AREWA:
A GANI NA . . .
Batun
halin da Arewa ta ke ciki na zubewar mutunci da kima da haiba da kamala da koma
baya ta fannin tattalin arziki da sukurkucewar Ilimi da lalacewar makarantu da
kiwon lafiyar da asibitai suka zama tamkar makabartu da al’amuran tsaro da suka
jagwalgwale suka hana kowa walwala da jin dadi, kusa wadannan da ma wasu sun
damu duk wani dan AREWA mai kishi babba ne ko karami, mace ce ko Namiji. Yau a
Arewa babu wani wanda zaka titsiye ka tambayeshi halin da ake ciki ya yi maka
hamdala da godiya da wannan hali da muke ciki, sai dai fa idan tantagaryar
makiyin Arewa ne makiyin Najeriya wanda baya son cigaban Arewa da Najeriya.
Halin da muke cikin ya wuce duk yadda ake zato, domin wani abin ma idan mutum yaji
sai yaji kamar ba gaskiya bane, ba wai kawai lalacewa Arewa ta yi ba, a’a
komawa baya ta ke a sukwane, Kamar Misalin motace ka baiwa dan koyo kuma ya
sanya giyar reverse yana gudun tsiya, shakka babu dole ya yi barna, ba wai
motar kadai zai mammokada ya lallauya tayoyin ba har da duk abinda ya samu akan
hanya sai ya bangajeshi mai gyaruwa ya gyaru wanda ya mutu ya mutu kenan; to
kamar misalin irin haka Arewa take a yanzu, a halin da muke ciki.
Matsalar
shaye-shayen miyagun kwayoyi ta addabi samarinmu maza da mata, Ilimin
makarantun hukuma ya tabarbare makarantun gwamnati sun zama garken jahilai,
malaman babu ilimi, daliban babu ilimi gwamnatocin kananan hukumomi da na
jihohi da sauran al’umma da ake kira “community” kowa ya kame hannunsa daga
lalacewar ilimi anyi ko in’kula, kowa ya gwammace idan zai iya ya dauki dansa
ya kaishi makarantar kudi, wanda kuma bashi da karfi alal-larurati ‘ya ‘yansa
suke karatu a makarantun gwamnati ba dan ransa yana so ba, sai dan bashi da
yadda zai yi. Irin wannan mawuyacin halin hannu baka hannu kwarya, ya sanya da
dama dagacikinmu suka fara yanke tsammani daga Ubangiji, wasu suka bazama neman
yaki halal yaki haram, Mutane burinsu su tara dukiya babu ruwansu da tsarkinta.
Yanzu
a Arewa yaro da babba, mace da Namiji, almajiri da wanda ba al’majiri ba, mai
gata da mara gata, mai mulki da wanda ake mulka; Kusan kowa neman damar dan
uwansa yake, ta ina zai samu dama ya kwashe kafufuwan duk wanda Allah ya dorawa
kaddarar fitar rabo. Cuta da cutarwa ta zama ruwan dare gama duniya, babu
malamai babu jahili, masu hankali da marasa hankali kowa neman hanyar cuta
yake, yan kasuwa da masu sari, leburori da iyayan gidansu; daman ma’aikatan
gwamnati ya zamar musu tamkar halaliya yin almundahana da kayan hukuma, a sace
duk abinda zai iya satuwa, tundaga masu gadi har oga kwata-kwata duk wanda ya
samu abin dauka indai na hukuma ne, to gaban kansa yake ya dauka, tamkar wanda
ubansa ya mutu ya bar masa gado shi kadai, a sace man jannareto, a sace fanka a
saci tabarma da darduma, wani abinma bai kai a sace shi ba, amma saboda tsabar
mutuwar zuciya, sai ma’aikata su dinga satar abinda ko kadan ba zai amfanesu
ba, illa kawai wani tunani da ya dade da yin tsiro a zukatan al’umma na cewa
“raba arne da makami ibada ne” dan haka ake ganin kayan hukuma kamar ganima.
Wannan
yanayin shi ne wani irin mawuyacin lokaci da Arewa bata taba mafarkin samun
kanta a cikin irinsa ba. Magabatan shugabanninmu sun barmana kyakkyawan abin
gado, sun gina harsashin samun ingantacciyar rayuwar wadan da zasu zo baya, sun
samar mana da Gidan jaridar NNN da gidan Radio Najeriya Kaduna, da kamfanonin
murza auduga na Arewa da Babban Bankin Arewa da makarantun tundaga kwalejoji da
jami’o’I da makarantun koyon sana’a, da makarantun horas da malamai da sauransu
da dama, amma basu yi sa’ar samun hannu na gari da zai iya alkinta su ba,
wannan duk wanda ya san Arewa ya san halin da ta ke ciki zai iya bayar da
shaida akan haka. To amma hakikanin gaskiya tafiya tayi tafiya, tura ta kai
bango, lokaci ya yi da za’a zauna zama na gaskiya a kalli halin da muke ciki
dan dawo da martabarmu da aka yi mana shaida da ita tun a baya.
Haka
kuma, lokaci ya yi da zamu ja layi akan dukkan wasu laifuka da muke ta zargin
kawukanmu da aikatawa, tunda halin da muke ciki ya shafi kowa da kowa, babu
wanda yake walwal cikin jin dadi da kwanciyar hankali, kusakurai an riga anyisu
manya da kanana, dan haka, abinda ya kamata mu maida hnaklai shi ne kokarin
nemo mafita da bakin zaren halin da muke ciki. Shugabannin baya da kuma wadan
da suka nannada kansu Shugabancin Arewa a yanzu duk sunyi abinda zasu iya,
wadan da suka tafka ta’adi da wadan da suka yi abin kirki duk sunyi, kuma anga
abin da kowa ya yi, Allah ya sakawa kowa da gwargwadon abin day a aikata, idan
khairan khairn, idan sharran sharran.
Wata
rana Shehu Jaha ya aiki diyarsa ta debo masa ruwa a tulu, sai ya yi mata
kashedin kada ta sake ta fasa masa tulu, idan kuwa ta fasa to zasu gauraya, har
ta kama hanya ta tafi sai Shehu ya kirata ya tsinko tsumagiya ya shashshauda
mata, wani abokinsa ya ce haba Shehu yaya ka gargadeta kar ta fasa, bayan kuma
bata fasa ba ka doketa. Sai Sheshu ya kada baki yace, babu amfanin na doketa a
lokacin da ta riga ta fasa tulu, domin dukan ba zai sanya tulu ya dawo ba.
Kamar misalin haka ne na irin halin da muke ciki, yawan zargin junanmu da
laifin halin da muke ciki babu abinda zai kara, illa kara wagegen gibi a
tsakaninmu, tunda matsaloli dai ana cikinsu tsamo-tsamo, batun ko laifin su
wane ne ko ba laifin su wane bane, duk ya kamata mu wuce wajen, batun da ya
kamata mu maida hankali shi ne ta yaya zamu fito daga cikin wannan halin da
muke ciki shi ne abinda dukkanmu ya kamata mu maida hankali akai.
Dukkanmu
dole mu ji tsoron Allah a cikin al’amuranmu, mu sanya gaskiya da amana a cikin
mu’amalolinmu, shugabanni su zama adalai a ajiye komai a inda ya dace, a baiwa
kowanne mai hakki hakkinsa, babu wasu mutane daga Ingila ko Faransa ko Amerika
da za su zo su fitar dam u daga cikin halin da muke ciki, mune muka san kanmu,
muka san halin da muke ciki, muka san irin azaba da radadin da muka shiga ciki,
ya zama tilar mu hada karfi da karfe wajen fito da sahihan hanyoyi da zasu
amfani ‘yan bayanmu masu zuwa nan gaba. Mu shata layi kamar yadda na fada, ko
da bamu yafe irin satar da ‘yan uwanmu suka dibga ba, to mu dakatar da abin
haka, kudin hukuma ba na uban kowa bane, na dukkanmu ne, idan mun alkinta
dukiyarmu kanmu muka alknta, idan mun barnatar kanmu da jikokinmu muka yiwa
illa.
Ya
zama dole da Masu mulkinmu na Siyasa wadan da hakkin jagorancinmu yake a
hannunsu, da shugabanni masu rike da sarautu, da malamai da kungiyoyi mu samar
da wata Hadaka da zata fitar da mu daga cikin halin da muke ciki. Kamar yadda
aka samu hadewar jam’iyyu dan kawai ga gaci da samun nasara, muma dole sai mun
hade kanmu mun hade kungiyoyinmu, sannan mu samu nasarar fita daga cikin wannan
mawuyacin halin da muke ciki. Akasin haka, babu abinda zai yi mana illa kara
jefa mu cikin bakin ciki da damuwa da ba za su iya yi mana maganin halin da
muke ciki ba, idan banda kara nesanta mud a juna. Dole mu dawo da ‘yan uwantaka
tsakaninmu da kaunar juna, da taimakekeniya, mu cire kyashi, mu daina hassada,
mu yiwa kanmu tarbiyyar hakuri da halin ‘yan uwanmu, mu kuma yi hakuri da halin
talauci da kuma baiwa mawadatanmu uzuri. Ya Allah ka karkato da hankulanmu gaba
daya mu fahimci juna dan ciyar da Arewa da Addininmu gaba, Allah ka taimakemu
ba dan halinmu ba, ba dan munanan ayyukan da wasu daga cikinmu suka aikata ba.
Allah ka taimakemu ka sa wannan shi ne lokacin da zamu yi ban-kwana da dukkan
irin sarkakiyar da muke ciki da wahalar rayuwa. Allah ya taimaki Arewa da
Najeriya baki daya.
Yasir
Ramadan Gwale 26-10-2-13