan zamani na yaduwar bayanai cikin sauki ya baiyana cewa babu wata al’umma da za ta taru gaba daya a cikin bata. Wato dai azzaluman cikinmu sun zama haka ne saboda wadansu tawaye da suke da su ta fannin akida, ilimi, ko ma lafiyar kwakwalwa. Kasancewar Boko Haram ta samo tushe a arewa ba dalili ba ne na tsangwamar daukacin ‘yan arewa ko kuma Musulmi; haka kuma satar mutane da garkuwa da su tare da kaurin sunan da ‘yan bindiga masu tada kayar baya suka yi a baya a kudancin kasar nan ba hujja ba ce ta tsangwamar daukacin ‘yan Niger Delta. Bugu da kari, kisan gillar baya-bayan nan da wasu daga cikin mutunen kabilar Eggon da aka sani da zaman lafiya a jihar Nassarawa suka yiwa ‘yan sand aba zai zama madubin nazarin kabilar baki daya ba. Babu wani mutum a duniyar ne da ke farin ciki da samun rauni. Su kuwa wadannan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran masu kokarin kawo bambance-bambance a tsakaninmu tamkar rauni a jikin kasarmu baki daya. Wadannan abubuwa na bukatar shugabanci ne mai kishin al’umma. Wannan shi ne kiranmu, kuma ya zama wajibi mu yi adalci ga tarihinmu.
Su waye mu…a Dimokradiyya

Babbar yaudarar da muke fuskanta ita ce amincewa da zantukan kwararo da ake yi cewa wai Najeriya wata kasar dagogo-rago ce da aka hada ta karfin tsiya. Ba na wata shakka cewa wannan babban kuskure ne. Gaskiyar tafi haka sauki. Babu wani yanki na Najeriya da ke kunshe da kabila guda tal kafin zuwan turawan mulkin mallaka. ‘Yan siyasa masu neman gindin zama ne su ka kirkiro wannan batun na bambancin kabilu. Tarihi ya nuna Najeriya kasa ce da a baya ta kunshi dimbin garuruwa da masarautu, inda a kudu maso yamma Ijebu da Egba ba su dauki kansu a matsayin day aba, balle a kira su Yarabawa. A kudu maso gabas babban laifi ne a kira mutanen misali Arochukwu da Onitsha a matsayin al’umma daya, don haka ba su kallon junansu a matsayin Igbo. Kasar Hausa ma ba a hade take ba domin kuwa Hausawan Kano da Katsina ba sa alakanta kan su da kabilarsu sai dai da garuruwansu. Amma duk da wadancan bambance-bambancen suna maraba da duk wanda ya ke son zama dan kasarsu.

To mai ya kawo wannan sabuwar rarrabuwar kai da kabilancin da ake ganin kamar ba za’a iya warwarewa ba? Hakika mun yaudari kanmu idan muka yarda cewa akwai wani yanki a Najeriya da zai dore a matsayin kasa guda idan har muka bari ‘yan barandan kabilanci suka samu nasarar raba Najeriya. Babu wata kasa a duniyar nan da ta kunshi mutane iri daya, masu bukatu da manufa iri daya. Kokarinmu na amincewa da juna, da daidata bambance-bambance mu shi ne ya samu zama kasa guda. Sai dai kuma kash! Mun zabi siyasar kabilanci inda mutane ke fifita yarensu da addininsu fiye da kishin kasa. Wannan baragurbin zabin da ya haifar mana da karuwar kabilanci, san kai, rashin gaskiya da kuma tada kayar baya, ya zama makami a hannun makiyan sauyi da suke rushe duk wani buri da muke da shi na ganin Najeriyar da mu ke fata – Najeriyar da zamu sadaukar da kabilunmu don bautawa kasarmu.
Mu su waye a dimokradiyya ba wani abu ne mai rikitarwa ba; mu ‘yan kasa ne masu dama da hakki madaidaita! Mu ‘yan kasa ne kurum, ba Hausa-Fulani ba, ba Igbo ba, ba Yoruba ba, ba Jukun ba, ba Ijaw ba, ba ‘yan arewa ba, ‘yan kudu ba, kuma komai kin amincewarmu, komai ikonmu ko dukiyarmu, gaba daya dai kuri’a daya tak mu ke da ita a tsarin dimokradiyya.

Mu menene…a Dimokadiyya

Menene mu? Mu ne canji! Mu ne ‘yan kasar nan da ke warwatse, ba mu san junanmu ba, da bamu da dangantaka ta jini amma muke da akida guda, ta ganin al’ummarmu ta na aiki, wato masu burin samun sabuwar Najeriya. Canji a wannan zamani na hauma-haumar siyasa shi ne kaifin basirar keta farfagandar da ake yi mana ta tarwatsa kasar nan. Canji, a wannan mawuyacin lokaci shi ne jajircewa wurin cigaba da kasancewa tare duk da karuwar bama-baman da ke tashi a sassan kasarmu. Canji, a wannan lokaci na rashin yarda shi ne yin watsi da shaci-fadin dillalan wariya da ke tattara matsalolin kasar nan kan wani yanki, ko wasu mutane, ko ma dai duk wani “bare” da ba ya cikin “mu”.

Canji, a wannan zamani na juyin juya halin intanet, shi ne amfani da damar da muka samu a wannan fasaha da ta baiwa duk wani mai kwamfuta ko wayar salula damar yin magana a ji. Sai dai kuma an jima ana cewa batutuwan da ake yi game da Najeriya a shafukan intanet sun sabawa ainihin abinda ke faruwa a kasa. Kodayake na amince da cewa Najeriyar intanet ba ta wakiltar Najeriyar zahiri gaba daya, tunda da miliyoyin ‘yan kasarmu da basu iya karatu da rubutu ba basu da damar shiga a dama da su, ya zama wajibi mu fahimci tasirin da masu amfani da intanet ke da shi wurin kawo sauyi a kasarmu. Dunkulewar da ake cewa duniya tayi zuwa kauye guda ba karya ba ne, duk da jan kafar da Najeriya ke yi wurin shiga wannan fage na intanet, kawo yanzu mu ma mun fara ganin irin abubuwan da ada sai dai mu kara a jaridun kasashen waje. Dunkulewar duniya guri guda ya zamo makaranta mai koyar da alheri da sharri, kuma a yanzu tasirin ya zarta tsirarun masu kudi. Karuwar amfani da intanet tsakanin talakawa na bada damar yada bayanai da manufofi cikin sauri. Hakan ya faru a Tunisia. Ya faru a Masar. A nan ma yana faruwa…Sai dai, ya zama wajibi mu sadaukar da kanmu ga canji kafin mu samu canjin da muke fata!
Mecece manufarmu…a Dimokradiyya

Dimokradiyya ba ta armashi idan ta zama dandalin masu kudi zalla. Irin wannan mahangar dimokradiyya na sa tsarin ya yi tsada sannan kuma ya gurbace. Daga lokacin da kuka dorawa ‘yan takararku alhakin sayen kuri’unku kun rasa damar da kuke da ita na kalubalantar yadda suke tafiyar da amanarku. Na amince da malamin siyasar nan na Australia farfesa Dryzek inda ya yi bayanin ainihin Dimokradiyya kamar haka: “Yada Dimokradiyya ba wai shi ne kowane sashe na duniya ya ce yana dimokradiyya ba, ma’anarsa shi ne fadada wadannan abubuwa guda uku…Na farko shi ne kara yawan mutanen da ke da damar fada a ji wurin tafiyar da shugabancin al’umma. Na biyu shi ne fadada yawan abubuwan da ke karkashin ikon dimokradiyya. Na uku shi ne baiwa mutane iko na gaske ba wai na jeka-na-yi-ka ba, ta yadda za su iya amfani da ra’ayin kansu wurin lura da yadda ake tafiyar da al’amuransu.”

Don haka, a yunkurinmu na tabbatar da dimokradiyya a Najeriya, ;ya zama wajibi mu yi amfani da damar da mu ke sakaci da ita. Azzaluman nan fa a tsarin dimokradiyya mutane ne daga cikin al’umma suka zabi zama dakarun magudin zabe domin cutar da al’umar da suka fito daga cikinta. Idan nace mutane mutane ba wai ina nufin masu kada kuri’a kurum ba. Jami’an zaben da suka amince ayi amfani da su wurin murdiya na yin kafar ungulu ga samuwar kasa ta gari a yayinda kuma suke cin amanar mutanen da ake zalunta wadanda su ma suna cikinsu. Siyasa ba tsafi ba ne; lissafi ne na irin alheri da sharrin da muke yi wurin neman mulki. Anan ne muke bukatar hada karfi da karfe mu tabbatar dimokradiyyarmu ta yi karko; mu yi watsi da duk wani lakabi da zai takaita mu daga zama “yan kasa” sannan kuma mu kauracewa duk wani ‘kishin kasa’ da ke neman wani abu sabanin canji zuwa ga kyakkyawar rayuwa. Mu tashi tsaye mu rusa duk wata kungiya da ke kira zuwa ga rarrabuwar kai da wariya. Matukar bamu cire kwadayi da son zuciya daga cikin kishin kasarmu ba, hakika burinmu na kafa gwamnatin da al’umma suka zaba ba zai taba tabbata ba.

Tunkarar dimokradiyyar zamani
Kafin bayyanar intanet, kungiyoyin masu fafutuka da jam’iyyun adawa su aka sani da gwagwarmaya a fagen siyasa. Fasahar intanet ba ta tsaya kan samar da kafar yada bayanai cikin gaggawa ta hanyar musayar ra’ayi da muhawara ba har ma ta zama wani dandali na kyankyasar akidun siyasa, zaburar da al’umma, da ma tawaye. Babban misali anan shi ne matashin mai tallan lemon nan, Muhammad Bouazizi na kasar Tunisia, wanda hallaka kansa da ya yi sanadiyyar zaluncin ‘yan sanda ya zamo ummulhaba’isin kifewar gwamnatin ta jima tana kama karya a wannan kasar da ke arewacin Afrika. Babu wanda zai san da mutuwar Bouazizi da ban da yayata hotunansa da aka yi ta intanet da wayar salula ba, abinda ya harzuka al’ummar kasar. Nasarar da masu zanga-zanga suka samu kan Ben Ali ta aika muhimmin sako ga duk mutanen da ke cikin kangin zalunci, sakon da ya zarta iyakar yankin arewacin Afrika.

To ko me ya hada wannan da Najeriya? Tasirin Bouazizi bai tsaya kan haddasa juyin juya halin kasashen larabawa ba, domin ya koya ‘yan kasar da ke da korafi a fadin duniya su baiyana fushinsu a zahiri ba intanet kadai ba. Ya koyar da hanya mafi inganci ta yin Allah wadai da dokokin da suka sabawa cigaban jama’a. Ya kowa ‘yan Bahrain su nemi ‘yantacciyar tsarin siyasa. Ya koyawa ‘yan Masar su tashi su nemi sabon shugaban kasa. Ya koyawa ‘yan Libya su dauki makamai su yaki shugaban kasar da suka hambarar sannan suka kasha shi. Ya koyawa ‘yan Yemen su kori shugaban kasarsu. Idan muka dawo gida kuma, ya yiwa ‘yan Najeriya kaimi su fita kan tituna domin zanga-zangar kin amincewa da cire tallafin farashin man fetur a watan Janairun 2012.

Yayinda muka yabawa matakin kalubalantar manufofin da basu dace da bukatun al’umma ba muna sane da cewa abu ne mai wuya a sa ran samun cikakkiyar natsuwa a wurin matasan da aka harzuka su har suka fito titi zanga-zanga. Anan ne ya zama wajibi mu tattauna, a matsayinmu na iyali guda, wurin neman mafita daga wannan masifa da muka shiga; ta yaya zamu kawo karshen mulkin danniya da rashin damuwa da talaka ba tare da mun gayyatowa kanmu harsasan wadanda ake turowa domin su kora mu gidajenmu ba, inda ba ma tarar da komai sai takaici da bakin ciki? Da yaya zamu gayawa shugabanninmu na siyasa cewa sun gaza ba tare da an harbe mu ba? Na ce “mu” ne saboda nima wannan lamarin ya dame ni kamar yadda ya dame ku! Na ce “mu” saboda idan muka sake aka rabamu zuwa “mu” da “su”, babu yadda zamu samu nasarar wannan gwagwarmayar. Masu kawo rabuwar kan da su kirkiro “su” domin wargaza shirin hadin kan “mu” gaba daya sune mutanen da ya wajaba mu yaka, kuma hanya daya ce tak ta rage da zamu cimma wannan buri: shigar ‘yan kasa cikin gwagwarmayar siyasa!

Ma’anar Gwagwarmayar Siyasa

A fahimtata gwagwarmayar siyasa a tsarin dimokradiyya shi ne mutum ya fahimci hakkinsa, bayan yin nazari akan nukusanin da ke cikin tsarin da burin da aka ci masa ya gaza samuwa. Ruhin gwagwarmayar siyasa shi ne jajircewa wurin sauke nauyin da tsarin mulki ya dorawa ‘yan kasa ta hanyar kalubalantar manufofi marasa kyau ko kuma da zimmar bada gudunmawa ga gwamnatin da mutum ke ganin ta gaza. Bisa la’akari da sauye-sauyen siyasar zamani, ya kamata mu karkata ga hanyar zaburar da ‘yan kasa ba tare da tashin hankali ba ta irin salon da Bouazizi ya bi. Anan ba ina nufin mu cinnawa kanmu wuta domin nuna bacin ranmu ba. Manufa ita ce amfani da adadin da Allah ya bamu a zaurukan intanet da kuma wuraren taro na zahiri domin bincike da kalubalantar rashin adalcin masu mulki; ina nufin watsi da duk wani kokari da ‘yan-araba za su yi na ganin su rarraba kanmu a kokarinmu na zakulo dan takarar da ya cancanta; Ina nufin mu fahimtar cewa in dai muna neman yin tasiri, gwagwarmaya a shafukan intanet kadai ba ta isa ba sai mun hada da aiki na zahiri. Don haka anan ma muna da gagarumin aiki a gabanmu na zaburar da ‘yan kasa.
Najeriya: Shiga siyasar zamani

A 1999, muka yi maraba da dimokradiyya tare da fatan gina tsarin mulkin farar hula inda kowanne dan kasa ke da rawar takawa. Shekaru goma bayan nan tsarin dimokradiyyarmu ya shiga halin rudani inda ake amfani da bambance-bambancen kabila da addini domin raba kawunanmu. Wannan wata manakisa ce da aka kulla da gangan domin ballo kofar bala’in da muka rufe shi tun karshen yakin basasa – kai, tun ma kafin wannan lokacin. Mun rayu a cikin kasar da ke kokarin yafe kura-kuran da aka yi wa juna a baya, sai dai a yayinda muke fuskantar wannan kalubale, wadansu ‘yan araba sun mayar da tsarin dimokradiyyarmu ya zamo wani dandali da za su samu kuri’un kabilunsu saboda ba za’a su iya samu bisa cancantarsu ko kuma tarihin aikin da suka yi a baya ba. Wannan tsari mummunan tafarki ne mai tarwatsa kasa wanda kuma ya bukatar mu hada kai mu dauki matakan gaggawa na kwato makomarmu daga hannun wadanda ke hawa dokin kabilanci da bambancin addini wurin azurta kansu.
Kalubalen da ke gabanmu gagarumi ne. Kalubalen shi ne mu kafa kungiyoyi da za su yaki mummunan kudirin masu neman raba kanmu da rashin tsari a cikin kasa. A lokacin da ake cikin bala’i kowa dan siyasa ne. Wannan lokaci ne na bala’i a kasarmu. A irin wannan lokaci babu wani lakani da ya dace damu sai na kasancewarmu ‘yan kasa. Mu ‘yan kasa ne da ke fuskantar kalubale, mutanenta ke cikin rudani da matsi, dukiyarta na shan sata a hannun shugabannin da babu abinda ya dame su sai dai adadin dalolin da ke cikin asusun ajiyarsu na banki. A takaice dai ana zaluntar mu a zahiri da kuma kwakwalenmu. Don haka ni ma maganin da na tanada don warware matsalar zai fara ne daga kwakwalwa.

Na farko, duk da yake kabilanci da bambancin addini sun yi katutu a tsakaninmu, ya zama wajibi mu tabbatar cewa a tsarin dimokradiyya babu daya daga cikinsu da yayi tasiri musamman ma idan mun je kada kuri’a face kasancewarmu ‘yan Najeriya. Wajibi ne mu tsaya akan wannan domin shi ne ke nuna mai kishin kasa.

.Na biyu, mu tabbatarwa da zukatanmu a koda yaushe cewa siyasa ba tsafi ba ce kuma mutane suna samun irin gwamnatin da suka cancanta ne. Idan masu zabe su ka yi amfani da kishin kasa wurin zaben shugabannin da suka dace, tilas ne malaman zabe su fahimce cewa magudi cin amana ne ga ‘yan uwansu da za su koma gida su tarar. Babu dai dan takarar da zai iya magudi ba tare da amincewar jama’a ba.
Na uku, gwagwarmayar siyasa ta intanet da ta zahiri wajibi ce ga duk wanda kasarsa ke cikin rikici. Kodayake na sha fadar cewa Najeriya kasa ce da bata cigaba ba don haka kada mu yaudari kanmu da batun intanet. Rukunin ‘yan Najeriya da basu da alaka da intanet na da matukar muhimmanci don haka wajibi mu hada da su a cikin duk wata manufa da muke kokarin cimma.

Na hudu, shiga kungiyoyi da majalisun siyasa, cigaban al’umma da na aikin gayya ita ce babbar hanyar dakushe bambance-bambancen da ke tsakaninmu. Yawan haduwarmu da tattaunawarmu kan kalubalen da ke fuskantar al’ummarmu ba tare da zama ‘yan amshin shatan masu son raba mu ba, shi ne zai sa mu fahimci juna muka jurewa duk wata farfaganda da za’a yi mana. Hakki ne akan dan Najeriya na wannan zamani ba tare da la’akari da bangaren day a fito ba, ya shiga a dama da shi cikin duk wata tattaunawa da za ta yi tasiri kan yadda ake mulkarsa. 

A karshe, ya kamata mu fahimci cewa kasarmu ta shiga cikin hatsari ta fuskantar shugabanci da mu kadai muka fahimce shi kuma zamu iya magance shi. Mu kudurce a zukatanmu cewa a cikin wanann hali dukkanmu ‘yan siyasa ne.

Kammalawa 

Halin da muke ciki a Najeriya a yau ya na kalubalantarmu da yin watsi da duk wasu bambance-bambancen da ke tsakaninmu mu rike matsayinmu na ‘yan kasa a kokarinmu na ceto kasarmu daga hatsarin da ta shiga. Gaba daya rikicin da muke gani na kabila, addini, ko yanki ya samo tushe ne daga siyasa. Wannan ita ce hujjar da ta sa nace a kasar da cikin hatsari, wajibi kowane dan kasa ya zama dan siyasa. Dan siyasa dan kasa ne da ya san me kasarsa ke ciki, babban tambarin dan siyasa shi ne kishin kasa, dan siyasa matashi ne da tsoho, dan siyasa mai kudi ne da talaka, dan siyasa mai tunani kuma mai aiwatarwa, dan siyasa mai aikin yi ne da mara aikin yi, dan siyasa mai kishin al’umma ne mai kishin kasa, dan siyasa malami ne kuma dalibi, dan siyasa kai ne, da ke, da ku, da ni.
Nagode kwarai.

Mallam Nuhu Ribadu

1 comment:

  1. KAMI SEKELUARGA MENGUCAPKAN BANYAK TERIMA KASIH ATAS BANTUANNYA MBAH , NOMOR YANG MBAH BERIKAN/ 4D SGP& HK SAYA DAPAT (350) JUTA ALHAMDULILLAH TEMBUS, SELURUH HUTANG2 SAYA SUDAH SAYA LUNAS DAN KAMI BISAH USAHA LAGI. JIKA ANDA INGIN SEPERTI SAYA HUB MBAH_PURO _085_342_734_904_ terima kasih.

    KAMI SEKELUARGA MENGUCAPKAN BANYAK TERIMA KASIH ATAS BANTUANNYA MBAH , NOMOR YANG MBAH BERIKAN/ 4D SGP& HK SAYA DAPAT (350) JUTA ALHAMDULILLAH TEMBUS, SELURUH HUTANG2 SAYA SUDAH SAYA LUNAS DAN KAMI BISAH USAHA LAGI. JIKA ANDA INGIN SEPERTI SAYA HUB MBAH_PURO _085_342_734_904_ terima kasih.


    KAMI SEKELUARGA MENGUCAPKAN BANYAK TERIMA KASIH ATAS BANTUANNYA MBAH , NOMOR YANG MBAH BERIKAN/ 4D SGP& HK SAYA DAPAT (350) JUTA ALHAMDULILLAH TEMBUS, SELURUH HUTANG2 SAYA SUDAH SAYA LUNAS DAN KAMI BISAH USAHA LAGI. JIKA ANDA INGIN SEPERTI SAYA HUB MBAH_PURO _085_342_734_904_ terima kasih.

    ReplyDelete