Saturday, July 26, 2014

Abin Al-Ajabi Mai Ban Tausayi

ABIN AL'AJABI MAI BAN TAUSAYI

Da yawa daga cikin jaridun kasashen larabawa na yau Asabar sun ruwaito labarin wata jaririya mai cike da ban tausayi da kuma ban al'ajabi. Ita dai wannan jarirya an haifeta ne bayan da mahaifiyar ta da ke dauke da cikinta ta rasu. Mahaifiyar wannan jaririya mai suna Sheima tana kwance kan gadonta a dakinta a birnin Ghazza a daidai lokacin da sojojin Israela suka harbo wani makamin roka da ya sauka akan gidansu, nan take gidan ya rushe gaba daya, mahaifiyar wannan jaririya ta yi kokarin kubutar da ranta da na d'an cikinta, amma ina! Sheima ta rasu a sakamakon munanan raunuka da ta samu sakamakon manyan duwatsun da suka rufto akanta, cikin gaggawa matasan Palasdinawa masu taimako suka tono Sheima daga cikin barguzan ginin da ya rushe akanta aka garzaya da ita Mustashfa.

Bayan da aka garzaya asibiti da wannan baiwar Allah ne aka tarar tuni Allah ya yi mata cikawa. Ba tare da wani bata lokaci ba likitoci suka shiga kokarin ceton abinda ke cikin matar, cikin taimakon Allah aka yi sa'ar farka cikin matar aka ciro jaririya da ranta. Ita dai wannan jaririya yanzu haka tana asibiti ana kula da ita, likitan da ya yi aikin ceton wannan jaririya Dr. Fadi ya yiwa Allah godiya da ya basu ikon ceton ran wannan jaririya, sannan ya kuma yi bayanin cewa hakika ya tausayawa wannan jaririya domin ta zo duniya a wani irin yanayi na tashin hankali da ya mamaye yankin Ghazza, gashi an kashe mahaifiyarta an kuma kashe mahaifinta.

Yanzu dai tuni dangin wannan jaririya suka bayyanawa duniya cewar sun mayarwa da jaririyar sunan Mahaifiyarta. Allah ya jikan mahaifiyar wannan jaririya ya gafarta mata. Allah ya taimakin Musulunci da Musulmi ya kaskantar da kafurci da kafurai. Mutanan Ghazza Allah ya taimake su akan abokan gaba.

Yasir Ramadan Gwale
26-07-2014

No comments:

Post a Comment