Monday, June 24, 2013

SHIN KO ZUKAR TABA SIGARI HARAMUN NE?


SHIN KO ZUKAR TABA SIGARI HARAMUN NE?

Addinin Musulunci baya cika ga mai yinsa sai ya shaida tare da kudurcewa a zuciyarsa, Babu wani abin bauta bisa gaskiya da cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammad Bawan Allah ne, kuma Manzon Allah ne. Addinin Musulunci Addini ne da Allah ya aiko ManzonSa Salallahu Alaihi Wasallam, dan ya sanar da su addinin gaskiya, haka kuma, addinin Musulunci shine rayuwar dukkan Musulmi, ya koyar da Musulmi hanyoyin da zasu gudanar da rayuwarsu. A cikin sura ta 90, aya ta 10 Allah mai girma da daukaka yana cewa “haka kuma, mun sanar da shi (Manzo) hanyoyi guda biyu, hanar gaskiya da kuma hanyar bata”.

Haka kuma, Allah madaukakin Sarki ya cigaba da cewa: a cikin sura ta 7 aya ta 175 “Mun kyale su suyi dukkan abinda yake dai dai ne, mun kuma hanesu daga dukkan abinda yake bata ne”. Tun daga abubuwan ci da na sha’ da sauran abubuwan bukatun rayuwa.

Shin zukar taba sigari Haramun ne? Bari mu kalli yadda lamarin yake, sanin kowa ne cewa zukar taba sigari yana kaiwa zuwa ga halakar rayuwar mai shanta, domin tana haifar da ciwon sankarar huhu, sankarar jinni, bugun zuciya, da sauransu, wadannan kuma cututtuka ne da suke saurin halaka mai su. Allah ya fada a cikin sura ta 4 aya ta 29 cewa “kada ku kashe kanku…” sannan ya kara da cewa a cikin sura ta 2 aya ta 195 cewa “kada ku jefa kanku cikin halaka…”. A cewar Malam Musulunci da dama wadannan ayoyi sun isa su haramta shan taba sigari da dangoginta.

Kamar yadda kowa ya sani ne, cewar Shan-Taba ‘bata dukiya ne tare da almubazzarantar da ita. Allah mai girma da daukaka ya fada cewa “kada ku kasance masu almubazzaranci da dukiyar da kuka mallaka, Almubazzari abokin shaidan ne, shi kuwa Shaidan kangararre ne wa Ubangijinsa” Sura ta 17 aya ta 26-27. Shan-Taba bayan barnatar da dukiya, jefa kai cikin hadari ne, da jefa rayuwa cikin mummunan garari.

Mai shan-Taba, yana cutar da mutane ta hanyar busa musu hayakin ta, wanda masana suka yi bayanin cewar babbar ill ace a dinga busawa mutum hayakin taba sigari. Haka kuma, manyan kamfanonin da suke yin taba sigari sun rubuta baro baro a jikin kwalayen taba cewar, shan ta yana sa mutum ya mutu da wuri.

Allah ya shiryi masu zukar taba sigari su daina, Allah ya karemu yak are al’ummar mu daga fadawa bin hanyar shaidan.

Yasir Ramadan Gwale
24-06-2013

No comments:

Post a Comment