Wednesday, June 26, 2013

SU WAYE ZASU ZUBA JARI DAN BUNKASAR TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA?


SU WAYE ZASU ZUBA JARI DAN BUNKASAR TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA?

A nahiyar Afurka Najeriya ita ce kasar da Allah ya huwace mata arzikin da bai huwace wa wata kasa ba. Allah cikin ikonsa da falalarsa, ya albarkaci Najeriya da dukkan dangogin albarkatun kasa da ake iya samu, baya ga shimfidaddiyar kasar Noma mai albarka ga yabanya. Sannan, ga ma'ada nai da dangoginsu, wadannan duk Allah ya huwacewa Najeriya sama da kowacce kasa a fadin Afurka. Amma cikin rashin sa'a da 'yan Najeriya suka yi, fiye da rabin wannan dumbin arziki da Allah ya huwacewa Najeriya, ko dai yana tafiya a iska, a mahio, ko kuma wadan da suka fimu wayo da dabara da sanin alfanu da amfanin arzikin da Allah ya huwace mana suna zuwa suna sacewa hankalinsu a kwance, saboda bamu ma san da abin ba, balle mu san amfaninsa.

Idan mutum ya dauki harkar Noma da Kiwo kadai ta isa ta rike Najeriya da wasu kasashen Afurka ta yamma. Allah ya bamu albarkar kasar Noma, kusan duk wani abu da muka shuka kasarmu tana iya karbarsa, amma shekara tana zuwa ta wuce Miliyoyin Kadadar Noma haka take karewa a bushe ba tare da amfanarta ba. Gwamnati da ya kamata ta yi kokarin fahimtar da mutane akan muhimmancin Noma bata baiwa abin wani kulawa ta musamman, mutananmu na karkara da suke yin noman duke irin na zaminin shekaru aru-aru kullum sakinsa suke yi suna komowa cikin birane inda rayuwar karya take! Abinda zai baka mamaki, mutum yana da gona da dabbobi a kauye da zai lura da su, amma zai tsallake su ya zo cikin birni yana tallar yalon bello, ko gyartai, ko yankan farce da sauransu. Ya gwammace da wannan sana'ar sama da Noman, ita kuma hukuma babu wani shiri da take da shi ingantacce dan karfafawa kananan manoma guiwa wajen dagewa da noma.

Kamar yadda naji wani rahoto cewa kaso mai yawa na lemon gwangwani da kamfanunuwan da suke Najeriya suke sarrafawa suna shigo da su daga waje ne. Misali Najeriya tana iya samar da Abarba da takai Ton 800,000 a cikin shekara guda, a yayin da kasar Afurka ta kudu take iya samar da tan 100,000 kacal. Amma duk da haka manyan kamfanonin Najeriya sun dogara da kasashen wajen wajen yin Lemon abarbar da ake yi a Najeriya. Wannan kenanfa. Idan ka dauke 'ya 'yan itatuwa, akwai bangaren kiwon kaji da kifi, da kwarar manja, da rake, da auduga, da tafarnuwa da citta da kanimfari duk wannan zamu iya samar da su da zasu iya raya mana masana'antunmu amma abin ba'a cewa komai.

Wani abin mamaki kuma abin dariya, shine irin yadda gwamnatocinmu suke bin yawan kasashen duniya suna kiran turawa su zo Najeriya su zuba Jari. Su kuma kawai saboda san kudi su rungumo kudi su taho najeriya. Bayan a kullum su wadancan masu arziki ko kamfanonuwa da ake kirawowa suna samun labarin halin da Najeriya take ciki na rashin wutar lantarki, rashin tsaro ga kuma tsabar cinhanci. Kamfanin zaka kafa dan kasamu riba jama'a su samu aikin yi, kasar ita ta amfana amma sai ka bayar da cin hanci kafin ka samu iznin kafa kamfani dan bunkasa kasuwancinka. Ka gayamun kasar da ake irin wannan kazamin cin hancin ta ina zata cigaba. Misali, duniya ta kalli yadda aka yi badakalar cin hanci da rashawa tsakanin Kamfanin Halliburton na amerika da wasu manyan jami'an gwamnatin Najeriya. Haka abin yake da kamfanonuwa irinsu Baswani Brothers na Indiya da sauransu. Irin wadannan kamfanonuwa ne fa ake son su zo su zuba jari a Najeriya.

Alhamdulillah, lokacin da akayi bikin Dimokaradiyya a ranar 29 ga watan Mayu, Gwamnan jihar Jigawa ya shirya taron yadda za'a bunkasa tattalin arzikin jihar Jigawa. Wani abin sha'awa shine masana da dama sun tattauna a wajen wannan taro cikinsu kuwa harda turawa, wani bature a wajen taron ya fadi gaskiya. Yace kamata yayi gwamnatocin Najeriya kafin su je wata kasa neman masu zuba jari a Najeriya, su 'yan Najeriya su fara zuba jari a kasarsu, tunda akwai masu dimbin arziki a kasar da zasu iya yin haka. Hakika wannan magana da Baturen ya fada gaskiya ce, ai ba wayo ko da bara muka fi turawan da zasu zuba mana jari ba, kuma ba son kudin ne basa yi ba.

Wani abin dariya shine manyan masu kudin Najeriya suna kwasar dumbin dukiya suna zuwa kasashen waje suna kafa kamfanonuwa sannan kuma, idan sun dare madafun iko suna bin yawon kasashen turawa suna kiran azo a zuba musu jari a johohinsu, kaga wannan abin dariya ne na hakika. Mu buga misali da tsohon gwamnan Dalta Mista James Ibori, kamfanonuwa nawa ya mallaka a kasar ingila? Amma kuma irinsu ne suke zuwa kiran masu zuba jari. Ira iren James Ibori da suke da dumbin arziki a kasashen waje suna da yawan gaske, sun talauta gida suna gina dawa, sannan kuma suna kiran na dawa ya zo ya gina musu gidansu, kaji mahaukata!

Ai a yadda Allah ya huwacewa Najeriya arziki wallahi bama bukatar wani daga waje yazo ya kafa mana kamfanin yin lemon zobarodo ko kamfanin kindirmon gwamgwani. Amma saboda tsiya da lalacewarmu hatta gidan abinci shugabanninmu buri suke 'yan kasashen waje su zo su bude a Najeriya. Kaje gidajen manyan abinci kaga yadda masu mulki suke kashe kudi akan dan abinda zasu karya kumallo da shi. Komai namu ya koma baya. Sannan kuma, duk da masu mulkinmu suke kiran azo a zuba jari a garuruwansu kwata-kwata basa yin amfani da abubuwan da aka sarrafa a Najeriya! Kaji wata sabuwa kuma, kai akwai wadan da hatta Naman miya daga Ingila ake shigo musu da shi duk mako, kaji gwamna yaje kasar waje ya siyo daskararrun zakaru ya zo da su Najeriya. Lallai idan da gaske arzikin Najeriya ake son habakawa dole al'umma su tashi da gaske su nemi haka, kuma a tursasa gwamnati ko da kuwa bata so.

Yasir Ramadan Gwale 
26-06-2013 

No comments:

Post a Comment