Siriya: Bashar Al-Assad . . . Sarari Mai Kare Gudun Doki!
Kusan yanzu an kwashe watanni sama da goma sha hudu ana dauki babu dadi da gwamnatin Siriya da kuma al'ummar kasar. Wannan bore tare da zanga-zangar neman shugaba Bashar Assad ya kama gabansa, ya samo asali ne daga guguwar sauyi da ta kada a kasashen larabawa kusan shekara daya da rabi kenan, kamar yadda kowa ya sani wannan guguwa tayi sanadiyar tafiyar ruwa da shugabannin larabawa 'yan kama karya irinsu Ben Ali na Tunisiya da Muhammad Hosny Mubarack na Masar da Mu'ammar Ghaddafi na Libya da Ali Abdallah saleh na Yeman. Har ila yau wannan bore da zanga-zanga shi ya janyo sauye sauye masu yawa a yanayin yadda kasashen larabaya ke tafiyar da shugabancinsu, misali kasashen Saudiyya da Bahrain da Kuwati da Qatari da Daular Laraba da Oman da Jordan duk sun aiwatar da sauye-sauye masu ma'ana wajen kaucewa fadawa cikin irin wannan zanga-zanga.
Tun bayan da wannan zanga-zanga ta barke a kasar Siriya, Shugaba Bashar Assad ya ke ta bin hanyoyin da zai kaucewa sauka daga shugabancin wannan kasa. Kamar yadda ya faru a sauran kasashen larabawa, cewa, al'ummar kasashen ne suka fito kan tituna suna neman shugabanninsu su san inda dare ya yi musu, haka abin ya faru a siriya, inda al'ummar kasar suka fito suna nuna adawa da mulki ko shugabancin Bashar Assad inda suke neman shima yabi takwarorinsa irinsu Ben Ali, amma Assad yace Allah ya kasheshi bazai bar wannan shugabanci da ya gada daga mahaifinsa ba shima dan kama karya.
Wato abin da ya ke faruwa a Siriya ya sha bamban da yadda ya faru a sauran kasashen larabawa. Kamar yadda muka gani, a sauran kasashen gabas ta tsakiya, al'ummarsu sunyi alla wadai da wasu gwamnatocinsu kuma suka nemi su sanya takalmansu su kama gabansu, amma kuma, idan ka kalli ita wannan kasa ta siriya kamar yadda gwamnatin kasar tayi shi ne inda ta maida abin tsakanin gwamnati da tsageru ko 'yan tada kayar baya kamar yadda suke cewa, kaga kenan, azahirin gaskiya ta sauyawa abin kama, domin yanzu suna ta kokarin su nunawa al'ummar duniya cewa ba wai 'yan kasar Siriya ne suke bore ba kamar yadda ya faru a sauran kasashen larabawa, a'a suna nunawa duniya cewa, wannan 'yan tada kayar baya ne suka hana zaune tsaye a kasar, kamar yadda jakadan Siriya a majalisar dinkin Duniya Bashar Jafari ya shaidawa kwamitin sulhun majalisar cewa wadan nan mutane 'yan ta'adda ne da suke samun goyon baya daga kasashen Qatari da Saudi Arebiya.
Wato kamar yadda ya faru a kasar Libiya, inda masu neman shugaba Ghaddafi ya kama gabansa suka dunkule suka kafa kungiya da zasu yi Magana da murya daya wato Libyan National Council, tare da bayyana sabuwar tutarsu mai launin baki da ja da kore da kuma taurari, kuma kasashen duniya da dama suka amince da wannan kawance na Libiya, wannan ta sanya kungiyar kasashen NATO ta taimakawa da wannan kungiya da makamai da kudaden gudanarwa domin ganin hakarsu ta cimma ruwa wajen yin awon gaba da Ghaddafi; to irin wannan abu ne ya faru a kasar Siriya, inda suma kungiyoyi masu neman ganin Shugaba Assad ya tafi suka kafa kungiya da zasuyi kawance domin suma suyi Magana da murya daya, wato suka ci nasarar samar da kungiyar Siriyan National Council ko SNC a takaice, sannan suma suka samar da tutarsu mai launin kore da fari da baki da kuma ratsin ja jayen taurari a tsakiyar farin, amma Assad ya sanyawa idonsa toka ya kira wannan kawance da cewa kawancen 'yan ta'adda ne.
Bashar Assad ya yi amfani da manyan makamai domin murkushe wannan kungiya ta SNC. Tabbas, Assad ya halaka dubban mutane a garuruwan Homs da Dar'a da Hama da Aleppo da Baba Amr da Idlib da kuma wani bangare na garin Damascus, kuma duk wannan abin da Assad yake yi, ya kwan da sanin cewa, manyan kasashen duniya masu kujerun naki a majalisar dinkin duniya ya zamemusu kadangaren bakin tulu, domin a gefe guda Amerika da Birtaniya da faransa suna goyon bayansa domin suna tsoron ya kubuce a samu wani shugaba mai kishin addini wanda zai zama barazana ga kasar Israela, sanna kuma, a daya bangaren kasashen Rasha da cana suna goya masa baya, domin tsarin da Siriya take tafiya akansa na gurguzu wanda wadan nan kasashe su ne suke yi masa jagoranci yanzu a duniya, don haka ne duk wani kuduri da za'a kawo akan Siriya a majalisar dinkin duniya Rasha zata hau kujerar naki tare da goyon bayan cana, shi ya sanya Bashar Al-Assad yake rawa tare da yakinin cewa namansa na jaka.
Idan kuma aka bi ta barauniyar hanya, za'a ga cewar Amerika da 'yan kanzaginta suna goyon bayan Assad ya sauka. Ba don komai suke neman Assad ya sauka ba, sai don irin mawuyacin halin matsin tattalin arziki da kasashen turai da amerika suke fama da shi, domin sanin kowa ne, Amerika da 'yan kanzaginta basu ji da dadi ba, a yakin da suka kwashe sama da shekaru goma suna gwabzawa da 'yan Taliban ko Al-qa'ida a Afghanistan da Pakistan domin kuddadene suka bi iska masu yawan gaske, kuma ba tare da anbiya wata bukata ta kuzo mu gani ba, don haka, akallo irin na harara garke Amerika na kallon irin kudin da suka salwanta kuma suna tsoron sake salwantar irin wadan nan kudade akan kasar Siriya. Shakka babu, Amerika da Birtaniya da Faransa zasu so Assad ya tafi a wannan marra ba don suna so ba, misali a sabbin alkaluma na baya bayan nan sun kara nuna cewa sabon shugaban kasar Faransa Hollendes yana fuskantar barazanar karuwa marasa aikin yi a kasar domin bayanai sun ce kusan kashi 12 na faransawa suna fama da rashin aikin yi, don haka dole faransa zata ji tsoron zura kudade cikin yakin da sun san babu nasara.
A karshen makon da ya gabata wakilin musamman na majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashen larabawa mista Kofi Annan ya gabatar da bayani a gaban zauren majalisar dinkin duniya, akan hakikanin abin da ya ganewa idanunsa a kasar ta Siriya da kuma yadda ya tattauna da Shugaba Assad akan kudurorin da ya je masa da su guda shida, inda farat da garaje yace, Assad ya yi watsi da su, kuma yace yana tsoron barkewar yakin basasa na iya barkewa a wannan kasa, zaman wanda ya gudana karkashin shugaban majalisar dinkin duniya Nassir Abdulaziz Al-Nassir da kuma babban sakataren majalisar Ban-ki-Moon, shima a lokacin da yake nasa jawabin sakatare janar na majalisar Banki-Moon yace kusan sama da mutum miliyan daya ne ke neman agaji na gaggawa a kasar siriya a yanzu haka. A wani rahoton kuma, danmajalisar dattawa daga majalisar dattawan Amerika Sanata John McCain ya nemi kasar Amerika da ta taimakawa da 'yan tawayen Siriya da makamai domin fatattakar shugaba Assda.
Idan bamu mantaba a 'yan kwanakin da suka gabata ne, dakarun gwamnatin Assad suka yi luguden wuta a garin Houla inda mazauna garin galibinsu sunni ne suka kashe sama da mutane 108 wanda mafiya yawancinsu mata ne da yara kanana, wannan abin da ya faru, kusan ya tayar da hankula sosai a duniya domin ya kara nuna karara yadda gwamntain Assad take cigaba da yin kisan kare dangi akan al'ummar kasar musamman mabiya sunnah, amma da yake Assad bashida kunya ya ce wai 'yan ta'adda ne suka kai wannan hari. Sannan kuma yanzu haka rahotannin da suke fitowa daga kasar ta Siriya suna cewa wasu mutane da ake kyautata zaton dakarun Assad ne sun kai wani mummunan hari a kauyen Hubair inda suka kashe mata da yara kanana kuma suka cinna mu su wuta wal-iyadubillah, a saboda haka ne majalisar dinkin duniya ta nemi a gudanar da bincike a akan wannan kisan gilla da akayiwa mutane a wannan kauye na Hubair, shi ma a lokacin da yake aikowa da gidan talabijin na BBC da rahoto daga kauyen, wkilin BBC yace da mutum ya shiga kauyen zaiji kaurin gawarwaki da aka kone duk da ya ce, jami'an gwamnati sun kwashe su, amma kuma kakakin gwamnatin kasar ta Siriya ya musanta wannan batu inda yace 'yan ta'adda ne suka kai wannan hari kuma a cewarsa mtum tara ne kacal aka kashe, duk wadan nan abubuwan da suke faruwa suna kara nunawa mutane su waye 'yan ta'adda tsakanin Assad da kuma al'ummar kasarsa, kuma a wannan gaba muke tabbatarwa da shugaba Assad cewa Hausawa suna cewa sarari mai kare gudun doki, don haka ga fili ga mai doki, idan zai iya ya karar da mutanan kasar ko kuma musulmi Ahlussunnah a Siriya, da ace Assad zai iya hana kansa mutuwa to da shi ne ya ci nasara, amma tunda yake a bayyane ta ke a gareshi cewa mahaifinsa Hafiz Al-Assad baya raye a wannan duniyar to watan wata rana shima haka zai bi shi, kuma zai tarar da abinda ya shuka kamar yadda shima mahaifinsa yake ganin abinda ya shuka a can.
Itama a nata bangaren kungiyar 'yan kasuwar kasar Siriya Siriyan Business Forum da suke a kasashen larabawa sunyi taro a kasar Qatar inda suka bayyana cewa zasu taimakawa da kungiyar SNC da kudade domin samun agaji da kuma karfafa musu gwiwa. Muna amfani da wannan dama wajen rokon Allah ya sakawa dukkan wadan da aka zalunta a kasar Siriya, ya Allah mata da yaran da aka kashe a birnin Houla basuji ba basu gani ba, ya Allah ka jikansu ka sanya al-jannah makomarsu, iyalansu kuma ka basu hakurin jure wannan rashi, sauran wadanda suka rasa rayukansu a sauran garuruwa Allah ka jikansu da rahama, ka sanya mutuwa ta zama hutu a garesu, gwamnatin zalunci ta Bashar Al-Assad kuma, Allah ka hanata zaman lafiya, ka gwara kansu, ya Allah ka wargaza sha'aninsu, Ya Allah ka kawowa bayinka dauki ta inda basu zataba. Allah ka taimaki musulunci da musulmi.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
A siriya hadin guiwar Amurka, Saudiya, Qatar, Turkey da Isra'ila ne suke son kifar da Gwamnatin Shugaba Basshar al-Asad, saboda irin gudunmawar da yake bawa kungiyar Hizbullah da kuma Palastinawa 'YanHamas, da kuma hulda qawance da yake yi da qasar Ira,
ReplyDeleteAl'ummar kasar Siriya su na son shugabansu, duk wata zanga-zanga da ake cewa ana yi da mutane da ake cewa sojojin Gwamnati na kashewa, qarya ce gidajen talabijin na al-Jazeera da Al-Arabiyya da BBC suke yadawa. Hotunan ma da suke nunawa, a wasu kasshe ne abun ya taba faruwa, si su dauko su ce a Siriya abin ya auku.