Friday, July 3, 2015

Sanata Muhammad Ibn Rabiu Ibn Musa Alkwankwasy: CIKI DA Gaskiya . . .


SANATA MUHAMMAD IBN RABIU IBN MUSA AL-KWANKWASY: CIKI DA GASKIYA .  . .

Tun bayan da Rabi'u Kwankwaso ya zama Gwamnan Jihar Kano a 2011 bayanai sukai ta fitowa daga Gwamnatin  da Kwankwaso ke Jagoranta cewar tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya saci kudi masu dumbin yawa a zamanin mulkinsa na shekaru takwas, Gwamnatin Kwankwaso ta yi ta karad'i akan wannan batu, aka kasa nuna daidai inda Malam Shekarau yayi almundahana.

Mai magana da yawun tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau wato Malam Sule Yau Sule ya nemi da cewar Gwamnatin Kwankwaso ta gurfanar da Malam Ibrahim Shekarau a gaban hukumar EFCC ko a kai shi kotu dan ya gurfana, amma karshe sai muka ji Gwamna Kwankwaso na cewar sun bar Malam Shekarau  da Allah. Wanda wannan ba komai ya nuna ba sai tsabar bita da k'ulli  da Hassada da akaiwa Malam Ibrahim Shekarau.

Domin indai gaskiya ake so kuma gyara aka zo da niyyar yi bai kamata a bari Malam Shekarau ya sha da kud'in al'umma ba, indai da gaske ne Gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso tana da masaniyar cewar Malam Shekarau ya kwashi kud'in al'umma ba bisa ka'Ida ba kuma aka barshi ya sha da kud'in jama’a to ba shakka Kwankwaso ya cuci mutanan Kano.

Kullum abinda muke kira shi ne cewar Gwamnati ta jama’a ce, kuma domin jama'a ake yinta,  dan haka babu yadda mutum zai yi Gwamnati ya kwashi kudin jama’a sannan a bar shi ya sha, ace masa je ka ka gani, ai ya gani tun anan! lallai ko waye a kamo shi ya dawo da hakkin jama’a tunda ba gadon gidan su bane.

Gwamnatin Kwankwas tayi ta maganganu na batanci akan Malam Shekarau da nuna cewar yana yiwa ma'aikatan Gwamnati da suka ci dukiyar al'umma Allah ya isa, amma suka kasa kasa nuna wadan da Malam din ya yiwa Allah ya isa, karshe suka b'ige da yiwa Malamin Allah ya isa.

Yau cikin ikon Allah gashi Gwamna Kwankwaso kuma sabon Sanatan Kano ta tsakiya yabar Gwamna amma yana ta guje guje da lab'e lab'e Kada a kama shi a bincike shi, tir kashi! Indai cikin Kwankwaso da gaskiya, kamata yayi ya kai kansa EFCC dan a wanke shi daga zargin da ake masa na almundahana da kudin tsaffin ma'aikatan Gwamnati na fansho. 

Gwamnan Jigawa Malam Sule Lamido da yasan cewar cikinsa da gaskiya babu wata wuk'ar EFCC  da zata huda shi, shi da kansa ya kai akansa ofishin EFCC  din kuma aka bincike shi dan tabbatar yayi sama da fad'I ko bai yi ba, babu ko Shakka Malam Sule Lamido ya nuna jarumataka da kuma nunawa duniya cewar shi ba b'arawo bane.

Dan haka abinda muke Fata ga Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon Gwamnan Kano Muhammad Ibn Rabiu Ibn Musa Kwankwaso ya yiwa Allah ya kai kansa EFCC domin a wanke shi daga dukkan zarge zargen da ake masa na wawure dukiyar al'umma. Wannan kuma babu abinda zai rage na daga ayyukan da Kwankwason yayi, domin su wadan da suka shigar da karar Kwankwaso a EFCC basu yi hakan dan nuna cewar bai yi aiki ba, illa suna ganin anyi zarmiya da dukiyarsu. 

Wannan abin da ya faru ya kara nuna mana hikimar Allah Subhanahu Wata'ala da bai sa Malam Salihu Sagir Takai ya samu Nasarar zama Gwamnan Kano ba a wannan lokacin, domin watakila da a karkashin Gwamnatin Malam Salihu  Sanata Kwankwaso ke wannan b'oye b'oye al'umma ba zata tab'a yarda cewar ba bita da k'ulli ake masa ba, sai gashi karkashin Gwamnatin Gwamna Gandujen Kwankwasiyya wannan abu ya bijiro.

Mu fatanmu shi ne hukumar EFCC ta yi bincike tun daga 1999 zangon farko na Gwamnatin Kwankwaso  da kuma zango biyu na Malam Ibrahim Shekarau  a cikinsu duk wanda ya dauki dukiyar al'umma ba bisa ka'Ida ba ya dawo da ita kuma ayi masa hukunci daidai da abinda ya aikata,  domin wannan shi ne gatan da za ai musu anan duniya, domin a Lahira akwai Shari'ah ta gaskiya da babu EFCC da ICPC babu Lauyoyi. 

Yasir Ramadan Gwale
02-07-2015

No comments:

Post a Comment