Thursday, July 24, 2014

Gaskiya Daya Ce

GASKIYA DAYA CE

Mu 'yan Arewa muna addu'ar Allah ya yi mana maganin abubuwan da suke faruwa na tashe-tashen Bama-bamai, amma a gefe guda kuma mun kauda kai daga ainihin masu laifi muna jingina laifi ga Goodluck Jonathan da cewa shi ne yake kashe 'yan Arewa, su kuma 'yan Kudu suna ganin duk dan Arewa dan BH ne, a gefe guda kuma su 'yan Boko Haram da na yi Imani sune suke aikata wannan ta'addancin mun kauda kai daga garesu suna ta cin karensu babu babbaka.

Wallahi matukar muka cigaba da juya baya ga gaskiya haka zamu wayi gari sun mamaye ko ina da hare-harensu, tunda muna kauda kai a garesu. Indai da gaske muke fatan karbuwar addu'armu akan abubuwan da suke faruwa dole mu nemi inda gaskiya ta ke dan ayi amaganin wannan al'amari. Ta yaya ido yana ciwo ana cewa laifin kafa ce sannan a yi zaton samun waraka? Ya zama dole mu gayawa kanmu gaskiya, ga inda laifi yake, ga inda matsala ta ke muna ji muna gani amma muna yin buris da cewa ba hakan bane.

Yakamata mu ajiye duk wani batu na Siyasa mu fuskanci gaskiyar abubuwan da suke faruwa, rayukan al'ummarmu suke salwanta dare da rana. Duk wanda ya kalli Video da Sahara Reporters suka sanya na sojan Air Force mai suna Umar Abubakar da su 'yan BH suka kama suka yanka, zai tabbatar da cewa abinda ke faruwa sune suke aikatawa, domin su basu yarda cewa Muluncin da muke yi gaskiya ba ne, a wajensu duk wanda ya saba da aqidarsu dagutu ne jininsa ya halatta. Tayaya mutanan da suke da irin wannan ra'ayi da tunani da suka yi imani su mutu akansa, zasu tausayawa al'umma?

Indai gaskiya muke nema dole mu nemi inda ta ke, idan kuma zamu cigaba da kauda kai ga masu laifi, to babu shakka har jikokinmu zasu bamu labari ko bayan ranmu na irin abinda ke faruwa. Wasu da yawa kanyi tambayar wai a ina su 'yan BH suke samun makamai da kudade. Wannan tambaya ce mai kyau, amma kuma an manta cewa duk kumgiyoyin 'yan Ta'adda irinsu Al-Qaida da Alshabab da Hizbola da sauransu duk jirgi daya ya kwaso su da BH inda suke hanyarsu duk iri daya ce. Shi Shedan ai danginsa yawa garesu kuma sashinsu na taimakon sashi.

Yasir Ramadan Gwale
24-07-2014

No comments:

Post a Comment