Sunday, June 3, 2012

Shaye-Shaye Tsakanin Matasa: Suwa ke da Laifi?

 Ahmadu Giade Shugaban Hukmar hana sha da fataucin Miyagun kwayoyi ta Najeriya

Shaye-Shaye Tsakanin Matasa: Suwa ke da Laifi?
Wannan harka ta shaye-shayen miyagun kwayoyi  tana daya daga cikin matsalar wannan zamani, kuma tana zamowa babban kalubale da yake fuskantar gwamnatoci da daman gaske a kasarnan. Hakika dabi'ar shaye-shaye mummunar dabi'ace musamman tsakanin matasa wadan da ake ganin su ne manyan gobe, matasan da idan lokaci ya yi ko hali ya kama su ne zasu jagoranci wannan kasa domin kaita ga gaci. Wannan babbar matsalace da ta ke barazana ga zama lafiyar kowace irin al'umma. Domin wajibin hukumomi ne tsarewa al'ummarsu hankalinsu da lafiyarsu, musamman acikin wannan mawuyacin lokaci.
Kusan yanzu, hakar shaye shaye ta sauya ba kamar yadda aka santa a shekarun baya ba. Yanzu kusan komai yana tafiya ne da zamani, da a yadda muka sani, daga mashaya taba sigari, sai masu zukar tabar wiwi wadan da sune muke kallo da cewa 'yan iska ne na kwatance, mai shan shalisho kuwa daman wannan kazami ne, ko su kansu wasu daga cikin 'yan shaye-shayen suna kyamar dan sholi, idan kuwa aka ce mutum yana shan giya, shakka babu lamari ya lalace, wannan mutumin babu wanda zai kalleshi da kima ko daraja. Idan kuwa aka ce wane dan kwaya ne to watakila yana shan Ajigarau ne, ko wani magani da ake kira da suna buta ko alabukum ko daagaa wanda duk wadan nan magungunan aji garau ne.
Amma yanzu wannan batu ba haka yake ba. Shaye Shaye ya daukin wani sabon salo ta yadda bawai kawai ga maza ya tsaya ba abin har da mata, ta yadda suke shan kwayoyi masu yawa domin su bugu, akwai magunguna da aka sani na tarine ko na mura sai mutum ya yi ta afasu yana korawa da ruwa tun yana gane mutane har sai ya dena, zakaji mamaki idan kaji yadda matasa suke baiwa wannan mummunan aiki muhimmanci, kuma wani Karin abin bakinciki da takaici har da manyan mutane da matsakaitan matasa da kuma dimbin yara sabbin balaga a wannan harka.
Magungunan da ake sha domin a bugu sun hada da Benelin da Totalin da emzolin da Rocci da sauran dangogin maganin tari ko mura, irin maganin da ake zubawa acikin 'yar karamar kwalba ake sha da dan karamin cokali sai ka samu yaro ko yarinya sun daddakeshi a lokaci guda, wanda wannan ya wuce over dose ya tafi alamar hauka, domin maganin da likita zai rubuta da za'ayi akalla mako biyu ana sha amma mutum ya shanyeshi a lokaci guda, wannan hauka ne ko hankali? wannan ya saba da duk wani lafiyayyan hankali. Galibi yanzu masu irin wannan shan magani domin buguwa mata sukafi yawan yinsa, wasu sukance idan aka hadashi da lemon lakasera ya fi tafiya dai-dai; Allah ya kiyaye.
Akwai kuma wasu 'yan uwa matasa da yawa musamman maza da suke shan wasu nau'ikan da ba wadan nan ba. Misali akwai wasu magunguna da ake kira Rafanol da Tiriftizon wanda wadan nan magunguna har doki ake baiwa su, amma saboda kaiwa makura irin ta matasanmu sai dan adam ya sha wadan nan magunguna domin ya bugu; a lokacin da ake tambayar wani da yake ta'amali da kayan buguwa waishin wane irin dadi yakeji idan ya bugu? Ya fadi cewa shi dai idan yasha ya bugu ji yake kamar yana tafiya akan katifa, yace zai ji iska na shigarsa ta ko ina, wai a tunanisa wannan shi ne jindadin shaye-shaye, wasu kuma su ce maka wai sunfi samun nutsuwa idan sukayi wannan shaye-shaye, ko kuma wai idan ran mutum ya baci to ya samu yadan busa taba sigari ko wiwi a lokacin wai zai ji dama.
Bayaga wannan, akwai wata kwaya da take fitowa acikin ciyawa. Ita dai wannan kwaya ciyawace kamar hatsi da ta ke fitowa a waje mai tsandauri, ana kiranta da sunan zakami, wanda idan mutum yasha idan mai karamar kwakwalwa ne idan ba'ayi hankali ba shi kenan ya tafi, duk wannan domin a bugu aji garu, sannan harwa yau akwai 'yan wiwi suna nan suma suna yin nasu shaye-shayen, wanda 'yan siyasarmu da dama suka taimaka musu da wannan taba ta wiwi domin suji dadin yin aiki, me kake jin zai faru a lokacin da mutum yasha yaji tayi masa karo? komai ma zai iya yi; kuma da yake shi Ubangiji ba azzalumin bawansa bane su irin wadan nan 'yan siyasa da suke lalata yaran wasu ta hanyar saya musu kayan maye, suma 'ya 'yansu suna can kasashen da aka kaisu karatu, suna koyan shan tabar shisha irin wadda larabawa suke zuka, da shan kwayoyi.
Ka duba cikin garuruwanmu cike yake da mahaukata da tababbu. Akwai mahaukata da yawa wadan da ta sanadiyar shaye-shaye suka sami wannan tabi na hauka, wasu kuma, ba mahaukata bane tuburan zautuwa kawai sukayi, suna nan suna yawo kwararo-kwararo kuma suna baraza ga rayuwar mutane, amma kuma, hukuma tayi ko inkula da su, sai kaga narkekyan kato ya haukace kuma yana yawo da sanda ko wani karfe da ya iya ji wa duk wanda ya samu ciwo da shi amma kuma hukumomi sun barsu kara zube suna yawo cikin mutane ba tare da yin wani yunkuri akan su ba.
Kamar yadda hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NAFDAC ta bayar da wasu alkaluma da suke nuna cewa a jihar KANO ana kara samun adadin 'yan kwaya ko 'yan wiwi yana karuwa cikin sauri. Wannan babban kalubale ne ga hukuma, hakkin hukuma ne ta tsarewa al'umma hankalinsu, gwamnati tafi kowa sanin duk inda ake sayar da wadan nan miyagun kwayoyi, akwai fitattun unguwanni a kano da suka shara da hada-hadar wadan nan miyagun kwayoyi kuma hukuma tasan das u, amma saboda su wadan nan matasa da suke shan miyagun kwayoyin suna yiwa 'yan siyasa amfani shi yasa basu cika daukar wani mataki na kuzo mu gani ba, lallai ya zama wajibi gwamnatocin jihohi da gwamnatin Tarayya su tashi tsaye haikan wajen yaki fafur da wannan mummunar dabi'a ta shaye-shaye tsakanin matasa.
Shaye-shaye babban laifi ne da ya sabawa hankali da tunanin dan adam, haka kuma ya saba da dokokin kowace irin kasa, above all kuma ya sabawa addini da al'ada da tarbiyyarmu da zamantakewarmu, lallai wannan babban laifine da ya shafi bangarori da daman gaske, kama daga su kansu masu shaye-shayen da iyaye da al'umma da kuma gwamnati.
Iyaye suna da laifi babban akan wannan batu. Domin wasu da yawa suna sane da cewa 'ya 'yansu na shaye-shaye amma kuma basa daukar wani mataki na magance hakan, misali, zaka samu galibin yaranmu sukan fara koyon shaye-shaye ne a lokacin bukukuwan Sallah, wasu suna kiran abin da suna happy sallah, wato a more a gwangwaje yadda ake so, inda zakaga kananan yara na koyar zukar taba sigari, wanda daga nan ake cigaba zuwa busa tabar wiwi idan kuma akayi rashin nasara abin ya dore sai kaji yaro ya iya shan komai. Kaga wannan iyaye ne suka yi sakaci sosai akan 'ya 'yansu, domin zaka samu ba'a cika lura da zirga-zirgar yara ba a lokacin bukukuwan sallah, kowane uba yabar 'ya 'yansa su shanawa yadda suke so batare da kwabar sub a, ko bibiyar inda suke zuwa, da abinda su ke yi.
Lallai wajibin iyayene su tashi tsaye haikan wajen ganin sun yaki wannan mugunyar dabi'a ta shaye-shaye. Kamar yadda Bahaushe yake cewa d'a na kowane, dole iyaye da dattawa da masu unguwanni su tashi domin yaki da wannan mugunyar dabi'ar, wani abin takaicin shi ne wasu masu mulkin sukansu 'yan kwaya ne, domin nasan wani mai unguwa da a cikin zauren gidansa ake yin shaye-shaye kuma hardashi, idan kazo ba ka da ko kwabo to insha Allahu bazaka rasa 'yar tabar da zaka zuka a wajensa ba, kaga wannan shi ne baya babu zani kenan, wai mai dokar barci ya bige da gyangyadi.
Haka kuma, wajibin hukumomi ne su tashi tsaye domin yaki da sha da fataucin wadan nan miyagun kwayoyi, ta hanyar yin hukunci mai tsanani ga duka wanda aka kama yana harkar safarar wadan nan miyagun kwayoyi da kuma masu sha, lallai dole gwamnati ta takawa 'yan siyasa birki domin suna taka muhimmiyar rawa wajen jefa 'yan uwanmu matasa cikin wannan mummunan yanayi, da yawansu su ne suke sayamusu wadan nan kayan maye, da basu makamai domin su farwa abokan 'yan hamayya.
Sannan yana da kyau gwamnati ta samar da wata hukuma ko ma'aikata wadda zata ringa tallafawa irin wadan nan matasa da sukayi shaye-shayen kuma suka dena. A tallafa musu ta hanyar koyamusu sana'o'I da basu jari da mayar dasu makaranta, tare kuma da sama musu malaman da zasu koyar da su tsarki da alwala da sallah da sauran hukunce-hukuncen addini, wallahi da yawan wasu masu wannan shaye-shaye idan kayi hira dasu zaka samu suna da kwakwalwar gaske, domin na taba ganin wani dan shaye-shaye da duk lissafin duniya zaiyi maka shi da ka batare da yayi amfani da kwakuleta ba, irin wadan nan matasa masu kwakwalwa muke sakaci da su suke haukacewa a banza da wofi, batare da yi musu wani tanadi ba wannan babbar hasara ce garemu.
Sannan su kansu al'umma(society/community) su sani wadan nan matasa 'yan uwanmu ne, daga cikinmu suke. Lallai ya zama wajibi a garemu wajen janyo su tare da nuna musu muhimmanci rayuwa, da kuma illar wannan harka ta shaye-shaye, domin wasu zaka samu suna jin Magana, suna daukan shawara, matsalar kawai itace wanda zai kirasu yayi musu nasiha ne babu, kowa ya kame hannu tunda babu dansa to dan kowa ya mutu, abinda Bahaushe yake cewa idan jifa ya shallake kanka . . . lallai sai mun tsaya tsayin daka wajen ganin munbi hanyoyin da suka kamata wajen ganin anshawo kan wannan matsala ta shaye shaye wadda barazanarta tana da yawan gaske. Allah ya shirya mana al'ummarmu. Amin.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadagwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment