Friday, June 27, 2014

Jan Kunne Dangane Da Batun Mubarak Bala

JAN KUNNE DANGANE DA BATUN MUBARAK BALA

Na bibiyi yadda naga ‘yan uwa da dama suna yin tsinuwa tare da la’anta ga Mubarak Bala a saboda abinda ya faru da shi. Babu shakka wannan kuskure ne mai girma dan wani dan uwa Musulmi yayi abinda yake kuskure ne a dinga aibata shi maimakon yi masa addu’ar shiriya. Alal akalli duk wanda ba zai iya yiwa wannan bawan Allah addu’ar shiriya ba, to kamata ya yi mutum ya kame bakinsa daga fadin mummunar Magana akan shi. Duk cikinmu babu wani wanda yake da garantin shiga Al-Jannah, babu wanda aka rubata masa cewa shi dan al-jannah ne, illa kawai fata da kwadayin Rahamar Allah da muke yi a ko da yaushe. Naji takaicin irin kalaman da wasu suka dinga yi babu linzami kamar su din suna da wata masaniyar cewar an lamunce musu Al-Jannah.

Yana da kyau ‘yan uwa su sani, Annabin Allah Nuhu AlaihisSalam, shi ne Annabin farko da Allah ya aiko zuwa doron duniya domin ya shiryar da mutane zuwa ga hanyar Allah, amma Allah ya kaddara mutane kalilan ne suka yi Imani da Annabi Nuhu AS, daga cikin wadan da ba su yi imani da shi ba har da d’ansa na cikinsa, wannan kuma haka Allah ya hukunta, shiriya tana hannunsa Subhanahu Wata’ala. Namu kawai shi ne isar da sakon ga al’umma Allah kuma shi ne yake juya zukatan bayinsa.

Annabin Allah Lud AS shima daga cikin wadan da ba su yi Imani da shi ba har da matarsa (iyalinsa). Allah shi ne buwayi gagara misali kuma shi ne yake jujjuyawa zukatan bayinsa Subhanahu Wata’ala, haka ya kaddara duk da kafirci da mutakabbiranci irin na Fir’auna amma matarsa ta kasance ‘yar Al-jannah tsarki ya tabbata a gareshi.

Wata rana Manzon Allah SAW yana cikin taron Sahabbai sai aka kawo wani mutum ya sha giya, aka yi masa bulala, bayan wani lokaci aka sake kawo wannan mutum, aka kuma yi masa bulala akan laifin shan giya, an yi masa haka har sau uku, sai wasu daga cikin Sahabbai suka dinga aibatashi akan laifin da yake aikatawa! Manzon Allah SAW yace da su shin zaku taimakawa Shaidan akan dan uwanku ne, ko zaku taimakawa dan uwanku akan Shaidan! Manzon Allah SAW yace da su, idan kuka aibatashi kuka la’ance shi, Shaidan yaci nasara akansa, amma idan kuka yi masa addu’ar fatan shiriya, sai ku taimakeshi yaci Nasara akan Shaidan La’ananne.

Da yawa naga suna tuhumar Iyayan Mubarak Bala cewa laifinsu ne da basu bashi tarbiyya ba. Wanda duk wanda ya jingina laifin zuwa ga iyayansa hakika ya zalunce su, duk wanda yasan Dakta Bala Muhammad tsohon Darakta Janar na hukumar Adaidaita Sahu ta jihar Kano, yasan mutum ne mai cikakkiyar tarbiyya ta addini, mai kuma san dukkan wasu lamaura da suka shafi addinin Musulunci, Bala Muhammad tsohon ma’aikacin gidan Radiyon BBC ne, dan haka mutane su koma su tambayi me ya sa Bala Muhammad ya bar aikin BBC, ya bari ne a saboda kishinsa da kaunarsa da tarbiyya irin ta addinin Musulunci.

A baya-bayan nan kafin zamansa shugaban hukumar Adaidaita Sahu ta jihar Kano. Bala Muhammad mutum ne mai yawan halartar tarukan kungiyoyin addinin Musulunci a ciki da wajen Najeriya, duk wadan da suka yi harkar MSSN a Najeriya zasu shaidi Bala Muhammad da juriya da san taimawa addini ta kowanne fanni. Dan haka zai zama zalinci a zargi Bala Muhammad da cewa bai bawa iyalansa tarbiyya ta Musulunci ba.

Bahaushe yana cewa ka haifi Mutum ne baka haifi halinsa ba. Wannan abu da ya faru da shi kansa Mubarak Bala abu ne da kusan yake sabo a cikin al’ummarmu, ace mutum ya fito irin haka cewa ga wani yayi Ridda a bainar jama’a, sau da dama irin haka kan faru ba tare da ansani ba. Kuma abinda yafi wanda Mubarak Bala ya aikata yana faruwa a cikin birnin Kano.

Ansha samun mabiya wata darika na ikirarin cewa Shehunsu shi ne Allah Wal’Iyazubillah. Wasu da dama kan kira kansu da Alloli, wannan wata tsohuwar shirkace da anjima ana yinta a jihar Kano, duk kuwa da masu yi din suna ikirarin su Musulmai ne, amma zaka ji a lokuta da dama bayanansu ko wakokinsu suna kore samuwar Allah Subhanallah, mutane zasu iya tuna irin wannan da ya faru da wani mawaki wanda ta kai har Khalifa Isyaka Rabiu ya fito ya barrantar da kansu daga kalaman da mawakin yayi na shirka, wanda har yanzu mawakin ba’a jishi ya yi nadamar abinda ya aikata ko ya nuna cewa kuskure ya yi ba.

Dan haka, a halin da muke ciki bin sahihiyar koyarwar addinin Musulunci da ta kunshi Al-Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW it ace kadai mafita a garemu wajen kaucewa fadawa hanyoyin shaidan La’ananne. Lallai ne mu lizimci wajen da ake yin karatun addini mu kuma lizimci tuntubar Malamai a duk lokacin da wasu al’amura suka shige mana duhu dan samun waraka.

Muna addu’ar Allah ya shiryi wannan bawa nasa Mubarak Bala ya dawo kan hanya madaidaiciya, ya ganar da shi kuskurensa, ya fahimtar dashi addinin Musulunci shi ne addini a wajen Allah. Allah ka shiriyi al’ummarmu shiriya ta addini, Allah ka tabbatar da duga-duganmu wajen yi maka da’a da bauta. Allah ka shiryemu shirin addini.

YASIR RAMADAN GWALE 
27-06-2014

Wednesday, June 25, 2014

Anya Za'a Iya Yiwa Mubarak Bala Hukunci A Dokar Kasa Kuwa?

ANYA ZA’A IYA YIWA MUBARAK BALA HUKUNCI A DOKAR KASA KUWA?

Matashin nan da rahotanni a jiya suka nuna cewar ya sauya addininsa daga Musulunci zuwa wani abin daban ya zo da sarkakiya a tsarin shari’ar kasarnan. Shi dai wannan matashin bayanai sun nuna cewar ba wai ya canza sheka daga Musulmi ne zuwa kirista ba, illa iyaka yace shi bai yadda da samuwar Ubgajinmu Mahaliccinmu ba, Babbar Magana! A kashin gaskiya irin wannan batu na Mubarak Bala ba wani sabon abu bane, domin wannan na daya daga cikin aqidar Dirwaniyanci (Darwinism) abinda kawai za’a iya zamewa mutane sabo shi ne, shi Mubarak Bala ya karanta sashin kimiyyar hada sinadarai ne (Chemistry), sabanin idan a ce ya karanta “Sociology” ne wanda amfi samun masu irin wannan ikirarin a cikin wadan da suka karanci tsantsar sociology babu karatun addini a tare da su.
Amma wannan abinda da Mubarak Bala ya aikata duk kuwa da cewar ana tuhumar hankalinsa, ko da gaske yake yi akan batunsa ko bad a gaske yake yi ba, to lallai mu sani Mubarak Bala yana da cikakkiyar kariya ta kundin tsarin mulki da ba za’a iya zartar masa da hukuncin kisa ba, ko da kuwa ya kekesa kasa akan batun da yake ikirari.

A kundin tsarin Mulkin Najeriya na 1999, sashi na 38 karamin kashi na daya (1) ya baiwa duk dan Najeriya damar yin addinin da yaga dama, sannan kuma ya canza addinin da yake bi a duk lokacin da yaga dama ba tare da an tuhumeshi da aikata wani laifi ba. Wannan na daya daga cikin sashin da ya baiwa wata baiwar Allah mai suna Aisha waddata ta koma Musulunci daga Kiristanci kwanakin baya a jihar Neja wadda batun ta ya janyo kace-nace.

Haka kuma, sashi na 36 karamin kashi na goma sha biyu (12) yace babu wani abu da mutum zai yi ace laifi ne har sai idan wannan abin ya kasance a rubuce cikin wata doka wacce Majalisar kasa ko ta jiha ta yi doka akansa. A dan haka, a bisa dogaro da kundin tsarin Mulkin Najeriya wanda dukkan masu Mulki sunyi rantsuwar tabbatar da zasu bashi kariya a kowanne irin hali, wannan matashi ba za’a iya zartar masa da hukuncin kisa ba ko da kuwa ta tabbata ridda ya yi.

Dan haka, wannan yana daya daga cikin inda aka samu tarnaki a kundin tsarin Mulki da ya sabawa koyarwar addinin Musulunci. Wannan kuma kalubale na babba ga majalisun dokokin da suke aiwatar da Shari’ar Musulunci. A dan haka, yana da kyau jama’a su sani, a dukkan wasu kundin dokokin Panel Code da aka samar a jihohin da suke aiki da Shari’ar Musulunci babu inda aka ayyana hukuncin kisa ga wanda ya bar addininsa zuwa wani addinin daban. Saboda haka, a tsarin da muke kai a Najeriya, babu wani alkali da zai iya yankewa Mubarak Bala hukuncin kisa a irin wannan lamari sai fa idan laifin ya kasance rubutacce ne a cikin dokar kasa, wanda wannan babu shi a rubuce.

Babu shakka wannan al’amari zai bude wani sabon babi a kundin tsarin Mulkin kasarnan, zai kuma janyo wani sabon cece-kuce na daban, Allah ya kiyaye. Gwamnati dai ba zata iya zartarwa da wannan matashi hukunci kisa ba matukar ba kotu ce ta sameshi da laifin abinda ya aikata bat a ce ga hukuncinsa.

Haka kuma, tsarin Mulkin Najeriya yace dukkan wata doka ko wani tsari da yaci karo da kundin tsarin Mulkin Najeriya, to “constitution” zai kasance a sama da wannan tsarin ko da kuwa koyarwar wani addini ne. Wannan kuma shi ne babban tarnakin da kundin tsarin Mulkin Najeriya ya yiwa koyarwar addinin Musulunci, wanda zamu iya komawa majalisun dokoki na jihohin dan yin wasu dokoki da suka dace da koyarwar addininmu na Musulunci.

Dan haka, yana da kyau al’umma su sani cewar babu yadda masu Mulkin da suka rantse domin kare kundin tsarin Mulki tare da yi masa biyayya zasu yi wani hukunci da ya saba masa, saboda haka, a kurkusa abinda za’a iya yi tunda ba zamu iya canza kundin Mulki a yanzu ba, shi ne, a samu Malamai da masana su zauna da wannan bawan Allah Mubarak Bala su yi masa wa’azi da Nasiha ko Allah zai karkato da hankalinsa ya fuskanci irin hadarin day a jefa rayuwarsa idan hart a tabbata cewa yana da lafiyayyan hankali ya dauki hukuncin day a zabawa kansa na kin amincewa da samuwar ubangiji.

Sannan kuma, ya zama dole a aiwatar da bincike na me ya sanya wannan bawan Allah ya bar Musulunci zuwa wani abin daban, dan a samu bakin zaren yiwa wannan tufkar hanci. Allah ya kare mana Imaninmu, ya sa mu mutu muna cikin Imani mu tashi muna masu imani da Allah da ManzonSa Sallallahu Alaihi Wasallam. A gaba kuma zamu zo da abinda Musulunci yace game da abinda Mubarak Bala ya aikata In Sha Allah.

YASIR RAMADAN GWALE
26-06-2014


Ridda A Sudan Da Kano

RIDDA A SUDAN DA KANO

A jiya muka ji labarin matarnan da ta yi ridda ta bar addinin Musulunci a kasar Sudan cewa ta haihu a gidan kaso inda kuma kotu ta bayar da umarnin a saketa bayan da matar  Mariam Ibrahim Yahya ta daukaka kara akan hukuncin da kotun farko ta yanke mata na haddin kisa ta hanyar rataya. Ita dai Mariam Yahya Ibrahim ta auri mijinta Daniel Wani dan kasar Amurka, inda daga bisani ta bar Musulunci ta koma Kiristanci bayan da suka yi aure. Har ya zuwa jiya da ta shafe kwanaki 21 a gidan yari ana tsare da ita, Mariam bata gamsu ta sauya addini daga kiristanci ta dawo Musulunci ba ta cigaba da kafewa akan addinin Kirista.

Kwatsam kuma, a wani labari mai kama da wannan, sai muka ji a Kano ma wani matashi Mubarak Bala ya yi ridda ya bar Musulunci, duk da bayanan da suka fito sun nuna cewar shi Mubarak Bala ya nuna bai yadda da samuwar ubangiji ba ne, Wal Iydhu Billah! Lallai wannan abu ne mai tayar da hankali ace mutane suna fita daga Musulunci suna komawa kiristanci a garuruwan da suke da kusan Musulmi dari bisa dari.

Sanin kowa ne Sudan kasa ce ta Musulunci kamar yadda Kano gari ne na Musulunci amma ace irin haka ta faru wadannan mutane sun bar Musulunci a garin Musulunci. Ba shakka akwai tashin hankali a cikin batun.

Dan haka,  Addinin Musulunci ya yi tanadi akan wadan da suka bar Musulunci suka koma wani addinin daban, Malamai zasu yi bayanin irin hukuncinsu, musamman shi Mubarak Bala In Sha Allah, haka kuma wajibin hukumomi ne su tabbatar da zartar musu da hukuncin da yake kansa a Musulunce.

A gefe guda kuma, daga cikin munafukan kungiyoyin Shaidan dake kasashen Turai da Amurka sun samu dama ta yin abida suke so wajen nuna dole a baiwa kowa 'yancin yin addinin da yaga dama, wanda ko muma a Najeriya kundin tsarin Mulkinmu ya yi tanadin baiwa kowa damar yin addinin da yaga dama, amma dai babu shakka idan har Mubarak Bala bai dawo daga wancan tunani ba, dole a jingine kundin tsarin Mulki a yi masa hukuncin da Musulunci ya tanada. Allah ya shiryi al'ummarmu.

YASIR RAMADAN GWALE
25-06-2014


Tuesday, June 24, 2014

Wasika Daga Mundubawa Gidan Sardaunan Kano

Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano
WASIKA DAGA MUNDUBAWA GIDAN SARDAUNAN KANO

Bayan gaisuwa da fatan alheri ga al’ummar jihar Kano. A yanzu haka muna cikin wani lokaci da aka jarrabe mu da fitina da motsuwar zukata, muna cikin yanayi mara dadi, addu’ah da riko da sababin karbar addu’ah zasu yi tasiri matuka wajen fitarmu daga cikin halin da muke ciki, ta yiyu Allah ya dubi gajiyayyu daga cikinmu ko yaran da hankalinsu bai nuna ba ya kawo mana dauki ta inda bamu zata ba.

Kamar yadda kowannemu ya sani, a jiya Litinin al’ummar jihar Kano musamman wadan da ke yankin unguwar Kofar Nassarawa da unguwar bayan gidan Malamai (TSB) da sabuwar Kofa da Rumfa Kwaleji sun shiga dimuwa sakamakon wata fashewa mai karar gaske da ta faru a makarantar School of Hygiene, inda daga bisani bayanai suka tabbatar da cewar harin Bam ne aka kawo! Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un! Ba shakka dole hankula su dungunzuma, zuciya ta karaya, sakamakon abinda ya faru kuma ya zo da asarar rayuka.

Dan haka, ko a APC mutum yake, ko a PDP mutum yake, abu mafi muhimmanci shi ne, mu al’ummar Musulmai ne, kuma ba muda wani gari da ya wuce Kano. Wannan ta’addancin mu aka yiwa, al’ummar Musulmi ne suka shiga damuwa sakamakonsa, mutanan da suka mutu a dalilin wannan hari ‘yan uwanmu ne ‘yan jihar Kano Musulmi.

Ya ‘yan uwa masu girma, yana da kyau mu sani, idan masifa ta zo bata tambayar katin jam’iyya balle waye dan gari ko bako kafin ta afkawa mutum. Abinda ya fi dacewa mu yi a irin wannan lokaci shi ne addu’ah tare da komawa zuwa ga Allah, ba yin cece kuce da ba zai iya dawo da rayukan wadan da suka rasu ba. Lallai mu yawaita ambaton Allah, mu kuma rage aikata ayyukan sabo, muji tsoron Allah a cikin mu’amalolinmu na yau da kullum mu nemi agajin Allah a halin da muke ciki.

Allah ka tsare mana Imaninmu da mutuncinmu da rayukanmu. Ya Allah ka amintar da mu a cikin gidajenmu da garuruwanmu, Allah ka yaye mana wannan damuwa a cikin zukatanmu, iyalanmu da ‘yan uwanmu da abokanmu da dukkan al’ummarmu Allah ka zama gatanmu.

Muna kuma yin addu’ah ta musamman akan wadan da suka rasu, Allah kajikansu ka gafarta musu ka sa bakin wahalarsu kenan, masu aikata wannan aikin ta’addanci Ya Allah idan sun faku a garemu kai basu faku a gareka ba, Allah ka bi mana hakkinmu, Allah karka baiwa ‘yan ta’adda dama akan al’ummarmu. Allah ka wargaza shirinsu ka mayar musu da kaidinsu garesu.

Muna mika sakon jaje ga Gwamnatin Kano da al’ummar jihar Kano baki daya. Allah ya kare Jihar Kano da Najeriya baki daya. Wannan sako ne a madadin Mai Girma Sardaunan Kano Mallam (Dr.) Ibrahim Shekarau da dukkan Masoya da ‘yan uwa da abokan Mudubawa Avenue Kano.

ZABEN EKITI: Ekitawa Sun Guntulewa Bola Tinubu Yatsa Daya

Bola Tinubu Madugun APC

ZABEN EKITI: Ekitawa Sun Guntulewa Bola Tinubu Yatsa Daya

Zaben da aka yi a makon da ya gabata a jihar Ekiti, shi ne zabe na baya-bayan nan da hukumar zaben Najeriya karkashin jagorancin Farfesa Attahiru Jega ta bugi kirji da shi wajen cewa anyi tsantsar gaskiya da adalci a zaben, abinda ya kara gasgata hukumar zabe shi ne, sakon karbar kaddara da dan takarar APC kuma Gwamna me ci Kayode Fayemi ya fitar a ranar Lahadi, inda ya taya dan takarar PDP Ayo Fayose da ya samu nasara murna ya kuma yi masa fatan alheri.

Babu shakka Ekitawa sun zabawa kansu makomar da ita suke ganin ta fi zama a’ala a garesu. Gwamna Kayode Fayemi ya burgeni ainun akan abin da ya faru, inda ba tare da wani bata lokaci ba ya karbi sakamakon zaben ya kuma taya sabon Gwamna murnar samun nasara, irin wannan siyasar da muke gani a Amerika da sauran kasashen turawa muke fatan ‘yan siyasarmu su yi koyi wajen karbar kaddarar faduwa zabe ba tare da wani kunji-kunji ba, duk da cewa ba laifi bane wanda yake ganin an zalince shi ya je kotu dan a bi masa hakkinsa.

Sai dai wannan zabe ko shakka ba zai yiwa Madugun jam’iyyar APC Bola Tinubu dadi ba, domin daga cikin ‘yan yatsunsa guda biyar Ekitawa sun guntule masa daya a yankin da yake tunkaho da takama da shi, har ake yi masa kirarin mutum mafi buyawa a siyasar yankin Kudu maso yamma day a kunshi Yarabawa Zalla.

Amma ga duk wanda ya san tarihin siyasar sabon Gwamna Fayose ba zai yi mamaki da wannan nasara da ya samu ba. Domin ya yi gwamna a baya kuma ya nuna kwazo, gashi matashin manomi mai matukar kaunar Talakawa, mutum mai son shiga cikin jama’a yana mu’amala da su, wannan ta sanya talakawa suka saki jiki da shi sosai, mutane da dama sun bayar da shedar irin karamci da son jama’arsa da Fayose yake yi.

Yanzu kuma babu wani abu da ya rage illa mu tsumayi zaben jihar OSUN da shima yake tafe nan gaba a wannan shekarar ta 2014. Shin suma Osunawa zasu sake guntulewa Tinubu yatsa ko kuwa zai sake karfafa ikonsa a siyasar jihar, wannan lokaci ne kawai zai bayar da amsa, amma dai ba shakka Gwamna Rouf Aregbesola na daga cikin gwamnonin da suke kamanta gaskiya a tsakanin Gwamnonin yankin Yarabawa. Da alheri.

23-06-2014

Wednesday, June 11, 2014

Risala Zuwa Ga Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi


RISALA ZUWA GA MAI MARTABA SARKIN KANO MALAM SANUSI LAMIDO SANUSI

Bismillahir Rahmanir Rahim. Ina fara bude wannan Risala da sunan Allah, mai gamammiyar Rahama, mai gamamman jin 'kai, tsira da AmincinSa su 'kara tabbata ga fiyayyan halitta, Manzon tsira cikamakin Annabawa, Annabi Muhammad SAW da alayensa da Sahabbansa masu daraja da wadan da suka biyo bayansu da kyautatawa har yazuwa ranar sakamako. Dukkan wanda Allah ya shiryar da shi shi ne hakikanin shiryayye, wanda duk Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi.

Da farko, ina mai yin amfani da wannan dama, wajen kara mika ta'aziyata ga sabon Sarkin Kano Mallam Sanusi Lamido Sanusi, a bisa rasuwar tsohon Sarkin Kano Alh. Ado Abdullahi Bayero, Allah ya jikansa ya gafarta masa, Allah ya kyauta bayansa. Ina kuma kara taya Mai Martaba Sarki murna da kuma alhini; ina taya Mai Martaba Sarki murnar zama sabon Sarkin Kano na 14 a dangin Sullubawa, na 57 a tarihin Masarautar Kano, ina kuma taya Mai Martaba Sarki jimamin abubuwan da suka faru yayin wannan nadi na shigar al'amuran siyasa da boren da wasu fusatattun matasa suke yi, babu shakka wannan abin bai yi dadi ba.

Haka kuma, ina amfani da wannan damar wajen yin kira ga sabon Sarkin Kano Malam Sanusi Lamido Sanusi, da ya yi watsi da dukkan al'amuran siyasa da suka faru a yayin wannan nad'in sarauta, ya rungumi al'ummar Kano da kasa baki daya dan samun zaman lafiyarsa da dorewar mulkinsa. Ya Mai Martaba Sarki, hakika shigar al'amuran siyasa cikin wannan abu bai yi mana dadi ba, domin dukkan masu mulkin siyasa wa'adi garesu takaitacce da baya wuce shekaru 8 a yayinda Sarki ke da wa'adin iyakar rayuwarsa.

Ya mai martaba sarki, a dan saboda a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da dorewar Mulkin sarautar jihar Kano, ina kira a gareka da ka rungumi dukkan masu mulkin siyasa daga ko wace jam'iyya suke dan hidimtawa al'umma. Abu ne mai muni, amfanin da 'yan siyasa suka yi da wannan kujera ta sarautar Kano dan biyan bukatunsu na siyasa, wanda a karshe babu wanda za'a bari a cikin al'amarin sai ita masarautar Kano. 

Ya Mai Martaba Sarki, adawa ko nuna tirjiya ga gwamnatin tarayya wadda it ace Gwamnatin koli a Najeriya babu abinda zai janyo mana face faduwar daraja da zubewar girma da gurbacewar al'amura, lallai ne, Mai Martaba Sarki ya yiwa Gwamnatin Tarayya da'a da biyayya wajen ciyar da rayuwar al'umma gaba, kin yin hakan babu abinda zai haifar face rashin nasara da rashin biyan bukatu.

Ya isa abin misali yadda marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Ado Bayero ya kame kansa daga shiga al'amuran siyasa da daukar bangare daya, tafiya da kowa tare da rashin nuna bambanci ko wariya na daga cikin sirrin nasarar mai martaba sarkin kano Allah ya kai rahama gareshi.
'Yan siyasa suna yin komai ne dan biyan bukatunsu na siyasa ba tare da la'akari da halin da al'umma ta ke ciki ba. Su wadannan 'yan siyasar da suka shigo cikin wannan al'amari ba sunyi abinda suka yi bane, dan nuna kishi ga al'ummar jihar kano, illah manufarsu ta siyasa ta bakantawa gwamnatin tarayya da suke hamayya da ita rai, tare da cimma nufinsu na siyasa, bayanan da suke fita daga bakunansu sun tabbatar da hakan.

A lokacin zaben 2011, Gwamnan jihar Nassarawa Aliyu Akwe Doma ya sanya sarakunan jihar a cikin al'amuran siyasa wanda hakan ya janyo musu zubewar kima da daraja da jefa su cikin wulakanci da kaskanci, sai da takai an fasa motar da Sarkin lafiya yake ciki, aka janyo rawaninsa ya fadi kasa, a dalilin halin da gwamnan jihar ya sanya shi na nuna adawarsa karara ga jam'iyyar Adawa ta Buhari, inda gwamnan ya umarce su da kada su sake su karbi tawagar Buhari da zata zo yakin neman zabe cikin fadarsu, wannan al'amari bai yi musu kyau ba, akan biyayyar da suka nunawa Gwamna ta yadda suka sanya kansu a cikin sha'anin siyasa, yanzu dai gwamna y agama wa'adinsa ya tafi su kuma suna nan a matsayin sarakuna, wanda wannan ba komai zai janyo ba sai da na-sani.

Ya Mai Martaba Sarki, kada ka saka kanka a cikin wani yanayi irin wannan, ta yadda Gwamnatin Kano da ke hamayya da gwamnatin tarayya zata sanyaka cikin sha'aninsu na siyasa, sanya kai cikin wannan al'amari babban koma baya ne ga masarautar Kano da kuma al'ummar kano, Mai Martaba Sarki uban kowa ne, dan siyasa da wanda ba d'an siyasa ba, talakawa da masu kudi. Kaucewa shiga sha'anin siyasa shi ne abinda zaifi zamarwa Mai Martaba Sarki alheri da mutunci a idan duniya. Sanin kanmu ne, shugabanni na siyasa sune a gaba, sune wadan da suke da Kotu da 'yan sanda da kuma uwa uba dukiyar al'umma ke karkashin kulawarsu, lallai tafiya tare dasu wajen ciyar da al'umma gaba shi ne yafi komai muhimmanci ga Mai Martaba sabon Sarkin Kano Malam Sanusi Lamido Sanusi, rashin hakan kuma ba zai haifar da d'a mai ido ba.

A dan haka, wannan ba yana nufin Sarkin Kano ya je ya kwantawa gwamnati ta taka shi irin yadda taga dama ba. Yana da kyau, Mai Martaba Sarki ya hada kai da gwamnati wajen ciyar da al'ummar kano gaba. Ita gwamnati ba zata taba kame hannu wani mahaluki ya zamar mata karfen kafa a sha'anin tafiyar da gwamnati ko Mulkinta ba! Ya isa abin misali, Sardaunan Sokoto tsohon Firimiyan Jihar Arewa, wanda shi ne mutanan Arewa suka rika a matsayin shugaba na kurkusa mafi Adalci a mulkinsa, amma kuma a gefe guda shi ne ya kawar da rawanin sarkin Kano Muhammadu Sanusi.

Mun ga yadda al'amuran siyasa suka mamaye Sarautar Sarkin Musulmi Dasuki wadan da basu yi dad'i ba, haka kuma, munga yadda siyasa ta shiga tayi awan gaba da Mai Martaba Sarkin Gwandu Almustapha Haruna Jakwalo, wadannan dukkansu siyasa ce ta shiga ta damalmala al'amuran sarautarsu ta nemi zubar da kimar masarautunsu.

Dan haka, kame kai daga shiga harkokin siyasa ga Mai Martaba Sarkin Kano Malam Sanusi Lamido Sanusi tare da rungumar kowa, shi ne abinda zai fi zama alheri a tsawon wa'adinsa, kuma zaifi jawo masa kima da mutunci a idan duk wata gwamnati da zata zo ta tafi, idan muka bari sarauta ta koma kamar mulkin siyasa, to haiba da muhibba da kwarjini na sarakuna ya gama zubewa kasa warwas, haka kuma masarautar Kano alkibla ce ta sauran dukkan masarautu da ke fadin tarayyar Najeriya.

Wadannan fitintinu da ke faruwa da wadan da ke shirin faruwa Allah ya tsagaita su, Allah ya kawar mana da dukkan wani abin 'ki da Alla-wadai. Ina kara jaddadawa Mai Martaba Sarki uban kowa ne ba tare da la'akari da siyasar da mutum ke bi ba. Allah ya taimaki Masarautar Kano da sauran masarautun Najeriya baki daya, Allah ya tabbatar mana da dawwamammen zaman lafiya. Allah ya warware wannan sabatta juyatta da ke faruwa.

11-06-2014

SABON SARKIN KANO: Kaddara Ta Riga Fata


SABON SARKIN KANO: KADDARA TA RIGA FATA

Ina mai amfani da wannan damar wajen sanar da al'umma musamman wadan da sukai ta turmin sakon Inbox wadan da hannuna yakai garesu da kuma wadan da hannuna bai kai garesu ba, da wadan da suka kirani a yawa tun jiya, cewar ni Yasir Ramadan Gwale ina taya sabon Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi murnar zama sarkin Kano da ya yi a jiya. Allah ya yi masa jagoranci, Allah ya yi riko da hannunsa wajen aiki da daidai.

Babu shakka, zuciyarmu ta kadu, rai ya sosu da muka ji cewar ba Chiroman Kano Alhaji Samusi Lamido Ado Bayero aka zaba ba a matsayin sabon Sarkin Kano. Wannan kuma ba shi ne yake nuna cewa bamu yarda da kaddara ba, ai akan yiwa mutum mutuwa yaji zafi har yayi kuka, daga karshe kuma ya mika lamarinsa ga Allah, kuma Allah ya bashi ladan hakuri, dan Allah shi ne yake hukuntawa. Idan sanmu ne Chiroman Kano ya zama Sabon Sarkin Kano, tunda kuma Allah bai hukunta masa ba, munji mun bi, sami'ina wa'ada'ana.

Allah ya jikan Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero. Allah ya kai rahama gareshi. Ina kuma amfani da wannan damar wajen kara sanar da 'yan uwa kamar yadda Malaminmu Dr. Bashir Aliyu Umar ya sanar a shafinsa cewa, lallai Sabon Sarkin Kano ba dan Shi'ah bane. Ina kuma kira ga daukacin al'ummarmu da su yi hakuri da Abinda ya zo haka ba wanda aka zata ba, a Musulunci biyayya ga Shugabanni wajibi ne ko da kuwa ba akan daidai Shugabannin suke ba, matukar ba umarni suke yi da sabn Allah ba.

Allah ya ja zamanin Sabon Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, ina kuma amfani da wannan dama har iala yau wajen yin kira ga sabon Sarkin Kano da ya nada Dakta Bashir Aliyu Umar a Matsayin Sabon Wazirin Kano, ina da yakinin hakan zai sanya Natsuwa a zukatan da dama wadan da suke jifansa da Shi'anci. Allah ya zaunar da kasarmu lafiya, ya zaunar da Kano lafiya, masu bore kuma ayi hakuri a karbi abbinda ya faru a matsayin kaddara. Daman Imani baya cika sai mun yarda da kaddara mai kyau da mara kyau. 

Daga Karshe ina mika Ta'aziya ta ta rasuwar tsohon Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ga Mai Girma Sardaunan Kano Mallam Ibrahim Shekarau, ina kuma taya shi murnar nada abokinsa Dan Majen Kano a matsayin sabon Sarkin Kano. Na gode.

09-06-2014