Friday, July 3, 2015

Hadisin Abacha


HADISIN ABACHA 

An ruwaito wani hadisi daga tsohon Shugaban Kasa Marigayi Sani Abacha, wanda aka ce 'yarsa Gumsu ce ta ruwaito daga mahaifin nata, cewar "duk wani rikici da ya haura sa'o'i 24 Gwamnati batai maganinsa ba to akwai alamar tambaya akanta". Gaskiya ban san Inganci Isnadin wannan hadisi ba. Amma dai babu shakka a baya zamanin shudaddiyar Gwamnatin Goodluck Jonathan an bayar da fatawa sosai da hadisin kuma mutane da yawa sun yi ammana da wannan fatawa.

Shin tsakani da Allah har yanzu mutane suna da tunanin cewar babu wasu Boko Haram Gwamnati ce da ta shude ke iya-shegenta da sunan Boko Haram, ko kuwa da dama sun dawo daga rakiyar waccan fatawa ta Hadisin Gumsu? 

Yana da kyau mu fahimci gaskiya dangane da Boko Haram, sannan mu gayawa kanmu gaskiya. Shin mutanan da aka kashe jiya a Masallaci a Borno suna Sallah su waye suka kashe su? Shin har yanzu muna kore hannun Boko Haram akan irin wannan ta'annati da tunanin cewar Musulmi ba zai iya kashe Musulmi ba? Duk inda za'a je a dawo sai an komawa gaskiya idan ana san gaskiya.

YASIR RAMADAN GWALE
03-07-2015

No comments:

Post a Comment