Saturday, December 15, 2012

UMAR LAWAN MUHD: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook (2)


UMAR LAWAN MUHD: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook (2)
Da sunan ALLAH mai gamammiyar Rahama, mai gamamman jin kai, tsiranSa da AmincinSa su kara tabbata ga baban fatima Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam. Ina shaidawa babu abin bauta bisa gaskiya da cancanta sai ALLAH kuma shi ya aiko mana Manzon ALLAH da sakon musulunci.

Kamar yadda ya gabata a fitowa ta farko, na zabi Malam AbdulQadir Muhammad Bello ya zama gwarzo na daya, kuma wannan munasaba ta kama na zaben gwarzo na biyu. Alhamdulillahi na sake lalubawa da kuma yin nazari akan wannan bawan ALLAH Umar Lawan Muhd. Hakika shima kamar Malam AbdulQadir yana kokari babu dare babu rana wajen ganin ya shiryar da mutane suwa ga hanayar ALLAH karkashin koyarwar Salafussaleh.

Hakika duk mai bibiyar sakonnin da suke fitowa daga turakar wannan bawan ALLAH a shafinsa na facebook zai gasgata ni. Yana da himma da kwazo ainun wajen ganin ya isar da sakon ALLAH zuwa ga ‘yan uwa. Ina bibiyar kusan dukkan sakonnin da wannan bawan ALLAH yake fitarwa ta shafinsa. Na bibiyeshi a lokacin da yake kawo tarihin sahabbai khulafa’urra Shidun da sauran Asharatul Mubashshirina Bil jannah, ya yi kokari matuka gaya wajen bayyanawa mutane irin darajar wadannan bayin ALLAH abokan Manzon ALLAH Salallahu Alaihi Wasallam. Bai gajiya ba wajen wannan muhimmiyar karantarwa wadda muke matukar kishirwarta a wannan lokaci, hakika muna bukatar mutane hazikai kuma jajirtattu irinsu wajen kokarin shiryar da mutane zuwa ga hanyar ALLAH ta wannan shafin.

Haka nan, kaima Malam Umar Lawan Muhd, Ina mai yi maka addu’ah ta fatan alheri tare da tawassuli da sunayan ALLAH tsarkaka madaukaka, ALLAH ya sanyawa rayuwarka Albarka, ya kareka daga da-nasani da kuma kasawa. ALLAH ya yi maka jagora a dukkan lamuranka, Ya sadaka da alkhairan duniya da lahira, ALLAH ya ya daukaka darajarka. ALLAH ya amfanar da al’ummar musulmi da rayuwarka.

Ya ALLAH wannan bawa naka Umar Lawan Muhd ka yafa masa kurakuransu wadan da ya sani da wadan da bai sani ba. Ya ALLAH kasa muyi tarayyah da shi acikin Al-jannarka. ALLAH ka karfafeshi ka kara masa juriya da kwarin guiwa, Ya ALLAH kar ka baiwa Shaidan dama akansa.

Daga karshe ina mai kira ga Gwarzona Malam Umar Lawan Muhd da ya zage dantse ya kara kokari akan kokarin da yake da shi, haka kuma Ina mai yiwa kaina da kai da sauran ‘yan uwa Nasiha da muji tsoron ALLAH acikin dukkan lamuranmu, kuma mu dogara ga ALLAH a cikin dukkan lamuranmu, Lallai ALLAH mai rahama ne mai jinkai, kuma maji rokon bayinSa ne Subhanahu Wata’ala. ALLAH ya hada fuskokinmu a Al-Jannah baki daya.

Yasir Ramadan Gwale

Friday, December 14, 2012

ABDULQADIR MUHAMMAD BELLO: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook


ABDULQADIR MUHAMMAD BELLO: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook
Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga ALLAH madaukakin sarki, ubangijin talikai, wanda ya dauki wannan al’umma ya fifita ta akan sauran al’ummatai, ya sanya ta jagora ga sauran mutane don ta shiryar da su ga hanyar cin nasara a rayuwarsu ta duniya da lahira. Tsira da aminciSa su tabbata ga fiyayyen Manzanni, cikamakin Annabawa, wanda ALLAH ya fifita shi ya ba shi littafi mafi cika da kamala wanda ya ke shafe-zane ne ga sauran littatafai, Annabi Muhammadu da Alayansa da Sahabbansa dakuma wadan da sukabi tafarkinsu har ya zuwa ranar sakamko. Dukkan wanda ALLAH ya shiryar shi ne cikakken shiryayye, haka kuma duk wanda ALLAH ya batar babu mai iya shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai ALLAH kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonSa ne.

Hakika nayi nazari sosai kafin zabar wannan gwarzo nawa. Malam AbdulQadir Muhammad Bello matashi ne mai hazaka da juriya kuma jajiratacce. Hakika ina bibiyar dukkan wani rubutu da wannan bawan ALLAH yake yi da kuma wanda yake sharing dare da rana a shafin facebook, na yaba da kwazonsa da juriyarsa wajen kokarin shiryar da mutane ya zuwa ga hanyar ALLAH mikakkiya, bai taba gajiyawa ba wajen sadar da mutane da abubuwan da zasu taimakawa rayuwarsu ta duniya da lahira.

Wannan bawan ALLAH yana kokari matuka da gaske wajen yin da’awa ta gaskiya, tare da kira zuwa ga kadaita ALLAH da bauta akan tafarkin Sunnah da kuma fahimtar magabata na kwarai. Wallahi a wannan zamani Da’awar Sunnah tana bukatar mutane irinsu Malam AbdulQadir, domin samun mutum mai juriya da jajircewa abu ne mai matukar amfani musamman akan hanyar ALLAH.

Malam AbdulQadir ina bibiyar dukkan wasu sakonninka ko da kuwa baka ga comment dina ba. Hakika muna yiwa ALLAH godiya akan wannan baiwa da ya yi mana ta samun matasa jajirtattu masu hazaka irinka. ALLAH ya kara maka san alkhairi da yada shi ga sauran jama’a.

Ina mai yi maka addu’ah tare da tawassuli da sunayan ALLAH tsarkaka madaukaka, ALLAH ya sanyawa rayuwarka Albarka, ya kareka daga dukkan abubuwan ki da kuma kasawa. ALLAH ya yi maka jagora a dukkan lamuranka, Ya sadaka da alkhairan duniya da lahira, ALLAH ya ya daukaka darajarka. ALLAH ya amfanar da al’ummar musulmi da rayuwarka.

Ya ALLAH wannan bawa naka AbdulQadir Muhammad Bello ka yafa masa kurakuransu wadan da ya sani da wadan da bai sani ba. Ya ALLAH kasa muyi tarayyah da shi acikin Al-jannarka. ALLAH ka karfafaeshi ka kara masa juriya da kwarin guiwa, Ya ALLAH kar ka baiwa Shaidan dama akansa.

Daga karshe ina mai kira ga Gwarzona Malam AbdulQadir Muhammad Bello da ya zage dantse ya kara kokari akan kokarin da yake da shi, haka kuma Ina mai yiwa kaina da kai da sauran ‘yan uwa da muji tsoron ALLAH acikin dukkan lamuranmu, kuma mu dogara ga ALLAH a cikin dukkan lamuranmu Lallai ALLAH mai rahama ne mai jinkai, kuma maji rokon bayinSa ne Subhanahu Wata’ala.

Yasir Ramadan Gwale

Wednesday, December 12, 2012

ZOGALE SAMARIN DANGA


ZOGALE SAMARIN DANGA
Ada can akan yiwa zogale kirari da “zogale samarin danga” saboda itacansa bashi da wata wuyar samu a garuruwan Arewa. Zogale yakan fito ne birjik galibi lokacin da ruwan sama ya zuba wato lokacin damina. ‘yan uwanmu na karkara sukan yi kariyar gidajensu da itacansa, su ringa gyara katangar zana da shi inda a mafiya yawancin lokuta ake yin dirka da shi, domin rike dangar kara ko zana da akayi, amma cikin ikon ALLAH da albarkar kasa da muke da ita, ruwan sama na dukansa sai kaga ya yi tsiro kuma bishiya ta tashi a jikin dangar kara, sai aka wayi gari kusan galibin gidaje sai ka samu zogale ne ya kewayesu, wannan ta sanya ake masa kirari da zogale samarin danga. Saboda shi zai fara yi maka maraba idan ka shigo gida. Wannan ta sanya har manoma suke amfani da shi wajen sanya alama ta iyakar gona, saboda bashi da wuyar tashi.

Bayan haka, bincike a baya bayannan yana kara fitowa dangane da irin muhimmanci da ganyan zogale yake da shi. Masana a wannan zamanin suna ta kara fadada bincike dan gano irin muhimmanci da kuma irin sinadaran da zogale yake da su dan taimakawa rayuwar dan adam. A halinyanzu dai masana sun tabbatar da cewar babu wani ganye da yakai zogale amfani ga rayuwar mutane a wannan zamanin, domin yana dauke da sinadarar masu bayar da garkuwa ga lafiya, da kuma kawar da ciwace-ciwace. Kamar cowon suga, damuwa da sauran cututtuka da dama.

Mu kam a kasar Hausa munyi dace, domin tun tale-tale mun taso mun tarar da iyayanmu da kakanninmu suna dafa zogale inda ake yin kwadansa domin aci dan marmari. Wasu kuma suna yin miya da shi, kusan mu haka muke amfani da zogale tun zamani na dauri. Sai yanzu da ilimi da bincike na masana yake ta gano irin alfanun da zogale yake da shi. Domin ba wai ganyansa da muke ci ba, saiwarsa da itacensa da kwayoyinsa duk abubuwa ne masu matukar amfani da kara lafiya. Ana yin shayinsa a sha ko a tafasa shi a sha, yana maganin ciwuka irinsu shawara basur da sauransu.

Masana sun gano cewa Zogale yana dauke da sinadarin Betamin A wanda ake samu a jikin karas har sau 10, sannan yana dauke da kashi 17 na sinadarin da ake samu a jikin madara, sannan kuma yana dauke da kashi 5 na sinadarin betamin C wanda ake samu a jikin lemon zaki da dangoginsa da kuma kashi 15 na sinadarin da ake samu a jikin ayaba, dukkan wadancan sinadarai zogale ya hadasu shi kadai.

Saboda irin yadda bincike ya tabbatar da sahihancin magungunan da zogale yake yi ya sa kasashen Thailand da Malaysiya da Meziko da Kambodiya da Indonisiya da Afurka ta kudu da sauran kasashe da dama suka maida hankali sosai wajen nomansa da sarrafashi domin amfanin jama’a. Lallai muma bai kamata a barmu a baya ba, lallai mu tuntubi masana domin sanin irin alfanun da zogale yake da shi domin cin moriyarsu.
Yasir Ramadan Gwale

Thursday, December 6, 2012

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN


BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN



Ya maigirma shugaban kasa ina fatan wannan wasika tawa zata sameka cikin Aminci, Ina kuma fatan zaka samu zarafin karanta wannan wasika tawa. A matsayina na dan Najeriya na halaliya  ina ganin ina da hakkin yin kira a gareka dan gane da wani mataki mai cike da hadari da gwamnatinka ta dauka. Ko shakka babu wannan mataki bai kamaci wannan gwamnati taka ba, domin lamarine da ba zai haifarwa da kasar nan da mai ido ba. Ina mai cike da masaniyar cewa kana da mashawarta wadanda aikinsu ne su baka shawara kafin daukan dukkan wani mataki ko yanke dukkan wani hukunci, domin a matsayinka na shugaban kasa dole ka ringa tuntubar mashawartanka domin samun shawara ta gari kafin zartar da dukkan irin wani hukunci. Haka kuma, ina mai cike da masaniyar cewa mafiya yawan masu baka shawara ba al'ummar kasarnan ce a gabansu ba, illa kawai suna baka shawarane bisa san ransu da san zuciyarsu, sama da doraka akan turba sahihiya wadda zata yi maka jagorar samun nasara.

Ya maigirma shugaban kasa, bayan wannan abin Ashsha da ya faru na kai harin bom a coci dake cikin barikin sojoji a Jaji, shugaban hafsan sojojin Najeriya Adimiral Ola Saad Ibrahim ya bayar da umarnin sauke wasu manyan sojoji daga mukamansu a barikin soji dake jaji. Wadannan mutane sune Air Vice Marshal Abdullahi Kure da Manjo Janaral Muhammad D Isa. A matsayinka na shugaban kwamandan rundunar askarawan sojojin Najeriya, nayi Imani babu yadda za'a dauki irin wannan mataki mai matukar hadari ba tare da kana da masaniya akai ba, na tabbatar baza'a kasa tuntubar mashawarta ba kafin daukar wannan mataki mai cike da hadari, ko dai an baka wannan shawarar da gayya ne koma meye, lallai wannan wani muhimmin batu ne da ya kamata shugaban kasa ya yi masa karatun ta nutsu. Amma dai abu mafi muhimmanci shine yadda korar wadannan mutane zai iya haifar da gagarumar baraka a wannan kasa, wanda zan zayyano su kamar haka:

Abu na farko, wadannan manyan sojoji an sauke su ne daga mukamansu ba tare da wata kwakwkwarar hujja ko wani dalili gamsashshe ba. Yana da kyau ace anyi taka tsan-tsan sosai wajen daukar irin wannan mataki, domin sanin kowa ne Najeriya kasace da take a cikin wani irin wadi da ya yi kama da na tsaka mai wuya, sannan kuma Addini da kabila suna taka muhimmiyar rawa a dukkan wasu bangarori dangane da yadda ake tafiyar da wannan kasa. Ko wanne irin yanayi ko hali ake ciki alhakin shugaba ne ya tabbatar da hadin kan wannan kasa tare da kaucewa dukkan wani abu da zai iya kawo zaman doya da manja ko yamusta kasar.

Abu na biyu, dukkan wadannan manyan sojoji da aka cire daga kan mukamansu gaba dayansu Musulumi ne, sannan aka yi gaggawar maye gurbinsu da Kiristoci. A bisa tsarin aiki ana iya canzawa mutum wajen aiki ne a duk lokacin da bukatar haka ta taso, kuma a matsayinka na shugaban kasa kuma shugaban rundunar tsaro ta Najeriya lallai akwai bukatar yin la'akari da halin da kasarnan take ciki na sukurkucewar al'amuran tsaro kafin daukar wannan mataki. Domin har yanzu bamu gama farfadowa daga mawuyacin halin da muka shiga ba tun bayan rikicin da ya biyo bayan sakamakon zaben 2011 da ya gabata. Lallai shugaban kasa ya kamata ya yi aiki da lura musamman wajen sauya Musulmi da wanda ba musulmi ba, musamman waje irin wannan mai cike da kalubale, domin daukar irin wannan mataki abu ne da zai iya tayar da kura da yamusta hazo.

Abu na uku, maye gurbin wadannan manyan sojoji musulmi da kiristoci a cikin irin wannan mawuyacin lokaci da muke ciki na gaba kura baya sayaki, kamar yadda muka karanta a shafukan jaridu cewa yanzu maganar da ake yi Barikin sojoji dake jaji ta dawo karkashin kulawar kiristoci tun bayan sauke Air Marshal Abdullahi Kure da Manjo Janar Muhammad D Isa, ina son shugaban kasa ya kwan da sanin cewar tabbas wannan wani mataki ya dauka na wargatsa kasarnan domin shugabanni na addini da shugabanni na al'umma bazasu zura ido suna kallon irin wannan abun yana faruwa ba, kuma za'a ringa kallon wannan a matsayin wani mataki na kakkabe hannun duk wasu musulmi daga Manyan ayyuka musamman irin wannan mai matukar muhimmanci a wannan lokaci da muke ciki.

Ya maigirma shugaban kasa, Babban dalilin rubuta maka wannan wasika, da kuma buga maka wadannan misalai da na kawo shine, domin na ja hankalinka akan wata guguwa da ka iya kunno kai a tsakanin rundunonin sojin kasarnan, musamman tsakanin Musulmi da Kirista. Tabbas sojojin Najeriya suna cikin wani hali da muke fatan samun tabbataccen hadinkai a tsakanin rundunonin sojin dake wannan kasa. Domin a baya lokacin da kasarnan ta samu kanta a cikin wani mawuyacin hali, wadannan sojoji sune suka sadaukar da rayuwarsu wajen tabbatar da dorewar wannan kasar, sun taka muhimmiyar rawa a yakin basasar kasarnan wajen maido da ita kasa daya al'umma daya. Sojojinmu ba wai kawai kokarinsu iya Najeriya ya tsaya ba, sun taimaka gaya wajen dawo da doka da oda a kasashe makwabta da dama, misali, kasar kwango a shekarar 1950, da kuma kasar Saliyo da Laberiya a shekarar 1990, haka kuma yanzu haka sojojinmu suna aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Darfur. Amma abin da yafi kowanne muhimmanci wanda sojoji suka yi shine kauda kansu daga al'amuran siyasa da sukayi tun bayan da mulki ya komo hannu farar hula a shekarar 1999, shakka babu wannan shine lokaci mai tsawo a tarihin kasarnan wanda aka samu dogon lokaci ana mulkin siyasa ba tare da samun wani tsaiko daga soja ba. Haka kuma, duk da halin rashin tabbas da aka shiga a kasarnan lokacin rashin lafiya marigayi shugaban kasa Malam Mumaru Musa 'YarAdua soja sun kauda kai daga shiga al'amuran siyasa, inda suka yi zamansu a cikin barukokinsu, wannan ce ta baka damar zama mukaddashin shugaban kasa a wancan lokaci, har kuma daga baya ka zama shugaban kasa mai cikakken iko lokacin da mutuwa ta yiwa marigayi YarAdua yankan hanzari. A wancan lokaci duka sojojin kasarnan Musulmi da Kirista sun yi aike tare wajen ganin lamura basu lalace ba, kuma an samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu. Tabbas shugaban kasa zai iya daukar wani muhimmin darasi dangane da wannan abin da ya faru.

Daga karshe, Ya maigirma shugaban kasa, ina mai baka shawara ka guji dukkan wani abu da zai iya yamusta kasarnan musamman ta fuskar soji, domin sakamakon abinda zai biyu baya ba zai zama mai kyau ga al'ummar kasarnan ba. Kuma ina fatan shugaban kasa zai yi duba na tsanaki dangane da abinda ya faru a kasarnan tundaga shekarun 1960 har zuwa shekarun 1970 sannan ya duba irin darauusan da suke cikin wannan zamani da kuma kallon irin yadda al'amura zasu wakana nan gaba. Ina kuma fatan shugaban kasa ya tattauna sosai da magabatansa domin samun sahihan bayanai dangane da harkar soji a Najeriya.

Allah ya taimaki Tarayyar Najeriya.

Wannan wasika na samota ne daga wajen Dr Muhammad Jameel Yusha'u, wadda ya rubuta da turanci domin amfanin wadan da basu samu zarafin karanta ta turancin ba.

Yasir 
Ramadan Gwale.
yasirraramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com/

SANUSI LAMIDO SANUSI: BAZAN DAINA MAGANA BA


SANUSI LAMIDO SANUSI: BAZAN DAINA MAGANA BA

Gwmanan Babban Bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi ya mayar da martani a jiya dan gane da masu sukarsa akan kalaman da ya yi a makon da ya gabata. A makon da ya gabata dai an ruwaito Sanusi Lamido yana cewa kusan kashi 70 na dukiyar kasar nan gwamnati take kashewa kanta, yayin da ake kashewa al’ummar kasa kashi 30 kacal, ya ce tattalin arziki zai bunkasa ne idan aka zabtare kashi 50 na masu karbar dirka dirkan albashi.
Tun bayan da Sanusi ya yi wadancan kamalamai ne ake ta mayar masa da martani kama daga ‘yan majalisar tarayya da kungiyoyin kwadago da sauran al’umma. Inda suke ta kira ga gwamnati akan lallai ta sallame shi daga Babban banki.

Amma sanusi da ya yi jawabi a wajen taron National Econmic Summit ya mayar da martani akan masu sukar kalamansa. Ya ce shi kam ba zai taba daina magana ba, dole ne na cigaba da yin fashin baki akan tattalin arziki inji shi. Zan ta yin fashin baki akan sha’anin tattalin arziki har sai naga al’amura sun daidaita. Kuma Ina son jama’a su fahimta daman ni aikina ba yana nufin kullum na saka jama’a cikin farinciki bane. Duk mai bukatar farin ciki da annashuwa ta ya tafi wajen iyalisan su kashe dare. Dan haka jama’a su sani aikina shine na gano yadda tattalin arzikin kasarmu zai samu bunkasa. Ai daga lokacin da muka daina magana saboda tsoron kada a kalubalance mu, to daga wannan lokacin tattalin arzikinmu zai shiga cikin halin ha’ula’i.

Sanusi Lamido ya zargi kundin tsarin mulkin Najeriya da cewa ya sanya al’umma cikin mawuyacin hali ta hanyar sahalewa da masu rike da mukaman siyasa masu yawan gaske, wadan da suke karbar dirka dirkan albashi da alawus ba tare da sunyi wani aiki na ku zo mu gani ba. Dan haka wadannan wasu matsaloli ne da dole mu kalubalance su, kuma mu samo hanya sahihiya da za’a fita daga cikin al-mubazzaranci da dukiyar kasa. Yana da kyau mu fahimta gwamnati ba wai kawai tana biyan ma’aikata albashi bane. Muna da kananan hukumomi 774 kowacce daga cikinsu tana da shugaba da mataimaki da akalla kansiloli 10, shin nawa kake jin yake tafiya wajen hidimta musu?

Bari mu buga misali da jihar kano, idan ka dauki tsohuwar jihar kano, yanzu ta zama Kano da Jigawa. Lokacin da tana a matsayin jiha daya tana da gwamna daya da mataimaki da kwamishinoni akalla ka ce goma, amma yanzu fa? Waccan jihar guda daya ta zama biyu, dan haka kana da gwaman biyu mataimakin gwamna biyu, idan da kwamishinoni 10 ne yanzu sun zama kusan 40 da ‘yan majalisu sama da 80, masu bada shawara da mataimaka na musamman kuwa ALLAH ne kadai ya san yawan wasu.  Nawa kuke zaton ana kashewa wajen yiwa wadannan mutane hidima? Maganar ba wai ta kungiyar kwadago ko majalisa bace, muna maganar ‘yan Najeriya ne kusan miliyan 167. Dan haka wannan kundin tsarin mulki da muke amfani da shi, kwata kwata baida wata ma’ana, ga al’ummar kasa.

Kundn tsarin mulki yayi tanadin cewa dole ne kowace jiha a fadin tarayyar Najeriya ta samu minista guda daya wanda zai wakilce ta. Bari na tambayi masu ilimi, shin meye alakar minista da jiharsa? Wannan yana nuna kenan idan kana da jihohi 50 dole ka samu ministoci 50, haka kuma, idan kana da jihohi 100 dole ka samu ministoci 100 ko shakka babu wannan dirkaniyace a cikin kundin tsarin mulki. Me ya sa mu kadaine muke da irin wannan a duk fadin Nahiyar Afurka?

Malam Sanusi Lamido ya kara da cewa hakkin gwamnati ne ta kula da dukkan bukatun al’ummarta. Yanzu idan har za’a ce gwamnati na kashe kashi 70 na kudin kasa wajen yiwa kanta da ma’aikatanta hidima, sannan ta kashe kashi 30 kacal domin al’ummar kasa, shin korar Sanusi daga aiki zai zama masalaha kenan? Yanzu ‘yan majalisa suna gyaran kundin tsarin mulki, bamu da bukatar ‘yan majalisa 500 domin su yi doka. Ya kara da cewa wata babbar matsala da Najeriya take fuskanta bayan cin-hanci ita ce rashin mutane na gari a matsayin shugabanni. Ba'a yin k’mai bisa doka, am maida komai ya zama kabilanci da bangaranci, ga mutane da suka cancanci a basu wasu muhimman ayyuka da zasu hidmtawa al’umma amma sai a kauce musu saboda bambancin kabila.

Kuma ina kalubalantar ku kanku ‘yan Najeriya mai makon jama’a su mayar da hankali wajen tattauna muhimman al’amura da suka shafi cigaban wannan kasa sai suka bige da tattauna wace irin mota wane yake shiga? Ina wane yake zuwa? Me ya sa bazamu maida hankali wajen tambayar kanmu shin titi mai tsawon kilomita nawa aka gina mana a yankunanmu ba? Me ya sa bazamu maida hankali wajen tattaunawa akan me ya sa haryanzu wutar lantarki bata samu ba? Shin yara nawa ne suka samu nasarar cin darasin Turanci da Lissafi a makarantun sakandare! Lallai muna da babban kalubale kuma muna da babbar matsala agabanmu.

Wednesday, December 5, 2012

RISALA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNA: Engr (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso FNSE


RISALA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNA: Engr (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso FNSE

Bayan Sallama irin ta addinin musulunci, Assalamu Alaikum, Ya maigirma Gwamna, ina son nayi amfani da wannan damar wajen yabawa tare da jinjina a gareka bisa namijin kokari da gwamantinka ta yi wajen samarwa da yankinmu na Arewa maso yamma jami’a wadda aka radawa sunan yankin, hakika wannan wani babban ci-gaba ne kuma abin a yaba, mun gode maigirma gwman, haka kuma, sauran kwalejojin da aka kirkiro ko ake kan kirkirowa wannanma wani babban al’amari ne kuma abin a yaba, sannan uwa uba, ga dimbin al’ummar kano da aka dauka aka kaisu kasashen da dama domin karo ilimi wannan ma wani muhimmin ci-gabane ya maigirma gwamna muna yabawa tare da fatan alheri. Sannan kuma, dole mu gode tare da yabawa musamman yadda gwamnati ke ci-gaba da kawata cikin birnin kano, da kunna fitulu a manyan tituna, da tsabtace gari, duk wannan abun a gode ne kuma abin a yaba.
Ya maigirma gwamna, Ina mai amfani da wannan damar wajen yin fatan alheri a gareka da kuma gwamnatinka. Hakika Ya maigirma Gwamna wannan wani muhimmin al’amari ne akanka a matsayinka na shugabanmu kuma jagoran jihar kano, ina fatan ALLAH ya sa ka gama da wannan shugabanci lafiya. Ya maigirma gwamna na kira wannan sako nawa zuwa gareka da sunan RISALA wanda asali kalmar larabci ce, wadda take nufin SAKO, ina fata sakona ya isa zuwa gareka cikin aminci.

Ya maigirma gwamna a ranar 21 ga watan Nuwamban da ya gabata, a shafinka na facebook ka saki wani sako kamar haka “Mu duk wata sarauta ta gado muna yinta, amma sarauta ta kale ba ruwanmu da ita, mu duk wani nadi da baka gajeshi ba sunansa TUKUNKUNJI” wannan shine sakon da ya fito daga shafinka a wannan rana, inda kuma ya ja hankalin mutane da yawa. Ya maigirma gwamna, kai shugabane kuma jagora ne na duk al’ummar Jihar kano walau ‘ya ‘yanta ne ko baki, duk mutumin da yake kano karkashin ikonka yake. Ya maigirma Gwamna, hakika wannan magana da ta fito ta shafinka magana ce ta kananan mutane bayan kuma mun san kai ba karamin mutum bane.

Ya maigirma gwamna, duk wani mutumin kano na haliliya yana girmama masarautar kano. Duk wata sarauta da mai martaba sarki ya bayar ga kowa ye, muna kyautata zaton cewa mai martaba sarki ba zai baiwa mutumin banza sarauta ba, haka kuma, duk wata sarauta da wani ke da ita a jihar kano indai masarauta ce ta bashi muna kallon masarauta ne ba shi mai rike da sarautar ba. Ya maigirma gwamna akwai al’amura da yawa a gabanka wadanda ya kamata su dauke maka hankali sama da kankananan maganganu irin wadannan. Ya maigirma Gwamna, dukkan gwamnonin Najeriya 36 kai yayane a garesu domin lokacin da ka zama gwamnan farar hula a zangonka na farko, wasu daga cikinsu ko ritaya daga aikin gwamnati basu yi ba, abin da muke fata, Ya maigirma gwaman, shine ka zame musu alkibla kuma jagora, kamar yadda Jihar kano ta yiwa sauran jihohi zarra a fadin tarayyar Najeriya, haka muke fatan ka yi zarra a tsakanin takwarorinka gwamnaoni.

Ya maigirma gwamna, duk wani mutumin kano burinsa jihar kano ta ci gaba ko da kuwa waye yake rike da akalar gwamnati a jihar kano. Col. Dominc Oneye ba Bahaushe bane karewa ba ma Musulmi bane amma ya bautawa jihar kano da al’ummar jihar kano, haka muke fatan duk wani mutum da zai hidimtawa jihar kano ko waye kuma ko daga ina yake matukar zai kiyaye da yanayinmu da addininmu, Ya maigirma gwamna, hakika muna kyautata maka zaton cewa kai me kishin jihar kano ne da kuma son ci-gabanta da al’ummarta, kuma Alhamdulillah babu abinda zamu ce sai ala-san-barka.

Ya maigirma gwamna, a kwanakin baya kayi wata muhimmiyar magana wadda ta tayar da kura musamman a majalisarku ta gwamnonin Najeriya, wannan magana ta rabon arzikin kasa, da kuma batun man da ake hakowa a cikin teku da kuma man da ake hakowa a tsandauri (off-shore On-shore Dichotomy), Ya maigirma gwamna lallai wannan magana da ka kawo kuma da yawa daga cikin gwamnoni ka motsasu dangane da wannan batu, irinsu muke fatan ji daga bakinka a koda yaushe, domin kare martabar yankin Arewa da al’ummar Hausawa, amma Ya maigirma gwamna, yawan maida martani ga Babban abokinka kuma Amininka tsohon gwamna Malam Dr. Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, wannan ba girmanka bane Ya maigirma gwamna. Malam Shekarau ya yi gwamna a Kano kuma ya bautawa jihar kano tsahon wa’adinsa, fatanmu shine ku kasance abokai kuma aminan juna kasancewar kun hidimtawa al’ummar jihar kano.

Ya maigirma gwamna, a har kullum a rayuwa bama fatan a ce jiya tafi yau, domin wannan shine ma’auni da yake nuna rashin ci-gaba, kullum fatanmu a ce Yau tafi Jiya. Batun da ake ta yawan yi na cewa gwamnatin da ta gabace ka ta Aminika, kayi aikin da bata yi ba a cikin shekaru takwas, wallahi kullum fatanmu shine na-gaba ya fi na baya, idan har kullum zamu ringa cewa na baya yafi na gaba lallai babu ci-gaba, dan haka fatanmu shine gwamnatinka ta yi sama da abinda gwamnatin baya bata yi ba, kamar yadda muke fatan duk gwamnan da zai biyo bayanka ya yi sama da abinda ka yi, wannan shine zai daukaka martaba da kimar jihar kano.
Ya maigirma gwamna, babbar matsalar da take damun al’ummar jihar kano bata wuce matsalar tsaro da zaman zullumi da jama’a suke ciki ba. Ya maigimra gwamna lallai kamar yadda kake da labari kuma ka sani al’umma suna cikin hali na rashin kwanciyar hankali da zaman zullumi wanda yau Takai mutum hatta a cikin gidansa ba shi da kwanciyar hankali kasancewar yana tsoron ko za’a iya jefo masa wani abu da zai halaka shi nan take, Ya maigirma Gwamna nemo hanyar da za’a magance wadannan matsaloli sune abinda suka kamata su daukewa gwamnatinka hankali, ba maganganu irin na hamayya ba, hakika kamar yadda muka sani kuna yin kokari akan haka, fatanmu kuma shine ku kara kokari akan kokarin da kuka yi a baya.

Ya maigirma gwamna, Lallai babban abinda mu al’ummar jihar kano muka dogara da shi shine kasuwanci (saye da sayarwa) lallai makiya da mahassada suna ta yin aiki babu dare babu rana wajen kassara kasuwancinmu, domin yanzu duk kasuwanninmu sun rage lokacin tashi, kasancewar mafiya yawansu matasa ne, masu amfani da kananan ababen hawa, ga kuma dokokin da aka sanya saboda su, lallai ya maigirma gwamna a duba wannan lamari da halin da al’umma suke ciki, domin wani ya fito kasuwa ana kiran sallar la’asar kuma za’a fara tunanin tashi daga kasuwa wanda ko shakka babu wannan gurgunata kasuwanci ne ainun.

Daga karshe, Ya maigirma gwamna ina fatan alheri a gareka da gwamnatinka. Ina kuma yi maka addu’ah ta musamman tare da tawassuli da sunayan ALLAH tsarkaka madaukaka ALLAH ya sahale maka gamawa lafiya da mulkinka, ALLAH ya yi maka jagora a dukkan lamuran rayuwaka, sannan ina fata Ya maigirma gwamna yawan kalamai na hamayya da suke fitowa daga bakinka zasu samu raguwa, duk da cewa ba laifi bane idankayi hakan a siyasance, amma muna ganin girmanka da kimarka ya wuce a ji wasu kalaman daga bakinka. Ya maigirma gwamna ina mai yi muku fatan alheri da fatan gamawa da duniya lafiya kai da Babban abokinka kuma Amininka Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano. ALLAH ya taimaki Jihar Kano ya bamu lafiya da zama lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

Tuesday, December 4, 2012

ME KA SANI DAN-GANE DA HALITTAR RAKUMI


ME KA SANI DAN-GANE DA HALITTAR RAKUMI

Rakumi daya ne daga cikin dabbobin ni’ima guda huda da ALLAH ya yi yiwa musulmi nuni izuwa garesu domin yin lallai ko hadaya. Rakumi wata dabbace da ALLAH ya halitta ba domin kawai a yanka a ci ba, rakumi kan yiwa mutane hidima da dawainiya, ALLAH ya halicci mafiya yawan rakuma a yanki mai cike da sahara, yanki mai zafin rana. Yankin gabas ta tsakiya kusan nanne madinar Rakuma domin ALLAH ya halicci miliyoyin rakuma a wannan yanki haka kuma yankin Arewa wacin Afurka nanma akwai rakuma masu yawan gaske, kasar Somaliya kusan ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan rakuma a yankin da ake kira kahon Afurka. Haka kuma, akwai wasu miliyoyin rakuman a yankin Asiya mai nisa wato kasashen Azarbaijan da Tajikistan da Turkuminstan da Uzbakistan da Kyrgistan suma suna da tarin rakuma masu yawan gaske, daga nan kuma sai Arewaci da kudancin Amerika wanda rakumansu kalilan ne sosai.

Rakuman da suke a yankin Sahara sun sha bamban da rakuman da suke a yankin Asiya mai nisa musamman a wadancan kasashen da muka lissafa. Rakumansu ba kamar sauran rakuma bane na gabas ta tsakiya ko Arewacin Afurka, rakuma a yankin suna da yalwar gashi mai yawa kasancewar yanki ne da suke da yanayi na dusar kankara mai yawan gaske, dan haka mafiya yawan dabbobinsu suna da gashi mai yawa a jikinsu, haka suma rakumansu suke. Amma bayananmu zasu fi karkata ne zuwa ga rakuman da suke rayuwa cikin sahara.

Rakumi yana iya yin gudu na tafiyar kilomita 65 a cikin awa guda ba tare da ya gajiya ba. ALLAH mai girma da daukaka ya sanyawa rakumi juriya wajen tafiya, domin a mafi yawancin lokuta sai dai mai jan rakumi ya gaji ya huta amma ba dai rakumin ya gaji ba. Haka kuma, duk da irin wannan juriya ta rakumi sai ya dauki lokaci bai sha-ruwa ba, domin rakumi yakan iya kai watanni uku ba tare da ya sha ruwa ba, kasancewar ALLAH ya halitta masa wani tanki a cikinsa wanda yake adana ruwa. Rakumi yakan sha ruwa lita 200 kimamin galan 53 a cikin mintuna uku, rakumi na iya shan ruwan da ya kai lita 600 a lokaci guda.

ALLAH subhanahuwata ala ya halicci wasu dabbobi da hikimomi da baiwa mai yawan gaske, kamar yadda ya halicci kare zai iya sansano wani abu da aka boye ko gano inda aka boye shi, haka shima rakumi, idan yana bukatar ruwa yana iya sansano inda ruwa yake daga kimanin nisan mita 200, kamar yadda Shamuwa kan sansano zuwan damina, a wasu garuruwan da dama alamun zuwan ruwan sama ko damina shine ganin Shamuwa tana ya yawo domin tana jiyo alamar zuwan ruwa. ALLAH buwayi gagara misali.

Duk acikin dabbobin da ALLAH ya halatta cin su Rakumi ne dabbar da yafi kowacce kawaici da kunya da kuma sanin ya kamata. Rakumi yana da ladabi ainun domin yana bin duk umarnin da aka bashi baya kaucewa, kamar yadda duk inda aka aiki jaki zaije ya dawo ba tare da ya tsaya ba, haka shima rakumi yake, sannan yana daga cikin hikimar da ALLAH ya yiwa rakumi baya mantuwa ko da kuwa shekaru nawa zai dauka, rakumi baya manta uwarsa ko ubansa, sannan baya manta ‘yan uwansa ko abokansa, wannan ta sanya ko barbara zaiyi baya yi tare da ‘yan uwansa da suka fito ciki daya, sabanin sauran dabbobi irinsu akuya da rago. Haka kuma, kamar yadda sauran dabbobi irinsu mage suke da sabo da masu su haka shima rakumi yake da sabo da mai, domin sau da yawa rakumi yana yin kewar rabuwa da uban gidansa.

Rakumi kusan a cikin dabbobin da aka halattamana cin-su dan layya ko hadaya yafi kowacce dabba daukan tsawon shekaru a raye, domin rakumi yakan rayu tsawon shekaru daga 40 har zuwa 60. Sannan kuma, rakumi duk da irin jarumtakarsa ALLAH ya sanya kunama tana cin galaba akansa, domin duk cikin halittun ALLAH babu abinda rakumi yake jin tsoron gamuwa da shi kamar kunama, kasancewar kafarsa tana da taushi sosai kamar ta dan-Adam, wannan ta sanya rakumi yana iya hango kunama daga waje mai nisa, kuma muddin ya hangota to ba zai bi wannan hanyar ba.

Kamar yadda muka bayyana cewa Rakumi yana da hakuri sosai, sannan kuma yana da fada sosai idan aka shiga gomarsa. Kusan duk cikin dabbobin da makiyaya suke kiwo rakumi ne kada ba’a dukansa, domin na farko shi yasan ya kamata gwargwadon irin tarbiyyar da mai shi ya bashi, rakumi yana jin magana kamar mutum kuma yana bin dukkan umarnin da aka bashi, dan haka mai kiwon rakuma zai iya yin gaba ya bar rakumansa ya yi musu umarnin su sameshi a waje kaza kuma so sameshi. Rakumi duk mutumin da ya cuceshi sai ya rama komai tsawon lokaci, kuma rakumi yasan Yaro misali idan Yaro ya tsokaneshi baya damuwa kuma baya masa komai.

A dukkan dabbobin da ALLAH ya halitta Rakumi ne kadai dabbar da babu wani abu a jikinsa da bashi da amfani. Bayaga yanka shi da ake a ci nama,  ana amfanuwa da nononsa da fitsarinsa da kashinsa, wannan ya sa rakumi ya yi zarra a cikin dabbobi domin shi fitsarinsa ba najasa bane kuma ba haram bane. Haka kuma, ALLAH ya yi ishara dangane da yin tsinkaye dangane da rayuwar rakumi a cikin al-qur’ani mai tsarki a sura 88 aya ta 17.

Haka kuma, wasu masana sun tabbatar da cewa Rakumi ya taba rayuwa a wannan duniyar a shekaru sama da miliyan hamsin da suka gabata! Tsarki ya tabbata ga ALLAH da ya halicci rakumi, masanan sunce rakuman da suka rayuwa a wancan lokacin girmansu bai wuce na Akuya ba, sannan sun rayuwa a can a wani yankin kudancin Dakota a kasar Amerika kenan.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com