AZUMIN OBAMA:
A yau jaridar The Citizen ta kasar Sudan ta ruwaito cewar shugaban kasar Amurka Barack Obama
yana Azumi kuma yana gayyatar dukkan al'ummar Musulmi zuwa fadar White
House domin yin buda baki da shi. Obama na yin azumi ne dan taya
al'ummar Musulmi murnar shigowar watan Ramadan mai alfarma. Obaman yace
ba wannan ne karon farko da ya taba yin azumi ba, kuma zai buda baki da
Dabino ne da bakin ruwa kamar yadda Musulunci ya koyar.
Sai dai a wata sanarwa da kungiyar al'ummar
Larabawa ta kasar Amurka mai suna American-Arab-Anti Discreminiation
Committee fitar ta yi kira akan dukkan Larabawa da sauran Musulmi da su
kauracewa wannan shan ruwa da Obama ya kira, a cewarsu sunyi hakan ne
dan nuna fushinsu akan irin goyon bayan da Obama ya ke baiwa Israela na
gallazawa al'ummar Ghazza da ta ke yi a 'yan kwanakin nan.
YASIR RAMADAN GWALE
17-07-2014
17-07-2014
No comments:
Post a Comment