Sunday, December 1, 2013

PDP: Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da G-7!!!

PDP: TSAKANIN FADAR SHUGABAN KASA DA G-7!!!

Tuni sanarwa ta gama karade ko ina cewar tsagin gwamnonin PDP guda bakwai da suka darewa uwar jam'iyyar PDP zasu gana da Shugaban kasa a yau. Kafin wannan ganawa dai an jima ana kai ruwa rana tsakanin wadannan Gwamnoni da fadar Shugaban kasa, har ta kai a ranar talatar da ta gabata, shugaban tsagin nPDP Alhaji Kawu Baraje ya bada wata sanarwa a dukunkune cewar sun hade tsakanin nPDP da kuma babbar jim'iyyar Hamayya ta APC. Tambayar da zamu yi anan ita ce, Shin Shugaban kasa zai gana da wadannan gwamnoni a matsayinsu na nPDP ne ko kuwa a matsayin sabbin Gwamnonin APC, ko kuma 'yan kan-katanga? Duk da cewar Gwamnan Jigawa da na Neja sun bayyana matsayarsu akan waccan sanarwa da Baraje ya bayar.

A ranar juma'ar da ta gabata, a cikin shirin BBCHausa na Ra'ayi Riga, sun tattauna wannan al'amari na turkaturkar PDP. A cikin wannan tattaunawa, sakataren tsare-tsare na PDP bangaren Bamanga Tukur Abdullahi Ibrahim Jalo ya yi wata tambaya mai muhimmanci, amma aka kewaye ba'a bashi amsar tambayar ba. Ya yi tambaya kamar haka, "Shin su wadannan Gwamnoni sun shiga APC ne a matsayin sauya sheka daga PDP zuwa APC, ko kuwa hadewa ce irin wadda ANPP da ACN da CPC suka yi" wannan tambaya tana da muhimmanci a yi bayaninta, amma cikin shirin aka kewaye mata. Domin bayan da Baraje ya bayar da wannan sanarwa, Gwamnan Jihar Kano Alh. Rabiu Kwankwaso ya yi wani bayani a BBC mai rudarwa kan cewa zasu koma su tattauna da jama'arsu sannan su yanke matsaya; wannan ya nuna cewar kamar ba su shiga APC din ba kenan.

Dangane da ita waccan tambaya da Jalo ya yi, yana da kyau suma APC su yi mana warwarar wannan al'amari, domin dai mun san cewar tsakanin ANPP da ACN da CPC da suka yi hadaka ba da baki suka yi ba, sai da kowacce ta mayar da satifiket dinta ga hukumar zabe sannan wannan hadewa ta tabbata, dan haka, su wadannan gwamnoni na nPDP sun dawo da nasu satifiket din ne ko anyafe musu, ko kuwa sauyin sheka suka yi? Wannan al'amari yana da kyau kada a dinga tafiya da 'yan Najeriya a dukunkune.

A dangane da Gwamnonin G-7, shin Me zai faru idan suka tabbatarwa da Shugaban kasa cewar suna nan daram dam dam a PDP? Bukatunsu a bayyane suke ga al'ummar Najeriya, manyan bukatunsu guda biyu dai sune na cewar (a) Dole Shugaban kasa ya ajiye batun tsayawa takara a 2015. (b) Dole a kori Bamanga Tukur. Anan ma zamu iya yin tambaya, shin wadannan Gwamnoni sun gamsu da yadda gwamnatin Jonathan ke tafiya ko kuwa kawai bukatarsu kada shugaban kasa ya tsaya zabe a 2015? Me ya sanya ba zasu tsaya kai da fata wajen ganin shugaban kasa da Gwamnatin Tarayya sun yiwa al'ummar Najeriya ko Arewa Adalci ba? Sanin kowa ne Shugaban kasa yana nuna bambanci da zalunci tsakanin bangarorin kasarnan a bayyane, babu wanda ya yi haka, idan banda gwamnan Kano da na Kwara da suka yi batun rashin adalci a tsarin rabon arzikin kasa na Man da ake tonowa a cikin Ruwa da kuma wanda ake tonowa a kan tsandaurin yankunan da suke da man (Off-shore da On-Shore) Wannan korafin wadannan gwamnoni sun yi ne a kashin kansu tun kafin haifar da G-7.

Ko shakka babu irin wadancan bukatu su ne suka damu al'ummar Najeriya. Dole a yiwa kowa adalci a baiwa ko wanne mai hakki hakkinsa, amma gabaki daya al'amarin PDP babu gaskiya a cikinta, da wanda yake zagin PDP da me yabonta duk ba masu gaskiya bane, illa nadiran indai 'yan PDP ne. Domin Atiku Abubakar da Abubakar Rimi babu irin abinda basu kira PDP ba, amma kuma suka yi mata kome daga baya. Yana da kyau al'ummar Najeriya su fadaka cewa, PDP wani gungu ne na 'yan MAFIA babu wani wanda ya isa ya kauce daga tsarin da aka gindaya, dole dan PDP ya yi mata aiki yana so ko baya so, ya yarda ko bai yarda ba, duk wanda yaci ladan kuturu dole ya mar aski. Yana da kyau mu sani su PDP wadannan gwamnoni basa tayar musu da hankali illa kawai tashin hankalinsu shi ne kada darewar wadannan Gwamnoni ta haifar da barakar da PDP zata rasa rinjaye a majalisar wakilai ta tarayya, amma indai tafiya zasu yi daga PDP ana iya hada musu da gyaran Gwamnonin Kebbi da Katsina da Bauchi. Kayar da PDP ba abu bane mai sauki, domin rijiyar da ta cika da datti da dagwalo baza a taba iya yasheta daga waje ba, ya zama dole a shiga ciki a kwarfe ruwan da yake ciki sannan a samu ruwa mai kyau, ko kuma a cike ta a sake tona wata. Dan haka, Gasa Rago A Murhun Alade Bai Zai Taba Haramta Naman Rago Ba.

YASIR RAMADAN GWALE
01-12-2013

No comments:

Post a Comment