Monday, July 30, 2012

Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #3



Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #3

Ya yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan lokaci mai dumbin falala na azumin watan Ramadan. Muna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya nuna mana kashin farko cikin uku na wannan wata, Allah ya sa ibadun da muka gabatar a cikin wadan nan kwanaki goma da suka gabata karbabbu ne, Muna rokonsa tare da tawassali da sunayensa tsarkaka madaukaka ( Subahanahu wata'ala) ya sa ba kishirwar banza mukayi ba! ya Allah kaine kace mu roke ka zaka amsa mana, ya Allah mamallakin komai, muna rokon kayi mana rahama da iyayenmu da 'yan uwanmu da abokanmu baki daya, Allah ka amintar da mu a garuruwanmu, Allah ka bamu lafiya da zama lafiya a kasarmu baki daya, haka kuma 'yan uwanmu da suke cikin tsanani a kasar Siriya Allah ka kai musu dauki.

Ya 'yan uwa masu giram, kamar yadda muka sani yanzu Azumi kusan ya zama ba bako ba, zamu ce ya zama dan gari. Yanzu masallatai da guraren karatuttuka sun fara ja da baya, a farkon Azumi masha Allah, sai kaga dukkan guraren Ibada cike suke da jama'a amma kuma yanzu abin ya ja baya, da fatan 'yan uwana matasa zasu dage kada su karaya wajen Ibada.

Ya 'yan uwa masu girma, Ramadan wata makaranta ce, wadda ba wai kawai ta tsaya iyakar kwanakin Azumi ba, a'a ana son dukkan darasin da muka koya a Ramadan mu cigaba da dabbaqa shi har bayan azumi, shakka babu yana da kyau mu sani kuma mu sakankance, cewar dukkan wani wa'azi ko Nasiha da muka ji, tabbas ya zama hujja akanmu, don haka dole mu dage mu yaki shedan wajen aikata ayyukan da aka kwadaitar da mu, ya dan uwa, Ba lallai ba ne sai kazama Abdullahi Dan Abbas wajen sallah da karatun al-qur'ani da kiyamullaili ba, a'a ana son lallai mu ringa kwatanta irin darusan da muka koya a Ramadan, misali wani yana nan tun shekarar bara rabonsa da yin sallar Asubahi a cikin Jam'i amma yanzu alhamdulillah Ramadan ta sa yana fitowa sallah  tare da jama'a, to irin haka ake so mu dore ba kawai Idan Ramadan ya wuce ba shi kenan mun daina Sallah a jam'i mun daina ciyarwa mun dai sadaqa mun daina zakka mun daina taimako, lallai ne bayan wucewar Ramadan mu cigaba da dabbaka irin abubuwan da makarantar Ramadan ta koyar da mu, wannan shi ne yake nuna mana cewar lallaia mun amfana da lokacinmu a Ramadan.

Ya 'yana uwa, yana daga cikin abinda malamai suke gaya mana cewa idan kaga mutum ya dore da ibada a bayan watan Ramadan alama ce da ta ke nuna cewar lallai Allah ya karbi addu'o'insa da kuma ibadunsa, haka kuma yana daga cikin abinda yake nuna cewar ayyukan bawa iyakacinsu inda ya yi su, shi ne aga mutum ya koma mummunar rayuwar da yake yi kafin Ramadan kaga wannan ya nuna mana cewa wannan mutumin bai amfana da lokacinsa a cikin Ramadan ba, illa iyaka ya bata lokaci ya walar da kansa wajen yunwa da kishirwa, wannan babban abin tashin hankali ne kwarai da gaske ya 'yan uwa masu girma.

Yau ma anan zan dakata sai Allah ya kaimu wani makon domin dorawa a inda muka tsaya, muna rokon Allah ya shiryemu shiriya ta addinin musulunci, Allah ya sa ibadunmu karbabbu ne, marasa lafiyarmu gida da asibiti Allah ya basu lafiya, mu da muke da lafiya Allah ya karamana, 'yan kasuwarmu Allah ya sanya albarka a cikin kasuwanci, ma'aikata kuma Allah ya sanya albarka a cikin albashi, matan da suke neman mazaje nagari Allah ka basu, mazan da suke neman mataye na kwarai suma Allah ka basu, muna da dumbin matasa masu son aure tsakani da Allah amma babu yadda zasuyi muna fatan Allah ya hore mana gabaki daya.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Monday, July 23, 2012

Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #2


Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #2

Ya ‘yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan makon domin cigaba da bayanin da muka somo a makon da ya gabata akan muhimmancin amfani da lokaci a cikin wannan wata mai dumbin falala na Ramadhan. Ya ‘yan uwa masu girma kamar yadda muka sani, yanzu tuni azumi ya fara samun waje yana baje kolinsa, gari tuni ya gama daukar haramar karbar wannan bako, alhamdulillahi bako ya sauka lafiya, kusan duk inda ka shiga acikin garuruwanmu zaka ga alamun cewar lallai akwai azumi a bakin mutane, domin yawan ciye-ciye da lashe-lashe da akeyi da rana kusan yanzu babu, masallatai sun cika da ambaton Allah, duk inda ka zaga sautin karatun Tafseer ne ke tashi, gidajen Radiyo da Talabijin kusan duk sun maida hankulansu kacokan akan wannan wata, muna fatan Allah ya sa muna daga cikin ‘yan tattun bayi.

Ya ‘yan uwa masu girma, ya zo a cikin ingantaccen Hadisi wanda Bukhari ya fitar da shi a cikin littafinsa, wanda sahabin Manzon Allah sallalahu alaihi wasallam Huzaifa Ibnul Yaman Allah ya yarda da shi ya ruwaito cewa, naji Manzon Allah sallalahu alaihi wasallam yana cewa “Fitinar mutum ga iyalansa, da dukiyarsa, da makwabcinsa yin sallah da Azumi suna kankare wannan fitina”. Ya ‘yan uwa kamar yadda muka sani yana daga cikin fituntunun wannan zamani, Allah ya jarrabi mutum da muguwar mata, ko kuma Allah ya jarrabi mutum a cikin dukiyarsa ko kuma Allah ya jarrabeka da mummunan makwabci. To idan Allah ya sanya ka tsinci kanka a irin wannan hali ka sani Manzon Allah ya riga ya baka mafita.

Lallai wannan lokaci na Azumi lokaci na da ake bukatar mu zage dantse wajen yin Ibada. Ibada ta Azumi da Sallah da kyauta da Sadaqa da sada zumunci, wadan nan sune abubuwan da ya kamata mu baiwa muhimmanci a cikin wannan wata, alhamdulillahi kusan yanzu idan ka je masallatanmu a lokacin sallar tarawihi ko kuma Asham zaka samu masallatai sun cika makil da jama’a, hakika wannan babban abin farinci ke ne kwarai; amma wani kuma abin mamakin da yake cikin wasu daga cikin matasanmu zaka samu suna tozarta sallar farilla, misali zaka samu wani tunda Allah ya wayi gari babu sallah ko daya da ya halarta a cikin Jam’I amma kuma yana gaggawar zuwa jam’in sallah Asham, kaga ko shakka babu wannan ya tozarta sallar farilla, domin ita ce ahakku akan ya yi ta cikin jam’I amma ya ki yin haka, lallai wannan babban kuskure ne ya ‘yan uwa lallai mu dage da yin dukkan salloli cikin jam’i.

Sannan kuma, akwai wani Nau’I na matasanmu wadan da su kuma suna Azumi amma ba sa yin sallar kwata-kwata. Wannan ma wani babban tashin hankali ne, ace mai azumi baya kiyaye sallah, lallai mu sani tozarta Azumi ne, mutum ya ki yin sallah dagangan, wasu sun dauka lokacin Azumi lokaci ne na a shafe tsawon dare anata kallon tashoshin Zee Aflam ko MBC2, MBC MAX, MBC Action, domin a shagaltar da idanu, wai saboda a samu damar yin dogon bacci da rana, wannan babban kuskure ne ya  ‘yan uwa masu girma, lallai yadda muke rayar da rana da Azumi da karatun al-qurani da zikiri, to haka ya kamata mu rayar da dare, domin samun dacewa da rahamar Allah acikin wannan wata

Yan ‘yan uwa masu girma, yana daga cikin kuskuren da muke aikatawa a cikin azumi da kuma bata lokacinmu shi ne, a duk lokacin da aka ce maka yamma tayi jama’a kowa na hanzarin ya koma gida domin buda baki tare da iyali, sai ka samu mutane suna warware ladan azuminsu ta hanyar zage-zage da cin mutuncin juna akan hakkin amfani da hanya, dan hakuri kalilan da mutane zasu yi, amma sai ka samu ana ta tayar da jijiyar wuya da maganganu marasa dadi, lallai wannan babban kuskure ne, kuma hasarar lokaci muke yi mai daraja, domin gab da faduwar rana, ko lokacin faduwar rana wannan shi ne lokacin buda baki, a kuma wannan lokacinne ake son mutum ya yi addu’ar buda baki bayan ya sanya wani abu a cikinsa, amma sai kaga muna hasarar wannan dama. Ya ‘yan uwa lallai mu guji aikata dukkan wasu ayyuka da zasu iya kaiwa zuwa ga warwarar azuminmu.

Ya ‘yan uwa, masu girma lallai ya kamata mu sani cewa lallai azumi garkuwa ne, a cikin wani hadisi da sahabin Manzon Allah Mu’azu bin Jabal ya ruwaito wanda turmizi ya fitar da shi yana cewa, wata rana Manzan Allah ya ce min Ya Mu’az shin bana nuna maka kofofin alkhairi ba, sai n ace e ya manzon Allah, sai ya ce Azumi garkuwa ne. lallai idan muka kalli wannan hadisi zamu gane cewar lokacin da muke dauke da Azumi a bakinmu ba lokaci bane da zamu tsaya muna bata lokaci ko cacar baki akan wani abu kankani ba.

Yauma zan dakata anan sai Allah ya kaimu mako mai zuwa zamu ci gaba da wannan bayani. Allah ya karbi wannan ibada tamu, Allah ya sa ba kishirwar banza muke yi ba. Allah ya sa muna daga cikin wadan da zasu samu rahamarsa subahanahu wata’ala.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@gmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Wednesday, July 18, 2012

Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci A Watan Azumin Ramadhan

Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi

Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah ubangijin halittu tsiranSa da AmincinSa su kara tabbata ga fiyayyan halitta Manzon tsira Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wasallam, da alayansa Alu Akilu, Alu Abbas, Alu Jafar, Alu Aliyu da sahabbansa wadan da sune sukayi mana tsuwurwurin wannan addini har ya kawo garemu, Allah ya yarda da su baki daya, da kuma wadan da suka bi tafarkinSa har ya zuwa ranar sakamako. Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne, dukkan wanda Allah ya shiryar shi ne hakikanin shiryayye, dukkan wanda Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi.

Ya ‘yan uwa kamar yadda muka sani lokaci na kara turawa gaba, muna kara kusa ga wata mai alfarma wato Ramadhan. Kuma ga mai hankali yasan da cewa kwanakinmu muke cinyewa a hankali, lokutanmu ne suke tafiya, hakika dukkan lokacin da ya tafi to ya riga ya shiga kundin tarihi, lallai mun kasance al’umma masu hasarar lokutanmu masu tsadar gaske bamu sani ba ko kuma muna gafale.

Kamar yadda Allah yake fada a cikin sura ta 2 aya ta 164 an sanya dare da rana masu shudewa, wanda yake nuna mana cewa wucewar dare da rana alama ce ta tafiyar lokaci a garemu, kuma muna kara kusa ga ajalinmu ne bamu sani ba, muna ta addu’a “Allahumma Balligna Ramadan” amma kuma muna kara kusanta kanmu ya zuwa ga ajalinmu ne ashe. Lallai lokaci abu ne mai tsadar gaske a cikin rayuwarmu, a saboda muhimmancin lokaci ne Allah ta’ala da kansa ya yi rantsuwa da lokaci a cikin sura ta 103 dan ya nuna mana muhimmancinSa subahanahu wata’ala, tsarki ya tabbata a gareshi.

Ya ‘yan uwana, kamar yadda Allah ya bamu labari acikin al-qurani mai tsarki; wannan wata da yake tun karomu na Ramadhan shi ne watan alqurani kamar yadda Allah ya shaida mana a cikin sura ta 2 aya ta 185, Allah ta’ala da kanSa ya yi kira a garemu cikin wannan aya da cewa duk wanda ya halarci wannan wata ma’ana duk wanda ya riski kansa a wannan lokaci to ya azumceshi. Haka kuma har ila yau Allah ya cigaba da shaidamana acikin wannan sura aya ta 183 cewa shi wannan wata kwanaki ne kididdigaggu, kamar Allah yana cewa ne muyi amfani da lokutanmu ta hanyoyin da suka dace a cikin wannan wata.

Ya ‘yan uwa masu Girma, kamar yadda muka sani, mun bata tare da hasarar lokuta masu yawa muna barci da da shagaltuwa da wasu abubuwa wadan da ban a larura ba a kusan watanni 11 da suka gabata. To lallai yana da kyau a wannan watan muyi dukkan mai yuwuwa wajen ganin mun ribaci wannan lokaci. Wannan wata na Ramadhana kamar yadda malamai suke ta bayani yana daga cikin watanni masu dimbin falala kuma kwanakinsa guda 29 idan ya yi tsawo ya cika kwana 30, darensa da wuninsa duka cike suke da dimbin falala, kamar yadda ya zo a cikin ingatattun hadisai cewa ana bude dukkan kofofin alkhairi a wannan watan haka kuma ana kulle dukkan kofofin sharri a wannan watan. Haka kuma acikin wannan wata ne ake da dare guda daya wanda ya dari watanni dubu alkhairi(lailatul Qadri).

Kamar yadda muka sani wannan watan yana da makwanni 4 da kwanaki 29, acikin kowace rana akwai awanni 24, haka kuma acikin kowace sa’a muna da dakika 60, don haka idan muka hada lissafi muna da awanni 696 a cikin wannan wata, lallai akwai bukatar mu tsaya mu kalli wadan nan awanni mu tsara lokutanmu da kuma kokarin kiyaye ka’idar da muka sanyawa kawunanmu.

Sauda yawa wasu daga cikinmu sukan dauka watan azumi lokaci ne na aci kayan dadi a more kawai. Lallai akwai bukatar muci daga cikin abinda Allah ya hore mana, amma kuma mu zage dantse wajen yin idaba karatun al’qur’ani dare da rana safe da yamma, zikirin safe da na yamma, sallolin farilla cikin jam’I da kuma sallolin Nafila da kiyamullaili. Idan aka ce maka watan Ramadan ya kama a farko-farko idan kaje masallatanmu abin gwanin ban sha’awa domin duk masallacin da kaje zaka ga ya cika da jama’a wani zubin mutane har a waje suke sallah, masallacin da akeyin sahu biyu a sallar asuba sai ka tarar ya cika makil a farkon Ramadan; amma daga zarar ance maka an tsallake goman farko sai ka fara ganin karancin mutane a masallatai, da guraren karatuttuka.

Haka kuma, a cikin sahihin hadisi Manzon Allah  yana cewa ku fanshi kanku daga wuta ko da da barin dabino ne. lallai wannan babbar Magana ce, muyi kokari wajen yawan aikata alkhairi da ciyarwa a wannan watan gwargwadon hali, idan kana da ikon sayan dabino na Nera goma yi gaggawa ka siya domin ka fanshi kanka kamar yadda manzon Allah ya fada salallahu Alaihi Wasallam. Lallai hanyoyin amfani da lokuta a wannan wata suna da yawa, kamar yadda nasan ‘yan uwana da suke gabatar da shirye-shirye a filaye daban daban zasu yi bayani, mai gamsarwa.

Zan dakata a wannan gaba sai mako mai zuwa idan Allah ya kaimu, zamu dora daga inda muka tsaya. Kuma wannan fili namu na MATASA JIYA DA YAU zai ringa kawo mana tsokaci kan azumi a tsawon wannan watan gabaki daya, Allah ya sa mu dace, Allah kuma ya sanya muna daga cikin wadan da zasu sami rahama a wannan wata.

Yasir Ramadan Gwale

Yasirramadangwale@gmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Monday, July 16, 2012

Tsakanin Jama'atu Nasrul Islam Da Sarkin Musulmi Sultan Sa'adu Abubakar Wa Ke Jagorancin Musulmi A Najeriya?

Tsakanin Jama’atu Nasrul Islam Da Sarkin Musulmi Sultan Sa’adu Abubakar Wa Ke Jagorancin Musulmi A Najeriya?
Kusan kamar yadda dukkan Musulmin Najeriya mu ke bibiye da halin da Musulmi suke ciki a garin Jos da sauran sassan jihar plateau mun san da cewa halin da suke ciki mawuyacin hali ne ainun. Shakka babu kamar yadda  alamu suke nunawa, kuma bayanai suke kara bayyana shi ne, Gwamnatin jihar Plateau karkashin jagorancin Jonah David Jang tana yin dukkan kokarin kakkabe al’ummar Musulmi daga wannan jiha, ta hanayar amfani da rundunar tsaron Special Task Force (STF) kamar yadda muka ji a makon da ya gabata cewar wannan runduna karkashin jagorancin sabon shugabanta Maj. Gen. Hanry Ayoola sun baiwa musulmi dake zaune a karamar hukumar Reyom da Barikin Ladi wa’adin sa’o’I 48 da su fice daga gidajensu da dukkan abinda suka mallaka ko kuma su hada da fushin wannan runduna. Wannan abu kamar a mafarki, ace a Najeriya ake irin wannan batu, duk da tsarin mulki ya baiwa duk dan Najeriya izinin zama a duk inda ya ga dama.
Wannan abin da Gwamna Jang ya yi, kusan shine karo na biyu da aka yiwa Musulmi irin wannan cinkashin kaji a yankin Arewa, inda alkaluma suka tabbatar da cewa Musulmi sune sama da kaso 75 na al’ummar wannan yanki. Idan bamu manta ba a shekarar 2008 gwamnan jihar Neja Mu’azu Babangida Aliyu ya kori musulmi daga wani kauye da suke zaune a karamar hukumar Mokwa inda suka kira wannan kauye da suna Darul Islam, dukkan bayanai sun tabbatar da cewar mutanan wannan gari ba su da wata barazana ga tsaro, ko kuma tayar da zaune tsaye, gwamnati ta tura jami’an tsaro inda suka ringa caje mutane gida gida da nufin zakulo ko mutanan wannan sabon gari suna da makamai ko wasu abubuwa da zasu iya janyo salwantar rayuka, bayan wannan bincike ba’a samu komai ba. Amma duk da haka gwamnan Neja ya yi gaban kansa wajen tarwatsa al’ummar wannan gari.
Haka nan tarihi ya maimaita kansa a wannan lokaci a jihar Plateau, inda gwamnan Jang yake kokarin sanya takalmi irin na Babangida Aliyu wajen fatattakar Musulmi. Hakika wannan babban abin takaici ne ace haka na faruwa da Musulmi a yankinsu na asali, kamar babu hukuma ko kuma jagororin Musulmi. Dukkan shugabannin Musulmi suna kallo babu wani da ya firo ya yi Magana da kakkausan lafazai akan wannan shiri na Gwamna Jang, sai gashi abin mamaki kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa ta ACF ta bakin kakakinta Anthony Sani wanda kirista ne, wai su ne zasu je birnin jos dan ganin hanyoyin da za’abi wajen magance wannan matsala da ke faruwa a wannan jiha, anan sai mu tambaya shin tsakanin kungiyar Jama’atu Nasrul Islam da mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa’adu wa ye yake jagorancin Musulmi?
Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasarnan ya amince da kungiyar Christian Association of Nigeria ko CAN a takaice don ta kare muradun kiristoci a wannan kasa; da kuma kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ko JNI suma dan su kare muradun musulmi a wannan kasa. Ko shakka babu nasan babu wanda yake inkarin cewar kungiyar CAN tana yin iyakar kokarinta wajen ganin sun kare muradun dukkan kiristocin Najeriya ta duk hanyar da suke gani zasu iya, sharri da makirci da kutungwila babu wadda basa yi dan cikir burinsu, duk saboda su kyautata tare da dadadawa kiristocin Najeriya.
Mu kallai irin yadda shugaban kiristocin Najeriya Pasto Ayo Oritsejafor inda ya tsaya kai da fata sai ankamo kabiru sokoto wanda ake zargi da shirya kai harin coci a madalla, sunyi dukkan mai yuwuwa sai da hakarsu ta cimma ruwa, wanda yanzu haka Kabiru Sokoto yana hannu, tabbas bamu ga laifin CAN ba, domin babu wanda zaiso al’ummarsa su shiga matsala matuqar yana da yadda zai yi. Daga zarar wani abu ya faru da kirista sai kaji CAN sunyi ruwa sunyi tsaki, amma kuma idan aka kama kirista da laifi sai su yi ta boye wannan laifi da nuna cewa kuskure ne, ko su yi gum da bakinsu kamar yadda suka yi akan kiristocin da aka kama da yunkurin tarwatsa coci da bamabamai.
Haka kuma, duk lokacin da wani abu ya faru zaka samu shugaban CAN shi ne yake wucewa gaba tare da rakiyar mukarrabansa na wannan kungiya. Wani abin birgewa da wannan kungiya duk wani kirista zaka samu yana mubaya’a ga dukkan manufofinta domin sunyi imani cewar za’a kyautata musu da kuam kare muradunsu, haka kuma inda baka taba tsammani ba zaka samu wannan kungiya tana shiga domin kare muradun kiristoci, suna da sojoji da ‘yan sanda da yalo fifa, da kwastan da gandurobobi da dukkan dangin jami’an tsaro ba dan komai ba sai domin su kare muradun al’ummar kirista. Haka kuma, dukkan wani kirista yana da alaka da shugabannin wannan kungiya kai tsaye, duk wani kirista da yake son shigar da koke zai shigar babu hijabi tsakaninsa da shugabannin wannan kungiya.
Idan muka dawo ta bangaren kungiyar Jama’atu Nasrul Islam da Sarkin Musulmi sai mu kasa gane wanenen ba wanene ba. Don nikam har yanzu na kasa bambance menene aikin Sarkin Musulmi kuma menene aikin wannan kungiya ta JNI. Sarkin Musulmi yana can a fadarsa a sokoto, wanda kamar yadda muka sani tun bayan jahadin shehu Usmanu Dan Fodiya shi ne, Sarkin Musulmi kusan shi ne shugaban sarakunan Arewa, domin dukkan sarakuna suna karbar umarni daga gareshi. Wannan a sarautance kenan. Amma yanzu mun kasa gane shin menene ainihin aikin Sarkin Musulmi shin kare muradun Musulmi kamar yadda shugabannin CAN suke yi? Ko kuwa aikinsa shi ne yana baiwa sarakuna umarnin sanar da ganin jinjirin watan Ramadan ko shawwal? A daya gefen kuma ga kungiyar JNI wadda ke da shalkwata a Kaduna, shin aikinsu kamar na kungiyar kiristoci ne su kare muradun Muslmi a Najeriya ko kuwa ya ya abin yake?
Idan har ya tabbata cewar da Sarkin Musulmi da Kungiyar JNI aikinsu shine kare muradun Musulmi a Najeriya, sai muce ko kusa ba sa yin aikinsu. Domin a ina JNI da Sarkin Musulmi suke akewa Musulmi irin abinda ake yi musu a Jos da sauran sassan jihar Plateau da Zankowa da Zangon Kataf a jihar Kaduna da Tafawa Balewa a jihar Bauchi? Shin sun san abinda yake faruwa da Musulmi a sauran sassan Najeriya? Shin suna shiga lungu da sako domin ganin halin da Musulmi suke ciki a Najeriya da tunanin samar musu mafita? Lallai muna bukatar sanin ainihin aikin Sarkin Musulmi da kungiyar JNI.
Sannan shin sauran Musulmin da suke Kudancin Najeriya suna karkashin jagorancin wannan kungiya ta JNI da Sarkin Musulmi? Ko kuwa muslmin kudu daban na Arewa daban? Shakka babu, musamman mutanan Yamma yarabawa basa kallon JNI da sarkin Musulmi a matsayin jagororinsu, domin da sun yarda cewar suna karkashin jagorancin JNI da Sarkin Musuli da bazamu taba samun matsala da mutanan yamma ba a siyasance ko a addinance, amma a bayyane yake cewar Musulmin yamma daban na Arewa daban. Mun san da cewar akwai kungiyar Yarabawa Musulmi ta NASFAT wadda take aiki ka’in da na’in domin ganin ta kare muradun Musulmi yarabawa, suna da masallatai da makarantu da suke kula da su a kusan dukkan jihohin kudu maso yamma da Abuja, katafaren masallacin juma’a na Abuja na Lababidi da makarantar Lababidi duk yana karkashin wannan kungiya, kuma tabbas a kafatanin Najeriya babu wata kungiyar Musulmi da takai NASFAT kudi da tsari da kokarin ingantawa Yarabawa Musulmi.
Idan muka gangaro Arewa, shin Musulmi nawa ne a Arewa wadan da suka san da JNI da ayyukanta? Na tabbata da yawa daga cikin mutananmu na Arewa musamman wadan da suke zaune a can cikin kurya basu ma san da wannan kungiya ba, daman karkayi maganar birane domin mafiya yawa daga cikin matasa masu so da kishin addini da suke a makarantun islamiyyu a cikin biranen Arewa basu san da wannan kungiya ba. Ada can mun san ana debo matasa daga shalkwatar kananan hukumomi ko gidan hakimai duk juma’a ana rabasu zuwa masallatai da fararen kaya da shudiyar hula domin aikin bayar da agaji a lokacin sallar juma’a, amma yanzu ban san ba ko har yanzu ana yin haka.
Lallai idan har Jonah Jang ya cika wannan mummunan Nufi nasa akan al’ummar musulmi a jihar Plateau, Allah ya kiyaye, to tabbasa mun san babu wasu jagorori na Musulmi a Najeriya. Illa masu rike da sarautar gargajiya irin ta Oba na Ife dake Legas, JNI kuma itama zamu kalleta a matsayin kungiya ce kamar sauran kungiyoyi da suke neman kudi a Najeriya amma ba da sunan kungiyar kare muradun musulmi ba kamar yadda tsarin mulki ya amince. Allah ka zama gatan musulmi a wannan kasa ka shige mana gaba.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Saturday, July 14, 2012

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Kiristocin Najeriya Pasto Ayo Oritsejafor

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya Pasto Ayo Oritsejafor
Kamar yadda mai girma Pasto ya gabatar da takarda a gaban kwamitin kula da lafiya da ‘yancin dan Adam da ke kula da kasashen Afurka na majalisar dokokin kasar Amerika, Ya Pasto, ka gabatar da takarda mai taken Nigeria: west Africa’s Trouble Titan ranar 10 ga watan Yuli na wannan shekarar ta 2012. Kamar yadda ka yi bayani a gaban wannan kwamiti, ka yi bayani ne da sunan kiristocin Najeriya wadan da ka ke shugabanta, shakka babu daman babu wanda ya aikeka kayi bayani da yawun ‘yan Najeriya, don haka bamu yi mamakin irin salon da kabi ba wajen gabatar da wannan takarda ba, kuma daman babu wani musulmi da zai yi tsammanin zaka yi Magana da yawun musulmin Najeriya.
Na tabbata da Musulmi ne zai gabatar da wannan jawabi da kayi a gaban wannan kwamiti, to tabbas da zai yi bayanin asalin rikicin addini da samuwar Boko Haram a Najeriya, tundaga shekarar 1983 da aka fara samun rikicin addini a kudancin jihar Kaduna da rikicen rikicen zangon kataf da Tafawa Balewa a Jihar Bauchi da sauran fadace-fadace da suka faru kusan a mafiya yawa daga cikin jihohin Arewa kama daga Kaduna, Taraba, Adamawa, Bauchi, Gombe da kuma wanda yake faruwa yanzu haka kuma yaki ci yaki cinyewa na Jihar Plateau. Duk wannan al’amari da ya faru lokuta masu tsawo tarihi ya rike, kuma asalin rikicin addini a Najeriya babu inda musulmi suka taba takalar kirista da neman fitina.
Tunda muke a Najeriya babu inda aka taba rawaito cewar ga wani Musulmi ya zagi Annabi Isa ko Jesus ko kuma, ace ga Musulmi ya wulakanta littafin Linjila ko Baibul. Amma kiristocin da aka rawaito sun zagi manzon Allah ko sun wulakanta al-qurani a Najeriya bazasu lissafu ba.Ya mai girma pasto, ko kana da masaniyar daruruwan Musulmi da ‘yan sanda Najeriya wanda galibinsu kiristoci ne suka yiwa Musulmi kisan gilla a ciki da wajen Maiduguri da sunan farautar ‘yan Boko Haram a tsakanin watannin Yuni da Yuli na shekarar 2009, idan Pasto bai sani ba, kiristocin da yake jagoranata suka aikata wannan mummunan aikin ta’addanci, sannan kuma suka kashe shugaban Kungiyar ta Boko Haram wanda a tsarin Mulkin Najeriya aka kira da Extra Judicial Killing wanda wannan ta sanya mininstan Shari’a na wannan lokaci kuma Antoni Janar na shari’a na Najeriya Mista Micheal Kaase Aondoakaa ya tafi har kotun duniya ya bayar da hakuri akan cewa kisan da akayiwa shugaban kungiyar da kuke neman a sanyata cikin sahun kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya a matsayin cewa ankasheshi ba ta hanyar shar’ah ba, kuma yace wannan babban laifi ne da Najeriya take neman gafar kotun Duniya akansa.
Ya maigirma Pasto, ko kasan cewa jaridun Najeriya sun rawaito cewa kiristoci sun kashe sama da Musulmi 630 a kauyen Yalwa a karamar Hukumar Shandam a jihar Plateau a shekarar 2004, kuma suka yiwa dubban matan Musulmi fyade kafin su kashe su, baya ga kuma daruruwan yaran Musulmi da aka sace bayan ankashe iyayansu, aka maida su bayi a kasarsu ta haihuwa, wasu kuma aka yi musu zane a fusakarsu domin batar musu da kamanni, duk wannan ya faru a Najeriya kuma kiristocin da Oritsejafor ka ke jagoranta su suka aikata wannan ta’addanci. Bayan haka kuma masallatan Musulmi da kiristoci suka rusa su har kasa a jihar Plateau da Kaduna bazasu kirgu ba.
Sannan a shekarar da ta gabata kiristoci suka farwa Musulmi da harbi da sara da suka suna kisa babu ji babu gani a Jos yayin da Musulmi suka fito sallar idi, duk wannan kiristoci ne wadan da Oritsefor ka ke jagoranta suka aikata, wa kuka tuhuma da laifin aikata wannan harin na Ta’addanci?  Amma da ka gabatar da wannan takarda sai kayi Magana da sunan Kiristoci kawai, wannan bai bamu mamaki ba, kuma ba matsala bace. Kamar yadda ka ke fada a cikin takardar da ka gabatar kana cewa “ kiristoci suna bukatar ‘yanci a Najeriya, suna bukatar ‘yancin yin addini” to nima ina fada maka da babbar murya cewar Musulmi suna da bukatar ‘yanci kuma, suna bukatar ‘yancin yin addini kamar yadda dokar kasa ta baiwa kowa damar yin addinin da ya zaba.
Nayi mamakin irin yadda pasto ka ke cewar kiristoci suna bukatar ‘yancin yin addini a Najeriya. Shin akwai wanda ya hana kirista yin addininsa? shin shugaban kasar Najeriya ba kirista bane? Shin shugaban Majalisar Dattawa ba kirista bane? Shin wane irin ‘yancin addini ka ke kira ya kai wannan Pasto? A baiwa kiristoci dama su ringa kashe musulmi babu ji babu gani, su ringa fyade wa matan Musulmi ko kuwa su ringa sace ‘ya ‘yan Musulmi suna yi musu zane a fuska suna mayar da su kiristoci!
Idan mai girma Pasto ya koma baya ya kalli tarihi da kyau, zai ga cewar Turawan Mulkin Mallaka da suka shigo kasashen musulmi, shin ba yada addinin kirista suka zo yi ba? kuma suka kwashi bakaken fata da nufin kaisu kasashen turai domin suyi aikin Bauta. Ko Pasto ya manta da mutanan kasar Aborigines (Australia) kusan mutum Miliyan 20 da turawan Mulkin Mallaka suka mayar kiristoci, ko Pasto ya manta da Kusan mutum miliyan 150 daga cikin Indiyawan daji da aka mayar kiristoci ta karfi da yaji a kudanci da Arewacin Amerika(North and South America), duka wadan nan fa iya yan gidanka da ka ke neman tanyonsu da agajinsu suka aikata wannan da sunan addininka na Kirista.
Idan pasto ya sake komawa ba a tarihi, kusan Mutum miliyan 180 aka dauka daga cikin Musulmi da maguzawa a Arewacin Afurka da yammaci da gabashi da sunan aikin bauta kuma aka tilastamusu komawa addinin kirista ta karfi da yaji wanda bayanai suka tabbatar da cewar kusan kashi 80 yanka su akayi aka zuba a cikin tekun Atalantika, wannan ta sanya har sai da ruwan teku ya sauya launi zuwa launin jini daga nan aka samu Red Sea. Kashi 12 a cikin waccan lambar aka dauka zuwa turai domin aikin bauta bayan antilasta musu komawa kiristanci ta karfi da yaji.
Yakin duniya na farko da akayi a shakarar 1930 idan na tuna dai dai da kuma yakin duniya na biyu da akayi a shekarar 1945 duk su waye suka jagorance shi? Shin ba kiristocin da Oritsejafor yake neman agajinsu bane, kisan Yahudawa sama da miliyan shida (6m) da Hitler ya yi shin ba da sunan kiristanci ya aikata abinda ya aikata ba? Ya maigirma Pasto, kasar da ka ke ganin kamar itace ubangijinku, idan tace abu ya kasance zai kasance wato Amerika, ba it ace ta Harba Makaman Nukiliya masu guba ba ya yankin Hiroshima da Negasazki a kasar Japan? duk wannan ba aikin ta’addanci bane da kiristoci ‘yan uwanka suke aikatawa mutanan da bau san hawa ba basu san sauka ba? Kamar yadda ya zo a cikin littafin Mattew a sabon alkawari, idan aka mari kirista a kuncin dama to ya mika na hagun a sake mari, shin kiristoci kun gasgata wannan sura da ta yi wannan bayanin kuwa?
Ita dai wannan kasar Amerika da ka ke kiran da ta kawo muku agaji a Najeriya, shin ba sune suka aikata kisan kishayi a kasar Vietnam ba, suka yi amfani da makamai masu guba akan talakawa bayin Allah, wannan ya sanya har yanzu a irin wadan nan kasashe ake haifar yara masu larura tunta gubar da kakaninnsu suka shaka, take binsu har yanzu? Missoloni ba kirista bane musulmi nawa ya kashe a kasar Libiya da basu jiba ba su gani ba?
Ya kai wannan Pasto, shin su waye suke aikata kisan kiyashi ga Musulmin gabas ta tsakiya da Afghanistan? duk lokacin da sojan Amerika ya aikata kisan gilla wannan sai kuce kuskure ne, amma kuma duk lokacin da aka sami kuskure wani Musulmi ya maida martini wannan shi ne dan ta’adda a wajenku shin wannan shi ne abinda iyayanku suka karantar da ku ken an, ko kuwa kuna son ku nuna mana cewa wannan it ace koyarwar addinin kirista?.
Idan muka dawo gida Najeriya, shin Musulmi nawa ne suka gamu da ajalinsu akan hanyar zuwa Jos a hannun kiristoci ‘yan kabilar Berom a jihar Plateau? Ko duk wannan Pasto bai san da shi ba, haka kuma, Musulmi nawa ne suka rasu a hannun tsagerun kiristoci a hanyar Kaduna zuwa Abuja a dai-dai kauyen Gonin Gora? Ko wannan shima Pasto bashi da Labari, duk fa wadan nan kiristoci ne suke aikatawa.
Kuma ita wannan kungiya ta Boko Haram da Pasto ya nace sai ansanyata a sahun kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya, shin kiristoci kadai suke kaiwa hari? Bayanai sun tabbatar da cewar duk wanda aka kama da sunan Boko Haram idan banda Kabiru Sokoto duk kiristoci ne, da Lucy Dangana da aka kama da safarar Makamai a kan iyakar Adamawa da Kamaru da kiristocin da aka kama bila adadun da yunkurin tarwatsa coci-coci da nufin gogawa musulmi kashin kaji, a ina Pasto yake duk wadan nan abubuwa suke faruwa? Me kuma ya yi akan wadannan al’amura da suka faru?
Mutum nawa sojojin JTF wanda galibinsu kiristoci ne suka kashe da sunan farautar Boko Haram, a Yobe da Maiduguri da Kano, su shiga gidan mutane suyiwa matan musulmi Fyade a gaban ‘ya ‘yansu a gaban mazajensu, kuma sannan su kashe mazan bayan sun kamala aikata badala da iyalansu, duk fa wannan ba wani boyayyan al’amari bane. Kuma ita wannan kungiya ta BH mu muslmi muna zargin tana da alaka da ku kiristocin Najeriya, domin a baya rahotannin sun nuna cewa magabacinka Jerry Gana ya taba yin belin tsohon shugaban BH da aka taba kamawa, shin babu alaka tsakaninku da wannan kungiya? Idan babu rami me ya kawo batun rami, lallai biri ya yi kama da mutum!
Ya kai wannan Pasto, muna tabbatar maka cewa mu Musulmi wallahi ba matsorata bane, kuma bamu taba yin nadamar kasancewarmu Musulmi ba, duk da wuya da tsanani da tashin hankalin da muke gani, wannan babu abinda yake kara mana illa kaimi da kara samun nutsuwa akan wannan addini namu, mun shaida cewa Allah mahaliccinmu yana nan kuma yana kallon duk abinda ke faruwa, Mun shaida cewa Manzon Allah annabin Allah ne, kuma mun shaida cewa Lahira gaskiya ce, aljanna gaskiya ce, wutar jahannama gaskiya ce, Ya mai girma Pasto muna tabbatar maka da babban baki da wasali cewa mu musulmi bazamu taba zama karakshin inuwar kiristanci ba a Najeriya, zamu cigaba da kasancewa mutane masu ‘yancin yin addininsu a duk inda muka tsinci kanmu.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Gwamnan Jihar Plateau Jonah Jang Ya Aikata Laifukan Yaki Da Ya Cancanci Hukuncin Kisa

Gwamnan Jihar Plateau Jonah Jang Ya Aikata Laifukan Yaki Da Ya Cancanci Hukuncin Kisa
Rahotannin baya bayan nan da suke fitowa daga jihar Pilato suna nuna irin yadda al’amuran tsaro ke kara dagulewa. Rahotannin sun bayyana cewar sojojin JTF da suke aikin samar da tsaro a jihar Pilato kusan yanzu sune babbar matsalar wannan jihar domin sun hada kai da kabilar Berom, irin yadda bayanai suka nuna cewa sojojin sun shiga garuruwan Fulani dake karamar hukumar Barikin Ladi da Riyom suna cinnawa ardon Fulani wuta babu gaira babu dalili, saboda kawai su dadadawa ‘yan kabilar Berom da gwamna jang. A lokacin da yake zantawa da  sashen Hausa na Gidan Radiyon BBC sakataren Miyatti Allah na Barikin Ladi Mallam Ado Muhamma ya kara da cewa “yanzu haka da nake Magana da kai sojoji suna kunnawa gidajen mutane wuta a song II da wuro Bello da Gure Dangere da Dyola da Rakweng da Sharu da kuzeng da Luggel da Rachi Matse” ance sun kona sama da gidaje 160, abin mamaki a lokacin da yake maida martini kakakin rundunar JTF ta jihar pilato sai yake shaidawa BBC Hausa cewar ba sojoji bane suke aikin sanyawa gidajen mutane wuta. Abin tambaya anan shi ne a ina sojojin JTF suke har wasu suka zo suke kona gidajen mutane babu ji babu gani?
Kamar yadda rahotanni suka nunar cewar an kashe wani jami’in ‘yan sandan kwantar da tarzoma kuma akayi awon gaba da bindigarsa. Wanda rahotanni sun tabbatar da cewar shi wannan jami’in tsaro da aka kashe, dauko gawarsa akayi zuwa unguwannin Fulani domin a gogamusu kashin kaji. Wannan ta sanya sojoji karkashin jagorancin Sabon kwamandan rundunar JTF Major Henry Ayoola suka yiwa garuruwan da ke Bangwai a karamar hukumar barikin Ladi inda babu wani bincike aka afkamusu tasa da ta kasa ana harbi da manyan makamai da kuma rowan bomabomai ta sama. Abin tambaya a nan me ya sa yanzu abin ya sauya salo Berom ne kawai ke kashe Hausa-Fulani? Shin Berom ne kawai kabilar da ta ke zaune a Jihar Pilato? Shin me ya sa wannan fada ya takaita ga yankunan da Berom suke da rinjaye? Me ya sa JTF suke hana Fulani komawa gidajensu da aka kona?
Sannan kuma, duk wannan abinda yake faruwa a Jihar Pilato na kashe talakawa bayin Allah, bai ja hankalin gwamnati ba sai da aka bayar da rahotannin mutuwar Sanata da shugaban masu rinjaye na jihar pilato dukkansu ‘yan kabilar Berom, abin tambaya akwai wani rai da yafi wani rai ne? duk wadan da ake kashewa basu damu gwamnati ba sai yanzu aka taba mutane ko? Irin yadda Berom ke kokarin shafe Hausa-Fulani daga yankunan Sabon Gidan danyaya da Dorawar Babuje da Barikin Ladi duk bai ja hankalin hukumomi ba, wannan fa shi ne irin tsabar rashin adalcin da hukumominmu suke yi a jihar pilato ta hanyar fifita kabilar Berom sama da kowacce kabila dake wannan jihar. Kamar yadda General Jeremieh Useni ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewar Gwamna Jang shi ne kanwa uwar gamin a duk wadan nan abubuwan da ke faruwa, kuma bad a gaske yake son kawo karshen wadan nan tashe-tashen hankula ba.
Tarihi ya nuna cewa fiye da shekaru 400 Hausawa da Fulani makiyaya suke zaune da dabbobinsu lafiya lau da sauran kabilun da ke zaune a wannan jiha ta pilato suna kiwo tare da samar da arziki ga wannan yanki, domin babu wanda zai iya kididdige shanun Fulani da madarar su da Berom suka ci ko suka sha a iya tsawon wadan nan shekaru, sai gashi yanzu Jang yana son ya sauya akalar tarihi; haka kuma, Jonah Jang da kansa yake fada cewar asalin rayuwarsa ya taso a hannun Fulani ne, sune suka sanya shi makarantar firamare kamar yadda shima mai martaba Gbong Gwom Jos Da Jocub Gyang Buba ya taba fadar cewar Fulani sunyi masa komai a rayuwarsa don haka ne ma yake amfani da sunan Fulani a cikin sunansa wato “buba”.
Wannan rikici da tashin hankali da ake fama da shi a jihar pilato kusan ya samo asali ne tun shekarar 2001 da kuma 2004, lokacin da tsohon gwamna Joshua Chibi Dariye ya so ya shafe al’ummar musulmi daga karamar hukumar  Yalwan Shandam da Langtang da Wase da sauransu, a wannan lokaci abin ya yi kazantar da har sai da gwamnatin tarayya karkashin Obasanjo ta sanya dokar ta baci a jihar, inda gwamnan ya kau daga karagar mulki har na tsawon wata shida kafin daga bisani ya koma karagar mulki kamar yadda doka ta tanada. Tun bayan wannan lokaci ne ake ta samun takun saka tsakanin Hausa-Fulani da kabilar Berom.
Lokacin da wannan gwamnan mai ci a yanzu Jonah Jang ya zama gwamna bayan karewar wa’adin Dariye, al’amuran tsaro sun dan kyautata a wannan jihar wadan da suka gudu sun dawo, harkar kasuwanci ta fara komawa dai-dai, kafin daga bisani su kacame, bayan da Jang ya gama zama daram a kujerar gwamna kuma ya gama fahimtar al’amura, sai suka shirya manakisar zaben karamar hukumar Jos ta Arewa inda nan ne fadar gwamnatin jihar Pilato, kuma Hausa-Fulani suke da rinjaye a wannan karamar hukuma, duk kuwa da hukumomin tsaro a wannan lokacin sun gargadi gwamnati kan gudanar da wannan zabe, makircin da akayi a wannan zabe a shekarar 2008 shi ne sai aka sanya wannan zabe ranar alhamis sabanin ranar asabar da galibi ake sanya ranakun zabe a Najeriya, wato bayan da akayi wannan zabe ranar alhamis washe gari juma’a musulmi zasu fita kwai da kwarkwata domin gudanar da ibadar sallar juma’a, a gefe guda kuma arna sun shirya tsaf da makamansu.
Bayan da aka bayar da sanarwar cewar dan kabilar Berom ne ya yi nasarar wannan zabe. Musulmi suka nuna rashin amincewarsu, inda daga nanne abubuwa suka yi kazantar da basu taba yi ba a tarihin wannan jihar ankashe dubban musulmin da basu ji ba basu gani ba, aka yanka wasu aka zuba a cikin rijiyoyi da shadda wasu kuma aka ringa banka musu wuta da ransu, duk wannan ya faru ne a idon jami’an tsaro a unguwannin Dogo na Hauwa da Unguwar Rogo da Bauci road da Rokkos da sauransu, kusan tun daga wannan lokaci akayi bankwana da zaman salama a musamman Jos ta Arewa, inda kusan kullum sai kaji ankashe mutum ko dai ta kisan kan mai uwa da wabi, ko ta kisan mummuke da ‘yan kabilar Berom ke yiwa musulmi nan da can, duk wannan gwamnatin jonah jang tana da masaniyar hakan. Wannan rayuka kenan, bayan dimbin dukiyar da Allah ne kawai ya san iyakarta wadda ta salwanta a sanadiyar wadan nan fadace-fadace.
Anci gaba da tashin hankali a wannan jiha ta Pilato tsakanin Musulmi Hausa-Fulani da kabilar Berom har kawo wannan lokaci. A shekarar da ta gabata lokacin da Musulmi suka je sallar idi a babban masallacin idi na garin Jos aka afka musu da sara da harbi da bindigogi babu kakkautawa, inda jinin al’ummar musulmi ya ringa kwarara a kasa kamar ruwa, har kawo wannan lokaci babu wani abu da gwamnatin Jonah jang tayi na kokarin binkito tare da hukunta wadan da suka kaiwa musulmi wannan mummunan harin ta’addanci, wannan shi ne cikakken rashin adalci, wanda kuma shine silar dukkan abubuwan da suke faruwa a wannan jihar, domin babu wani mahaluki da zai zauna ana kashe masa mutane a gaban idon hukuma kuma babu wani mataki da ake dauka, sannan ya zauna ya zubawa sarautar Allah ido, ya zama tilar kowa ya nemi hanyar da zai baiwa kansa kariya tunda gwamnati ta gaza.
Haka kuma, Hausa-Fulani da suke sana’ar kabu-kabu da Babura suma ankashe daruruwa daga cikinsu, domin Berom zai hau babur ya sanya a kaishi unguwannin da Berom suke, su kashe me baburdin kuma su gudu da babur din, wannan haka aka ringa yiwa ‘yan acaba irin wannan dauki dai-dai. Duk wadan nan abubuwa da suke faruwa ba wai a boye ake yinsu ba, ana yinsu ne da sanin dukkan bangarorin jami’an tsaro na wannan jihar.
Bayan haka, a kwanakin baya wasu mutane da rahotannin suka tabbatar da cewa kiristoci ne suka kai harin kunar bakin wake a cocin church dake a jihar ta pilato. Inda nanma akayi hasarar rayuka, wannan ta sanya ‘yan kabilar Berom suka dauki doka a hannu inda suka ringa kisan Hausa-Fulani Musulmi da basu san hawa ba basu san sauka ba. Bayan kuma shi wanda ya kai wannan hari ance sananne ne yana zuwa wannan coci dan yin sabis. Gwamnatin da jami’an tsaro duk suna ji suna kallo anata kashe musulmi a wannan jihar, saboda cimma boyayyar manufarsu tabice Hausa-Fulani Musulmi daga wannan jihar ta pilato.
Wani abin da zai sake tabbatar da wannan mugun nufi na kabilar Berom shi ne, a kwanakin baya rundunar ‘yan sanda ta kasa suka kama wani jami’in kwastam dan kabilar Berom da safarar makamai zuwa ga kabilarsa ta Berom don su cigaba da aikin da gwamnatin Jang ta sanya su na kisan musulmi babu kakkautawa a wannan jihar, sai gashi abin kunya kakakin gwamnatin pilato ya fito kafar watsa labarai yana kare wannan mugu azzalumin kwastam da aka kama.
Idan har duniya da gaskiya, kuma adalci ake son tsaidawa a ban kasa to ya kamata kotun duniya ta yi sammancin Gwamnan Jihar Pilato David Jonah Jang saboda ya aikata laifukan yaki. Kamar yadda tsohon mai shigar da kara na kotun duniya Lius Morino Ocampo ya bayar da sanarwar sammacin kamo shugaban kasar Sudan Umar Hasan Al-Bashir a saboda ana zarginsa da aikata laifukan yaki a yankin Darfur ga mayakan larabawan Janjaweed, to lallai Jonah jang ya yi abinda ya ya dara na el-bashir domin kuwa a karkashin umarninsa aka yiwa garuruwan Fulani rowan bama bamai.
Kamar yadda aka gurfanar da Thomas Lubanga da Tsohon Shugaban Kasar Liberia Charles Taylor shakka babu ya cancanci a gurfanar da Jang kuma a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Idan har kotun Duniya tana kallo za’a yankewa Marigayi Saddam Hussein tshon Shugaban Iraqi hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda zarginsa da akayi da kisan Kurdawa 34, to kuwa babu abinda zai hana zartas da irin wannan hukunci akan Jonah Jang, domin ko Ojukwu da ya jagoranci yakin Biafara bai aikata ta’addancin da Jang ya aikata ba.
Haka kuma, suma kungiyoyin kare hakkin Bil-adama idan da gaske suke aiknsu to lallai ya kamata su shiga jihar Pilato su ceto dubban al’ummar da busu san hawaba basu san sauka ba, ake ta aikata musu kisan kai babu kakkautawa, kamar yadda aka aikata kisan kiyashi a serebranica ga musulmin Bosniya to lallai irinsa ake aikatawa ga Musulmi a jihar pilatu.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Sunday, July 1, 2012

Kwallon Kafa: Siasia Yana Karbar Albashin Mutum 277



Kwallon Kafa: Siasia Yana Karbar Albashin Mutum 277
Najeriya a harkar kwallon kafa a shekarun baya ba kanwar lasa ba ce. Don idan muka tuna lokacin da akayi gasar cin kofin duniya a shekarar 1994 a kasar Amurka, Najeriya ta taka rawar gani sosai domin ta samu tsallakewa daga rukuni har takai matsayin kwata final, kafin a fitar da ita daga wannan gasa, irin rawar da Najeriya ta taka a wannan gasa ta 1994, ya kara mata kima da daraja a idon duniya sosai da sosai, wannan ta sanya Najeriya baza ta manta da manyan 'yan kwallon da suka yi kwallo ta kishi ba irinsu Tijjani Babangida da Garba Lawal da Emmanuel Amonike da Ikedia da Austin Eguavoen da Kanu Nwankwo da Sunday Olushe da marigayi Rasheedi Yakini da kuma tsohon mai tsaron gida wato Peter Rufai da sauransu da dama.
Sunan Najeriya bai kara daukaka ba a harkar kwallon kafa sai a gasar Atlanta 1996, inda Najeriyar ta lallasa kasar Brazil a wasan karshe, wanda wannan ya baiwa Najeriya nasarar zamowa zakara, wannan nasara da Najeriya ta samu ta bangaren dan wasan ta Kanu Nwankwo hakika babbar nasara ce da ba'a taba tsammani ba, domin kuwa kowa yasan yadda kasar Brazil take a harkar kwallon kafa, tun bayan wannan gasa ce sunayan mutane irinsu Daniyal Amokashi da Kanu Nwanko da Jay Jay Okosha suka yi suna a duniya, duk sadda dan Najeriya ya fita zuwa kasar waje sai kaji ana tambayarsa ya labarin 'yan wasan Najeriya wadan da muka lissafa.
Sannan sunan Najeriya ya buwaya a kasashen Afurka baki daya ta fannin kwallon kafa, domin duk fadin Nahiyar babu 'yan wasan da suka kai na Najeriya iya taka leda, duba da irin nasarar da suka ringa samu ta lashe gasar cin kofin Nahiyar Afurka, wannan ya karawa sunan Najeriya martaba sosai a kasashen Afurka ta fannin tamaula.
Haka kuma, a gasar cin kofin duniya na shekarar 1998 da akayi a kasar Faransa wannan ma 'yan wasan Najeriya sun yi rawar gani. Domin sun kai wasan kusa da nakusa da na karshe, kusan zamu iya cewa tundaga wannan shekara ce Najeriya ta fara komawa baya a harkar kwallon kafa, kafin daga bisani ta durkushe baki daya.
Wani abin mamaki shi ne, babu wani abu da yake hade kan 'yan Najeriya waje daya kamar kwallon kafa, hakika duk lokacin da ake yin kwallo da Najeriya zaka sha mamakin ganin yadda 'yan Najeriya ke fatan alheri ga tawagar Super Eagles, babu maganar kudu ko Arewa Musulmi ko Kirista kowa murna yake yi idan aka samu nasara, haka kuma zaka ga 'yan Najeriya cikin damuwa sosai idan aka lallasa Najeriya babu maganar Bahaushe ko Beyerabe ko Inyamuri kowa nuna damuwa yake yi.
Haka kuma, idan ka shiga gidan kallon kwallo a lokacin da ake yin kwallon kafa da Najeriya, zaka ga yadda kusan dukkan kabilun Najeriya ke haduwa ana raha da juna a gidajen kallon kwallo, babu maganar wane ba wane ne ba, idan kuwa akaci nasara kaga bahaushe ya rungume beyerabe bafulatani ya rungume inyamuri ana murna ana sowa da nasarar da wannan kasar tamau ta samu.
Harkar kwallon kafa yanzu a Najeriya kusan zamu iya cewa ta zama tarihi. Shakka babu bazai zama kuskure ba idan mutum yace kwallo ta zama tarihi a halin yanzu, sai dai a baiwa yara na baya labarin irin kokarin da 'yan kwallonmu sukayi a baya, babu batun babban kulab na kasa Super eagles ko Flying Eagles ko Super Falkons ko matasa 'yan kasa da shekaru 20 ko 18 da dai sauransu kusan gabaki daya harkar wasanni ta koma baya, kuma irin kishi da dokin da 'yan Najeriya suke dashi a harkar kwallon kafa kusan shima zamu ce ya zuwa yanzu kusan ya zogaye fiye da yadda aka sanshi; da gwamnatin Najeriya da gaske take akan hadin kan kasarar nan da batayi sake da harkar wasanni ba, domin kamar yadda muka fada babu wani abu kaf Najeriya da yake hada kan 'yan kasa kamar wasan kwallon kafa ko kuma kace Super Eagles, amma akayi sakaci da wannan dammar da gangan ta zogaye a banza.
Tsohon dan wasan Najeriya a shekarun da suka gabata Samson Siasia yanzu shi ne mai horas da 'yan wasan super Eagles kulab din da ya taba bugawa kwallo. Sai muce Najeriya bata taba samun koma baya ba a harkar kwallon kafa kamar yadda ta ke samu a yanzu karkashin kulawar Siasia wanda yana daya daga cikin Wadan da suka fito da sunan Najeriya a harkar kwallon kafa a shekarun baya, duk kuwa da irin makudan kudin da yake karba a matsayin albashi, kamar yadda majalisa tayi doka cewar mafi karancin albashi a gwamnati shi ne Naira 18,000 kusan zamu ce Siasia yana karbar sama da albashin mutum 277 don yana karbar kusan Naira Miliyan 5,000,000 a duk watan duniya da sunan mai horas da 'yan wasan Najeriya.
Haka kuma, kungiyar ta super Eagles har yanzu ta kasa tabuka wani abin kirki a karkashin kwac Siasia domin har yanzu ko kwalba basu dauko mana ba da sunan samun nasara, harkar siyasa da kabilanci kusan zamu iya cewa su ne ummul haba'isin durkushewar harkar wasanni a Najeriya, domin akwai 'yan wasa wadan da suka iya kuma suka cancanta amma saboda kabilanci sai a kyalesu a dauki wadan da basa iya tabuka komai sai kashe musu kudi da akeyi ana zagayawa da su yawan buda ido da sunan kwallo. Lallai ya kamata hukumar NFF su yi dukkan mai yuwuwa wajen kawo gyara a harkar wasanni a Najeriya.
Muna fatan watan wata rana sunan Najeriya ya sake buwaya a harkar kwallon kafa a duniya, ina burin ganin lokacin da kulab din Super Eagles zasu ciwo gasar kofin duniya su zo da shi Najeriya su zagaya da shi Najeriya gabaki daya, inama zan samu damar dazan daga wannan kofi domin nuna murna da nasarar da kasata ta samu a gasar cin kofin duniya, lallai ina fatan ganin wannan ranar, Allah ya nuna mana da alheri.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com