MALAM NUHU RIBADU NA IYA ZAMA SHUGABAN PDP NA KASA
Jaridar Leadership Newspapers ta ruwaito cewar tsohon Shugaban hukumar EFCC kuma tsohon dan takarar Shugaban kasa a Rusasshiyar Jam'in yar ACN Malam Nuhu Ribadu na iya zama sabon Shugaban jam'iyyar PDP na kasa nan gaba a babban taron PDP na kasa da zai gudana.
Ba shakka wannan labari ne mai faranta rai, samun mutum irin Nuhu Ribadu a matsayin shugaba zai baiwa PDP damar yaki da cin hanci da rashawa a cikin jam'iyyar, wanda hakan zai bayar da damar samun nagartattun 'yan takara wadan da basu ci amanar kasa ba. Allah ya taimaki Nuhu Ribadu a wannan sabon mukami da zai samu, Allah kai masa jagoranci ka bashi ikon kawo sauye sauye masu alfanu ga rayuwar al'umma.
No comments:
Post a Comment