OJUKWU DA RAWAR DA YA TAKA A JUYIN MULKIN 1966!!! (3)
Ga ‘yan Najeriya da basu san Ojukwu ba har suke zaton bashi da
hannu a aika aikar janairun 1966 su sani :rahoto ya inganta cewa Ojukwu ya fita
kasashen waje ba da sanin ofishin sa ba a 9 zuwa 13 ga janairu. Wani jami’ain
soja dake aiki a kano ya tabbabar da haka. Domin a jirgi daya suka fita daga
kasar tare das hi Ojukwu. A 14 ga wata kuma Ojukwu ya shiga garin Kaduna- yamma
zuwa farkon dare tare da wata mata da ya ajiye a Hamdala Hotel ya gana da wasu
mutane. Wanda ya fitar da maganar yasan matar. Ya tambayeta bayan nan kuma ta
tabbatar masa da hakan. Awoyin farko na 15 ga wata ya mamaye filin jirgi da
Gidan radio a kano bisa tunanin manyan Arewa zasu sulalo don gudun hijira… duba
littafin Let Truth be Told na David Muffett.
Chif Christian Onoh, shima, tsohon gwamnan Anambara, amini kuma
suruki ga Ojukwu cewa yake “tun Disambar 1964 zuwa Janairun 1965 Ojukwu yaso
yin juyin mulki. Da hakan bata samu ba sai ya yaudari wasu yara 5 masu mukamin
Manjor don cimma burin sa a 1966. Bayan matasan sun kwace kasar sai wasu manyan
soja bisa jagorancin Ironsi Mai-kada suka murkushe su (juyin mulki cikin juyin
mulki). Ganin haka sai Ojukwu ya juya wa wadancan kananan sojoji baya da yin
biyayya ga Ironsi. Bai’ar da yayi tasa Ironsi nada shi gwamnan jihar gabas.
Samun wannan matsayi ta sashi wulakanta Azikiwe da yake ganin yazame masa
kadangaren bakin tulu ga kasancewar sa shugaban kasa. (C.C Onoh yaci gaba da
cewa) ta kai ga Azikiwe rubuta takardar koke ga Ironsi don ya tsawata wa
Ojukwu. Wannan Fada ya faro ne daga lokacin da Ojukwu ya roki Azikiwe daya
bashi hadin kai don kawar da Tafawa Balewa a 1964, shi kuma wancan tintirin
jahili (kamar yadda yake kwatanta Ironsi) watau Birgediya Ironsi suyi masa
ritaya. Da yin haka sai Azikiwe ya zama shugaban wucin gadi ko Piraminista shi
kuma ya zama shugaban sojoji. A cewar sa hakan zai kawo zaman lafiya da
kwanciyar hankali a kasa. A matsayin Azikiwe na wanda ya yarda da
dimokaradiyya, yaki yarda. Daga nan basu kara zama inuwa daya da Ojukwu ba.
Hadin kan da Zik bai bayar ba yasa Ojukwu yaudarar wadancan
tsageru. Ya tsara yadda zasu kawar da Ironsi a matsayin Shugaban
Hafsan-hafsoshin sojojin Najeriya da Tafawa Balewa Prime-Minister a Lagos da
yadda zasu kame Gidan radiyo da bayyana shi a shugaban gwamnati kuma jagoran
sojojin Najeriya gaba daya.
(C.C Onoh ya kara da cewa) kashe Ironsi dai bai samu ba, karshe
ma ya amshe ragamar gaba daya. Dole Ojukwu ya mika wuya, shi kuma ya saka masa
da gwamnan yankin gabas… Wannan bayani yana nan cikin wani karamin littafi da
Farfesa Tom Forsyth yarubuta mai suna The Heroes Of Change.
Ga mai neman sanin abin da ya faru a janairun 1966 lallai dole
ya shiga duhu ya kuma shiga haske. A Arewa Magana daya ce, saboda hadamar mulki
aka zabi madaukakan ta aka kashe da gangan. Hasken kenan. Amma a inda duhun
yake shi ne a kudu musamman yankin gabas inda makasan suka fito. kowa so yake
ace shi gwani ne. shi ne mafifici cikin inyamurai. Tahsabuhum jami’a,
wakulubuhumut-shaattah, sun hada baki amma zuciyar su a rarrabe. Ojukwu ya
kitsa juyi don zama shugaban kasa, akayi juyi shugabanci bai samu ba. Ironsi ya
zama shugaban kasa ba da son Ojukwu ba. shi kuma Ojukwu daya kafa Biafra,
Nzeogwu bai so ba. Dalili kenan ma ya ra’ba ya har’be shi a wani artabu kusa da
garin Nsukka. Bayan nan ya hallaka Ifeajuna wai suna shirin yi masa juyin mulki
a kasar Biafra. A dunkule Ojukwu da mutanen sa sun so danne yan Arewa ne, Allah
bai basu dama ba.
A shekarun baya irin wancan ra’ayi na bayar da kariya ga Ojukwu
da mutane irin sa na fitowa ne daga kudu. Ko a 1987 a wani littafi nasa mai
suna “Nzeogwu” Chif Obasanjo ya bayyana Nzeogwu da mutumin kirki, mai saukin
kai, mai hangen nesa da tausayi. To a yau gashi ‘yan Arewa sun fara. Sai muce
Allah ya sauwaka. Don haka dalilan da zasu sa wani koyi da marigayi Ojukwu,
koda kuwa ibo ne, marasa tushe ne. Balle kuma ace dan Arewa da yakai matsayin
gwamnan jiha kuma jagoran gwamnonin jihohi 19 da a baya suke karkashin kulawar
Sardauna.
No comments:
Post a Comment