WAYAR SALULA DA INTERNET SUN ZAMA ALAKAKAI
Yana daga cikin alkhairan da mu al'ummar wannan zamani muka samu shi ne na wayoyin salula da internet da suka saukake mana al'amura. Kusan yanzu komai mutum zai iya yi da wayarsa, ya shiga duniyar gizo ya wataya. A da wani abun idan ya faru a garinaku da safe karfe goma ba zaka sani ba watakila sai lokacin BBC ko wata kafar watsa labarai ta waje, amma yanzu cikin sauki mutane na samun dukkan irin labarin da suke so dake faruwa ko ina a duniya.
Yanzu halin da ake ciki wayar salula ta kashe kasuwar abubuwa da yawa. Yawan masu amfani da computer ya ragu, domin yanzu duk abinda computer zatai maka wayar salula ma zata iya, sai fa kadan. Yanzu babu bukatar ka jibge tarin kasakasan Radiyo dan jin wa'azi ko disco. Kasset 100 ko 200 da zaka ajiye ya cinye maka guri yanzu dan karamin abu da bai wuce maballin riga ba zai kwashe su duka.
Idan ka kalli wancan janibi sai kaga wayar salula ta kawo nakasu ga kasuwar Radiyo da Computer da kuma masu sana'ar sai da kaset na kida ko na wa'zai. Domin abinda sai ka saya da kudi a da yanzu kusan a bagas zaka same shi, wajen wanda baka sanshi ba be sanka ba, wuyarta kawai kana da Internet.
Kwanaki dan uwa Malam Hamisu Nasidi Baban Auwaab yake bamu labari cewar, suna zaune bayan sun gaida kakarsu sai kowa ya koma gefe ya dauko waya yana latse latse, abinda kakar ta ce musu "ku matasan yanzu bakwa yin lazimi sai latse latsen waya" a hakikanin gaskiya lokacin da naga wannan magana ta tsaya min a Rai, domin yadda naga yadda muke amfani da wayoyinmu abin na neman zamar mana alakakai.
Kusan yanzu abinda muke fara yi daga tashinmu daga bacci shi ne danna waya, haka kuma abu na karshe da galibi muke yi shi ne danna waya. Da yawa tuni suka dena yin Azkar na safe da yamma, kai yanzu hatta azkar na bayan idar da Sallah wasu sun dena, sabida gaggawa mutum ana idar da Sallah zai dauko waya yana duba Whatsapp ko Facebook da sauransu, kuma wannan lamari babu batun su wane, kusan duk munyi tarayya da Limamai da masu bin Sallah da kowa da kowa.
Wayar salula ta ragewa mutane yawan magana. A da sai kaga mutane sun hadu ana tattaunawa, amma yanzu daga an gaisa sai kaga kowa ya dauko wayarsa yana latsawa, hatta a makabarta wajen binne gawa sai kaga mutane na daddanna waya, haka wajen makoki ko gidan biki da sauransu. Wayoyin sun dauke mana hankali da lokaci fiye da yadda muke tsammani.
Mutane hatta abinci basa iya ci a nitse sai suna danna waya, sabida kowa baya san wani abu ya wuce masa.Aboki sai ka je wajensa amma idan kai lissafi sai kaga yawan danna wayar ku yafi yawan maganarku. Rayuwarmu ta zama kowa ba shi da lokaci, da yawan mutane suna Ikirarin karancin lokaci amma a zahiri lokacin duk yana wayoyinsu.
Gaskiya dai ga wasu waya ta zamar musu alakakai. Domin hatta sirri yanzu mutane ba su da shi sosai, domin wani ko ina za shi sai ya rubuta ya sanar, kai wani ko bandaki yake sai kaga ya dauki hoto ya sa a facebook wasu kagansu adakin girki wani a can cikin daki zaka ga ya dau hoto,mata kuwa suyi ta abinci yana konewa sabida waya.
Ni kaina na sha dora girki abincin ya kone sanadiyar dannan waya, wannan ya faru yafi karfin lissafi. Gaba dayan lokutanmu suna Whatsapp da facebook da Twitter da sauransu. Kuma abin mamakin irin wadannan tashoshi na haduwarsa mutane kullum sabbin ake kirkirowa wani zaure idan ka shiga sai kayi zaton babu kowa, amma sai kayi rajista ka shiga kaga jama’a dankar na ta watayawa.
Lallai ya kamata mu farga kan yadda babu gaira babu dalili aka dauke mana lokaci. Dalibai basa iya tsayawa suyi karatu da kyau, Malamai basa iya karantarwa da kyau, Kaga Malami na danna waya dalibai ma na dannawa ana shiga shafukan zamunta. Kuma hatta a lokacin Jarabawa duk da gargadi da ake amma sai ka samu wasu suna duba Whatsapp ko Facebook, zakai mamaki mutum ya rubuta cewar yanzu haka ina dakin jarabawa ina neman addu'ar ku.
Wani yace yanzu hatta hadari idan ya faru maimakon mutane sukai agaji, kawai sai su fara daukar hotuna. Kaga kawai mutane na yada hotuna na tashin hankali dan kawai suna san bada labarin wani hadari da ya afku, musamman wannan lokacin da Allah ya jarrabemu da tashin Bom mutane daga zarar Bom ya fashi a inda suke, to sun samu aikin daukar Hoto ana yadawa, a wani hoto da na gani a Gombe da wani Bom ya tashi ga mutum ya a kone da ransa amma naga mutane ba ta shi suke ba daukar too kawai suke.
Yana da kyau mu karawa kanmu lokacin kara kusanta ga Allah. Allah ka shiryemu.
Yasir Ramadan Gwale
29-07-2015