LABARIN DA YA TAYAR MIN DA HANKALI A CIKIN AZUMIN NAN
Furera Bagel ta bayar da wannan labari akan Timeline dinta kamar haka:
Tana cewa, ina cikin matukar damuwa da tashin hankalin abinda ya faru,
inda har na dinga ganin abin a mafarki. Tace, wani lokaci na ziyarci
gidan yayata dan sada zumunci, sai na sameta cikin wani irin yanayi
marar dad'I kwarai da gaske. Da na tambayeta dalilin halin da ta ke ciki, ta bani labarin kamar haka:
Wannan abin ya faru da wata 'yar uwarmu ne, wannan matar tana cikin
wani irin matsananci halin rayuwa, daga baya kuma wani mummunan al'amari
ya kuma bijiro musu. Ita dai wannan matar sunyi aure da mijinta Shekaru
25 da suka gabata, wanda tun bayan aurenta da mijinta aka kama mata
dakin haya guda daya tana cikinsa tsawon kusan shekaru 20; kwatsam bayan
wani lokaci sai mijin matar ya kara yin wani sabon aure, anan ne mijin
ya kara karbar wani dakin haya guda daya a gidan da yake zaune, inda
kowaccensu take zaune a daki daya.
Amma wannan mutumin bai
kama daki ko guda daya ba, domin 'ya 'yansa da suka tasa su zauna a ciki
ba! Matar takan kwana da 'ya 'yanta budurwoyi a daki daya idan mijinta
na dakin daya matar, amma yaranta maza sai su tafi makwabta su kwana
tare da sauran 'yan uwansu maza. Can bayan wani lokaci, dan wannan mata
mai kimanin shekaru 12 ya kamu da rashin lafiya, inda aka kaishi asibiti
dan yi masa magani. Amma bayan wani lokaci rashin lafiyar wannan yaro
ta sake tasowa, anan ne suka yanke shawarar daukar yaron dan kaishi a yi
masa gwaje-gwaje dan gane cutar da take damunsa.
Bayan da aka
dauki jinin yaron dan skekaru 12 aka auna ne, aka tabbatar musu da cewa
yaron yana dauke da cutar HIV mai karyar garkuwar jiki. Inna Lillahi Wa
Inna Ilaihi Raji'un! Uwar yaron ta shiga cikin damuwa da tashin hankalin
yadda yaro kankani ya kamu da cutar kanjamau irin wannan!
Tun
farko, matar bata taba samun nutsuwar danta yaje gidan makwabta ya kwana
da wadan da suka grime shi a shekaru ba, amma kasancewar mijinta yaki
kamawa yaransa dakin haya a gidan, babu wani abu da zata iya yi illa ta
kyale yaron yaje makwabta ya kwana duk dare, amma daga wannan lokacin
matar ta kudiri aniyar dole al'amura su sauya daga yadda suke faruwa.
Nan ne fa matar ta kuduri aniyar samarwa kanta da 'ya 'yanta mafita, ta
fara yin sana'ar toye-toye a bakin titi duk safiya, ta sanyawa ranta
burin mallakar gida dan tsugunar da 'ya 'yanta.
Allah buwayi
gagara misali, ya baiwa wannan mata ikon mallakar fili, cikin
hukuntawarsa Subhanahu Wata'Ala, ta gina gida mai daki biyu da falo da
kicin da ban-daki da tsakar gida. Amma a lokacin da ta mallaki wannan
gidan tuni 'ya 'yanta mata guda biyu sunyi aure, kun san abinda mijinta
yayi kuwa? Kawai sai ya saki waccan matar da ya kara aurowa daga baya,
sannan yabi matarsa sabon gidan da ta gina ya tare tare da ita.
Dan wannan matar da yake yaro ne mai shekaru 12, yana nan yana cigaba
da karbar shawarwari da magunguna akan cutar da yake dauke da ita mai
karya gaekiuwar jiki, adaidai wannan lokaci ne kuma, ciwon yaron ya sake
tsananta, dukkan karfin jikinsa ya kare, garkuwar jikinsa tayi matukar
rauni. A lokacin da yayar Furare Bagel ta ziyarci mahaifiyar yaron ne ya
yi musu bayanin yadda aka yi ya kamu da cutar HIV! Yaron yace, "lokacin
da nake zuwa gidan makwabta na kwana ina karami sosai, idan ina kwance
sai wani mutum ya zo ya tilasta min kwanciya tare da shi dan biyan
bukatar sha'awarsa tare dani, yakan yi min ta karfi ba dan ina so ba,
mutumin ya ciga da zuwa wajena duk dare yana tursasamin kwanciya da shi
lokaci mai tsawo da ya wuce. Mutumin da yake yi min wannan abu kuwa shi
ne makwabcinmu da nake kwana a gidansa, yaron yace mutumin kamar mahaifi
yake a wajensa"! Wannan shi ne labarin da yaron ya basu, inda ya nuna
cewar wannan mutumin da yake zuwa wajensa da daddare yana kwana da shi
ne ya sanya masa wannan cuta ta HIV.
Hakika wannan labari ya
tayar min da hankali a cikin wannan azumi matuka. Furare Bagel a cikin
jawabinta ta ce, shin me yasa ba zamu taimakawa wannan mata ba wajen
kama wannan makwabcin nasu dan gurfanar da shi a kotu a tuhumeshi da
laifin yin lalata da kananan yara ba? Ina lauyoyi daga cikinmu masu san
taimakon masu karamin karfi? Lallai ya kamata mu taimakawa wannan mata
da aka riga aka kashe mata yaro.
YASIR RAMADAN GWALE
07-07-2014