Sunday, July 5, 2015

Gwamnatin Kano Ta Bar Farilla Ta Kama Yin Nafila


GWAMNATIN KANO TA BAR FARILLA TA KAMA YIN NAFILA 

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin sabon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta bayar da Umarnin rufe dukkan makarantun Gwamnati na Firamare da Sakandare a fadin Jihar Kano ba tare da an kai karshen zango na uku na karatu ba. Duk da cewar a tsarin kalandar karatu ta wannan Shekarar 2015, zango na uku (third term) zai zo karshe ne a ranar 10 ga watan Yulin nan.

Babban abinda da ya zo da mamaki shi ne yadda makarantu masu zaman kansu a fadin Jihar Kano suke cigaba  da aiki yayin da na Gwamnati suke a garkame, wannan ne ya ja hankalin wata kungiyar mai kwarmato bayanai ta duniya ta Kwarmato wannan batu, Sanusi Bature Dawakintofa​ shi ne wanda ya sanya hannu a madadin kungiyar.

Sakamakon bincike ya nuna cewar sabuwar Gwamnatin Kano, wai ba zata iya ciyar da daliban sakanadare dake makarantun kwana ba a fadin Kano baki daya a cikin wannan wata na Ramadan mai dumbin falala, sannan suma daliban Firamare da ake ciyar da su sau daya, suma Gwamnati ba zata iya ciyar da su ba, dan haka ne ya sanya Gwamnatin  daukar matakin kulle makarantun sabida karanci kudi.

Wannan babban abin mamaki ne da kuma takaici duba da yadda Gwamnatin ta ware Miliyoyin kudi domin rabawa mutane akan titi koko da kosai a wannan watan na Azumi, wanda wannan Farilla ne ba wajibi ba ne a gareta, amma ta saki wadan da suke Farali ne a gareta ta kama yin aikin Nafila. Misalin hakan, kamar mutum ne Yaki yin Sallar Isha ya kama yin Sallar Asham da zaton watakila Asham din tafi Lada.

Ko Shakka babu wannan abu da Gwamnatin Kano tayi tozarta Ilimi ne. Ta yaya za'a rufe makarantun Gwamnati wadan da 'ya 'yan  Talakawa suke karatu a yayin da makarantu masu zaman kansu da masu karfi kan iya kai 'ya 'yansu su kasance a Bude.  Wannan ko Shakka babu, durkusar da ilimi ne, da dakushe karatun 'ya 'yan talakawa. Hakan kuma, na bayyanawa duniya irin yadda wannan sabuwar Gwamnatin ta Kano sam bata damu da karatun yaran Talakawa ba.

Dan haka lallai muna kiran sabuwar Gwamnatin Kano ta mayar da dalibai makaranta, ko kuma a dakatar da karatun makarantu masu zaman kansu, alabashshi a tafi tare. Idan ba haka ba kuwa, an yiwa karatun yara mummunar illah a Jihar Kano. Kuma irin wannan ne, ke sabbaba mummunar faduwar jarabawar 'yan sakanadare ta WEAR da NECO. 

YASIR RAMADAN GWALE​
05-07-2015

No comments:

Post a Comment