Thursday, November 21, 2013

Al-Amarin Kare Na Daga Cikin Abubuwan Ban Mamaki


AL-AMARIN KARE NA DAGA CIKIN ABUBUWAN BAN MAMAKI

Kare yana daga cikin dabbobin da Allah ya haramtawa Musulmi cin namansa. Ba shakka kare wata dabba ce da ba wata mai kima ko daraja ba ce a wajen mutane da dama, musamman Musulmi. Cikin ikonSa Subhanau Wata'ala, ya sanya fahimtar juna tsakanin Kare da Bil-Adama, babu shakka dukkan dabbobin da Allah ya hiltta babu wata dabba da ta kai kare sabo da Mutane, wannan ta sanya a kasashen Turai da Amerika ake lissafa kare a zaman daya daga cikin Iyalin gida, ko ahalin gida, kare yana samun kulawa ta musamman a wajensu. Sukan bashi wata irin daraja da ta shallake irin wadda wasu mutane suke samu a wasu sassa na duniyar nan! Allah buwayi gagara misali, shi ya sa da ya tashi bayar da labarin ASHABUL-KAHFI a cikin al-qur'ani mai tsarki, sai ya bayar da labarin har da karen da yake tare da su, wato kare ya lizimci mutanan kirki! 

Shin waye kare? Wani bincike ya nuna cewar, kare ya rayu a cikin wannan duniyar kusan fiye da shekaru 100,000 da suka shude, sannan  asalinsa, tsatso ne na dangin "wolf" wata dabba da ake samu a Arewacin Amerika da Turai da Kuma Asia, ita wannan dabba ta yi kama da Kare ta fuska, amma ta sauran sassan jiki sun sha bamban da kare, kuma amfi samun sa a waje mai sanyi da dusar kankara. Haka kuma, wani binciken ya nunar da cewr akwai sama da karnuka Miliyan 400 da suke watangaririya a duniya. Allah masani! Amma dai mun san cewa Allah ya halicci dukkan "DABBATIL ARD" bisa kaddarawarSa subhanahu wata'ala, shi ne ya halicci Mutum, da Aljani da kwado da gafiya da Barewa da Kunkuru da Matsaatstsaku da Rakumi da dukkan sauran ababen Halitta bisa Kaddarawarsa Alkhaliqu, tsarki ya tabbata a gareshi.

Kare shi ne kadai yake da dogon tarihin sabo da yiwa 'yan Adam hidima tun kusan fiye da shekaru 33,000 da suka shude a cewar wasu masana, musamman ta fannin da ya shafi kiwo, farauta, jan-kaya a cikin dusarkankara, da kuma taimkawa jami'an tsaro wajen gano wasu baoyayyun abubuwa da suka gagri dan-adam ganowa. Kare yana da rikon amana ainun, duk irin bala'i da masifa ta kura, da kuma irin yadda Allah ya sanyawa kare tsoron Kura, yakan mutu wajen kare dabbobin da yake rakiya a duk lokacin da kyarkyeci ya kawo musu farmaki ko barazana. Kare ne kadai dabbar da ake iya bashi kiwon wata dabba 'yar uwata! Subhanallah, kaji al'amarin ubangiji. Allah cikin hukuntawarsa ya sanyawa kare fahimta mai yawa da kuma lura da ganewa.

Allah ya halicci kare daban da sauran dabbobi. Domin yadda kare yake kallon duniya ba haka sauran dabbobi suke ganinta ba, sinadaran da suke cikin Idon kare suna ganin fari ne da baki kawai, a tarihin rayuwarsa bai taba ganin wani launi sabanin fari da baki ba, a bisa yadda Allah ya yi masa halittarsa. Kare yana daga cikin dabbar da bai damu da duniya ba, babu ruwansa, shi yasa a koda yaushe yafi son zama waje mai sanyi mai danshi mai ni'ima, watakila kamar yadda muka fada a baya tsatsonsa danginsu wolf suna rayuwa ne a waje mai sanyi watakila wannan ta sanya kare ke son sanyi da danshi.

Kamar yadda kare ya dauki tsahon lokaci tare da mutane, wannan ta sanya yake samun cigaba gwargwadon yadda mutane ke samun cigaba. Domin yanzu bincike ya nuna kare yana iya yin tarayya da mutane wajen yin wasu ayyuka da dama. Misali ba sau daya ba, ba sau biyu ba ansha cewa kare ya kubutar da wani yaro ko yarinya daga halaka, ko kare ya halaka garin kokarin kubutar da dan-adam daga halaka. Bayan ayyuka na tsaro da bincike da Kare yake taya dan-adam, kare na iya yin wasu ayyuakn da dama kamar bude kofa da rufewa, kunna hasken lantarki da kashewa, kallon talabijin, sannan kuma, kwanakin baya muka ji cewar an fara koyawa kare tukin mota a Amerika. Ba shakka a kasashen turai har aiken kare suke yi, kuma idan bai gane ba ya yi tambaya a yi masa kwatance. Kare baya magana amma yana jin magana kuma yana fahimta, gwargwadon tarbiyyar da ya samu da kuma irin yanayin da ya taso a cikinsa.

Idan muka dauki batun "SABO" byanai sun tabbatar da cewar Kare ya samu shakuwa da dan-adam sosai, ta yadda baya iya rabuwa da mutanan da ya saba da su. Wata rana a cikin shirin taba kidi na BBCHausa suka fadi cewar wani kare da ubangidansa ya rasu, sai da karen yazo ya tare a gindin kabarin da aka binne ubangidan nasa na wasu tsahon lokuta, yaje ya yi farautar abinda zaici sannan ya dawo wajen ya kwanta. Akwai nau'ka na kare sama da kala 400 a cewar wani bincike. Hakika akwai abubuwan ban mamaki a tattare da rayuwar kare. 

Yasir Ramadan Gwale 
21-11-2013

No comments:

Post a Comment