Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mataimakin Shugaban Kasa Muhammad Namadi Sambo
Bayan sallama irin ta addinin Musulunci Assalamu Alaikum Warahmatullah, ya maigirma mataimakin Shugaban kasa ina fatan kana lafiya,ina kuma fatan wannan wasika zata riskeke cikin koshin lafiya. Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa, hakika lokaci ya yi da zamu fito fili mu bayyana maka gaskiyar abinda yake damunmu, musamman mu al'ummarka, wato mu mutanan Arewacin Najeriya, ya maigirma, shakka babu ko munki ko munso kai ne mutumin da dokar Najeriya ta ce shi ne mataimakin shugaban kasa, ko muna sonka ko bama sonka bamu isa muce kai ba mataimakin shugaban kasa bane, kaine zaka dafawa wannan gwamnati mai ci a matsayin mataimaki kamar yadda doka ta tanada. Don haka dole mu kawo kuka inda doka ta tanadar.
Kuma ba boyayyan al'amari bane cewar mu mutanan Arewa bama tare da wannan jam'iyya taku, wannan kuma bazai rasa nasaba da kasa samar mana da abubuwan more rayuwa da jam'iyyar taku ta shafe sama da shekaru 13 tayi tundaga shekarar 1999 har ya zuwa yanzu, babu wata matsala da jam'iyyarku ta dauka daga Arewa kuma ta kawo karshenta, amma kuma wannan ba zai zama dalilin da zai sanya a kasa yi mana adalci ba, domin muma 'yan Najeriya ne kamar yadda kowa yake da hakki haka muma muke da hakki, dan haka abinda ake kira romon demokaradiyya muna da hakki a cikinsa tunda gwamnatin bata 'ya jam'iyya daya bace, gwamnati ce ta 'yan Najeriya.
Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa, hakika idan zamu fadi gaskiya, babu wani mutum da yake da mukami mafi girma a fadin tarayyar Najeriya da ya fito daga yankinmu na Arewa face kai, duk wani wanda zai fito yayi ikirarin cewa shi ne shugabanmu a Arewa koma bayanka ne, domin kaine wanda doka ta sani, ya maigirma mataimaikin Shugaban kasa, da kai da gwamnonin Arewa 19 da sanatocin Arewa 58 da 'yan majalisun tarayya sama da 100 kune shugabanninmu a yankin Arewa, inada yakinin cewa abinda yake faruwa musamman game da yankin da ka fito wato Arewa ba boyayye bane a gareka, musamman al'amuran da suka shafi tsaro da talauci da rashin aikin yi da suka addabi galibin matasanmu da fatara da tayi mana daurin butar malan.
Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa ina mai tunasar da kai cewar, kai ne ka saba al-qurani mai tsarki a gaban miliyoyin 'yan Najeriya a filin Eagle Square da kuma ta gaban akwatunan talabijin kasha rantsuwar kama aiki, ka rantse da Allah cewar zaka tsare gaskiya da amanar da 'yan Najeriya suka baku, kuma zaku kare tsarin mulkin tarayyar Najeriya, ina mai cike da fatan cewa baka manta da wannan ranar ba, ya mai girma mataimakin shugaban kasa, hakika kai musulmi ne dan uwanmu, kamar yadda muke yiwa kawunanmu fatan samun rahamar Allah a ranar gobe kiyama, kaima muna fatan ka samu wannan rahama tasa subahanahu wata'ala, ranar da ya kirata da sunaye daban daban kamar Taghabun da sauransu, ranar kuma da yace 'ya 'ya da dukiya bazasu amfaneka da komai ba "illa man atallahu bi kalbin saleem" wato tsarkakkiyar zuciya ta gaskiya ita zata kubutar da dukkanninmu a wannan rana, Allah ya bamu ikon samun rahamarsa damu da kai baki daya.
Kamar yadda kowa ya sani ne cewar gwamnatinku ta gaza kwarai da gaske wajen kare rayukan miliyoyin al'ummar Najeriya. Ya maigirma, wannan maganar ko wanda ba'a Najeriya yake ba, idan dai har yana bibiyar al'amuran yau da kullum da suke fitowa daga Najeriya yasan da haka, ya mai girma, hakika, tabbas, duk wanda ya rasa ransa walau ta hanyar hadarin mota ko 'yan fashi da makami ko tashin bom ko harbin sari ka noke, koma wacce irin hanya mutum ya mutu ba tare da ya cancanci mutuwa a lokacin ba, wannan alhaki ne da ya rataya a wuyanku, kai da shugaban kasa, domin duk laifin da zai dauka to sai ka kama masa wajen dauka tunda gwamnatinku ce kuma kaine mataimaki.
Ya maigirma Mataimakin Shugaban Kasa, kamar yadda ka sani tun lokacin da aka bayar da sanarwar cewar jam'iyyarku ce ta sami nasarar zaben 2011 aka fara karya kumallo da asarar rayuka musamman a yankin da ka fito, kuma abin yafi muni ainun a jihar da kayi gwamna wato Kaduna, hakika mutane da yawa sun rasa rayukansu a garin zankowa a rikicin bayan zabe, ba dan sun cancanci mutuwa a wannan lokacin ba, ankashe mutanen da basu san hawa ba basu san sauka ba, saboda kawai zalinci da nuna cewa amfi karfinsu, bayan kuma dokar kasa ta baiwa kowa damar zama a duk inda yaga dama, ya maigirma mataimakin shugaban kasa dukkanmu 'yan Najeriya musamman mu 'yan Arewa mun taya 'yan uwanmu 'yan zankowa al-hinin abinda ya same su na rasa rayuka da kuma asarar dimbin dukiya, ya maigirma, wannan abinda ya faru a jiharka ne kuma mahaifarka, amma ko kodan bamuji ka kai ziyara domin jajanta musu abinda ya shafesu ba domin su dan rage radadain abinda ya samesu.
Ya maigirma, kamar yadda ka sani, babu dadewa da kammala wannan zabe abokinka, shugaban kasa yazo har wannan jiha taka inda yakai ziyara garuruwan da ke kudancin Kaduna kuma ya bude majami'a domin nuna godiya da yadda ka taimaka musu suka samar da Gwamna na farko dan kudancin Kaduna. Ya mai girma mataimakin shugaban kasa, kasani har yanzu mutanan wannan gari na zankowa suna nan a sansanin al-hazai dake Mando a cikin garin Kaduna a matsayin 'yan gudun hijira, wannan babban abin takaici ne a garemu, kuma a gareka, ace a kasarmu 'yan uwanmu suna gudun hijira a mahaifarsu, kuma muna da dan uwanmu da yake mataimakin shugaban kasa, wallahi wannan abin tambaya ne a gareka ranar gobe kiyama.
Ya mai girma, yanzu babban abinda ya damemu musamman a Arewa shine matsalar tsaro. Mun san da cewa kuna da masaniyar yadda al'amura ke wakana, kuma kullum kalaman da suke fitowa daga bakunanku sune cewar zaku dauki mataki ko kuma kuna nan kuna daukar mataki, amma kuma har wannan lokaci da nake rubuta wannan wasika ba muda aminci acikin garuruwanmu zaman zullumi karuwa yake, bama bamai kara fashewa suke, adadin rayukan da ake rasawa kara yawa suke. Ya maigirma, shakka babu wannan nauyi ne wanda ya rataya a wuyanku, na samar mana da tsaron rayukanmu a matsayinmu na 'yan Najeriya, idan har za'ace gwamnatinku ta gaza ta kowanne fanni baku iya samar mana da komai ba, to yakamata a ce muna da kariyar rayukanmu, ya maigirma, shin wane irin zafi ko radadi ka ke ji a ranka a duk lokacin da bam ya tarwatse al'ummarka suke ta halaka? ganin yadda jinin al'ummar da ka fito daga cikinta yake kwarara kamar ruwa a kogin gurara. Lallai ne zaku amsa tuhuma agaban Allah ranar gobe kiyama akan dukkan wani dan Najeriya da ya rasa ransa a lokacin da kuke rike da ragamar shugabancin wannan kasa.
Ya maigirma mataimakin shugaban kasa muna rokon ku, da ku duba Allah, ku tuna ranar da za'a kawo ku gaban ubangiji a daure da sarka, wanda malamai suka gayamana cewar adalcin kowane shugaba shi ne zai kwance shi, ku ji tsoran wannan ranar, ku taimakawa talakawa bayanin Allah, ku taimakawa marayu, ku taimakawa kananan yara da mata da tsofaffi ku samarmana da aminci acikin garuruwanmu, hakkin kowace gwamnati ne ta samarwa da al'ummarta tsaron rayukansu da dukiyoyinsu, ya maigirma, dan Allah wane irin dadi ko akasinsa ka ke ji a lokacin da ka fita wata kasar waje kaga al'umma na zaune cikin kwanciyar hanakali da lumana idan ka tuna al'ummarka?.
Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa, muna da bukatar samun diyyar rayukan 'yan uwanmu da suka rasa rayukansu a sanadiyar dukkan rikice rikicen da suka wakana a karkashin gwamnatinku da tashe tashen bama bamai a kusan daukacin jihohin Arewa, kamar yadda kuka bayar da diyya ga masu hidimar kasa 'yan kudu da aka kashe a Bauchi a sanadiyar rikicin bayan zabe a shekarar 2011, lallai muma muna rokon a bamu diyyar 'yan uwanmu da muka rasa a sanadiyar wadan nan tashe tashen bama bamai da sauransu ko al'ummarmu zasu samu su rage radadin abinda ya samesu, lallai idan kunyi haka watakila ku sami sassauci ranar gobe kiyama.
Ya mai girma, wani bangare da kuma yake kara cimana tuwo a kwarya shine fama da muke yi da bakin talauci da rashin aikin yi tsakanin dimbin matasanmu, da yawa suna nan sun kamala karatu babu aikin fari bare na baki, ga dimbin talakawa a kauyuka da birane wadan da basu sami dama sun yaki jahilci ba suma suna bukatar a taimaka musu ta fannin noma da sana'o'i. A kwanakin baya wata hukuma ta bayar da kididdigar cewar Arewacin Najeriya shi ne yankin da yafi kowane yanki fama da talauci a fadin Najeriya, kuma jihar Sokoto itace jiha ta farko a talauci, muna fatan gwamnatinku ta dubemu ta saukaka mana halin da muke ciki, kuma muna fatan gwamnatinku ta sauke nauyin da yake akanta na rage talauci a tsakanin 'yan Najeriya kamar yadda kukayi alkawari a lokacin da kuke fafutukar yakin neman zabe; muna da masaniyar wani shiri da wannan gwamnati taku ta fito da shi mai suna You Win saboda samarwa da dimbin matasanmu aikin yi, ya maigirma shakka babu wannan shiri mu mutanan Arewa bama amfanarsa yadda ya kamata, a matsayinka na shugabanmu ya kamata ka bincika ka gani.
Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa, harkoki da dama sun tabarbare a wannan kasar tamu, lallai idan kuka bari lokaci ya cimmuku baku iya yin kokari wajen sauke nauyinku ba, wallahi zaku kasance masu nadama a lokacin da bazata yi muku amfani ba, kuma ku sani zaku kasance ababen tuhuma a wajen Allah ranar gobe kiyama.
Daga karshe ya maigirma mataimakin shugaban kasa, ina mai amfani da wannan damar domin mika ta'aziyata gareka ta rashin da kayi na dumbin al'ummaka na Arewa a sakamakon rikice rikice da dama da suka hada da Jos da zankowa da sauransu, ina fatan Allah yakai rahama ga wadan da suka rigamu gidan gaskiya, wadanda suke kwance kuma a asibitoci Allah ya basu lafiya, Allah ya bamu lafiya da zama lafiya a Arewa da Najeriya baki daya, wassalam, Nagode ka huta lafiya.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
No comments:
Post a Comment