ZABEN
2015: ANYA ZA'A IYA KAYAR DA GOODLOCK KUWA?
Abinda
ya faru jiya a jihar Anambra ya kara tabbatar mana da cewar tun daga zaben 2011
har zuwa yau babu wani abu da ya canza dangane da harkar zabe a Najeriya. Zaben
Anambra duk da ba'a fadi sakamako ba, amma irin almundahanar da ta wakana ta nuna
cewa hukumar zabe babu wani kwarin guiwa akanta, dangane da aiwatar da sahihin
zabe. Tambayar da na yiwa kaina, anya hukumar zabe karkashin Attahiru Jega zata
iya shirya tsarkakkaken zaben da zamu iya yarda da sakamakonsa ko da kuwa ba
wanda muke so ba ne ya yi Nasara? Allah ya kiyaye.
A
kasar Kenya, babu abinda ya damu Moi Kibaki da duk mutanan da suka rasa
rayukansu domin duk talakawa ne suka kashe talakawa. Ya murda zabe yayi abinda
yaga dama, ya kammala wa'adinsa, kuma ya kama gabansa babu ko kara da aka daga
masa da sunan dukkan irin balahirar da aka tafka a zaben da ya mayar da Kebaki
kan kujerar Mulkin wa'adinsa na biyu. Sai abin ma ya zama wasan kwaikwayo, wasu
daban ake zargi da tashin hankalin da ya faru! Kura ta sha kashi shi kuwa gardi
ya cika lalitarsa.
A
kasar Senegal mun gani duk da irin dan banzan taurin kai da san dawwama a Mulki
na shugaba Abdullahi Wade, amma da aka yi zabe ya sha kaye ya hakura da kayen
da ya sha, kuma ya mika mulki ga zabin jama'a, ba tare da anyi asarar rayukan
talakawa ba, kamar yadda aka yi a Kenya. Watakila saboda yana da hasken Imani
na Musulunci a zuciyarsa ne. Allah masani.
A
babban zaben kasa na 2015, ko dai shugaba Goodluck Jonathan yabi irin hanyar da
Kebaki yabi a Kenya ya kashe kunnensa, ayi ta kashe-kashe da kone-kone tundaga
Gonin-Gora har Jibiya, tundaga Sokoto har Maiduri babu abinda zai sha masa kai.
Ko kuma ya nuna dattako irin na shugaba Wade idan ya sha kaye ya hakura ya mika
mulki ga zabin jama'a Alabashshi tarihi ya rubuta karfin hali da juriyar da ya
nuna na karbar kaddara. Wanda ba shakka abu ne mai kamar wuya haka siddan
wannan bakin arnen ya yarda ya sha kaye, balle da wuya har akai ga fagen shan
kayen.
Babban
abin tambaya ta shi ne, shin me ye zai biyo bayan sakamakon zaben kasa na 2015?
Anya kuwa jam'iyyar APC da muka saka a gaba ta shirya da gaske dan kwace goriba
a hannun-kuturu? Ba shakka talakawa suna cikin garari kwarai da gaske. Ina ji a
jikina cewa PDP na iya samun halattaciyar kuri'ah a kafatanin jihohin Najeriya,
tunda suna da kudin sayan kuri'u, ba shakka kuma za'a sayar musu. Amma dai
al'amarin akwai ban tsoro kwarai da gaske.
Wata
muhimmiyar tambaya da nake yiwa kaina, ita ce, meye makomar Musulmi a cikin
gwamnatin Jonathan idan aka ce shi ne ya ci zabe? nayi Imani shugaban kasa
Goodluck mutumne mara tsoron Allah. Meye makomar tashin hankalin da muke fama
da shi a Arewa musamman a jihar Borno da Yobe? Nasan da cewa, duk tsiyar
shugaban kasa da takadarancinsa ba zai haura shekara ta 2019 ba, to amma me zai
faru da mu kafin wannan lokacin? Allah shi ne masani.
Yasir
Ramadan Gwale
17-11-2013
No comments:
Post a Comment