Saturday, June 30, 2012

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mataimakin Shugaban Kasa Muhammad Namadi Sambo


Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mataimakin Shugaban Kasa Muhammad Namadi Sambo

Bayan sallama irin ta addinin Musulunci Assalamu Alaikum Warahmatullah, ya maigirma mataimakin Shugaban kasa ina fatan kana lafiya,ina kuma fatan wannan wasika zata riskeke cikin koshin lafiya. Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa, hakika lokaci ya yi da zamu fito fili mu bayyana maka gaskiyar abinda yake damunmu, musamman mu al'ummarka, wato mu mutanan Arewacin Najeriya, ya maigirma, shakka babu ko munki ko munso kai ne mutumin da dokar Najeriya ta ce shi ne mataimakin shugaban kasa, ko muna sonka ko bama sonka bamu isa muce kai ba mataimakin shugaban kasa bane, kaine zaka dafawa wannan gwamnati mai ci a matsayin mataimaki kamar yadda doka ta tanada. Don haka dole mu kawo kuka inda doka ta tanadar.
Kuma ba boyayyan al'amari bane cewar mu mutanan Arewa bama tare da wannan jam'iyya taku, wannan kuma bazai rasa nasaba da kasa samar mana da abubuwan more rayuwa da jam'iyyar taku ta shafe sama da shekaru 13 tayi tundaga shekarar 1999 har ya zuwa yanzu, babu wata matsala da jam'iyyarku ta dauka daga Arewa kuma ta kawo karshenta, amma kuma wannan ba zai zama dalilin da zai sanya a kasa yi mana adalci ba, domin muma 'yan Najeriya ne kamar yadda kowa yake da hakki haka muma muke da hakki, dan haka abinda ake kira romon demokaradiyya muna da hakki a cikinsa tunda gwamnatin bata 'ya jam'iyya daya bace, gwamnati ce ta 'yan Najeriya.
Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa, hakika idan zamu fadi gaskiya, babu wani mutum da yake da mukami mafi girma a fadin tarayyar Najeriya da ya fito daga yankinmu na Arewa face kai, duk wani wanda zai fito yayi ikirarin cewa shi ne shugabanmu a Arewa koma bayanka ne, domin kaine wanda doka ta sani, ya maigirma mataimaikin Shugaban kasa, da kai da gwamnonin Arewa 19 da sanatocin Arewa 58 da 'yan majalisun tarayya sama da 100 kune shugabanninmu a yankin Arewa, inada yakinin cewa abinda yake faruwa musamman game da yankin da ka fito wato Arewa ba boyayye bane a gareka, musamman al'amuran da suka shafi tsaro da talauci da rashin aikin yi da suka addabi galibin matasanmu da fatara da tayi mana daurin butar malan.
Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa ina mai tunasar da kai cewar, kai ne ka saba al-qurani mai tsarki a gaban miliyoyin 'yan Najeriya a filin Eagle Square da kuma ta gaban akwatunan talabijin kasha rantsuwar kama aiki, ka rantse da Allah cewar zaka tsare gaskiya da amanar da 'yan Najeriya suka baku, kuma zaku kare tsarin mulkin tarayyar Najeriya, ina mai cike da fatan cewa baka manta da wannan ranar ba, ya mai girma mataimakin shugaban kasa, hakika kai musulmi ne dan uwanmu, kamar yadda muke yiwa kawunanmu fatan samun rahamar Allah a ranar gobe kiyama, kaima muna fatan ka samu wannan rahama tasa subahanahu wata'ala, ranar da ya kirata da sunaye daban daban kamar Taghabun da sauransu, ranar kuma da yace 'ya 'ya da dukiya bazasu amfaneka da komai ba "illa man atallahu bi kalbin saleem" wato tsarkakkiyar zuciya ta gaskiya ita zata kubutar da dukkanninmu a wannan rana, Allah ya bamu ikon samun rahamarsa damu da kai baki daya.
Kamar yadda kowa ya sani ne cewar gwamnatinku ta gaza kwarai da gaske wajen kare rayukan miliyoyin al'ummar Najeriya. Ya maigirma, wannan maganar ko wanda ba'a Najeriya yake ba, idan dai har yana bibiyar al'amuran yau da kullum da suke fitowa daga Najeriya yasan da haka, ya mai girma, hakika, tabbas, duk wanda ya rasa ransa walau ta hanyar hadarin mota ko 'yan fashi da makami ko tashin bom ko harbin sari ka noke, koma wacce irin hanya mutum ya mutu ba tare da ya cancanci mutuwa a lokacin ba, wannan alhaki ne da ya rataya a wuyanku, kai da shugaban kasa, domin duk laifin da zai dauka to sai ka kama masa wajen dauka tunda gwamnatinku ce kuma kaine mataimaki.
Ya maigirma Mataimakin Shugaban Kasa, kamar yadda ka sani tun lokacin da aka bayar da sanarwar cewar jam'iyyarku ce ta sami nasarar zaben 2011 aka fara karya kumallo da asarar rayuka musamman a yankin da ka fito, kuma abin yafi muni ainun a jihar da kayi gwamna wato Kaduna, hakika mutane da yawa sun rasa rayukansu a garin zankowa a rikicin bayan zabe, ba dan sun cancanci mutuwa a wannan lokacin ba, ankashe mutanen da basu san hawa ba basu san sauka ba, saboda kawai zalinci da nuna cewa amfi karfinsu, bayan kuma dokar kasa ta baiwa kowa damar zama a duk inda yaga dama, ya maigirma mataimakin shugaban kasa dukkanmu 'yan Najeriya musamman mu 'yan Arewa mun taya 'yan uwanmu 'yan zankowa al-hinin abinda ya same su na rasa rayuka da kuma asarar dimbin dukiya, ya maigirma, wannan abinda ya faru a jiharka ne kuma mahaifarka, amma ko kodan bamuji ka kai ziyara domin jajanta musu abinda ya shafesu ba domin su dan rage radadain abinda ya samesu.
Ya maigirma, kamar yadda ka sani, babu dadewa da kammala wannan zabe abokinka, shugaban kasa yazo har wannan jiha taka inda yakai ziyara garuruwan da ke kudancin Kaduna kuma ya bude majami'a domin nuna godiya da yadda ka taimaka musu suka samar da Gwamna na farko dan kudancin Kaduna. Ya mai girma mataimakin shugaban kasa, kasani har yanzu mutanan wannan gari na zankowa suna nan a sansanin al-hazai dake Mando a cikin garin Kaduna a matsayin 'yan gudun hijira, wannan babban abin takaici ne a garemu, kuma a gareka, ace a kasarmu 'yan uwanmu suna gudun hijira a mahaifarsu, kuma muna da dan uwanmu da yake mataimakin shugaban kasa, wallahi wannan abin tambaya ne a gareka ranar gobe kiyama.
Ya mai girma, yanzu babban abinda ya damemu musamman a Arewa shine matsalar tsaro. Mun san da cewa kuna da masaniyar yadda al'amura ke wakana, kuma kullum kalaman da suke fitowa daga bakunanku sune cewar zaku dauki mataki ko kuma kuna nan kuna daukar mataki, amma kuma har wannan lokaci da nake rubuta wannan wasika ba muda aminci acikin garuruwanmu zaman zullumi karuwa yake, bama bamai kara fashewa suke, adadin rayukan da ake rasawa kara yawa suke. Ya maigirma, shakka babu wannan nauyi ne wanda ya rataya a wuyanku, na samar mana da tsaron rayukanmu a matsayinmu na 'yan Najeriya, idan har za'ace gwamnatinku ta gaza ta kowanne fanni baku iya samar mana da komai ba, to yakamata a ce muna da kariyar rayukanmu, ya maigirma, shin wane irin zafi ko radadi ka ke ji a ranka a duk lokacin da bam ya tarwatse al'ummarka suke ta halaka? ganin yadda jinin al'ummar da ka fito daga cikinta yake kwarara kamar ruwa a kogin gurara. Lallai ne zaku amsa tuhuma agaban Allah ranar gobe kiyama akan dukkan wani dan Najeriya da ya rasa ransa a lokacin da kuke rike da ragamar shugabancin wannan kasa.
Ya maigirma mataimakin shugaban kasa muna rokon ku, da ku duba Allah, ku tuna ranar da za'a kawo ku gaban ubangiji a daure da sarka, wanda malamai suka gayamana cewar adalcin kowane shugaba shi ne zai kwance shi, ku ji tsoran wannan ranar, ku taimakawa talakawa bayanin Allah, ku taimakawa marayu, ku taimakawa kananan yara da mata da tsofaffi ku samarmana da aminci acikin garuruwanmu, hakkin kowace gwamnati ne ta samarwa da al'ummarta tsaron rayukansu da dukiyoyinsu, ya maigirma, dan Allah wane irin dadi ko akasinsa ka ke ji a lokacin da ka fita wata kasar waje kaga al'umma na zaune cikin kwanciyar hanakali da lumana idan ka tuna al'ummarka?.
Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa, muna da bukatar samun diyyar rayukan 'yan uwanmu da suka rasa rayukansu a sanadiyar dukkan rikice rikicen da suka wakana a karkashin gwamnatinku da tashe tashen bama bamai a kusan daukacin jihohin Arewa, kamar yadda kuka bayar da diyya ga masu hidimar kasa 'yan kudu da aka kashe a Bauchi a sanadiyar rikicin bayan zabe a shekarar 2011, lallai muma muna rokon a bamu diyyar 'yan uwanmu da muka rasa a sanadiyar wadan nan tashe tashen bama bamai da sauransu ko al'ummarmu zasu samu su rage radadin abinda ya samesu, lallai idan kunyi haka watakila ku sami sassauci ranar gobe kiyama.
Ya mai girma, wani bangare da kuma yake kara cimana tuwo a kwarya shine fama da muke yi da bakin talauci da rashin aikin yi tsakanin dimbin matasanmu, da yawa suna nan sun kamala karatu babu aikin fari bare na baki, ga dimbin talakawa a kauyuka da birane wadan da basu sami dama sun yaki jahilci ba suma suna bukatar a taimaka musu ta fannin noma da sana'o'i. A kwanakin baya wata hukuma ta bayar da kididdigar cewar Arewacin Najeriya shi ne yankin da yafi kowane yanki fama da talauci a fadin Najeriya, kuma jihar Sokoto itace jiha ta farko a talauci, muna fatan gwamnatinku ta dubemu ta saukaka mana halin da muke ciki, kuma muna fatan gwamnatinku ta sauke nauyin da yake akanta na rage talauci a tsakanin 'yan Najeriya kamar yadda kukayi alkawari a lokacin da kuke fafutukar yakin neman zabe; muna da masaniyar wani shiri da wannan gwamnati taku ta fito da shi mai suna You Win saboda samarwa da dimbin matasanmu aikin yi, ya maigirma shakka babu wannan shiri mu mutanan Arewa bama amfanarsa yadda ya kamata, a matsayinka na shugabanmu ya kamata ka bincika ka gani.
Ya maigirma mataimakin Shugaban kasa, harkoki da dama sun tabarbare a wannan kasar tamu, lallai idan kuka bari lokaci ya cimmuku baku iya yin kokari wajen sauke nauyinku ba, wallahi zaku kasance masu nadama a lokacin da bazata yi muku amfani ba, kuma ku sani zaku kasance ababen tuhuma a wajen Allah ranar gobe kiyama.
Daga karshe ya maigirma mataimakin shugaban kasa, ina mai amfani da wannan damar domin mika ta'aziyata gareka ta rashin da kayi na dumbin al'ummaka na Arewa a sakamakon rikice rikice da dama da suka hada da Jos da zankowa da sauransu, ina fatan Allah yakai rahama ga wadan da suka rigamu gidan gaskiya, wadanda suke kwance kuma a asibitoci Allah ya basu lafiya, Allah ya bamu lafiya da zama lafiya a Arewa da Najeriya baki daya, wassalam, Nagode ka huta lafiya.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
 

Me Ya Sa Tarihi Ke Maimaita kansa?


Me Ya Sa Tarihi Ke Maimaita Kansa?
Kusan a bayyana ya ke cewar amsar wannan tamabaya gajeruwa ce. Shakka babu kamar yadda muka sani sau da dama a rayuwa tarihi kan maimaita kansa daga lokaci zuwa lokaci, muna iya cewa dalilin da ya sanya tarihi ke maimata kansa shi ne, saboda mutane basu cika daukar darasin da ke cikinsa ba, hakika Allah ya halicci dan adam mai yawan mantuwa, wasu lokutan mantuwa takan zama abin so kwarai da gaske, wani zubin kuma mantuwa takan zama abin zargi.
Hakika darasin da ke cikin tarihi, wata makaranta ce babba da kalilan daga cikin mutane ne sukan kammalata da kuma samun kyakykyawan sakamo, wasu kuma sukan fara su kasa gamawa, har mai aukuwa ta auku akansu, a lokacin da wadan da sukaci jarabarwar tarihi ke murna wasu kuma na cizon yatsa da dana sani a lokacin da ba tada amfani.
Idan muka duba tarihi shekaru 42 da Gaddafi ya yi yana mulkin kasar Libiya sunzo karshe ne a ranar 20 ga watan oktoban 2011; lokacin da guguwar sauyi ta kada kuma tayi awon gaba da shi, Gaddafi dai baiyi amfani da darasin da ke cikin tarihi ba don day a kalli wadan da suka gabaceshi da wata kila abinda ya sameshi bai sameshi ba, haka shi ma Saddam Hussein na Iraqi mulkinsa ya zo karshe ne a shekarar 2006, Husni Mubarack na Masar shima mulkinsa yazo karshe ne a shekarar 2011 da su Ben Ali na Tunisiya da Ali Abdallah Saleh na Yemen duk mulkinsu yazo karshe ne a shekarar 2011. Duka wadan nan shugabanni da suka gabata da sun kalli tarihi kuma sun yi aiki da shi da watakila basu fada cikin halin da suka fada ba, kuma abinda ya samesu babban darasi ne ga na baya.
Idan kuma muka kalli shugabanni irinsu Robert Mugabe na Zimbabwe wanda yake akan karagar mulki kusan tun shekarar 1980, da kuma Paul Biya na Kamaru wanda shima ya shafe tsawon Shekaru akan mulki kusan tun 1982 yake a karagar mulki, shima Yuwairi Musaveni na Uganda ba a barshi a bayaba wajen diban dogon lokaci akan mulki wanda shima yake akai tun daga shekarar 1985 har kawo yanzu; lallai wadan nan shugabanni ya kamata suyi karatun ta nutsu kuma su kalli tarihi su yi tunanin gobe da kuma abinda zai faru nan gaba, Shakka babu kamar shekaru uku da suka gabata, idan kace ka yi katarin haduwa da Husni Mubarack na Masar a sansanin shakatawar nan na Sham el-sheikh ka ce Muhammad Mursi shi ne magajinsa a shekarar 2012 watakila ya ce maka haka bazata taba faruwa ba, amma da yake tarihi baibar komai ba yau ga Mubarack na raye kuma yana kallon wani yana shugabancin Masar ba shi ba.
Shugaba Fidel Castro na kasar Cuba kusan shi ne ya yi katarin gamawa da mulkinsa lafiya. Hakika zaka iya cewa Castro ya taki sa'a, domin yabar karagar mulki ba dan al'ummarsa sun juya masa baya ba kamar yadda ya faru da Mubarack da Ben Ali da sauransu, hakika tsufa ya yiwa castro shigar sauri a lokacin da duniya ta ke kara komawa sabuwa kuma sabbin al'amura ke kara faruwa, tunani ke kara fadada, shakka babu da ba dan tsufa ba da Castro ana nan ana damawa da shi a harkar shugabanci da siyasa, to haka dai tarihi ke tafiya da al'amura daban daban, dukkan wadan nan abubuwa da suka faru tarihi ne yake ta maimaita kansa, sai dai wasu da yawa musamman daga cikin masu mulki sun gafala daga daukar darasin dake cikinsa.
Lallai masu Mulki su sani kuma su hankalta cewa babu wani mulki ko shugabanci da yake dawwama face mulkin ubangiji(tsarki ya tabbata a gareshi) subahanahu wata'ala, lallai duk wani mai mulki da yayi zaton zai dawwama shakka babu ya yaudaru da rudin duniya, kuma tunaninsa ya gaya masa karya, shuwagabanni da dama da suka gabata sunyi kokarin cigaba da kasancewa bisa karagar mulki amma kodai mutuwa tayi musu yankan hanzari irinsu marigayi Sani Abacha, ko kuma cutar nan da bata jin magani ta cimmusu basu shirya ba wato tsufa, ko kuma su fuskanci bore daga al'ummarsu duk kuwa da cewar sun kyautatawa al'ummar tasu wajen samar musu da abubuwan bukata kamar irinsu Gaddafi.
Mukam munyi katari a Najeriya ba mu da irin wannan matsala ta masu son tsawaita mulki. Hakika muma shugabanninmu ba dan basu da wancan tunani ne yasanya basa tsawaita mulki irin na su Mugabe ba, sai dai Najeriya ta sha bamban da sauran kasashen duniya, watakila saboda yawan kabilu da mabambanta ra'ayi da kuma yanayinmu na kudu da Arewa ko Muslmi da Kirista.
Inda Najeriya ta yiwa sauran kasashen Afurka shal shi ne muguwar sata da zamba da rubda ciki akan dukiyar al'umma da kuma cin hanci da rashawa da ya yi mana katutu. Shakka babu idan mutum yace babu wata kasa a duniya da ta ke da gungun barayi a matsayin shugabanni kamar Najeriya bai yi karya ba, irin satar da aka dibga a Najeriya bana jin akwai wata kasa a Nahiyar Afurka da za'a yi mata irin wannan satar ta kai labara. Tundaga lokacin da aka samu mulkin kai 1960 zuwa yau irin kudin da 'yan Najeriya suka sata daga aljihun gwamnati ya isa a rushe kasashen Afurka gabaki daya a sake gina sabuwar Afurka mai dauke da dukkan ababen bukata na rayuwar yau da kullum.
Hakika Allah ya albarkaci Najeriya da dumbin arziki na fitar hankali, tun daga albarkatun kasa da ma'adai babu iyaka ga man fetur da dangoginsa ga kuma albarkar jama'a sannan a gefe guda kuma ga mugayan barayi miyagu azzalumai. Cutar da ta ke damun 'yan Najeriya kusan tafi ta kowace kasa a Nahiyar Afurka, duk da cewa a Uganda da Kamaru da Zimbabwe da muka bada misali da su shugabanninsu sun tsawaita wa'adi da wakaci ka tashi amma sun wadata al'ummarsu musamman da wutar lantarki idan ka kwatatnta su da Najeriya. Abin da ake kira wutar lantarki dan Najeriya sai dai ya gani a wata kasar amma shikam ta gagareshi samarwa a kasarsa duk kuwa da arzikin da Allah ya huwa cewa wannan kasa tamu.
A kasar Brazil da kwanan nan shugaban kasa ya je, kuma tafiyar ta tayar da kura, a lokacin tsohon shugaban kasar Luis Inacio Lula De Silva sun kashe kudi kimamin dalar Amerika Biliyan Biyar ($5B) wajen samar da wutar lantarki mai karfin mega watt 120,000 a cikin shekara daya kacal, haka nan kurkusa ma kasar Afurka ta kudu sun kashe dala biliyan daya ($1B) wajen samar da wuta me karfin mega watt 5,000 acikin shekara daya suma. Idan kuma muka dawo gida Najeriya gwamnatin da ta gabata ta Cif Obasanjo ta kashe kudi dalar Amerika biliyan goma sha shida ($16B) akan samar da wutar lantarki, amma yanzu zancen da muke babu kudin kuma babu wutar lantarkin, haka nan Allah ya jarrabemu da muggan barayi a matsayin shugabannin.
Bana jin a duniya akwai wasu mutane da suke yin laftu na kudi suna kaiwa kasashen waje suna ajiyewa kamar 'yan Najeriya. Shakka babu irin yadda 'yan Najeriya suke daukar kudi niki niki abin sai wanda ya gani, ban sani ba ko gaskiya ne, ance akwai wani hamshakin attajiri a Najeriya sai da ya ciko kwantaina guda shake da daloli zuwa Najeriya daga Turai da Amerika, wannan bai bani mamaki ba, domin kuwa akwai wani yaro dan Najeriya da yaje wata jami'a a wata kasa yana neman admission suka bashi hakurin cewar sun rufe sai wata shekarar, amma da yaron nan ya tashi sai ya ce a nuna masa ofishin shugaban jami'a da yaje wajensa akwati ya dauko ya bashi cike da dalar Amerika yace masa ka dauki abinda kake so ka bani adimission, kaga kuwa duk abinda aka ce dan Najeriya zaiyi da kudi babu abin mamaki.
A irin wannan hali ne shugabanninmu suke yawo zuwa kasashen turai da Amerika karkashin tawaga mai tarin yawa da sunan neman masu zuba jari a Najeriya, kaji shugaban kasa ya kwashi mutane sama da dari (100) wai sun tafi neman 'yan kasuwar da zasu zo Najeriya don zuba jari, kudin otal din da za su kwana kwai ya isa arzikin wani kauyen a wata kasar, sai kayi mamaki shin su masu zuba jari mahaukata ne zasu kwaso kudinsu su zo su zuba a hudajjan aljihu, shugabanni a Najeriya sun kwashi dukiya sunkai kasashen Turai da Amerika saboda can yafi tsaro, amma kuma suna son wani ya kwaso dukiyarsa ya zuba a inda babu tsaro, alhali kuma duk kan kasashen da za'a nemo su zuba jari suna da ofishin jakadancinsu a Najeriya suna sanar da su irin halin da ake ciki a Najeriya na satar baki 'yan kasashen waje tare da yin garkuwa da su, idan da karar kwana akan kashe wasu daga cikinsu, shin su mahaukata ne kamar shugabanninmu zasu kwashi dukiya su zuba a cikin hudajjan aljihu?
Mafiya yawan jajayan fatar da suke kwaso kudi su zo Najeriya, idan ka bincika kodai suma barayi ne ko kuma kudin ainahi daga dukiyar 'yan Najeriya aka ranto a zo Najeriya a kara samun wata dukiyar ta banza, idan ka kalli badakalar kamfanin Halliburton zaka tabbatar da haka, galibin turawan da suke aiki a matatun man fetur suma barayi ne, ko kuma kaga bature dan tasha watakila a kasarsu shi ba komai bane, kawai ya kwaso sufanu da gajeran wandonsa yana budawa waishi injiniya yana karbar kudi a banza.
Shakka babu duk irin yadda zaka misalta barayi miyagu azzalumai to shuwagabannin Najeriya sun dara nan, har sai da ta kai tsohuwar shugabar EFCC take tuhumar hankalin shugabannin Najeriya saboda abinda ta gani ya shallake hankalin dan adam. Allah ya ce baya canzawa mutane sai mutane sun canzawa kansu kuma yana  baiwa mutane shugabanni dai dai dai da su, ba zai zama kuskure ba idan ka ce shugabannin Najeriya sunyi dai dai da 'yan Najeriya, domin dukkan irin waccan satar da muka ambata sai ka rasa waye mai gaskiya acikinmu, domin idan ka dauki kowa ka karkade shi sai kaga ashe shima wani karamin barawo ne dama ce kawai bai samu ba, duk wanda ya kalli badakalar cin hanci ta Farouk Lawan zai tabbatar da haka, domin mai dokar barci ne ya bige da gyangyadi, kuma Farouk ba shi kadai bane irinsa suna nan kamar jamfa a Jos.
Lallai 'yan Najeriya, idan muna son ganin gyara na hakika sai munji tsoron Allah mun gyara halayenmu tsakaninmu da ubangiji sannan mu sami abinda muke nema. Kullum muna kiran gyara da fatan samun shugabanni na gari masu adalci, amma akan kanmu bama yiwa juna adalci, ga zalinci tsakanin talakawa ya yi yawa ga gulma da munafurci da tsabar rashin tsoron Allah da karya da yaudara da ha'inci duk sunyi mana katutu, ga zinace zinace ga shan giya ga fyade ya karu, ga duk wani aikin badala ya karu, ga kuma uwa uba kisan kai na mutanan da basu san hawa ba basu san sauka ba, duk wannan abubuwan da suke faru sai mun gyara halayenmu sannan mu sami abin da muke nema na shugabanni adalai.
Suma a nasu bangaren shugabannin Najeriya su sani adalci shi ne zai zaunar da kasarnan lafiya, rashin adalcin da muke yiwa juna shi ne musabbabin dukkan irin halin da muke ciki, shugabanni basa jin dadi, talakawa basa jin dadi, to waye yake jin dadi a Najeriya? Lallai muna bukatar shugabannin suji tsoron Allah su yi adalci a tsakanin dukkan 'yan kasa, babu wanda ya fi karfin doka, don haka dukkan wanda ya karya doka a yi masa hukunci dai dai da abinda doka ta tanada.
Bahaushe ya ce abinda ya ci doma to fa bazai bar Awe ba, don haka misalin shugabannin da suka gabata darasi ne da dukkan wani mai hankali ya kamata ya kalla kuma yaji tsoron Allah ya gyara tsakaninsa da Allah, Masu Magana suka ce dukkan wanda yaki ji to bazai ki gani ba, gani ga wane . . .!
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

Friday, June 22, 2012

Al-Majirai Ma 'Ya 'Ya Ne Suna Da hakkin Samun Ilimin Boko amma . . .!




Al-Majirai Ma 'Ya 'Ya Ne Suna Da Hakkin Samun Ilimin Boko amma…!
Rahotannin sun tabbar ta da cewa akwai kusan al-majirai sama da miliyan 9 a Najeriya mai mutane kimanin sama da miliyan 165, wanda wannan yake nuna al-majirai sun kai kusan kashi 1.06 a Najeriya, kimanin yawan mutanan jihar Delta da Bayelsa. Lallai wannan adadi babbar barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar wannan kasa, kuma alamu sun nuna cewa wannan adadi yana karuwa cikin sauri. Kusan idan baka ce duka ba, to sama da kashi 8 cikin goma na wannan adadi sun fito ne daga jihohin Arewa, wanda masana ke cewa talauci yana da yawa a kusan jihohin Arewa maso gabas da kuma Arewa maso yamma, lallai wannan babban kalubale ne ga gwamnatocin wadan nan jihohi da kuma masu hannu da shuni domin ganin antashi tsaye haikan wajen yakar fatara da bakin talauci da suka mamaye wannan yanki.
Kamar yadda muka sani a yanzu kusan dalilin da yake sababba al-majiranci shi ne mawuyacin hali da galibin mutanan kauyuka ke ciki na rashin iya daukar dawainiyar iyalansu, dan haka ne wasu suke yanke shawarar turasu karatun allo inda rayuwa ta ke da dama-dama, inda galibi yanzu zaka samu almajirai suna watangaririya a kusan manyan birane, domin neman abinda zasu ci, wasu kuma suna ragaita babu karatun sai neman dari da kwabo.
A can baya ana tura yara zuwa gabas ne kamar yadda ake cewa domin neman karatun al-kurani, inda kusan duk bayan kammala noma da girbe amfanin gona ake tura yara zuwa musamman kasar Barno, domin haddar al-kurani mai tsarki, alhamdulillahi a wancan lokaci birnin Maiduguri ya ya ye dalibai da daman gaske wadan da suka hardace alkurani mai girma hadda ba ta wasa ba, wannan ta sanya birnin ya shahara da mahaddata al-kurani har ya zuwa yanzu, amma kuma zance na gaskiya yanzu abin ba haka yake ba, domin galibi yaran da ake turawa da suke da kananan shekaru daga zarar sunyi wayo sun bude ido sai su watsar da karatun al-kurani su koma aikin neman abin batarwa agun 'yan daudu masu dafe-dafe ko kuma kaji yaro yabi makida 'yan koroso ya zama yaronsu, kaga kenan wannan ita ce cikakkiyar lalacewa domin yaron da yazo neman karatun al-kurani ya bige da bin 'yan daudau ai lamari ya baci, kuma lissafi ya rushe.
Ada can yadda muka sani, al-majirai suna da wasu 'yan sana'o'I da suke yi. Da yawan al-majiran wancan lokacin da wuya ka gansu yara kanana, kamar na yanzu, zaka samu suna yin sana'ar wanki da guga ko wanki tare da d'amin hula, ko kuma sana'ar wankin takalmi da dinkinsa (shushana), ko kuma sana'ar likin robobin da suka fashe ko suka tsage, galibi wadan nan sune mafiya yawan sana'o'in da almajirai suke yi a wancan lokacin sabanin na yanzu, da yaran kusan suka koma rabi suna bara rabi kuma suna sata, wato yaki halal yaki haram, watakila wannan ya faru ne bisa yadda kudade suke da yawa a hannun mutane, da kuma, yadda abun bukatuwar yau da kullum yake kara yawa.
Kamar yadda muka sani ne, a 'yan watannin baya da suka gabata shugaban kasa ya bude katafariyar makarantar boko da kuma allo ta zamani a jihar sokoto. Bude wannan makaranta yazo ne bayan shugaban kasa ya yi wannan alkawari a lokacin da yake yakin neman zabe cewa idan yaci nasarar zai gina irin wadan nan makarantu guda 121 a fadin Arewacin Najeriya, a cewarsu kuma anware kudade kusan Naira Biliyan dari hudu (400 Billion) domin wannan aiki. A daidai wannan gabar abubuwa da yawo zasu iya tasowa, kamar yadda dukkan ninmu muka sani Najeriya kasa ce mai yawan kabilu da mabanbantan al'adu da kuma addinin musulunci da na kirista, anya kuwa kiristocin Najeriya zasu iya shiru ko su zura ido suna kallon Shugaban kasa yana narkar da irin wadan nan makudan kudade da sunan gina makarantar Allo a Arewa? Domin kamar yadda yake a bayyane yake cewa, kiristocin Najeriya sun zama kamar kishiya ga musulmin Najeriya, domin duk sadda gwamnati ta yi wani abu da ya dadadawa musulmi suma sai sunyi korafi ko kuma kirkiro wani abu da suma za'a rika basu kudade, misali, kowa yasan gwamnati tana ware makudan kudade domin hidimar aikin Hajji da musulmi suke yi a kasar saudiyya a dukkan karshen shekarar Musulunci wato a watan zul-Hajji, irin yadda gwamnati take kashewa mahajjata kudi a kasa mai tsarki ya tsonewa kiristocin Najeriya ido ainun, domin idan zamu iya tunawa Solomon Lar a lokacin da yake Gwamna a Jihar Plateau ya yi ta korafi ga gwamnatin shagari cewa da taje tana kashewa musulmi kudi suna hawan duwatsu a kasar Saudiyya me zai hana su zo Jos su ringa hawan duwatsu, ya dauka cewar kawai duwatsu ake hawa a can, wannan ta sanya kiristoci suka kasa hakuri da jurewa inda suka kirkiro wani abu wai shi aikin Hajjin kirista wanda kowa yasan babu shi a addinin kirista.
Wannan ta sanya suma yanzu gwamnati take ware makudan kudade domin wadan da zasu tafi aikin Ibada Jerusalem a kasar Israela, ba komai ya sanya suka yi wannan ba illa kawai nunkufurci da bakin cikin yadda gwamnati take yiwa musulmi hidima, amma kuma duk da haka aikin ibadar nasu yaki yin kasuwa domin da wahala kaji talakawansu suna zuwa wannan ibadar galibi sai masu hannu da shuni wanda suma suna zuwa ne kawai bude ido da yawan shakatawa, domin ibadar batada wasu rukunai da wasu muhimman al'amura da ake gabatarwa a yayin ibadar; sun manta cewa aikin Hajji da musulmi suke zuwa kasar Saudiyya rukuni ne daga cikin rukunan musulunci.
Wannan ta sanya dole mu kalli wannan gina makarantu ta wannan fuska, domin idan har ba wata makarkashiya bace ko kuma wata manakisa a cikin shirin ba, to babu yadda za'ayi kiristocin kasarnan su tsaya suna kallon gwamnati tana kashe wadan nan makudan kudade ba tare da suma sun kirkiro nasu makarantun allonba, sannan idan muka tsaya tsayin daka muka yiwa wannan lamari kallo na tsanaki da kuma cire son zuciya zamu tarar akwai illa da yawa acikin wannan shiri, domin me ya sanya aka baiwa makarantar sunan ta al-majirai kawai? idan da gaske gwamnati ta ke yi me ya sanaya bazata ce al-majiran suje makarantar boko ta gwamnati kamar yadda 'ya 'yan kowa suke zuwa ba? Me ya sanya aka ware makarantar kawai sai al-majirai? Shin al-majirai sunfi kima a wajen gwamnati ne? ko kuma sunfi zama barazana gareta shi ya sanya ta killace su yasu yasu?
Kamar kuma yadda aka ce, tsarin karantarwar zai yi dai-dai da na makarantun boko, wato yara su sanya kayan makaranta (Uniform) da litattafai da azujuwa da kuma tebur da yara suke zaune, duk wannan ya nuna shirin ba da gaske akeyinsa ba, domin me yasa za'a ce yara sai sun sanya kayan makaranta? Ba bu wanda ke kin tsafta, amma a irin yadda muka taso a can baya bamu tarar ana zuwa makarantar allo da Uniform ba, don a fakaice wannan ana nunawa yara kyamar wancan tsari na karatun allo da ake yi da malami a zaune a kasa, kuma shi kansa zama akan tebur wannan ma wata matsala ce, domin ya ci karo da tsarin tarbiyyar da aka taso da karatun allo a kasar Hausa, ba laifi bane a shigo da sabbin tsare-tsare a dukkan harkar ilimi, amma yana da kyau a yi la'akari da irin yanayin zamantakewarmu da kuma al'adunmu. Shin su kuma makarantun Islamiyya na zamani da 'ya 'yan kowa da kowa suke zuwa me ce makomarsu?
Sannan a wannan sabon tsari na makarantu, yara zasu shiga aji kamar yadda tsarin makarantun boko yake inda malami zaizo yana koyar da su harshen turanci da lissafai kamar yadda aka tsara da safe sannan kuma da yamma suyi karatun allo tare da alaramma kamar yadda aka saba, nanma akwai illa mai yawan gaske, domin, da alaramman da yake karantar da yara tare da bulala a hannunsa yana zune akan buzu, da kuma malamin da yake karantar da yaran suna zaune akan kujeru yana basu karatu watakila har yana hadamusu da wake-wake irin wadan da akeyi a galibin makarantu, wa ka ke jin wadan nan yara zasu fi kauna? Wane darasi kake zaton yaran zasu fi sha'awa tsakanin karatun allo da kuma na makarantar Boko? Ba muki a koyar da al-majirai karatun boko ba, amma shakka babu game shi da akayi da karatun allo wannan akwai makarkashiya a ciki, domin a hankali za'a zarewa yaran son karatun al-qurani da kin duk wani darasi da yake da alaka da Al-qurani ko addini, kamar yadda a yanzu haka acikin makarantunmu na sakandare zaka samu galibin yaranmu basa son darasin Islamic Studies saboda duk makarantar da ka shiga zaka samu galibi malamin da yake koyar da darasin addini na Islamic shi ne mai horo(displine Master) wanda ga duk mai hankali yasan da gayya acikin wannan shiri, yara sun tsani malamin saboda irin yadda yake dukansu wannan ta basu damar tsanar darasin da yake koyarwa, bayan kuma ankai darasin karshen lokaci ta yadda duk yara sun gaji kowa alla-alla yake a kada karaurawa ya kama gabansa ya tafi, kaga duk wannan mun san akwai manufa a cikinsa.
Don haka wannan sabon shiri na gwamnatin tarayya na game makarantun Allo da na Boko ba shi ne alfanu ga almajirai ba, idan har da gaske gwamnatin ta ke son gyara harkar almajiranci da al-majirai. Idan har da gaske gyaran ake son yi kuma al-majiran ake son taimakawa domin su samu wannan ilimi na zamani, to wajibine gwamnati ta taimakawa da iyayansu ta hanyar yakar cinhanci da rashawa da kuma bijiro da ayyukan da mutane zasu samu aikin yi, da kuma inganta harkar noma ta wannan hanya kowane yaro sai ya koma gaban iyayansa ya yi karatun boko a gabansu, suna bashi kyakykyawar kulawa kamar yadda kowane uba ya ke lura da dansa, domin suma al-majirai 'ya 'ya ne kamar kowa.
Ko kuma, gwamnati ta inganta tsarin da muke da shi na karatun tsangaya ta hanyar zamanantar da tsangayar a gina musu bandakuna da dakunan kwana da famfunan samun ruwa da baiwa alarammomin abinda zasu ringa daukar dawaniyiyar yaran da kuma iyalansu, da kuma shirya musu bita akai-akai, sannan kuma gwamnati ta sanya su, su ringa zuwa makarantun boko na inda suke suna haduwa da sauran yaran al'umma suna karatu tare, duk wannan karkashin kulawar gwamnati da kuma alarammomin, sannan da koyar da su sana'o'in hannu da kuma basu dan abinda zasu juya, wannan ita ce hanyar da gwamnati zata ceci al-majirai amma ba ta hanyar game makarantun allo da na boko ba, Bahaushe ya ce ayi dai mu gani . . .!
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

AREWA: Kowa Ya Kwana Lafiya Shi Ya So!!!


AREWA: Kowa Ya Kwana Lafiya Shi Ya So!!!
Sa nin kowa ne cewa zama lafiya ya fi zama dan sarki inji masu iya Magana, ni kuma nace yafi zama sarkinma. Kamar yadda dukkanmu muka sa ni ne cewa yanzu kusan Arewa ta shiga wani irin mawuyacin lokaci da bata taba samun kamta a ciki ba a lokutan da suka gabata, kusan a kullum safiyar Allah babu wasu rahotanni da ake karya kumallo da su daga Arewa face harbe-harben bindigogi da tashin Bama Bamai da kisan mummuke da kuma harbin kanmai uwa da wabi da jami'an tsaro karkashin rundunar JTF suke yi a kusan galibin jihohin Arewa, a kullum safiyar Allah.
Hakika wannan tashin hankali ba karamin durkusar da yankin Arewa ya yi ba  ta fannin zaman lafiya, kasuwanci da tattaln arziki. Tun bayan harin boma bomai na ranar 20 ga Janairun wannan shekara ta 2012 da aka kai cikin birnin kano ya dagula al'amuran kasuwanci a wannan birni da ke da tsohon tarihin saye da sayarwa a Yammaci da Arewacin Afurka, kamar yadda muka sa ni kusan gabaki dayan kan iyakokin Najeriya da ke yankin Arewa sun cigaba da kasancewa garkame bayan da gwamnati tayi zargin cewa ana shigo da makamai ta wadannan iyakoki da suka hada da Jimhuriyyar Nijar da Chadi da kuma Kamaru, dubunnan 'yan kasuwa ne suke ratso wadan nan iyakoki domin harkar tijara a Najeriya musamman yankin Arewa, amma yanzu sun durkushe saboda wannan dalili na tsaro da tashin bam da ya addabi Arewa.
Shakka babu, wannan hali na rashin tabbas da kuma tashin boma bomai ya wuce dukkan lissafinmu, domin irin yadda ake kai hare-hare babu kakkautawa ya firgitar da kuma razanar da duk wani mutumin Arewa danta ne ko mazauninta, kasancewar babu wanda yake da masaniyar inda wadan nan miyagu azzalumai zasu kai wadan nan hara-hare na su a kowace rana.
kamar yadda abin ya samo asali, inda muke jin ana kaiwa jami'an tsaro wadannan hare-hare tare da halaka su da jikkata wadan da suke da sauran kwanaki. Yanzu kusan zamu iya cewa abin ya sauya salo, domin daga hare-haren da ake kaiwa jami'an tsaro ankoma hari kan majami'u wato wajen ibadar kiristoci, kusan duk karshen mako sai mun wayi gari da harin kunar bakin wake da ake kaiwa irin wadan can guraren ibada na kirista, tare da hasarar rayukan wadan da basu jiba basu gani ba.
Su wadan nan, wadan da suke kai irin wannan mugun harin, har yanzu kamar yadda hukumomi suke cewa ba'a san ko su waye ba, shakka babu abin zai zama me daure kai da kuma ban mamaki ace duk da irin kwarewa ta jami'an tsaronmu da iya bankado mai laifi amma ankasa sanin su waye hakikanin wadan da suke kai irin wadan nan hare-hare babu kakkautawa, sai dai kawai wata kungiya da ke ikirarin kai wadannan hare-haren ta hanyar amfani da yanar gizo ko intanet suce su ne ke da alhakin kai hari waje kaza da kaza, wanda a zahirin gaskiya babu wata kwakwkwarar shaida da zata nuna maka cewa su ne suke kai irin wadan nan hare hare. Kuma babu yadda Magana a internet zata iya zama hujja domin kowa na iya amfani da internet yana cikin dakinsa ya yi dukkan abinda ya ke so, don haka babu yadda zamu yarda da maganar cewa wasu sun watsa a internet cewa sune suke da alhakin kai gari waje kaza da kaza.
Domin ta ya akayi suke fakar idon jami'an tsaro duk kuwa da suna nan a jibge akan manya da kananan hanyoyinmu, lallai wannan babban abin tuhuma ne ga jami'an tsaro, wani abu da yake bawa mutane mamaki shi ne irin yadda gwamnati ta ke yin karyar cewa suna nan suna aiki tukuru wajen samar da kwanciyar hankali, shin wane irin aiki akeyi wanda har yanzu zaman zullumi karuwa yake mai makon raguwa? ko kuwa irin aikin baban giwa ake yi ta hanyar tufka ta re da warwara, kuma abinda da yake faruwa yau da kullum ya tabbatarwa da al'ummar Najeriya cewa babu wani abu da gwamnati ta ke yi   na kawo karshen wannan tashin hankali, illama amfani da wannan damar wajen dibga mahaukaciyar sata da yashe asusun gwamnati da sunan aikin tsaro.
Sau da dama, jami'an tsaron Najeriya kan kafa hujja da cewar su basu saba da irin wadan nan hare-hare na sari ka noke ba ko harin ta'addanci, anan sai mu ce duk jami'in tsaron da ya yi wannan Magana ya tabbatarwa da duniya cewa lallai basu san aikinsu ba, domin a har kullum shi mai laifi yana amfani ne da hanyar da zai kaucewa fadawa hannun jami'an tsaro, don haka yaushe jami'an tsaro zasu zauna su shanta ke a cikin ofisoshi suna hira suyi zaton masu aikata laifi zasu yi amfani da dabarun da jama'an tsaro suka sa ni, lallai wannan babbar kasawa ce jami'an tsaro suce wai yadda ake kai wadan nan hare haren ya saba da tunaninsu ko masaniyarsu, idan har wanda ba jami'in tsaro ba zai yi amfani da tunani da kwarewarsa wajen shirya shegantaka kuma yaci nasara, ina amfanin jami'in tsaron da ya koyi dabaru kala-kala akan abin da ya shafi harkar tsaro da kama tare da gurfanar da mai laifi.
Kamar yadda ya faru, ankai hare hare akan coci coci a jihohin Plateau da Kaduna da Maiduguri da Bauchi da Neja da sauransu. Abin ya fara kazanta ne bayan da kiristoci suka fara daukar fansa akan musulmi a Jos, inda suke kashe mutanen ba babu ruwansu kuma suke kona dukiyarsu, dukkuwa da bayanan da suke nuna cewa galibi wadan da ake kamawa da kokarin dasawa ko tayar da bom kiristoti ake kamawa da wannan laifi ko yunkuri a galibin inda akaci nasarar kamasu, domin rahotanni sun tabbatar da cewar wanda ya kai harin Cocin Church a Jos da Miyabarkate a Bauchi duk kiristocine, haka kuma ankama kiristocin da suke yunkurin tayar da bom a coci a Bauchi mutum bakwai, banda faston da aka taba kamawa da tarin makamai a Jos da kuma wata mata mai suna Lucy Danga kirista da ta ke safarar makamai zuwa kasarnan, sai gashi baya bayan nan ankama jami'in kwastam da samarwa da kabilarsa ta Berom da miyagun makamai, kuma abin haushi gwamnatin Jos ta fito tana kokarin kareshi, dukkansu babu wani musulmi da aka taba kamawa, amma kuma abin haushi da wadan nan tsagerun kiristoci sai su huce haushi akan Musulmi. Lallai rashin adalcin da hukumomi suke yi ya sake rura wutar wannan lamari, don haryanzu bamuji hukuncin da aka yankewa wadan da muka zayyana ba.
Ya kamata kiristocin Arewa su fahimta, sune mutanan da suka fi kowa cin albarkacin zaman lafiya a Arewa. Shakka babu wannan maganar haka ta ke, cewa kiristocin Arewa sune suka fi amfana da zaman lafiya tsakanin musulmi da kirista, domin galibinsu talakawa ne, don haka irin sana'o'in da suke yi musamman a cikin garin Kaduna zaka samu musulmi ne suke saye, misali masu soya kosai da doya a gefen titi da masu gasa masara da masu tallar ruwan leda na pure water da masu tallar burodi a kan danja da tashoshin mota da masu gidan abinci da masu kananan kantuna zaka samu duk Hausawa Musulmi sune kasuwarsu, da su suka dogara wajen samun dari da kwabo, kaga kuwa da suna da hange da tunani, da su zasu fi kowa son azauna lafiya da juna.
Wani abin mamaki shi ne, Shugaban kasa Kirista, Shugaban sojojin Najeriya kirista, me baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro kirista, babban daraktan 'yan sandan farin kaya na kasa SSS kirista, shugaban majalisar dattawa kirista, gwamnan Kaduna kirista, gwamnan Plateau kirista amma duk da haka sun gaza samar da tsaro ga guraren ibadar 'yan uwansu kirista, to inaga mu musulmi da muke addini daban da nasu? Don haka muna zargin dukkan wadan can bangarori da kitsa wutar wannan tashin hankali domin cimma wata boyayyar manufa da suke da ita, wanda ya zuwa yanzu ta bayyana cewa Gwamnatin Jos tana da hannu a galibin rikice-rikicen da ke faruwa a jihar.
Kuma tun daga fadar paparoma dake Vatican da kungiyar CAN dake Najeriya, babu wanda ya yi kira da a hukunta kiristocin da ake kamawa da yunkurin tayar da boma bomai ko dasa su, ko kuma masu safarar makamai; haka kuma, ankaiwa Musulmi hari ranar sallar a Jos babu wani kirista da ya ke da fada a ji a kungiyar CAN da ya fito ya bukaci lallai ayi bincike don gano wadan da suka kaiwa musulmi hari domin a hukuntasu, haka kuma, irin kisan kiyashin da akayiwa musulmi ana zubawa a rijiya da shadda a zankwa a lokacin rikicin bayan zabe babu wani kirista tundaga fadar paparoma da ya zargi kiristoci da aikata ba dai-dai ba. Amma wai har shuagab CAN Oritsejafor yake cewa wai musulmi basu fito sunyi allawadai dinda ta kamata ba da harin da aka kai a Madalla ta jihar Neja ba.
Amma tunda yake suna ganin wannan hanyar da suka biyo suna ganin itace mafita, muna tabbatar musu duk da musulmi suna cewa a zauna lafiya, su sa ni wallahi mu ba matsorata bane, kuma daga yanzu duk wanda ya kwana lafiya shi ya ga dama, kuma munce CAS ga duk wanda ya ce mana kule, mu daura zare da su, muga su wa zasu kasa, tunda yake jami'an tsaro sun gaza samar da tsaro a tsakanin 'yan Najeriya mu Musulmi wallahi zamu iya baiwa kanmu tsaron rayukanmu da dukiyoyinmu da taimakon Allah da kuma kwazon da muke da shi, kamar yadda duk  muka sani ankaddamar da aiki da shari'ah a Arewa kuma akwai 'yan Hizba a jihohinmu, dukkanmu mazanmu da matanmu sai mu zama 'yan Hisba domin baiwa garuruwanmu aminci.
Kuma wallahi kiristocin Arewa su sa ni, ta re matafiya musulmi da suke yi a kauyen gwanin gora akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, wannan su zata kwabewa, domin kauyen nawa yake, daga yanzu sai mu ringa tahowa cikin ayari duk karshen mako daga Abuja zuwa Kaduna zuwa da komawa, kuma kowa ya yi guzurin gora don kare kansa, muga idan da akwai dan iskan da ya isa ya tare mana hanya, kamar yadda yake a dokar kasa kare kai ba laifi bane, to wallahi zamu yi dukkan mai yuwuwa wajen muga mun kare kanmu har Allah ya maidamu gidajenmu Lafiya.
Idan kuwa sun zabi zaman lafiya, su sa ni wallahi mu Musulmi munfi kowa kaunar ganin a zauna lafiya, domin munyi imani da Allah da Manzon Allah kuma munyi imani da littafin Allah al-qur'ani, Allah baice ka kashe mutum don ba addininku daya ba, don haka duk wannan abin da yake faruwa al-qurani ya riga ya bamu mafita. Don haka wanda yake fatan a zauna lafiya muna maraba domin mu musulmi ba masu son tashin hankali bane, duk kuma wanda yake tunanin mu matsorata ne to ya tabbatarwa da kansa cewa ya yi kuskure a shirye muke mu fuskanci duk wani dan iska mara kaunar zaman lafiya.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@yahoo.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

Sunday, June 17, 2012

Muguwar Manufar Obasanjo na Kara Fitowa


Muguwar Manufar Obasanjo Na Kara Fitowa
Batun zargin karbar cin-hanci da aka yiwa Hon. Farouk Lawal (PDP Kano) shi ya mamaye galibin kafafen yada labarai na Najeriya a makon da yagabata. Wannan batu na karbar na goro da Farouk ya yi a hannun hamshakin attajirin nan Mista Femi Otedola, kusan ya zubar da kimar Hon. Farouk Lawal warwas a idon duniya, kamar yadda kowa ya sani ne wannan batu ya biyo bayan rahoton kwamitin da shi Hon. Farouk ya jagoranta, wanda suka fallasa manyan mutane da suke ci-da gumin talakawa, rahoton yace kusan Naira Tiriliyar daya akayi almundahana da su a cikin shekara daya da sunan tallafin manfetur, a karkashin wannan gwamnati ta Goodlucl Jonathan, inda rahotan ya zargi muhimman mutane da suka hada da babban kamfanin mai na kasa NNPC da minister kula da albarkatun mai Madam Dazieni Allasan Maduwake da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa zamanin Obasanjo Amadu Ali da kuma wasu kamfanoni da suka hada harda kamfanin mista Femi Otedola na Zenon Petroleum.
Tun bayan da wannan rahoto ya fito 'yan Najeriya ciki da waje sukayi ta tofa albarkacin bakinsu domin ganin anhukunta ko daukar mataki akan mutanan da rahoton kwamitin Farouk ya kama da laifin cin amanar kasa. Hausawa sunce kayi hankali da kama barawo, domin idan baka iya ka kamashi ba to tabbas zai ruftaka shi kuma ya kama gabansa, kusan wannan shi ne abin da ya faru da Hon. Farouk Lawal, inda aka shiraya masa gadar zare kuma ya hau kanta dodar, dole muga laifinsa domin me ya kaishi gidan Otedola har ya karbi wannan kudi da kansa, duk da rahotannin sun nuna cewa Farouk ya sanar da rundunar 'yan sanda ta kasa akan cewa Otedola yana kokarin bashi hanci, tun bayan fallasar wannan abin kunya ne, majalisar kasa ta yi wani zama na gaggawa domin tattauna batun da ya shafi daya daga cikin manyan shugabanninta, kuma matakin da majalisar ta dauka ya yi dai-dai.
Duk wannan abin da yake faruwa, ko ya faru, ya kara nuna yadda muguwar manufar Obasanjo ta ke kara fitowa fili. Kamar yadda muka sani Hon. Farouk kusan a wuyan Obasanjo yake, domin, shi ne ya jagoranci wata kungiya a majalisa da ake kira Integrity Group wadan da sukayi silar fatattakar kakakin majalisar ta wancan lokaci Patricia Ette, wadda ake mata kallon babbar diyar gaban goshin Obasanjo, bayan samun nasarar tunkude Ette da su Farouk suka yi, sun sake cin nasarar shigo da babban dan adawar Obasanjo da ita Etten a matsayin kakakin majalisar dokokin tarayyar Najeriya, Rt. Hon. Oladimeji Sabur Lawal Bankole wanda ya ci nasarar zama shugaban majalisa da gagarumin goyon bayan 'yan Integrity Group, Farouk Lawal ya zamewa Obasanjo wani karfen kafa, wannan ta sanya Obasanjon yake a kufule da Farouk Lawal da kuma Dimeji Bankole.
Obasanjo da mukarrabansa sunyi dukkan me yi wuwa wajen ganin sun kwashewa Bankole kafafu a zaben 2011. Cikin nasara wannan hakar tasu ta cimma ruwa, Bankole ya sha kasa a hannun ACN, wannan ta sanya aka ringa yiwa Bankole bita da kulli, inda alamu ke nuna cewa da hannun Obasanjo aka yi kokarin shiryawa Bankolen gadar zaren da ya tsallake ta da kyar bayan ya shafe kwanaki a komar 'yan sanda, an zargi Bankole da sama da fadi da kudaden majalisa da suka kai kusan Biliyan 4, kafin daga baya kotu ta wanke shi, shi da mataimakinsa Hon. Bayero Usman Nafada.
Tun bayan da Obasanjo da mukarrabansa da Jam'iyyar PDP suka ci nasarar shatale Bankole, suka shirya tsam domin ganin Hon. Mulikat Adeola da ke zaman 'yar majalisa daya tilo ta jam'iyyar PDP daga shiyyar yamma ta maye gurbin Bankole a matsayin kakakin majalisar kasarnan, nan ma dai su Obasanjo da jam'iyyar PDP basu ji da dadi ba, domin su Farouk Lawal sun takawa abin birki duk kuwa da irin barazanar da akayi musu, inda suka yi nasarar shigo da Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal a matsayin kakakin majalisa ta bakwai, a wannan majalisa ta kasa, wannan ya sake dagulawa su cif Obasanjo lissafi domin duk wani yunkuri da sukayi sai su tarar Farouk da jama'arsa sun tare hanya babu kuma yadda suka iya.
Tun bayan da aka gama waccan sabatta juyatta ta waye zai zama kakakin majalisar kasa ta kare, majalisa ta shiga aiki ka'in da na'in; suma a nasu bangaren Obasanjo da PDP suka shiga nasu aikin ka'in da na'in domin ganin yadda zasu sanya zabari su kamo Hon. Farouk Lawal a cikin komarsu, cikin ikon Allah wannan haka tasu ta cimma ruwa domin Farouk ya yi kasadar fadawa cikin wannan tarko da aka shirya masa, inda bayanai suka tabbatar da cewa ya karbi dalar amerika dubu 620 a hannun Femi Otedola a gidansa da ke Abuja, shi dai Otedola shi ne ya nuna wannan faifan bidiyo da aka ga farouk yana karbar wannan kudi, kuma rahotannin sunce Obasanjo ya yi ta yamadidi da Hon. Farouk da wannan bidiyo inda ya ringa zuwa da kansa yana nunawa muhimman mutane wannan bidiyo.
Hausawa suka ce, ko wane allazi da nasa amanun. Kamar yadda kusan yake a siyasar Najriya, domin idan bamu manta ba, allazin marigayi Umaru 'YarAdua,shi ne Mista James Ibori, wanda ya fada komar jam'an tsaro a landan bisa zarginsa da lartar kudadan haram, wanda yanzu haka yake can yake zaman sarka na kusan shekaru 16 a birtaniya. Haka shima wannan shugaban na yanzu Goodluck Jonathan Femi Otedola, shi ne nasa allazin domin kuwa kafatanin jam'iyyar PDP babu wanda ya taimakawa da GEJ da kudaden da Otedola ya taimaka, wannan ta sanya ya kara samun babbar dama ta cin karensa babu babbaka a wannan gwamnatin, shi dai wannan mutum Otedola idan bamu manta ba yana daga cikin 'yan gaban goshin Obasanjo a lokacin da yake shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007, domin cikin kankanin lokaci Obasanjo ya mayar da Otedola mai arzikin gaske, domin bayanai sunce idan har za'ayi kidayar masu arziki a wannan lokacin to tabbas Otedola yana daga cikinsu, domin yana daga cikin tsiraru da aka baiwa dammar safarar manfetur da dangoginsa zuwa ciki da wajen Najeriya, wannan ta bashi dama ya kudance cikin dare daya.
Kamar yadda kowa ya sani duk wani mai kishin kasa ba zai goyi bayan cin-hanci da rashawa ba. Don haka, duk wannan abin da ya faru da Farouk Lawal muna da yakinin makarkashiya ce daga su Obasanjo da kuma wadan da rahoton kwamitin Farouk ya shafa, don haka, tabbas Farouk ya nuna kulafuci da son abin duniya inda ya jefa kansa cikin wannan bakin tarihi, lallai akwai bukatar a gudanar da bincike na gaskiya akan wannan batu, kuma muna fatan a hukunta Farouk Lawal daidai da laifin da ya aikata, domin zama darasi ga 'yan baya.
Idan ambit a barawo to abi ta mabi sawu. Kamar yadda Otedola ya bayyanawa 'yan jarida cewar ya baiwa Farouk Lawal cin hanci, har yace yana da faifan bidiyo da yake tabbatar da ikirarin nasa, shakka babu, kamar yadda dokar kasa ta ce, da wanda ya bayar da cin-hanci da wanda ya karba dukkansu masu laifi ne, muna nan mun zuba ido muga yadda za'a cukumo wuyan Otedola a gurfanar da shi gaban shari'a, domin ya tabbatarwa da duniya cewar ya bayar da hanci wanda kuma laifi ne, duk da cewa ya zuwa yanzu rahotannin sun nuna cewa Femi Otedola zakara ya bashi sa'a domin ya fice yabar kasarnan zuwa birtaniya, lallai muna bukatar a taso keyarsa domin yazo ya fuskanci shari'a akan wannan batu na cin hanci.
Duk da wannan abin da ya faru, bazamu manta da irin alkhaira ko kokarin da Hon. Farouk Lawal ya yi ba, ya kawo sauye-sauye masu yawa musamman a lokacin da ya rike da mukamin shugaban kwamitin kudi na majalisa da kuma shugaban kwamitin ilimi, muna fatan wannan abun da ya faru da shi zai zame masa babban darasi a rayuwa dama sauran 'yan Najeriya baki daya. Sannan zamu ci gaba da kallon Obasanjo a matsayin babbar baraza ga wannan kasar, Allah ya kyauta.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

Saturday, June 16, 2012

Me Ya Sa Maza Ke Shakkar Likitocin Al'aura???


Me Ya Sa Maza Ke Shakkar Likitocin Al'aura???

Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincinSa su kara tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammadu da alayansa da Sahabbansa da kuma wadan da suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar saka mako. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya bisa cancanta sai Allah, kuma, annabi Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa ne. Dukkan wanda Allah ya shiryar shi ne hakikanin shiryayye, haka kuma, dukkan wanda Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi.
Ya dan uwa mai karatu ina fatan gabanka bazai fadi ba da jin wannan kanu. Kamar yadda yake acikin al'adar musamman Hausa-Fulani ba kasafai ka ke jin maza na tattunawa akan batun da ya shafi al'aurar dayansu ba, shakka babu, wannan sabon abu ne ga 'yan uwana maza aji mutane suna irin wannan tattaunawa, amma ga mata wannan ba wani bakon abu bane kaji mata sun hadu ijunansu suna tattaunawa akan abin da ya shafi matanci ko al'aurar 'yar uwarsu ba tare da nuna wata damuwa ko kunya ba, ta irin haka ne kuma suke samarwa kawunansu da mafitar abin da yake damunsu, domin idan wata ta fadi matsalarta, sai wata ta ce ni da na fada wannan matsalar ga yadda na yi da ita, ga kuma hanyar da na sami mafita, mace ta sami mafita cikin ruwansanyi, ina fatan mai karatu yana biye da ni, wannan ya yi dai-dai da maganar nan da mata ke cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne.
Hakika, da yawan maza suna shakkar likitocin al'aura. Zaka sha mamaki tare da yin dariya sosai idan kaje asibiti, musamman kaga yadda maza ke shakkar duba al'aurarsu idan bukatar hakan ta kama, idan mace taje asibiti likata ya ce matsalarta tana bukatar sai anduba matancinta, zaka ga bata cika nuna damuwa ba, ba tare da wata tirjiya ba zaka ji mace ta bayar da hadin kai, amma kuma ga d'a namiji  wannan babbar Magana ce, domin duk wani namiji musamman Bahaushe babu abin da ya tsana kamar ace za'a duba al'aurarsa idan bukatar hakan ta kama, kaga mutum yana ta kauce-kauce da kokarin baiwa likita dabaru, wani lokacinma har da kokarin koyawa lokitocin aiki.
Al'aura wani muhimmin sashi ne a jikin dukkan halitta. Ina fatan mai karatu zai gafarceni, shakka babu, al'aura ba waje ne da ya kamata ayi sakaci da shi ba, duba da yadda yake da muhimmanci a rayuwar kowane irin mutum yaro ne ko babba, harma da dabbobi. Mutane da yawa, suna samun matsala a wannan muhimmin waje amma saboda abin da muka fada a baya sai suyi ta boyewa, sau da yawa, idan kaga andubawa namiji al'aurarsa to babu makawa, ya yi dukkan irin zille-zillen da zai yi ya gama,ko kuma ciwo yana cinsa babu yadda zai yi, to nan ne babu yadda ya iya, wannan ce ta sanya da yawan mazaje ke yawo da cututtuka ajikinsu, kaga mutum yana yawo da abu kamar kwallo (ball) a cikin wando,  wannan wata larurace da ta ke damun wasu mazajen, domin, wannan ciwo yana farawa tun daga dan karami ta yadda mutum zai ga warin marenansa na kara girma, amma wasu sun gwammace suyi shiru da bakinsu, har sai abin yakai makura wannan ciwo dai shi aka fi sani da "gwaiwa" ciwo ne da ana iya bayar da magani tun yana karami kamar yadda likitoci suka fada, to amma idan ya yi girma babu yadda aka iya dole a yanke wannan cuta, kaga kenan, ya dan uwana mai karatu wannan kunya bata yi amfani ba anan domin bazai yiwu ba kabar larura tana damunka, kuma kana da yadda zakayi akan wannan  larura, yana da kyau duk lokacin da aka fahimci wani canji a wannan muhimmin waje a garzaya wajen likita domin samun shawarwari da kuma mafita.
Haka kuma, sau da yawa ma'aurata suna fadawa cikin wani mawuyacin hali akan abinda ya shafi al'aurarsu amma sai su kama bakinsu, wasu da yawa sun gwammace su sami mai maganin gargajiya tunda yake shi ba fida yake ba, sai abin ya baka mamaki kaga mutum magidanci yana da larura irin wannan amma sai ya garzaya wajen me magani a hada masa hade-hade, duk kuwa da yana da masaniyar cewa mutumin nan ba karatu ya yi ba. Sannan suma irin wadan nan masu magunguna da suke basu sunaye daban daban, wasu su ce na gyaran aure ko firgita iyali da dai sauransu. Akwai magidantan da suna fama da larurar kankancewar mazakuta amma kuma sun yiwa abin shakulatun bangaro, ta kin zuwa wajen likita ya duba su, shakka babu wannan babbar matsalace da ta ke haddasa kasa sauke nauyin iyali, lallai yana da muhimmanci ga duk wanda yake da wannan larurar ya garzaya wajen likita tun abun baiyi nisa ba.
Wasu kuma, zaka samu irin kumburin da mazakutarsu ta ke da shi ya ragu ainun, amma suma sunyi shiru sunki Magana. Irin wannan matsala babbar matsala ce, domin duk lokacin da aka ce namiji ya kasa sauke nauyinsa a wajen iyalinsa an samu wawakeken gibi, wanda wannan gibi yana iya haifar da komai, hakika, sanin kowane ma'auraci ne cewar mata babu abin da suka fiso irin gamsuwa a yayin da ake tarayya kamar yadda masana suke cewa, irin wannan matsalar ce kan sanya wasu matan marasa tsoron Allah su keta alfarmar mazajensu na aure, ta hanyar fita domin cin amanar mazajen nasu, wannan yana faruwa ne da gagarumar gudunmawa da su mazajen suke bayarwa, ta hanyar kin daukar wani kwakwkwaran mataki tun lokacin da abun yake farko, lallai, ya dan uwana wannan matsala ce da bai kamata aji kunya akanta ba.
Da yawa wasu mazajen suna ha'intar matayensu a yayin ibadar aure. Sau da yawa wasu mazan basu cika lura da cewa su tsaya su biyawa matansu bukatarsu ba, kawai abin da ya dameshi shi ne ya biya tasa bukatar, shakka babu ya dan uwa matarka tana da hakki akanka, hakki na ibadar aure, kamar yadda wasu matan ke korafi, wasu mazan, a yayin ibadar aure, suna kulawa ne kawai da kansu, ba kuma tare da gabatar da wata mukaddima da zata kasance dan sako ga sha'awar matanba, kamar yadda wata ta fada cewa wallahi mijinta kamar yadda dabba ta ke yi haka yake yi, domin da yazo kawai gyara-gyara nan-da-nan ya biya bukatarsa, idan ta koma masa yace shi yagaji, wannan babbar kasawace ga mazaje, idan har iyalinka bata samun gamsuwa tare da kai to shakka babu lamari ya lalace, lallai yana da kyau mazaje su ringa tattaunawa da iyalansu domin tabbatar da cewa basu shiga hakkinsu ba akan wannan ibada.
Bincike ya nuna da yawan mazaje musamman wadan da sukayi haihuwa sama da daya, basa iya yin ibadar aure sai da taimakon magani. Shakka babu wannan babbar matsala ce, ta yadda namiji bashi da kuzarin da zai iya biyawa kansa bukatar larura ta sha'awa sai da taimakon magani, lokitoci sun fada, mafiya yawan wadan nan magunguna suna da illa mai yawan gaske ga lafiyar ita kanta mazakuta da kuma kuzarin namiji. Wani abin mamaki da mallam Bahaushe ya baiwa harkar ibadar aure mihimmanci sosai amma kuma yana yi mata rikon sakainar kashi, zaka sha mamaki idan ka shiga ma'aikatun gwamnati da kasuwanni da makarantu kai da dukkan wajen taron jama'a, kaga yadda ake kaiwa mutane irin wadan nan magunguna, sai kayi mamaki mutum ko sunansa bazai iya rubutawa ba, amma zai baka magani ya yi ta kafamaka ka'idoji kana dauka duk kuwa da digirorin da kake da su, idan ka shiga kasuwanni ko ka duba kan tituna kaga yadda mutane suke yawo da motoci da manya manyan lasifikoki suna yin batsa abin sai ya baka kunya, kaga mutane babu kunya sun taresu suna karbar magani; wallahi, wata rana da naga irin yadda mai sai da irin wannan magani yake yin batsa kiri-kiri a bainar jama'a har sai da naji kunya, kuma ka rasa wanda zai je ya yi masa nasiha, domin su irin wadan nan kalamai ba ko ina ake furtasu ba, don Allah ya zakaji a lokacin da ka ke tare da iyalanka irin wadan nan mutane suna yin muna nan kalamai na basta? Shakka babu abin kunya ne marar misaltuwa, wannan takan sanya kaji karamin yaro yana furta maganganu na ban mamaki.
Akwai cibiyoyi a asibitoci da mutum ya kamata ya je ya shigar da irin wannan korafi nasa na bukatar sha'awa, misali akwai, Heart-to-Heart Centre zaka je ka fadi damuwarka, zasu baka shawarwari masu inganci tare dabaka mafita akan matsalarka, lallai ya dan uwa irin wadan nan masu magunguna ba karya bane maganinsu yana aiki, amma kuma yana da illa, duk da cewa shima maganin na turawa yana da nasa illar, amma ta hanyar zuwa wajen likita shi ne za'a baka shawara, musamman irin abinda ya kamata mutum ya ringa ci da sha kafin ibadar aure.
Lallai bai kamata mazaje su yi shakkar likitocin al'auraba. Shakka babu wannan muhimmin abu ya kamata mu bashi kulawa ta musamman wajen kula tare da duba da kuma uwa uba kariya ta lafiya, da kuma, biyawa iyali bukatunsu cikin kwanciyar hankali, a tashi dan kallo lafiya mai wasa lafiya. Allah ya sa mu dace.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com