Sunday, June 30, 2013

LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN



LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN
Waye majnun lailah? Wani mutumne da aka yi a daular banu umaiyya abisa zance mafi inganci. Sunansa shine Qais Bn Mulawwah daga labilar Banu Amir, Qais balaraben kauyene, ya taso tare da ‘yar gidan kawunsa mai suna LAILA BNT MAHDI IBN SA’D Amfi sanin Laila da sunan Laila Aamiriya, tare suka taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balagha.

A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana ajikin Laila sai Qais ya rude soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya tashi. Domin a wannan lokacin ne Qais ya Llura da irin kyawun dirin da Allah ya yiwa abokiyarsa Laila, a kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi take yi a cikin zuciyar Qais, a cikin wannan yanayi ne Qais ya shiga rera mata waqoqin soyayya kala-kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi mahaifin Laila ya nemi da Qais ya fito dan maganar aure, saboda nuna soyayya da kauna said a Qais ya bayar da raquma hamsin gidansu Laila a matsayin kudin aure.

Ana haka sai ga wani mutum da ake kira WIRD BN MUHAMMAD wani dan hamshaqin attajiri ne daga cikin ‘ya’yayen masarautar Banu Umaiyya, katsahan yayi ido hudu da Laila a wata rana a cikin wani Lambu tana kiwon dabobinta. Daga wannan rana Soyayyar Laila ta hana Wird ya yi bacci  a wannan dare! Cikin yan kwanaki kadan Iyayenm Wird suka sauka a gidan su Laila dan neman aurenta ga dansu Wird. A wannan rana da Iyayan Wird suka je ga mahaifin Laila said a suka ajiye masa Manyan Raquma guda dari (100) a matsayin kudin aure, wato ribi biyu akan abinda Qais ya bayar!

Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadayi da son abin duniya. Bayan haka ne Mahaifin Laila ya kira ‘yarsa Laila cikin daki yanai mata hudunbar cewar ga mai kudi dan masu mulki shi zai aurawa ita! Babbar Magana! Laila taki amincewa da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai  ya yi mata barazanar cewar  zai  yanka ta idan har bata amince da auren Wird ba!

Kwatsam sai aka wayi gari Qais ya ji gari ya dauka da kace nace din anyiwa masoyiyarsa Laila aure, da Wird. Wanne irin hali Qais zai kasance a wannan ranar? Tun daga wannan lokacin bacci  yayi hijira daga idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin ciki gami da bacin Rai da takaici, zubar da hawaye babu dare babu rana, suka kasance tare da Qais a matsayin abokai na din-din-din!


Wake waken soyayya sune zancensa, bashi da abokin hira sai wakar da yake yiwa laila ga kadan daga irin abinda yake cewa:


zuwa ga Allah nake kai kukan son laila
 kamar yadda maraya yake kai kukan maraicinsa zuwa a Allah.
Marayanda da kafasa ta karye gashi kuma dangi sun gujeshe
 Lallai rasa iyaye abune mai girman  gaske.

Haka Qais da aka yiwa lakabi da “Majnunu lailah” yake bin kwararo kwararo da saman manyan duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawa Laila wadannan baituka masu motsa zuciya bai gushe ba harse da akayi masa lakabi da “majnunu laila”....!

Duk da cewa itama Laila tana matukar son Qais(majnun) amma kuma hakan baya hanata ta wahalar dashi, a wasu lokutanma harda yi masa wulaqanci, baya ga yin amfani da mallakeshi da tayi wajen azabtar dashi, dama haka sha’anin mata yake shi yasa majnun awani baiti yace:

“Nace da wani babban malami da na gamu dashi a makka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar dani, azamanin da take jiji da kai (saboda ina sonta) shin hakan da take ba laifi bane?” Sai Malamin ya fadawa Qais cewa: “Wallahi da sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita hadu da bala’I”. Dagan an Qai yace, sai na kasa mallakar idona sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jiqa min aljihun rigata, sai nace, Allah ya yafe mata laifinta duk da yake a duniya dan kadanne samunta.


Qais ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan hali har sai da ya samu tabin hankali.  Domin ya kasance idan yaga yara suna wasan kasa yakan zauna tare dasu ya taro kasa ya rinqa gina gida irin wanda yara suke yi da kasa yana cewa cikin waqa: “abokaina kuzo kuga gidana nida laila”....!

A yayinda al-amari ya tsananta sai mutane suka baiwa mahaifin Majnun wato Qais shawara da ya daukeshi ya kaishi ka’aba (dakin Allah) ya umarce shi da ya roqi Allah ya cire masa son Laila! Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Laila ba . . . ataqaice haka majnun ya rayu cikin wannan yanayi na abin tausayi!

Ita kuwa Laila tuni wanda ya aureta ya dauke daga kasar Saudiyya gabaki daya zuwa kasar Iraqi. Haka itama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi abinka da ‘ya mace mai rauni said a rashin ganin Qais ya haddasa mata ciwon zuciya .......! Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin soyayyar Qais Majnun! Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin masoyinta Allah ya karbi rayuwarta! A lokacin da Majnun yaji labarin rasuwarta sai da yaje har kasar Iraqi ya nemi inda take, da inda aka binne ta, a makabartar da aka binne laila a daidai gindin kabarinta ya tare.....! Bashi da aiki sai kuka da wakokin soyayya a gareta. Wata rana da safe sai masu wucewa suka hangoshi (Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan qabarinta, ko da aka zo aka  duba sai aka tarar Allah ya yi masa cikawa! Haka fa Allah yake jarabtar wasu da soyayya, dan haka idan kaji Yasir na sambatu akan Zainab kada ka zargeshi.  

Yasir Ramadan Gwale
30-06-2013

Friday, June 28, 2013

SHUGABA MURSI ZAI BAIWA MARA 'DA KUNYA A MASAR INSHA ALLAH



SHUGABA MURSI ZAI BAIWA MARA 'DA KUNYA A MASAR INSHA ALLAH

Daga Yasir Ramadan Gwale

Nasarar shugaba Muhammad Mursi nasara ce ba ga siyasar kasar Masar ba, Nasara ce ga dukkan masu kishin Islama. Hakika idan shugaba Muhammad Mursi ya samu Nasarar aiwatar da mulkin Demokaradiyya bisa tsarin sauye sauye na Islama ya kawo wani babban cigaba a tsarin gwagwarmayar tabbatar da Mulkin Dimokaradiyya bisa tsarin Musulunci. Shugaba Mursi ya dare kan karagar Mulki a cikin wani irin mawuyacin lokaci da saiyasar kasar Masar ta auka ciki tun bayan tunbuke gwamnatin Mubarak ta kama karya. Sanin kowa ne cewar tun bayan kifar da gwamnatin Mubarak kasar Masar ta kusan durkushewa ta fuskar tattain arziki da harkokin Diplomasiyya, bayan da soji suka karbe ragamar iko karkashin Filmashal Tantawi. 

A karon farko kafin bayyanar shugaba Mursi, wani fitaccen attajiri a cikin Jam'iyyar Muslim Brotherhood da ake kira Khairat Al-shata tauraruwarsa ta haska kafin daga bisani a haramta masa tsayawa zabe. Haramtawa su Khairat Al-shata tsayawa zabe ya baiwa Muhammad Muhammad Mursi damar shiga jerin sahun masu zawarcin kujerar gwamnati. Fitowar Mursi ta fara sauya akalar Siyasar kasar, domin yanayi ya nuna cewar masu kishin Islama daga Muslim Brotherhood ne zasu karbe ragamar ikon kasar. Bayan da aka yi zabe Mursi ya kai labarai wadan da basu yi nasara ba musamman daga cikin 'yan Adawa wadan da galibinsu gyauron gwamnatin Mubarck ne, suke ta aiki babu dare babu rana wajen ganin Mursi bai ci nasarar kawo sauye sauye masu ma'ana ba.

Da farko shugaba Mursi ya fada wani wadi na tsaka mai wuya, wanda za'a iya kiransa da gaba kura baya siyaki, domin yayi ta kiran mutane su zo su taimaka masa amma suna zillewa, sannan a gefe guda kuma, al'ummar kasar sun zurawa shugaba Mursi ido dan ganin ya kawo sauye sauye cikin kankanin lokaci, wannan ta sa da dama suka kasa baiwa shugaba Mursi uzuri, inda rahotanni suka dinga nuna cewar ana yawan samun arangama da daui ba dadi tsakanin magoya bayan Muslim Brotherhood da magoya bayan 'yan adawa wadan da ake hurewa kunne daga kasashen Turai da Amerika wajen ganin sun gurgunta tafyar siyasar shugaba Mursi.

Da yawan kasashen yamma basa son Masu kishin Islama su samu nasarar tafiyar da gwamnati bisa tsarin Musulunci. Wannan ta sanya suke mara baya ga 'yan adawa dan hanawa masu bin tsarin Islama zama lafiya a cikin gwamnatinsu. Irin haka ne ya faru a siyasar kasar Algeria inda su Boutouflika suka hana masu kishin Musulunci tafiyar da mukin bisa tsarin Isama zama lafiya. Yanzu ma irin misalin haka ne yake faruwa a kasar Tunisiya tun bayan tafiyar Zain-el Abideen Ben Ali.

Da dama daga cikin masu yin fashin bakin siyasar kasar masar, da kuma masu aiko da rahotanni musamman ga kafafan watsa labarai na waje, basa yin adalci ga gwamnatin Mursi, kullum suna ta yin kokari ne wajen nuna gazawar gwamnatin Mursi ba tare da bata wani uzuri ba, duba da irin yanayin da ta shigo, haka kuma, da dama daga cikin masu fashin bakin siyasar kasar daga ciki ko daga waje suna goyon bayan 'yan Adawa ne, wadan da suke da burbushin gwamnatin Mubarak a tare da su. Amma duk da haka insha Allah muna taya shugaba Mursi da addu'ah Allah ya bashi Nasara ya baiwa mara 'da kunya.

Yasir Ramadan Gwale 
28-06-2013

Thursday, June 27, 2013

HUKUNCIN KISAN DA AKA YANKE A JIHAR EDO HANNUNKA MAI SANDA GA MANJO HAMZA AL-MUSTAPHA


HUKUNCIN KISAN DA AKA YANKE A JIHAR EDO HANNUNKA MAI SANDA GA MANJO HAMZA AL-MUSTAPHA
A lokacin da za’a kashe Uwargidan Marigayi MKO Abiola, marigayiya Kudirat Abiola wasu abubuwa sun faru a daidai wannan lokacin da suke nuna alamaun cewar tsaro ya sukurkuce a daidai wannan yankin, a kuma wannan lokacin. Babu jimawa da yin wasu fashe fashe da salwantar rayuka aka kashe Alhaja Kudirat Abiola Allah ya jikanta. Haka abin yake lokacin da za’a kashe marigayi Shiekh Jafar Mahmoud Adam, sai da wasu al’amura suka faru da ke nunawa al’umma cewar akwai alamun cewa tsaro ya dan samu tangarda a yankin dorayi zuwa fanshekara da kewa, domin sai da aka samu rahoton cewa anyi fashi a caji ofis na Panshekara kuma an kwashi makamai an gudu, babu jimawa da aikata wannan fashin aka yiwa Shiekh Jafar Adam kisan gilla a wannan yanki. Allah shine masani!

A makon da ya gabata, gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole ya sanya hannu akan dokar zartar da hukuncin kisa akan wasu mutane da kotu ta yanke musu hukuncin kisa a jiharsa. Kafin zartar da wannan hukunci, tuni aka jiyo shugaban kasa Goodluck Jonathan yana karfafawa gwamnoni guiwa akan cewa duk mutumin da aka yankewa hukuncin kisa su gaggauta sanya hannu domin zartar masa da hukuncin kamar yadda doka ta tanada. Sakamakon da ya biyo baya ya bayyana cewar an aiwatar da wannan hukuncin kisa akan wadannan mutane da kotu ta yankewa hukunci, wala’allah bias umarnin Shugaban kasa Adams Oshiomhole ya sanya hannu. Wallahu A’alam!
Shakka babu wannan hukunci, hannunka mai sanda ne ga tsohon dogarin shugaban kasa Gen Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha cewar, za’a aiwatar da irin wannan hukunci akansa, matukar bai samu nasara ba a daukaka karar da yayi akan hukuncin kisan da wata kotu ta yanke masa a jihar Legas, ko da kuwan anje kotun Allah ya isa. Kamar yadda muka sani ne, cewar wata kotu ta yankewa Manjo Mustapha hukuncin kisa ta hanyar rataya a jihar Legas bisa zarginsa da ake yi wajen shirya da kisan da aka yiwa Marigayiya Kudirat Abiola. Allah shine masanin hakikanin wadan da suka kashe Kudirat.

Amma dai kisan Kudirat Abiola ba shine zai sanya a kashe Hamza Al-Mustapha ba ko da kuwa an tattabatar da cewar da umarninsa aka yi kisan. Sanin kowa ne, kamar kuma yadda shi kansa Manjo Mustpha ya bayyana, yasan sirrinin kasarnan ciki da waje, kuma yana da masaniyar irin yadda tsaffi da sabbin shugabannin Najeriya suka aiwatar da wasu al’amura na rashin gaskiya. Wadannan mutane da suka san da cewar Mustapha yana da masaniyarsu a hannunsa, dole zasu yi dukkan maiyuwuwa wajen ganin baifita raye ba, domin kuwa bazasu kai labari ba.

 Kasancewar Manjo Mustapha ya kwashe tsawon lokaci a daure wannan ta sanya ya samu tausayawar al’ummar Najeriya da dama a ciki da wajen Najeriya, wannan kuma wata manuniya ce da take nuna cewar dukkan ranar da Allah madaukakin sarki ya kaddari Manjo Mustapha da fitowa to hakika zai samu farin jini mai yawan gaske a idan talakawa wanda hakan kan iya zama silar shigarsa siyasa har ya kai ga tsayawa takarar Shugaban kasa, abinda ba zai yiwa Mafiyoyin kasarnan dadi ba.

Wadannan mutane da suke da wannan danyan kashi a gidinsu, shakka babu suna yin wannan lissafin, sannan kuma suna tunanin makomarsu. Dan haka kullum suke kwana suke tashi da batun Mustapha. Wannan ta sanya, Sai kaji an dauko shari’ar kamar da gaske za’a yita, sai kuma kaji ta lafa can sai bayan wani lokaci a kuma daukota a sake dogon turanci sannan a kara tafiya dogon hutu. Hakika tsare Mustapha tsawan wadannan shekaru babban zalunci ne da aka yi masa. Dan a kasarnan babu wata Shari’ah da ta taba daukar lokaci irin wannan. Domin kuwa ita kanta matar da ake zargin su Hamza Al-Mustapha da shirya kisan ta, ba wata muhimmiyar mace bace a tarihin siyasar Najeriya, babu wani mukami da ta rike wanda zai sanya a kalleta a matsayin wata mashahuriya, wancan laifukan da gungun mafiyoyin kasarnan suka aikata kuma suke da labarin Mustapha yana da masinyar inda aka je aka dawo, ya sanya aka yi amfani da shari’ar dan dauke hankulan mutane. Ai a Najeriya an kashe Su Tafawa Balewa da Sardauna da Murtala wadan da muhimman muatne ne wanda tarihin Najeriya ba zai taba cika ba sai an lissafo su, amma ba’a dauki wani mataki irin wannan da aka dauka akan kisan Kudirat Abiola ba, na shari’ah, ko kuwa wannan yana nuna mana cewar Kudirat Abiola ta fi su Sardauna da Tafawa Balewa da Murtala muhimmanci a Najeriya ne?

Al-Mustapha idan har anyi masa Shari’ah ta Gaskiya kuma an same shi da laifi aka yanke masa hukuncin kisa babu wanda zai ce ba’a kyauta ba. Amma shakka babu anzalunce shi a bisa tsawon lokacin da ya kwashe ba’a yi masa hukunci ba. Lokaci ne kadai zai bayyana mana gaskiyar yadda lamura suke. Allah ya raba nagari da mugu ya raba yari da barawo.

Yasir Ramadan Gwale

Wednesday, June 26, 2013

SU WAYE ZASU ZUBA JARI DAN BUNKASAR TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA?


SU WAYE ZASU ZUBA JARI DAN BUNKASAR TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA?

A nahiyar Afurka Najeriya ita ce kasar da Allah ya huwace mata arzikin da bai huwace wa wata kasa ba. Allah cikin ikonsa da falalarsa, ya albarkaci Najeriya da dukkan dangogin albarkatun kasa da ake iya samu, baya ga shimfidaddiyar kasar Noma mai albarka ga yabanya. Sannan, ga ma'ada nai da dangoginsu, wadannan duk Allah ya huwacewa Najeriya sama da kowacce kasa a fadin Afurka. Amma cikin rashin sa'a da 'yan Najeriya suka yi, fiye da rabin wannan dumbin arziki da Allah ya huwacewa Najeriya, ko dai yana tafiya a iska, a mahio, ko kuma wadan da suka fimu wayo da dabara da sanin alfanu da amfanin arzikin da Allah ya huwace mana suna zuwa suna sacewa hankalinsu a kwance, saboda bamu ma san da abin ba, balle mu san amfaninsa.

Idan mutum ya dauki harkar Noma da Kiwo kadai ta isa ta rike Najeriya da wasu kasashen Afurka ta yamma. Allah ya bamu albarkar kasar Noma, kusan duk wani abu da muka shuka kasarmu tana iya karbarsa, amma shekara tana zuwa ta wuce Miliyoyin Kadadar Noma haka take karewa a bushe ba tare da amfanarta ba. Gwamnati da ya kamata ta yi kokarin fahimtar da mutane akan muhimmancin Noma bata baiwa abin wani kulawa ta musamman, mutananmu na karkara da suke yin noman duke irin na zaminin shekaru aru-aru kullum sakinsa suke yi suna komowa cikin birane inda rayuwar karya take! Abinda zai baka mamaki, mutum yana da gona da dabbobi a kauye da zai lura da su, amma zai tsallake su ya zo cikin birni yana tallar yalon bello, ko gyartai, ko yankan farce da sauransu. Ya gwammace da wannan sana'ar sama da Noman, ita kuma hukuma babu wani shiri da take da shi ingantacce dan karfafawa kananan manoma guiwa wajen dagewa da noma.

Kamar yadda naji wani rahoto cewa kaso mai yawa na lemon gwangwani da kamfanunuwan da suke Najeriya suke sarrafawa suna shigo da su daga waje ne. Misali Najeriya tana iya samar da Abarba da takai Ton 800,000 a cikin shekara guda, a yayin da kasar Afurka ta kudu take iya samar da tan 100,000 kacal. Amma duk da haka manyan kamfanonin Najeriya sun dogara da kasashen wajen wajen yin Lemon abarbar da ake yi a Najeriya. Wannan kenanfa. Idan ka dauke 'ya 'yan itatuwa, akwai bangaren kiwon kaji da kifi, da kwarar manja, da rake, da auduga, da tafarnuwa da citta da kanimfari duk wannan zamu iya samar da su da zasu iya raya mana masana'antunmu amma abin ba'a cewa komai.

Wani abin mamaki kuma abin dariya, shine irin yadda gwamnatocinmu suke bin yawan kasashen duniya suna kiran turawa su zo Najeriya su zuba Jari. Su kuma kawai saboda san kudi su rungumo kudi su taho najeriya. Bayan a kullum su wadancan masu arziki ko kamfanonuwa da ake kirawowa suna samun labarin halin da Najeriya take ciki na rashin wutar lantarki, rashin tsaro ga kuma tsabar cinhanci. Kamfanin zaka kafa dan kasamu riba jama'a su samu aikin yi, kasar ita ta amfana amma sai ka bayar da cin hanci kafin ka samu iznin kafa kamfani dan bunkasa kasuwancinka. Ka gayamun kasar da ake irin wannan kazamin cin hancin ta ina zata cigaba. Misali, duniya ta kalli yadda aka yi badakalar cin hanci da rashawa tsakanin Kamfanin Halliburton na amerika da wasu manyan jami'an gwamnatin Najeriya. Haka abin yake da kamfanonuwa irinsu Baswani Brothers na Indiya da sauransu. Irin wadannan kamfanonuwa ne fa ake son su zo su zuba jari a Najeriya.

Alhamdulillah, lokacin da akayi bikin Dimokaradiyya a ranar 29 ga watan Mayu, Gwamnan jihar Jigawa ya shirya taron yadda za'a bunkasa tattalin arzikin jihar Jigawa. Wani abin sha'awa shine masana da dama sun tattauna a wajen wannan taro cikinsu kuwa harda turawa, wani bature a wajen taron ya fadi gaskiya. Yace kamata yayi gwamnatocin Najeriya kafin su je wata kasa neman masu zuba jari a Najeriya, su 'yan Najeriya su fara zuba jari a kasarsu, tunda akwai masu dimbin arziki a kasar da zasu iya yin haka. Hakika wannan magana da Baturen ya fada gaskiya ce, ai ba wayo ko da bara muka fi turawan da zasu zuba mana jari ba, kuma ba son kudin ne basa yi ba.

Wani abin dariya shine manyan masu kudin Najeriya suna kwasar dumbin dukiya suna zuwa kasashen waje suna kafa kamfanonuwa sannan kuma, idan sun dare madafun iko suna bin yawon kasashen turawa suna kiran azo a zuba musu jari a johohinsu, kaga wannan abin dariya ne na hakika. Mu buga misali da tsohon gwamnan Dalta Mista James Ibori, kamfanonuwa nawa ya mallaka a kasar ingila? Amma kuma irinsu ne suke zuwa kiran masu zuba jari. Ira iren James Ibori da suke da dumbin arziki a kasashen waje suna da yawan gaske, sun talauta gida suna gina dawa, sannan kuma suna kiran na dawa ya zo ya gina musu gidansu, kaji mahaukata!

Ai a yadda Allah ya huwacewa Najeriya arziki wallahi bama bukatar wani daga waje yazo ya kafa mana kamfanin yin lemon zobarodo ko kamfanin kindirmon gwamgwani. Amma saboda tsiya da lalacewarmu hatta gidan abinci shugabanninmu buri suke 'yan kasashen waje su zo su bude a Najeriya. Kaje gidajen manyan abinci kaga yadda masu mulki suke kashe kudi akan dan abinda zasu karya kumallo da shi. Komai namu ya koma baya. Sannan kuma, duk da masu mulkinmu suke kiran azo a zuba jari a garuruwansu kwata-kwata basa yin amfani da abubuwan da aka sarrafa a Najeriya! Kaji wata sabuwa kuma, kai akwai wadan da hatta Naman miya daga Ingila ake shigo musu da shi duk mako, kaji gwamna yaje kasar waje ya siyo daskararrun zakaru ya zo da su Najeriya. Lallai idan da gaske arzikin Najeriya ake son habakawa dole al'umma su tashi da gaske su nemi haka, kuma a tursasa gwamnati ko da kuwa bata so.

Yasir Ramadan Gwale 
26-06-2013 

Tuesday, June 25, 2013

BABU WANI BALA’I DA YAKE TUNKARO AL’UMMA DA YA KAI NA BAYYANAR DUJAL (Masi’hud Dajjal)

BABU WANI BALA’I DA YAKE TUNKARO AL’UMMA DA YA KAI NA BAYYANAR DUJAL (Masi’hud Dajjal)

“. . . Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, yace babu wani Annabi da ya gabace ni face, sai da ya sanar da al’ummarsa irin bala’in “Masi’hud Dajjal”. Ido daya gareshi, Allah kuma ba ido daya gareshi ba . . .” Bukhari

Da farko, yana da kyau mai karatu ya sani, Hakika babu wani bala’I a duniyar nan da zai zo nan gaba sama da bayyanar Dujal. Imran Ibn Hussain (RA) yace “Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, yace tun daga kan Annabi Adam, har zuwa karshen duniya babu wata fitina sama da ta Dujal . . . Muslim ya fitar da hadisin”. Lallai duk inda bala’I ya kai da girma to bayyanar Dujal ya wuce nan. Shi dai Dujal, Allah tuni ya riga ya halicce shi, kuma, yana nan boye a cikin wani waje da Allah shine kadai ya barwa kansa sanin inda yake, Subhanahu wata’ala tsarki ya tabbata a gareshi.

Manzon Allah (saw) ya yi wa al’umma bayanin Dujal, da bayyanarsa da kuma irin abubuwan da yake tafe da su na ban mamaki. Haka kuma, Dujal din zai bayyana dan gajere titturna mai hargitsatstsan gashi kuma gwame. Zai fito daga tsakanin kasashen Suriya da Iraqi, amma zai bayyana inda za’a ganeshi ne a garin ISFAHAAN da yake a cikin kasar IRAN a wani waje da ake kira JUDEA. (Gwari-gwari kace ‘Yan Shi’ah sune Mabiyan Dujal na farko), Yahudawan da suke zaune a Isfahaan sune mabiyan Dujal na farko! Hasbinallahu wani’imal wakeel, Ya Allah muna neman tsarikan daga wannan fitana.

Kamar yadda mafiya yawan Hadisai suka nuna, Dujal zai bayyana ne da Ido daya, anan Malamai sunyi bayanin irin yadda Idon Dujal yake. Da yawan mutane ana rudarsu da cewar Dujal zai bayyana ne da Ido daya a goshinsa, wanda a zahirin gaskiya wannan maganar ba tada asali, Dujal yana da fuska mai idanu guda biyu, amma sai dai shi Idonsa daya na gefen dama ya mutu baya gani da shi, wasu malamai suka ce ramin idon a shafe yake, wasu kuma suka ce da kwayar Idon amma matacciya ce. Al’muhim dai shine Dujal ido guda gareshi kuma ba’a tsakiyar goshinsa yake ba. Sannan kuma, a goshinsa an rubuta KAFIR wannan zai bayyana baro-baro yadda kowa zai iya karantawa.

A tun kusan shekaru da dama da suka gabata a kwai wani hoto na wani jariri mai Ido a goshi, da ake ta yawo da shi a Internet ana cewa shine Dujal, wanda wannan wasu ne kawai suka zauna suka tsara wannan hoto, domin kuwa babu inda aka ruwaito cewar Dujal haifarsa za’a yi, Dujal tuni yana nan a Duniya Allah ya riga ya boyeshi, dan haka wannan hoto da ake yadawa mutane karya ne ba gaskiya bane.

Haka kuma, Bayan bayyanar Dujal a Isfahaan a kasar Iran, zai karade duniyar nan cikin kwanaki 40 kacal. A lokacin da ya bayyana, kwana dayansa zai zama kamar shekara guda ne, kwana na biyu zai zama kamar wata guda ne, kwana na uku zai zama kamar mako guda ne, daga nan kuma sauran ranakun zasu cigaba kamar yadda rana da dare suke fitowa awanni 24. Dujal, yana da wuta yana da Al’jannah, wutarsa itace Al-Jannah ta hakika, duk wanda ya shiga wutar Dujal hakika ya shiga cikin Al-jannah madaukakiya kuma zai dawwama a cikinta. Haka kuma, Al-jannar Dujal ita ce wutar jahannama ta hakika, duk wanda Allah ya sa bashi da rabo ya shiga Al-jannar Dujal hakika ya shiga Jahannama zai dawwama a cikinta. Ya Allah kayi mana tsari daga shiga wuta, Allah ka  haramtawa wuta namanmu.

Imran Bin Hussain, ya ruwato daga Manzon Allah cewar duk wanda yaji labarin bayyanar Dujal to kada ya kuskura ya tunakari inda yake, Manzon Allah yace wasu zasu ce, ai su suna da karfin Imani, zasu je su yi kallon Dujal, irin wadannan mutanan daga lokacin da suka je kallo to sun halaka, domin kuwa sai sun bi Dujal. Domin yana da abubuwa na ban mamaki wanda sai wanda Allah ya tsare, yana tayar da wanda ya mutu ya rayar da shi, ya kashe me Rai, sannan yayi ruwan sama, ya sanya danyun ‘ya ‘yan itace su nuna. Abubuwa na ban mamaki ainun, sannan kuma ga shi da wuta da Al-jannah. Hasbinallahu Wani’imal wakeel, hakika Manzon Allah yayi gaskiya, duk wanda yaji labarin bayyanar Dujal to muddin yaje kallo sai yabi Dujal, domin babu yadda mutum zaiga irin wadannan abubuwa da Manzon Allah ya fada bai gasgata Dujal ba. Allah ka tsaremu ka tsare mana imaninmu.

A cikin kwanaki 40 da Dujal zai kewaye Duniya, zai bi har ta Gyallesu ya kwashi mutanansa su yi gaba, daga nan zai yi kokarin Shiga Makkah da Madina, amma zai tarar da Mala’iku suna gadin wadannan garuruwa masu tsarki zai yi dukkan yunkurin shiga amma zasu hanashi shiga, daga nan zai wuce zuwa kasar Sham ko Suriya inda anan ne zai hadu da Imam Mahadi na gaskiya (Ba mahadin ‘yan Shi’ah ba) inda zasu gwabza kazamin karan batta tsakanin Dujal da mabiyansa da kuma Rundunar Mahadi.

A wannan lokacin da gumu tayi gumu tsakanin Rundunar Mahadi da Dujal da mabiyansa Allah subhanahu wata’la zai saukar da Annabi Isa Dan Maryam daga sama. Kadiran ala-manya shi’u! Annabi Isah RA zai sauka ne a Dutsen da ake kira AFEEQ a gabashin Garin Damascus a kasar Suriya, zai sauko ne daga sama, akan hannun Mala’iku suna rike da shi, zai sakko cikin kyakykyawar kamala, kansa yana digar da ruwa gashinsa mai kyau. Abdullahi Ibn Umar Allah ya kara yarda da shi yace, wata rana nayi mafarki gani a gindin dakin Allah (Ka’abah) ina dawafi sai na hangi wani mutum ya sauko daga sama, kansa yana zubo da ruwa, gashinsa yana sheki, sai na tambaya waye wannan ake ce dani ai shine Isah Dan-Maryam, can sai na kuma juya fuska ta, sai naga wani mutum kuttubebe da wata irin mummunar kama, gashinsa dugujaja na tambaya waye wancan kuma, sai aka ce min ai shine Masi’hud Dajjal!

Sannan kuma, Annabi Isah Dan-Maryam zai bayyana ne a daidai lokacin Sallar Asubahi, za’a gabatar da shi dan ya yiwa Musulmi Sallah. Daga nan bayan an idar da Sallah, za’a yi shirin tunkarar Dujal, Annabi Isah zai ritsa Dujal a wani waje da ake kira Lydda inda Dujal zai fara zagwanyewa bayan yayi ido biyu da Annabi Isha Alaihis Salam, bayan narkewar Dujal ne kuma za’a yaki dukkan mutanansa da wadan da suka biyoshi daga Iran da Gyallesu duk za’a halaka su, alokacin nan ne Yahudawa zasu dinga buya a bayan bishiyu da duwatsu dan samun mafaka amma dutsen da bishiyun zasu dinga kiran Musulmi cewa su zo ga Bayahadu su halakashi. Allah buwayi Gagara Misali.

Ya dan uwa lallai ka sani bala’in DUJAL yakai bala’I Allah ya tsaremu ya tsare Iyalanmu. Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, babu wata zaman tahiya da zai yi face sai ya roki tsari daga fitinar Dujal, dan haka mu yawaita neman tsarin Allah daga wannan fitinnar ta Dujal. Abinda na fada ya kasance kuskure ne Allah ya yafemun ya gafarta min.

Yasir Ramadan Gwale
25-06-2013


Monday, June 24, 2013

SHIN KO ZUKAR TABA SIGARI HARAMUN NE?


SHIN KO ZUKAR TABA SIGARI HARAMUN NE?

Addinin Musulunci baya cika ga mai yinsa sai ya shaida tare da kudurcewa a zuciyarsa, Babu wani abin bauta bisa gaskiya da cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammad Bawan Allah ne, kuma Manzon Allah ne. Addinin Musulunci Addini ne da Allah ya aiko ManzonSa Salallahu Alaihi Wasallam, dan ya sanar da su addinin gaskiya, haka kuma, addinin Musulunci shine rayuwar dukkan Musulmi, ya koyar da Musulmi hanyoyin da zasu gudanar da rayuwarsu. A cikin sura ta 90, aya ta 10 Allah mai girma da daukaka yana cewa “haka kuma, mun sanar da shi (Manzo) hanyoyi guda biyu, hanar gaskiya da kuma hanyar bata”.

Haka kuma, Allah madaukakin Sarki ya cigaba da cewa: a cikin sura ta 7 aya ta 175 “Mun kyale su suyi dukkan abinda yake dai dai ne, mun kuma hanesu daga dukkan abinda yake bata ne”. Tun daga abubuwan ci da na sha’ da sauran abubuwan bukatun rayuwa.

Shin zukar taba sigari Haramun ne? Bari mu kalli yadda lamarin yake, sanin kowa ne cewa zukar taba sigari yana kaiwa zuwa ga halakar rayuwar mai shanta, domin tana haifar da ciwon sankarar huhu, sankarar jinni, bugun zuciya, da sauransu, wadannan kuma cututtuka ne da suke saurin halaka mai su. Allah ya fada a cikin sura ta 4 aya ta 29 cewa “kada ku kashe kanku…” sannan ya kara da cewa a cikin sura ta 2 aya ta 195 cewa “kada ku jefa kanku cikin halaka…”. A cewar Malam Musulunci da dama wadannan ayoyi sun isa su haramta shan taba sigari da dangoginta.

Kamar yadda kowa ya sani ne, cewar Shan-Taba ‘bata dukiya ne tare da almubazzarantar da ita. Allah mai girma da daukaka ya fada cewa “kada ku kasance masu almubazzaranci da dukiyar da kuka mallaka, Almubazzari abokin shaidan ne, shi kuwa Shaidan kangararre ne wa Ubangijinsa” Sura ta 17 aya ta 26-27. Shan-Taba bayan barnatar da dukiya, jefa kai cikin hadari ne, da jefa rayuwa cikin mummunan garari.

Mai shan-Taba, yana cutar da mutane ta hanyar busa musu hayakin ta, wanda masana suka yi bayanin cewar babbar ill ace a dinga busawa mutum hayakin taba sigari. Haka kuma, manyan kamfanonin da suke yin taba sigari sun rubuta baro baro a jikin kwalayen taba cewar, shan ta yana sa mutum ya mutu da wuri.

Allah ya shiryi masu zukar taba sigari su daina, Allah ya karemu yak are al’ummar mu daga fadawa bin hanyar shaidan.

Yasir Ramadan Gwale
24-06-2013

MASAR: HASSAN SHEHATA NA KASAR MASAR YA BAKUNCI LAHIRA SAKAMAKON ZAGIN NANA AISHA (Uwar Muminai) MATAR MANZON ALLAH (SAW)

Wani fitaccen Malamin Addinin Shi’ah Sheikh Hassan Shehata ya bakunci Lahira sakamakon zagin Uwar Muminai, Nana Aisha Radiyallahu Anha. Shi dai malamin daman ya shahara da zagi da aibanta sahabban Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam, tare da Iyalan Gidansa.

A ranar lahadin makon da ya gabata ne, al’ummar garin Giza dake kusa da babban birnin kasar Masar Al-Qahira, suka yiwa unguwar da Shehata yake tsinke. Inda daman tuni suke zarginsa da gina wani makeken gida wanda babu abinda ake yi acikinsa sai aikata zinace-zinace da sunan Mut’ah, wato auren taba ka lashe da shi’ah suke yi. Baya ga wannan, mutanan wannan unguwa suna cike da bakin ciki kwarai da gaske irin yadda Shehata yake zagi da aibanta Uwar Muminai Nana Aisha Matar Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam.

Da abin ya kai bango ne a ranar lahadin da ta gabata al’ummar suka yi kukan kura inda suka kunna kai cikin gidan da shahata yake aikata masha’a tare da sauran ‘yan shi’ar da ke cikin gidan. Rahotanni sunce akwai kimanin Mutane 38 acikin gidan suna aikata zinace-zinace a lokacin da matasan suka kunna kai cikin gidan, inda ba tare da wata wata ba suka aika da mutum hudu lahira, kuma suka ci nasarar damke kartaginsu, Hassan Shehata, rahotanni sun nuna sai bayan da matasan suka gama wasan kura da Shehata sannan ne suka aikashi lahira ba tare da wani bata lokaci ba.

Ministan Lafiya na kasar Masar ya tabbatar da mutuwar Shehata a hannun mutanan da suka kira Jihadi akansa. Matasan wadan da yawansu ya tasamma 3000 sunce daga yanzu sun shata layi ga duk wani dan Shi’ah da ya sake zagin Uwar Muminai ko Sahabban Manzon Allah a bainar jama’a, ballanata kuma su kama mutum yana aikata badala da sunan Mut’ah, sun ce duk wanda suka kama to sai dai fa uwarsa ta haifi wani.

A nasa jawabin wani fitaccen Malamin Sunnah a yankin Sheikh Muhammad Hassan yayi kira ga Shugaban Kasar Muhammad Mursi da kada ya sake ya baiwa ‘yan Shi’ah damar da zasu dinga cin mutuncin Sahabban Manzon Allah da Matansa. Ya kara da cewa idan kuwa gwamnati tayi kunnan uwar Shegu to Matasan Sunnah sun shirya mutuwa domin kare martabar Sahabban Manzon Allah da Iyalan Gidansa.

MADALLAH DA WADANNAN MATASA, ALLAH YA SAKA MUSU DA ALHERI YA TABBATAR DA DUGA DUGANSU AKAN BIN SUNNAH MANZONSA SALALLAHU ALAIHI WASALLAM. LALLAI MUNA FATAN WANNAN ABU YA ZAMA DARASI, KUMA WANNAN SHINE ABINDA DUK MATASA YA KATA SU YI KOYI DA SHI, DUK INDA AKAJI WANI YA ZAGI MATAR MANZON ALLAH KO SAHABBANSA TO YA BAKUNCI LAHIRA NAN TAKE BA TARE DA BATA LOKACI BA. ALLAH YA TAIMAKI MUSULUNCI DA USULMI YA KARYA SHI’AH DA SHI’ANCI, YA TURMUZA HANCIN MASU ZAGIN SAHABBAI DA IYAYAN MUMINAI.

Yasir Ramadan Gwale
24-06-2013

Sunday, June 23, 2013

TY. DANJUMA YA CANCANCI SARAUTAR DA SARKIN ZAZZAU YA BASHI


TY. DANJUMA YA CANCANCI SARAUTAR DA SARKIN ZAZZAU YA BASHI

A karshen makon nan ne, aka yi bikin nadin sarautar da sarkin Zazzau (Sarkin Adon Sarakuna), Maimartaba Shehu Idris ya tabbatarwa da Gen. Yakubu T. Danjuma. Hakika wannan sarauta ta JARMAI ZAZZAU da aka baiwa Danjuma, duk da cewa bani da masaniyar amfaninta a masarautar zazzau, amma ko shakka babu Maimartaba Sarki ya bayar da wannan sarauta ga mutumin da ya dace. Lallai Arewa tana da zakakuran ‘ya ‘ya wadan da suka hidimta mata kuma suka sadaukar da rayuwarsu, dan ganin cigaban yankin Arewa, irin wadannan mutane ba laifi bane idan an saka musu da irin wadannan sarautu.

Malam Yakubu T. Danjuma, daya ne daga cikin zakakuran ‘yan Arewa na tun farko, wadan da duniya ta shaida aikinsu. Hakika mutum irin Danjuma idan ba’a yabeshi ba to shakka babu idan aka zageshi akan Arewa, an zalunce shi. Da yawan mutunan Arewa musamman matasa da suke da karancin sanin me ya faru a baya, kusan tun zamanin su marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, an basu gurbataccen tarihin waye Danjuma, domin nakan ji masu san su soki Danjuma, sukan ce shi din makiyin Musulunci ne da Musulmi. Wannan kusan ita ce maganar da take fitowa daga bakunan masu san sukar Danjuma ko kuma kushe shi.

A matsayinmu na Musulmi Allah ya riga ya fada mana cewa kafurai makiya ne ga Musulmi. Wannan kam abu ne “wadeh” wanda Al-Qur’ani ya tabbatar kuma dukkan Musulmi yayi Imani da haka. Amma kuma, Allah cikin nufinsa da kaddarawarsa ya hada Musulmi da wanda ba musulmi ba zama waje guda, dan haka ya zama dole dukkan bamgarori su san yadda zasu zauna da juna lafiya, “ladarara wala dirara” babu cuta babu cutarwa. Allah masani!

Danjuma kusan dukkan mutanan da ake kira dattijan Arewa, babu wani mutum sama da shi, idan banda sa’o’insa irinsu Malam Adamu Chiroma. Tun zamanin Marigayi Sardauna Danjuma ya nuna kwazo da kishin Arewa, ina zatan wannan shine dalilin da ya sanya Sardauna a wancan lokaci ya ja mutane irinsu Danjuma a jiki, dan ya nunawa al’ummar Arewa musamman Musulmi muhimmancoin tafiya da mutanan da suke ba Musulmi ba, wajen ciyar da yankin Arewa gaba. Idan za’a yi Magana ta gaskiya, kuma za’a yi adalci. Dole ne mutanan Arewa su yabawa Danjuma, domin shine kadai Mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa a lokacin da aka kashe Sardauna, duk masu ihu da karadin Arewa, da cika duniya da surutu, watakila lokacin da Danjuma yayi wannan kasadar wa rayuwarsa dan ankashe Sardauna su suna zanin goyo, ko basu ma zo duniyar ba. Basu san lokacin da Danjuma yayi wannan kasadar ba. Ance Danjuma Igwa ya dauka zai tunkari mutanan kudancin kasarnan akan kashe Sardauna da aka yi. Allah shine masani!

Haka kuma, duk da irin gurbataccen tarihin da ake baiwa ‘yan Arewa akan Danjuma, a cikin manyan sojojin da suka rike manyan mukamai da ‘yan siyasa da wahala ka samu wanda ya taimakawa talakawa da dukiyarsa irin Danjuma (Bance babu ba). Danjuma bai rike mukamin shugaban kasa ko mataimakinsa ba, amma ya rike mukamin munista, kuma daya ne daga cikin mutanan da Allah ya yiwa arziki a yankin Arewa, abinda mutane da yawa basu sani ba, Danjuma kusan gaba daya dukiyarsa Musulmi ‘yan Arewa sune suke alkinta masa. Na tabbata mutane suna sane da irinsu Alhaji Amadu Chanchangi na Kaduna, da irin taimakon da yayiwa al’umma da Musulunci, sanin kowa ne cewar Chanchangi babban na hannun dama ne ga Danjuma, wanda kusan dukiyar da Amadu yake tafiyarwa ta Danjuma ce gaba daya, shin idan da Danjuma makiyin Arewa ne zai yarda ya danka amanar dukiyarsa a hannun irinsu Amadu Chanchangi?

Watakila wasu su ce ai Danjuma ya taimakawa da kungiyar CAN da maqudan kudade. Anan sai nace Danjuma ya taimakawa abinda yayi Imani da shi ne da kuma addinin sa, a kuma wannan gaba ne zamu kalubalanci dukkan manyan da Najeriya tayi musu wando da Riga dalilin Arewa suka kudance suka yi arziki dare daya, su me suka yiwa talakawan Arewa? Kowa yasan da cewa mutanan da suka rike manyan mukamai irinsu IBB da Abacha da AbdusSalam masu arzikin gaske ne, amma tsakaninmu da Allah wace Gidauniya suka kafa domin taimakawa talakawa da dumbin dukiyar da suka samu? Bar ta batun taimako, shin Zakkar da Allah ya umarci dukkan Musulmi su bayar suna bayarwa kuwa? Bari mu buga misalin irin dumbin arzikin da mutanan nan suka mallaka. IBB shine shugaban kasar Najeriya na soja, yayi tasarrufi da riyojin man kasarnan yadda yaga dama, a wannan lokacin ne ya baiwa Danjuma, kyautar rijiyar Manfetur ladan ganin ido. Kaji masu abin!

Wannan rijiyar manfetur da aka baiwa Danjuma kyauta ne, bayan ya kwashe tsawon lokaci yana amfanarta, sannan ya sayarwa da wani kamfanin kasar Koriya da wannan rijiya akan kudi Naira Biliyan Dubu, tashin hankali! Wadannan kudade da Danjuma ya samu, ya kafa Gidauniyar TY Danjuma, inda ya ware mata Naira Biliyan 15 domin kawai a taimakawa talakawa da marasa galihu da masu karamin karfi. Wannan kadan ne daga cikin misalin irin yadda Danjuma yayi tasarrufi da dukiyarsa.

Mukoma kan IBB, tunda shine muntahar, dan Allah mai karatu a tunanika IBB rijiya nawa zai baiwa kansa da iyalansa? Nawa kake zatan ya mallaka? Idan har mutum irin Danjuma an bashi rijiya daya ladan ganin Ido ya sayar da ita Naira Biliyan Dubu? Ba wannan ba ma, a lokacin IBB ne fa gwamnatin Najeriya karkashin jagorancinsa, zata tono danyan manfetur ta sayarwa da Matatun manfetur na IBB da yake dasu a Kwadebuwa da Benin sannan ya tace, ya dawo da tataccen ya sayarwa da gwamnati. Tirkashi, kaji mutum da kasar ubansa!

Kamar yadda bayanai suka nunar cewar Danjuma ya taimakawa da CAN da kudade a cikin waccan Biliyan Dubun dan gudanar da ayyukanta. Dan Allah kungiyar IZALA da IBB yake jingina kansa gareta Biliyan Nawa ya taba bata domin ayyukanta? Ko kuma kungiyar Jama’atu Nasrul Islam JNI nawa ya taba basu? Wace irin gidauniya IBB ya kafa dan taimakon Musulmi da Talakawa da ya fito daga cikinsu? Wannan IBB kenan fa kadai, ina ga irin dukiyar su Abacha da AbdusSalami da Aliyu Gusau da sauran manyan sojoji da suka kwashi dukiyar Najeriya kamar ta ubansu? Amma saboda san KAI da rashin fahimtar yadda gaskiyar lamura suke, sai mu kyale su IBB suna watayawarsu da dukiyarmu da suka sace, muna zagin su Danjuma. Allah ya kyauta!

Yasir Ramadan Gwale
23-06-2013

Saturday, June 22, 2013

MAGANA TA GASKIYA


MAGANA TA GASKIYA

Assalamu Alaikum Warahmatullah, Ya dan uwa, zance na gaskiya duk wani Malami komai tsawon gemunsa, komai girman rawaninsa, idan yace maka ga wata Sallah ko wani salati ko wata Ibada da zaka yi Allah zai baka ladan adadi na wasu Annabawa, wallahi summa tallahi tataccen makaryaci ne, kuma dan damfara ne, yayi amfani da irin tsabar san banzaka da san ka da shiga Al-jannah ba tare da kayi wani aiki mai yawa ba ya sa ya yaudareka. Ya dan uwa ka sani akwai Annabi Nuhu yayi shekaru Dubu babu Hamsin yana kira zuwa kadaita Allah da Bauta, da sauran dukkan Annabawa da suka biyo bayansa haka suka dinga jaddada wannan kiran. Wasu annabawan andokesu kai wasu har zarto aka sanya akansu aka raba su gida biyu, saboda kawai sunce Abi Allah.

Duk irin wannan wahalar da Annabawan Allah suka sha, sai kawai wani mutum yace maka ga wata IBADA da zakayi da bata wuce Awa guda ba, Allah zai baka ladan wadannan Annabawa. Tab! Wallahi wannan wasa da Allah ne, sai ka tambayeshi shin Ina matsayin wadancan Annabawa, tsakanin kai da akace Allah zai baka ladansu da kuma su, waye a gaban wani? Wallahi duk sallarka duk Azuminka da Zakkarka da Aikin Hajjinka baka isa ka kama kafar Sahabban Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam ba, ballantana ANNABAWA. Mutane suna son Aljannah suna son shigarta, amma basa san aikin wahala, Al-Jannah kuwa hanyoyinta cike suke da abubuwan da zuciya bata so, wallahi idan kana san shiga Al-Jannah da gaske sai kabi Allah kamar yadda Manzon Allah ya fada, kabi Al-Qur’ani da Sunnarsa Salallahu Alaihi Wasallam, sannan ne zaka rabauta, duk wani abu da ba wannan ba. Sunansa FANKAM FAYO.

Wasu mutane marasa tsoron Allah, suna fadin cewa akwai wasu sallolin Nafila da mutum zaiyi a daren rabin watan Sha’aban (Nisfu-Sha’aban) WAI Allah zai basu ladan Annabawa tun daga farkon duniya har karshenta! Hakika wannan ganganci ne, kuma galatsi ne ga Addinin ALLAH, duk mai furta irin wadannan muna nan kalamai hakika yana cikin tashin hankali ya sani ko bai sani ba.

Allahumma Ihdinas Siradal Mustaqeem.

Yasir Ramadan Gwale
22-06-2013

BAYYANAR YAJUJU DA MAJUJU (Gog And Magog)


BAYYANAR YAJUJU DA MAJUJU (Gog And Magog)

A karshen duniya wasu al’ummu guda biyu zasu bayyana, zamanin Allah ya dawo da Annabi Isah Dan Maryam Alaihis Salam. Wadannan mutane (yajuju da Majuju) zasu bayyana ne bayan zuwa da tafiyar Dujjal. Allah madaukakin Sarki zai halakar da Yajuju da Majuju a cikin dare daya, bayan Annabi Isah (AS) ya roki ubangiji akansu.

Abu-Huraira Allah ya kara yarda a gareshi, ya ruwaito daga Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, yana cewa “A kowacce ranar Allah wasu al’umma (Yajuju da Majuju) suna nan suna hake wata Katanga, da zasu shigo cikin wannan duniya tamu, sai sun yi haka har sun gaji, sannan zasu fara hango harsken rana, abinda yake nuna hakarsu ta kusa cimma ruwa, sai kawai shugabansu, ya umarce su da su koma su kwanta gobe zasu dawo su cigaba! Cikin hukuncin Ubangiji washe gari suna zuwa, sai su tarar Allah ya shafe wannan Katanga ta kara karfi da kwari, sama da yadda suka sameta a jiya, haka zasu sake cigaba da tone ko kwarzane wannan Katanga, su sake komawa, washe gari su sake ganinta kamar basu taba haketa ba, hakan nan zasu yi ta yi, har sai lokacin da Allah ya hukunta fitowarsu. Idan sunyi aiki har sun bula katangar sun fara hango hasken rana, anan ne shugabansu zai umarce su da su koma su kwanta, gobe idan sun dawo zasu cigaba, amma zai ce INSHA ALLAH wato yayi togaciya kenan! Bisa fadin Insha Allahu da shugabansu ya yi sai Allah ya amsa, washe gari idan sun komo zasu sami wannan Katanga yadda suka barta jiya!

Bayan dawowarsu ne, washe gari, zasu ci gaba da yin aikinsu na kwakwule wannan Katanga. Kuma cikin nufin Allah, zasu shigo cikin wannan duniyar daga katangesu da Allah yayi da al’umma, idan suka fito zasu shanye dukkan wani ruwa da sukayi ido hudu dashi, sannan zasu cinye dukkan wani abinci da suka gani, kai kusan dukkan wani abu da suka gani sai sun cinye shi, kama daga Bishiya tsirrai da dabbobi, sannan zasu shiga kisan mutane babu ji babu gani! Hasbunallahu wani’imal wakeel.

A wannan lokacin Yajuju da Majuju zasu dinga harba kibau sararin samaniya. Suna harba kibiyoyi da masuna, sannan suna fadowa kasa suna masu digar da jini a jikinsu, anan ne Yajuju da Majuju zasu ce, mun gama da al’ummar da take a ban-kasa sannan kuma wadan da suke sama suma mun gama da su! A lokacin da suka yi wannan ikirari ne kuma, Allah zai yi musu ruwan wasu irin tsutsotsi wadan da zasu dinga makalemusu a wuya suna cizonsu, haka nan, wannan tsutsa zata hakalasu gabaki dayansu a cikin dare daya! Allah buwayi gagara Misali, tsarki ya tabbata a gareka Ya Allah! Bayanin wannan Hadisi na Abu-Huraira yazo cikin Tirmuzi karkashi Tafsirin suratul Kahfi (hadisi 5160), 8/597-99. Haka kuma, kitaab al-fitan, (hadisi 4080), 2/1364, da kuma musnad na Imam Ahmad, 2/510, 511.).

Yajuju da Majuju dai, tsatso ne, na ‘dan Annabi Nuhu Alaihis Salam. A zamanin Annabi Ibrahim akwai wani sarki da ake kira Zulkarnaini, shi wannan sarki, Allah ya bashi iko da kuma Mulki tundaga Bangon Gabas har zuwa yamma, kuma mutumin kirki ne da ya shimfida Adalci, shine ya gina wannan Katanga da ta raba wannan duniya tamu da Yajuju da Majuju. Haka kuma, wannan Katanga an gina tane da narkakken karfe da duwatsu da kwalta da ruwan dalma. A zamanin Zulkarnain wadannan al’umma (Yajuju da Majuju) sun addabi mutane, shine al’ummar da Zulkarnaini yake mulka suka rokeshi da ya gina musu katangar da zata rabasu da Yajuju da Majuju.

Yajuju da Majuju sunyi ta kokarin fasa ko bula wannan Katanga su fito amma kuma sun kasa. Sunyi dukkan irin dabarunsu su yi tsalle su fito amma Allah bai basu iko ba, shine tun daga wancan lokaci har kawo yau suna nan suna kwakwule wannan Katanga domin su samu su fito, amma Allah ba zai basu iko ba, sai a karshen duniya.

Haka kuma, idan muka kalli Hadisin da Ibni Mas’ud Allah ya kara yarda a gareshi ya ruwaito daga Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam yana cewa. A daren da Manzon Allah yayi Isra’I ya hadu da Babansa Annabi Ibrahim da Annabi Musa da kuma Annabi Isah, dukkansu sun tattauna akan shin yaushe ne Alkiyama zata tsaya, sun fara tambayar Annabi Ibrahim yace bai sani ba, daga nan Annabi Musa yace shima bai sani ba, daga nan sai Annabi Isah yace babu wanda ya san wannan ranar sai Ubangiji mamallakin ranar sakamako, Tsarki ya kara tabbata a gareshi! Annabi Isa ya cigaba da cewa, abinda Ubangijina ya gayamin shine a karshen duniya, Dajjal zai bayyana, haka kuma, idan ya hadu da ni zai dinga narkewa yana zagwanyewa, Haka nan Allah zai halakar da shi (Dajjal), sannan Musulmi zasu yaki kafurai, har sai takai matsayin da Idan kafiri ya buya a bayan wani dutse ko bishiya, zasu yi Magana su kirawo musulmi suce masa zo ga kafiri ka kashi shi. Allah buwayi gagara misali!

Daga nan kuma, adalci zai yadu a ban kasa tsakanin Musulmi, can kuma sai Allah ya fito da Yajuju da Majuju. Zasu barko cikin wannan duniya ta gabas da yamma kudu da Arewa, suna shanye ruwa, suna cinye dukkan wani abu da suka yi arba das hi. Lahaula Walakuwwata Illabillah! A lokacin ne al’umma zasu je ga Annabi Isah suna mai rokonsa da ya roki Ubangiji Allah ya kade musu wannan Masifa da Bala’I na Yajuju da Majuju. Sai Annabi Isah ya daga hannu ya roki Ubangiji, Allah mai girma da daukaka ya amsa, sannan ya dinga saukar musu da tsutsotsi daga sama, suna halakar da su, bayan sun mutu duniya gabaki daya zata cika da warin gawarwakinsu da jinanansu, daga nan kuma Sai Allah ya saukar da Ruwan Sama wanda zai wanke duniya gabaki daya ya wanke dukkan dattin gawarwakin Yajuju da Majuju. Annabin Allah Isah dan Maryan Alaihis Salam, ya cigaba da cewa, daga zarar Allah ya saukar da wannan ruwa, to babu wani abu da yake gab da zuwa face Alkiyama, misalin haka shine, kamar matar da ta ked a juna biyu kuma ta shiga watan haihuwarta, daga lokacin da watan ya kama a kowanne lokaci zata iya haihuwa, to irin haka ne misalin yadda Alkiyama zata tsaya a wannan lokaci. Ya Allah ka sa mu mutu muna masu Imani kuma mu tashi cikin masu Imani, Ya Allah ka karemu daga fitinar Dujjal. Wannan hadisi yana nan a cikin ( musnad na Imam Ahmad 1/375da  ibn majah, cikin littafin kitaab al-fitan (hadisi 4081), 2/1365, 1366)

Yasir Ramadan Gwale
22-06-2013

TSAKANIN GWAMNA JANG DA KWANKWASO WAYE MAKIYIN AREWA?


TSAKANIN GWAMNA JANG DA KWANKWASO WAYE MAKIYIN AREWA?

Kusan a ‘yan makwannin nan babu wasu abubuwa da suka dauki hankalin Siyasar Najeriya kamar zaben Majalisar Gwamnonin day a gabata. Tun bayan zaben ne, majalisar gwamnonin ake ta cigaba da yamutsa hazo da tayar da kura, a tsakanin gwamnonin Najeriya akan wannan zabe. Kurar dai tafi turnikewa ne a jam’iyyar PDP wanda wannan zaben ake wa kallon zakaran gwajin dafi ne, da yake nuna waye zai iya zama dan takarar shugaban kasa a zaben 2015 da yake tafe a cikin jam’iyyar.

Tun bayan dawowar mulkin demokaradiyya a 1999, ba’a taba samun wani lokaci da aka samu hannun gwamnatin tarayya dumu-dumu a sha’anin majalisar gwamnoni ba, sai karkashin wannan gwamnati ta shugaba Jonathan. Majalisar gwamnonin Najeriya wani jigo ne babba wadda take taka muhimmiyar rawa wajan samar da dantakarar shugaban kasa, duk kuwa da cewa majalisar bata da wani gurbi a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Idan bamu manta ba, a watan mayun da ya gabata ne, wannan majalisa ta gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin shugabanta kuma gwamnan Ribas, Mista Rotimi Amaechi ta gudanar da zaben sabbin shugabannin majalisar, inda gwamna me ci Amaechi ya sake darewa kan wannan kujera, inda ya kayar da gwamnan Jihar Plateau Jonah Jang, wanda ake ganin kamar bisa sahalewar gwamnonin Arewa ya fito wannan takara. Sai dai bayanai na hakika sun nuna cewar gwamnan ya fito ne bisa goyon bayan gwamnonin da suke dasawa da fadar shugaban kasa, abin da yake nuni da cewa fadar shugaban kasa tana da hannu wajen fitowar gwamna Jang neman wannan kujera. Haka kuma, bayan da sakamako ya nunar da cewar Gwamnan Jang ya sha kaye, Shi (Jang) din yaki amincewa da Gwamna Amaechi a matsayin sabon shugaban majalisar, wannan ce ta sanya ficewar wasu daga cikin gwamnonin Arewa daga majalisar gwamnonin Arewa irinsu Gwamna Isa Yuguda na Bauchi da Gabriel Suswam na jihar Bunuwai.

Haka kuma, wannan ce ta sanya Gwamnan da ya sha kaye Jonah Jang ya ja tunga tare da gwamnoni 16 da suke mara masa baya a wannan zabe. Sai dai a lokacin da yake maida martini akan wannan dambarwa ta majalisar gwamnonin Najeriya Gwamnan Jihar Kano Engr. Rabiu Musa Kwankwaso yayi wata ganawa ta musamman da ‘yan jaridu a Abuja a wannan makon me karewa, gwamnan ya soki lamirin Gwamna Isa Yuguda na Bauchi da Suswam na Bunuwai akan ficewarsu daga majalisar gwamnonin Arewa.

Gwamna kwankwaso yayi Karin haske akan yadda wannan zabe ya gudana, da kuma yadda suka ki marawa Gwamna Jang baya, inda ya sha kaye a hannun Gwamnan Ribas Mista Rotimi Amaechi. Sai dai kuma a shafin farko na Jaridar SUN ta juma’a 21 ga wannan watan na Mayu, 2013, an ruwaito kakakin gwamnatin Jihar Plateau Rabaran Yiljip Abraham yana zargin Gwamna Kwankwaso da cewa “makiyin Arewa ne”. Haka kuma, abinda manazarta zasu tambaya daga wannan bayani da ya fito daga fadar gwamnatin Jihar Plateau tsakanin gwamna Jang da Kwankwaso waye hakikanin Makiyin Arewa?

Sanin kowa ne cewar a tarihin Arewa ba’a taba samun wata jihar da ta zama makwarar jinin jama’ar da basu san haba basu san sauka ba, kamar Jihar Plateau musamman lokacin wannan gwamnan Jonah Jang. A kusan shekaru shida da Gwamna Jang ya shafe a matsayin Gwamnan Jihar Plateau anyiwa al’ummar Hausa Fulani Musulmi kisan kiyashi a wannan jiha babu dare babu rana, ankashe al’umma babu sididi babu sadada. A tarihin Najeriya ba’a taba samun wani tambadadden Gwamna wanda ya nunawa al’ummar Musulmi Hausa Fulani kiyayya muraratan irin Jang ba. Labarin kashe al’umma da lalata dukiyarsa shine babban labarin da yake fitowa daga Jihar Plateau a kullum ta Allah.

Ba’a taba samun wani lokaci a tarihin kasarnan ba ko a jihar Plateau da aka mayar da kisan jama’a wani abin Karin kumallo ba sai lokacin Jang. Wannan kisan kiyashi mun san cewar an fara shine tun zamanin Gwamna Joshua Chibi Dariye, kafin daga bisani tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya sa gwamnan ya shiga taitayinsa. A dan haka, wannan bayani da ya fito daga fadar gwamnatin Plateau akan Gwamna kwankwaso babu wani abu da za a iya kiransa face tabarmar kunya ce wadda ake rufe ta da hauka, Gwamna Jang ya kidime yana ta hauma hauma da shirme da shirirta shi yasa yake iya shegensa yadda yaga dama. Sanin kowa ne cewar, irin kisan kiyashin da Jang yayiwa al’ummar Musulmi a tsawon Mulkinsa ba’a taba samun ko kwatankwacinsa ba, a zamanin mulkin gwamna Kwankwaso tundaga 1999 har zuwa yau dinnan a jihar Kano.

Jihar Plateau da ake yiwa kirari da cibayar zaman lafiya, ta zama kamar “Mogadishu” a kasar somaliya. Gwamnan Jang ya maida jihar mallakin kabilar Berom ce kadai da sauran tsirarun kabilun da suke tare da Berom. Bazamu taba mancewa da Watan Nuwamban 2008 ba, lokacin da tashin hankali ya lakume rayukan al’ummar Hausa Fulani Musulmi a wannan jihar. Haka kuma, kowa yasan da cewar, Jihar Kano jiha ce da take a matsayin gida ga kusan dukkanin al’ummar Najeriya Musulmi da Kirista.

Idan da ace Gwamna Jang zai sanya a gudanar masa da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar Najeriya, cewa wane Gwamna ne wanda wanda al’umma suka fi tsana, to lashakka zai samu kashi dari bisa dari sun zabe shi a matsayin wani mugun gwamna marar Imani wanda ya mayar da kisan al’umma a matsayin wani aiki da aka turoshi yayi.

Yasir Ramadan Gwale
22-06-2013

Friday, June 21, 2013

ZUWA GA GWAMNAN SOKOTO ALU MAGATAKARDA WAMMAKO

ZUWA GA GWAMNAN SOKOTO ALU MAGATAKARDA WAMMAKO

Assalamu Alaikum Warahmatullah, ina bude wannan wasika tawa da kalamai na yabo da godiya da kira ga Allah madaukakin sarki, mamallakin ranar sakamako, Ina shaidawa babu abin bautawa bias cancanta sai shi, kuma Annabi Muhammad BawanSa ne, kuma ManzonSa ne. Ya mai girma gwamnan, kamar yadda muka sani ba boyayyan al’amari bane a gareka irin yadda jama’ar sakkwato suke cikin matsananiciyar wahalar riwan sha. Ruwa shine rayuwa, kamar kuma yadda ake masa kirari, abokin aiki ne. Bisa la’akari da irin rahotannin da suke fitowa daga jihar sakkwato yana nuna cewa jama’a na kara tagayyara saboda matsananciyar bukatar ruwan amfanin yau da kullum, sannan kuma ruwan yayi karanci musamman a cikin daukacin babban birnin jihar sakkwato.

Mai girma gwamna, hakkinku ne, a matsayinku na shugabanni ku zama hadiman al’ummominku, wajen bayar da kulawa ta musamman da dukkan irin bukatun al’umma na rayuwa. Yanzu a wannan lokacin da muke ciki al’ummar da suka zabeka suka baka kuri’unsu dan tafiyar musu da jiharsu tare da alkinta musu dukiyarsu, ba su da wata bukata ta gaggawa da ta wuce ruwan-SHA. Kamar yadda na fada, maigirma gwamna ba zai kasa jin koken al’umma ba dare da rana akan wannan matsala ta ruwan sha, lallai, muna kira ga maigirma gwamna ayi dukkan mai yuwuwa wajen wadata al’ummar jihar sokoto da ruwan sha tsabtatacce, domin fitar da jama’a daga cikin mawuyacin hali.

Yara da mata da tsaffi da magidanta sun tagayyara matuka saboda halin da suka shiga na farautar ruwa. Duk wani wajen da ake samun ruwa, cike yake da jama’a makil, mutane tun asubahi suke fita domin neman ruwan da zasu sha su yi ibada. Muna fatan Allah ya sa maigirma gwamna yaji wannan kira kuma, a dauki mataki na gaggawa wajen inganta al’ummar jihar sakkwato da ruwan sha. Allah ya bada iko.

Allah ya taimaki Jihar Sokoto.

Allah ya taimaki Yankinmu Na Arewa Maso Yamma, Da Arewa da Najeriya gaba daya.

Yasir Ramadan Gwale
21-06-2013

LABARIN WATA MATA DA DANTA MAI CIKE DA BAN AL-AJABI

Wannan labari dai gaskiya ne, ya faru kamar shekaru goma da suka gabata. Jaridar Al-ahram ta kasar Sudan ta ruwaito shi. Wata rana wata mace da jaririnta ta je tashar mota zata hau mota dan yin balaguro. Matar rike da jaririnta a hannu ta samu mota saura mutum biyu ta cike, zuwanta ya sanya saura mutum guda ake jira, tana zuwa aka bata waje ta z...auna kafin ta shiga motar ta baiwa wani mutum jaririn nata ya rike idan ta zauna ta nutsu ya miko mata shi; mutumin yana mika mata jaririn sai kawai yaro ya tsandara kuka irin me firgitarwa dinnan, matar tayi ta rarrashi amma yaro yaki yin shiru, sai wani mutum daga bayan motar yace "malama ki fita waje ki rarrashe shi idan yayi shiru sai ki dawo" abu kamar wasa tana fita yaro yayi shiru, ganin haka sai ta koma cikin mota, tana zama yaro ya sake barkewa da kuka, ta sake fitowa yaro ya sake yin shiru. Sai da suka yi haka har sau hudu. Sai jama'a suka ce mata tayi hakuri tunda ga mutum biyu sun zo ta hau wata motar su zasu tafi, matar nan tana rokon su kyaleta zata rarrashi danta a haka, amma mutanan suka ce gaskiya bazasu tafi da ita yaro na kuka haka ba! Matar nan ta hakura ta hau wata motar abin mamaki tana zama da yaronta a hannu sai yaro yayi shiru yana dariyar kamar ba shine yake kuka a daya motar ba, bayan da mota ta cika aka fara tafiya can sun isa wani waje sai suka hangi wannan motar da matar ta shiga yaron ya dinga kuka, Motar tayi hatsari kuma duk mutanan da suke ciki sun mutu babu ko mutum daya da yake numfashi! Allahu akbar, ganin haka matar nan ta rungume yaronta tana kuka. Tana ta'ajibin abinda ya faru.

Yasir Ramadan Gwale
19-06-2013

Wednesday, June 19, 2013

ZAMFARA: Anya Kuwa Barayi Ne Ke Kashe Mutane?


ZAMFARA: Anya Kuwa Barayi Ne Ke Kashe Mutane?

Duk lokacin da aka ce barayi sun shiga jihar zamfara sun kashe mutane da dama, sai abin yayi ta dawurwura a zuciyata shin anya kuwa barayin ne da gaske? Abin mamaki, me barawo zai samu a Zamfara? Kuma a zamfarar ma a cikin kauye! Shin indai barayin gaskiya ne me ya hanasu zuwa Habuja su yi satar indai da gaske barayi ne? Duk barawon da zaije kauye a zamfara da muggan makamai ya kashe mutane, ai kuwa zai iya zuwa Habuja. Abin akwai daure kai matuqa da gaske, ace irin wannan kisa yana faruwa haka a jihar zamfara. Lallai hukumomi su tashi tsaye wajen baiwa rayukan al’umma kariya tare da dukiyoyinsu. Tun da jimawa ake kawo rahotannin wadannan barayi, maimakon abin ya lafa sai karuwa yake, adadin mutanan da ake kashewa yana karuwa cikin sauri. Tsoronmu kada barazanar da muke fuskanta a yankin Arewa maso gabas ce tayi tsallen badake ta diro a jihar zamfara Arewa Maso Yamma.

Wani Karin abin daure kai, shine duk lokacin da aka ce wadannan barayin sun shiga kauyukan to kisan da suke yiwa al’ummar yafi satar da suke yi, wannan yana kara bayyana mana gaskiya masu aikta wannan aiki ba barayi bane, wasu ‘yan ta’addane suke shiga rigar barayi suna kasha jama’a babu gaira babu dalili. Mutane suna gidajensu basu san hawaba basu san sauka ba, a farmusu da kisa babu kakkautawa. Abin na wannan karon yafi duk wanda akayi a baya muni domin kuwa wannan har ya hada da uban kasa, sannan ga mutane sama da arba’in a cewar hukumomi sun rasa rayukansu.

A kwanakin baya akayi irin wannan kisan na gilla a karamar hukumar birnin Gwari dake jihar Kaduna, inda nanma aka shiga kauye aka kasha jama’a da dama da sunan cewa barayi ne, daman kuma karamar hukumar mulki ta birnin Gwari tayi iyaka da jihar Zamfara. Lallai wannan al’amari akwai lauje a cikin nadi. Ya kamata ayi bincike na gaskiya akan su waye masu aikata wannan aika-aika da sunan fashi da makami.

Kuma anan zamu yi kira ga al’umma lallau su tashi tsaye wajen baiwa kansu da iyalansu da dukiyoyinsu kariya. Domin kuwa lokaci ya wuce da zamu dogara da hukuma kawai wajen tsare mana dukiyoyinmu da rayukanmu, su kansu hukumomin a tsorace suke, bukata suke a karesu suma. Lallai jama’a a dage wajen aikin sintiri na cikin unguwanni, sannan akai rahoton duk wanda aka gain ba’a gamsu da motsinsa ba cikin unguwa wajen jami’an tsaro, ta hanyar haka ne zamu taimakawa kanmu da iyalanmu, mu zauna lafiya.

 Allah ya jikan wadan da suka rigamu gidan gaskiya. Su kuma masu wannan mummunan aiki. Allah karka rufa musu asiri, Allah ka wulakantasu ka hana musu jin dadi. Allah ka karemu da kariyarka, ka tsaremana rayukanmu da dukiyoyinmu.

Yasir Ramadan Gwale
19-06-2013