BABU WANI BALA’I DA YAKE TUNKARO AL’UMMA DA YA KAI NA BAYYANAR DUJAL (Masi’hud Dajjal)
“. . . Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, yace babu wani Annabi da ya gabace ni face, sai da ya sanar da al’ummarsa irin bala’in “Masi’hud Dajjal”. Ido daya gareshi, Allah kuma ba ido daya gareshi ba . . .” Bukhari
Da farko, yana da kyau mai karatu ya sani, Hakika babu wani bala’I a duniyar nan da zai zo nan gaba sama da bayyanar Dujal. Imran Ibn Hussain (RA) yace “Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, yace tun daga kan Annabi Adam, har zuwa karshen duniya babu wata fitina sama da ta Dujal . . . Muslim ya fitar da hadisin”. Lallai duk inda bala’I ya kai da girma to bayyanar Dujal ya wuce nan. Shi dai Dujal, Allah tuni ya riga ya halicce shi, kuma, yana nan boye a cikin wani waje da Allah shine kadai ya barwa kansa sanin inda yake, Subhanahu wata’ala tsarki ya tabbata a gareshi.
Manzon Allah (saw) ya yi wa al’umma bayanin Dujal, da bayyanarsa da kuma irin abubuwan da yake tafe da su na ban mamaki. Haka kuma, Dujal din zai bayyana dan gajere titturna mai hargitsatstsan gashi kuma gwame. Zai fito daga tsakanin kasashen Suriya da Iraqi, amma zai bayyana inda za’a ganeshi ne a garin ISFAHAAN da yake a cikin kasar IRAN a wani waje da ake kira JUDEA . (Gwari-gwari kace ‘Yan Shi’ah sune Mabiyan Dujal na farko), Yahudawan da suke zaune a Isfahaan sune mabiyan Dujal na farko! Hasbinallahu wani’imal wakeel, Ya Allah muna neman tsarikan daga wannan fitana.
Kamar yadda mafiya yawan Hadisai suka nuna, Dujal zai bayyana ne da Ido daya, anan Malamai sunyi bayanin irin yadda Idon Dujal yake. Da yawan mutane ana rudarsu da cewar Dujal zai bayyana ne da Ido daya a goshinsa, wanda a zahirin gaskiya wannan maganar ba tada asali, Dujal yana da fuska mai idanu guda biyu, amma sai dai shi Idonsa daya na gefen dama ya mutu baya gani da shi, wasu malamai suka ce ramin idon a shafe yake, wasu kuma suka ce da kwayar Idon amma matacciya ce. Al’muhim dai shine Dujal ido guda gareshi kuma ba’a tsakiyar goshinsa yake ba. Sannan kuma, a goshinsa an rubuta KAFIR wannan zai bayyana baro-baro yadda kowa zai iya karantawa.
A tun kusan shekaru da dama da suka gabata a kwai wani hoto na wani jariri mai Ido a goshi, da ake ta yawo da shi a Internet ana cewa shine Dujal, wanda wannan wasu ne kawai suka zauna suka tsara wannan hoto, domin kuwa babu inda aka ruwaito cewar Dujal haifarsa za’a yi, Dujal tuni yana nan a Duniya Allah ya riga ya boyeshi, dan haka wannan hoto da ake yadawa mutane karya ne ba gaskiya bane.
Haka kuma, Bayan bayyanar Dujal a Isfahaan a kasar Iran , zai karade duniyar nan cikin kwanaki 40 kacal. A lokacin da ya bayyana, kwana dayansa zai zama kamar shekara guda ne, kwana na biyu zai zama kamar wata guda ne, kwana na uku zai zama kamar mako guda ne, daga nan kuma sauran ranakun zasu cigaba kamar yadda rana da dare suke fitowa awanni 24. Dujal, yana da wuta yana da Al’jannah, wutarsa itace Al-Jannah ta hakika, duk wanda ya shiga wutar Dujal hakika ya shiga cikin Al-jannah madaukakiya kuma zai dawwama a cikinta. Haka kuma, Al-jannar Dujal ita ce wutar jahannama ta hakika, duk wanda Allah ya sa bashi da rabo ya shiga Al-jannar Dujal hakika ya shiga Jahannama zai dawwama a cikinta. Ya Allah kayi mana tsari daga shiga wuta, Allah ka haramtawa wuta namanmu.
Imran Bin Hussain, ya ruwato daga Manzon Allah cewar duk wanda yaji labarin bayyanar Dujal to kada ya kuskura ya tunakari inda yake, Manzon Allah yace wasu zasu ce, ai su suna da karfin Imani, zasu je su yi kallon Dujal, irin wadannan mutanan daga lokacin da suka je kallo to sun halaka, domin kuwa sai sun bi Dujal. Domin yana da abubuwa na ban mamaki wanda sai wanda Allah ya tsare, yana tayar da wanda ya mutu ya rayar da shi, ya kashe me Rai, sannan yayi ruwan sama, ya sanya danyun ‘ya ‘yan itace su nuna. Abubuwa na ban mamaki ainun, sannan kuma ga shi da wuta da Al-jannah. Hasbinallahu Wani’imal wakeel, hakika Manzon Allah yayi gaskiya, duk wanda yaji labarin bayyanar Dujal to muddin yaje kallo sai yabi Dujal, domin babu yadda mutum zaiga irin wadannan abubuwa da Manzon Allah ya fada bai gasgata Dujal ba. Allah ka tsaremu ka tsare mana imaninmu.
A cikin kwanaki 40 da Dujal zai kewaye Duniya, zai bi har ta Gyallesu ya kwashi mutanansa su yi gaba, daga nan zai yi kokarin Shiga Makkah da Madina, amma zai tarar da Mala’iku suna gadin wadannan garuruwa masu tsarki zai yi dukkan yunkurin shiga amma zasu hanashi shiga, daga nan zai wuce zuwa kasar Sham ko Suriya inda anan ne zai hadu da Imam Mahadi na gaskiya (Ba mahadin ‘yan Shi’ah ba) inda zasu gwabza kazamin karan batta tsakanin Dujal da mabiyansa da kuma Rundunar Mahadi.
A wannan lokacin da gumu tayi gumu tsakanin Rundunar Mahadi da Dujal da mabiyansa Allah subhanahu wata’la zai saukar da Annabi Isa Dan Maryam daga sama. Kadiran ala-manya shi’u! Annabi Isah RA zai sauka ne a Dutsen da ake kira AFEEQ a gabashin Garin Damascus a kasar Suriya, zai sauko ne daga sama, akan hannun Mala’iku suna rike da shi, zai sakko cikin kyakykyawar kamala, kansa yana digar da ruwa gashinsa mai kyau. Abdullahi Ibn Umar Allah ya kara yarda da shi yace, wata rana nayi mafarki gani a gindin dakin Allah (Ka’abah) ina dawafi sai na hangi wani mutum ya sauko daga sama, kansa yana zubo da ruwa, gashinsa yana sheki, sai na tambaya waye wannan ake ce dani ai shine Isah Dan-Maryam, can sai na kuma juya fuska ta, sai naga wani mutum kuttubebe da wata irin mummunar kama, gashinsa dugujaja na tambaya waye wancan kuma, sai aka ce min ai shine Masi’hud Dajjal!
Sannan kuma, Annabi Isah Dan-Maryam zai bayyana ne a daidai lokacin Sallar Asubahi, za’a gabatar da shi dan ya yiwa Musulmi Sallah. Daga nan bayan an idar da Sallah, za’a yi shirin tunkarar Dujal, Annabi Isah zai ritsa Dujal a wani waje da ake kira Lydda inda Dujal zai fara zagwanyewa bayan yayi ido biyu da Annabi Isha Alaihis Salam, bayan narkewar Dujal ne kuma za’a yaki dukkan mutanansa da wadan da suka biyoshi daga Iran da Gyallesu duk za’a halaka su, alokacin nan ne Yahudawa zasu dinga buya a bayan bishiyu da duwatsu dan samun mafaka amma dutsen da bishiyun zasu dinga kiran Musulmi cewa su zo ga Bayahadu su halakashi. Allah buwayi Gagara Misali.
Ya dan uwa lallai ka sani bala’in DUJAL yakai bala’I Allah ya tsaremu ya tsare Iyalanmu. Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, babu wata zaman tahiya da zai yi face sai ya roki tsari daga fitinar Dujal, dan haka mu yawaita neman tsarin Allah daga wannan fitinnar ta Dujal. Abinda na fada ya kasance kuskure ne Allah ya yafemun ya gafarta min.
Yasir Ramadan Gwale
25-06-2013
No comments:
Post a Comment