KAMUN DA SSS SUKAIWA SHEIKH NAZIFI YUNUS JOS: AN FAKE DA GUZUMA . . .
Ba shakka kamun da hukumar SSS ta yiwa Dr. Yunus Jos dangane da zarginsa da ake yi da alaka da Boko Haram, ko kasancewa dan Boko Haram wani al'amari mai daure kai. An je har gidansa cikin tsakar dare aka kama shi a lokacin da yake tare da iyalinsa, aka keta masa haddi, aka ci zarafinsa, aka kuma yi masa dai-dai da kayan gidansa da nufin bincike dan samun wasu abubuwa da ake zargin 'yan BH na amfani da su wajen tayar da hanali, sai dai cikin ikon Allah haka aka fita ba tare da an samu ko da matsefata da sunan an ajiye dan tayar da hankali ba a gidansa.
Shugabar hukumar SSS Maryellen Ogar ta sha sharara karya akan zargin mutane da Boko Haram. Kamar yadda kowa ya sani ne, haka suka kashe matasa basu san hawa ba, basu san sauka ba a Apo a Abuja a kwanakin baya, da nufin zargin matasan da kasancewa 'yan BH. Abin tambaya, daman doka ta bayar da iznin kashe mutumin da ake zargi mai lafi ne? Na zata cewar ko mutum aka kama dumu-dumu yana aikata laifi sai an gabatar da shi gaban Shar'ah daga bisani kotu ta yi masa hukunci. Amma kiri-kiri ake keta haddin Mutane a Najeriya dan kawai su Musulmi ne, a kashe su ba da hakki ba, laifinsu kawai sunyi Imani da Allah da Manzon Allah. Muna fahimtar irin wannan sunkuru da hukumar SSS take yi karkashin wannan arniyar kokari ne na dakushe Musulunci da kuma fada da Musulmi a kai-kaice. Kawai an fake da BH ne dan a cuzgunawa Musulmi.
Duk wani Musulmi na gari a Najeriya yana yin Allah-wadai da dukkan wani Nau'i na tayar da hankali, kamar yadda addinin Musulunci yayi haramcin tayar da hankalin Mutanan da basu san hawa ba balle sauka, balle kuma har ta kai ga daukar makamai a dumfari mutane haka kurum a kawo karshen rayuwarsu ba tare da sun aikata wani laifi da suka cancanci hakan ba. Mun yi tir da dukkan wani dangi na zubar da jinin bayanin Allah, kuma ko waye ya aikata hakan muna kiran doka ta yi aiki akansa matukar an kama shi da laifi ko musulmi ne ko ba musulmi bane. Amma abin ya zama rainin wayo da rainin hankali, domin Kiristoci nawa aka kama dauke da makamai a Arewacin Najeriya zasu tayar da hankali, har Kwanturola na Kwastan aka kama da safarar makamai ta barauniyar hanya, amma me aka yi musu? Saboda kawai su Kiristoci ne suna da uwa a gindin murhu! Adalci shi ne a yiwa duk wanda aka kama da laifi hukunci dai-dai da abinda ya aikata ko daga wane yanki yake ko meye addininsa, babu yadda za'a maida wasu 'yan mowa wasu 'yan bora sannan a yi zatan dorewar zaman lafiya a tsakanin ko wacce irin al'umma; Mutum ko a tsakanin 'ya 'yansa ya fifita wani sai an samu rigima da rashin jituwa a tsakanin 'ya 'yan ballantana kuma al'ummar Najeriya da ake zaman doya da manja.
Bamu taba baiwa wani wanda ya aikata lafi kariya ba, ba kuma zamu taba zama inuwa daya da masu aikata laifuka dan basu kariya ba. Amma ya zama tilas a baiwa kowane dan kasa 'yancin walwala da yin addininsa kamar yadda kundin tsarin Muki ya bayar da dama, Kai ko tsarin Mulki bai bamu dama ba sai munyi Addinin Musulunci. Lallai sai an baiwa kowa 'yancinsa, domin babu yadda za'a dinga bin malamai na Musulunci ana yi musu dauki dai-dai sannan a ce mana ana son zaman lafiya, alhali ga kiristoci can anyi shakulatun bangaro da batunsu. Ina hukumar SSS take lokacin da Dokubo Asari ya yi barzanar kashemu idan bamu zabi Jonathan ba a 2015? Suna ina shugaban kiristocin Najeriya Oritsejafor yake kalamai na ganganci da gatsali ga Musulmi? Me suka yi ko kuwa dan an raina mu. Ba shakka Allah yana tare da wadan da suka yi Imani suka bada gaskiya.
Yasir Ramadan Gwale
02-12-2013

No comments:
Post a Comment